FARRAH HAUSA NOVELS COMPLETE BY M SHAKUR COMPLETE.doc

Author :  Maman Shakur Category :  Arewa Pen

Chapter   13 / 48

36K to 39K   out of 142.7K words

yay assuring nawa baisan komi kan mu da muka basu kwangilan ba, so kozai fadi wani abu idan yaji azaba saidai kansu bamuba, so for now asirin mu arufe, he s demanding abashi kudin aikin shi koya fasa kwai, sai magana tabiyu what s the way forward yanzu kowani security na gida da waje Yaya yayi doubling komi, tayaya zamu cimma burin mu jaka Hajiya Mariya tabude taciro wasu bandir bandir na 100 dollars ta ijiye guda biyar kan table tace  nidai ga payment dina, banda wata matsala data wuce Zayn, nasan kudi baya isan mutum aduniya mukaci nasara muka sami kudin Alhaji inaso, amman Zayn dai sainaga bayan yaron nan aduniya, duk sanda na ganshi nakanji wani abu ya tsayamin awuya na bakin tsanan shi uwa na lumamishi wuka aciki ya mutu nakeji, I think the easiest way dazan iya kashe yaron nan is da taimakon diya mace tunda shi Allah yayishi bunsuru ne wani dan murmushi Uncle yayi yace  aikam kinada aiki, Zayn abaiban mutum ne dazakiyi shekaru aru aru baki gane kanshi ba, miskilin mutum ne na karshe, haryau banga wacce Zayn yakeso aduniyan nan ba, kowace mace yasamu kawai kawad da sha awan shi yakeyi da ita yabarta anan, I believe ki chanza plan wani kalan murmushi Hajiya Mariya tayi sanan takalli Hajiya Fatima tace  kin tuna Layla Fatima ? Wani kalan makirin murmushi Hajiya Fatima tayi tace  natuna ta Uncle dabai gane me ake cewa ba yace  waye kuma Layla ? Murmushi sosai Hajiya Mariya tayi ta gyara zama tareda wani kalan juya kujeran datake kai tace  let s just say Layla is a girl I picked on from the street lokacin iyayenta na kangin talauci, infact irin buzayen nan ne dasuka zo from chadi, suna bara kan titi, long story short I sponsored education nata a England ta karanta Mass com, yanzu haka tadawo nasan tanama gida tana jirana, iyayenta sun mutu I am morethan iyaye awajenta, bantaba ganin yarinya mai kyau kaman ita ba, kowaye Zayn yayi kadan yay resisting yarinyar nan, I will use her to get to throat din Zayn tabe baki Uncle yayi yace  good luck with that yasa hannunshi ya tattaro kudaden da Hajiya Mariya ta daura akan table din yace  bani kudin ki Hajiya Fatima itama same amount da Hajiya Mariya ta ijiye ta ijiye Uncle ya tattara ya kwashe ajaka sanan yatashi yana rataye jakan yace  good luck Ladies, do your path while I do mine yawuce yafita daga dakin, juyowa Hajiya Fatima tayi tace  are you sure Layla zata iya aikin nan karyazo instead of tasamo miki throat na Zayn, Zayn ne zai sami throat nata you know what I mean just look at Zayn, yaron nan yahadu my god, ga kyau ga gayu ga body da mata keso ga shagwaba wani kalan murmushi Hajiya tayi tace  bakisan waye Layla ba saisa kike magana haka dariya suka dan yi, Hajiya Mariya tace  I want to see Mami tai kuka na bakin ciki kaman yanda ta kwacemin miji na, i want her to suffer tai experiencing pains danayi arayuwan nan ta dalilinta, kiri kiri yanzu idan Zayn na bukatan Alhaji zai hakura da Kwanan mu yaje wajen danshi, muyi kishi da Zayn muyi kishi da uwarshi, jiya adakina yake amman sabida wanan wayward son of his na tsoro ya kubuta yaje ya kwana dashi, I hate hate extremely hate that drug addict yaron nan nashi tabe baki Hajiya Fatima tayi tace  ni wlh da Allah yabani d a irin Zayn gwara ma na mutum nan haihu ba, babu kalan kwayan dabaya sha, tun kafin ya balaga Nany shi nakeji take gayama ubanshi takama shi da mace, yaro haka har abin sone  saisa nake addu a Allah ubangiji karya shiryashi yakare haka a wulakance ja irin yaro, tashi kiwuce kafin nima nafito yanzun nan kada aga duk mun dawo thesame time, ni tausayi ma amaryan shi Mariya kebani ta kwashe da dariya tace  tunda Zayn yadawo billahillazi Alhaji baimasan yanada wata Amarya ba tashi Fatima tayi tace  shag ya manta da ita, kinji Bari na wuce saikin shigo kema key motarta tadauka tana tabe baki tace  mu sauran matanshi mune bamu da bodyguard, Maman dan iskan danshi tanada shi hakama danshi dan dariya Hajiya tayi tace  karki damu komi yazo karshe wucewa Hajiya Fatima tayi tafice wata arniyan mota tashiga taja tabar gidan dasuke ciki wanda yake karamin sabon gida, almost one hoOur sanan itama HajJiya Mariya tafito tashiga tata motar tabar gidan.EPISODE 1?? 8??


Parking tayi abangarenta tafito, wata doguwan kyakkyawan budurwa ce tafito daga babban flat dinta, fara ce ita kal yarinyar tana sanye da jeans da riga babu dan kwali akanta tayi kitso da aka kara da attachment kalan blond daya sauko har waist nata, tana zuwa batai wata wata ba ta rungume Hajiya Mariya tace  oyoyooo Mommy rungumeta back hajiyan tayi tace  oyoyo my baby girl, my Lailarosh, how are you ? Murmushi tayi tabude baki zatai magana aka bude gate din gidan, kallo daya Hajiya tama motar Mami tadauke kai tacigaba da kallon Layla tace  how was your flight ? Murmushi tayi tace  fine daidai motan Mami yay parking kusada na Hajiya saukowa bodyguard yayi yazo dasauri yabude ma Mami kofa tafito Farrah ma na fitowa, daidai lokacin kuma motan Zayn ya dannokai cikin gidan shima, ganin Hajiya Mariya yasa Mami data kama hannun Farrah wacce daga Hajiya har Layla kallonta suke tace  Hajiya barka da rana murmushi Hajiya ta kakalo tace  Barkan mu dai Mami ya Zayn da jiki hope bai makance ba dan murmushi Mami tayi tace  Alhamdulillah komi yazo dasauki kallo Hajiya tabi Farrah dashi tace  wanan kuma fa daga ina tama Farrah wani kallon wulakanci, Farrah Mami takalla tana murmushi tace  itace Farrah, yarinyar data taimaki Zayn, she is going to stay damu for now, she don t speak hakanan jan Farrah Mami tayi ajikinta cikeda so tace  Farrah gaida Hajiya ahankali Farrah kanta akasa dan batasan mesaba batason kallon da Hajiya kemata tace  i& & i& .ina& & .yi& ni Zayn da fitowanshi daga motanshi kenan dan satan kallon Farrah yayi dayaji tai magana da kyar baisan mesa ba but har cikin zuciyanshi yaji muryan nata, dauke kai yayi batare daya kara kallonsu ba yawuce zaije side nashi kaman jira Hajiya Mariya take tace  Zayn ga friend namaka her name is Layla wani kalan juyowa yayi yakalli Hajiya yatsine fuska yayi irin nagayamiki I need friend ne sanan yajuya cikeda bacin rai zai wuce, da kakkausan murya Mami tace  Zayn chak ya tsaya sanan yajuyo ahankali sai alokacin yadan kalli Layla dake kallonshi kaman zata cinyeshi batare dayay magana ba, dasauri hajiya ta tabata tace  bazaki gaida yayanki ba murmushi Layla tayi cikeda siyasa tace  Hello Zayn adikile yace  Hey sanan yajuya yawuce, murmushi Hajiya tayi tace  itace diyar kanina daya rasu yabari shes 21 tagama school a england kallonta Mami tayi kana ganin Layla kasan tafi 21, kabata 25/26 dan zata iya zama mate din Zayn kawai Zayn yafita girman jiki ne, dan murmushi Mami tayi tace  bari nakai mara lafiya ciki takalli Layla cikeda wasa tace  sai kinzo tayani hira sanan takama Farrah dakebin gidan da kallo tawuce side dinsu.


Side dinsu suka shiga wanan karan Mami saida tai dariyan yanda Farrah ke kallon komi kamata tayi sukai sama tace  muje nakaiki dakin ki saiki wanka, za a kawomiki abinci, kika gama zanzo nabaki magani da allura, kome kikeso kifada min zan sa amiki, ki dauki gidan nan kaman gidanku sanan kidauke ni kaman mahaifiyar ki ki saki jikinki kinji sukai maganan daidai suna shiga wani lafiyayyen daki mai bala in kyau kan gado takai Farrah tace  nan ne dakin ki, ga bayi nan Mami ta nuna mata bayin, sanan tanuna mata wardrobe tace  kowani kalan kaya kikeso kisa yana nan, yau dasafe nasa aka sayo kaya aka sassaka miki aciki, bari naje nabaki wuri ko, kiyi sauri ki gama kisha magani Mami tai maganan tana juyawa zata fita, wani abu Farrah taji ya tsayamata awuya, ahankali tashiga bude bakinta dake wani kalan rawa yana shaking murya chan kasa sosai tace  Maaaami for the first time Mami taji muryan Farrah yadaki zuciyanta dawani kalan sauri Mami tajuyo, hawaye taga Farrah tasa hannu tashare daga kan fuskanta sanan ahankali tamike daga kan gadon, dawani kalan sauri tazo wajen Mami batai wata wata ba tawani fada jikin Mami sai kuka, sosai take kuka har saida Mami ta tsorata tace  Subhanallahi Farrah menene kike kuka haka kankameta Farrah tayi tana kuka sosai, fuskanta na jikinta ahankali tace  Mami naa& & .gode hawaye Mami taji sunzo mata idanu dasauri ta hadiye hawayen taciro Farrah daga jikinta, hararan fuskan Farrah tayi sanan tasa hannunta ta goge hawayen dasuka jika mata fuska, bawasa kan fuskanta tace  koda wasa kada ki kara cemin kin gode Farrah ni Maman kice, badan sabida ki taimaki Zayn nake all this ba, hakanan ko Allah yaga zuciyata kawai ina sonki Farrah, I look at you kaman baby girl dana dade nake kwadayi Allah yabani finally yakawomin ke, sOo yanzu imaza maza kiyi wanka Mami tai maganan tana kama hannunta zuwa bayJi, kunna mata ruwa tayi sanan tafice1?? 9??
Tsaf tayi wanka dan tanada karfin hali, tariga tasaba duk dukkan daza amata dole tai aiki, fitowa tayi daga bayin ta shirya, dadduman dataga an shimfida mata yana kallon gabas tahau ta tafara salla addu a tayi cikin salla kan Allah ya zaba mata abinda yami mata alkhairi arayuwanta.


Wuraren 4 na yamma Alhaji yashigo gidan, ana budemai mota ya sauko daga motan yana gyara zaman babban rigan dake jikinshi, direct side din Zayn yawuce bodyguards dake tsare gaban side din Dad yakalla tareda amsa gaisuwansu sanan yashiga flat din Zayn dake wani kalan lafiyayen kamshi ga sanyin AC tako ina daidai lokacin kuma Zayn dake sanye da bathrobe fari yadaure igiyan agaban rigan kafanshi sanye da bathroom slippers yafito daga kitchen dinshi da glass of milk a hannunshi yana kurba dasauri Alhaji yace  why are you getting milk dakanka bayan kanada masu maka ? Dan yatsine fuska yayi yana shigowa cikin falon, kan kujera yazauna tareda daura kafanshi daya kan dayan ahankali yace  I want to start doing everything myself from now, daga yanzu su daina shigomin cikin daki su tsaya nan bakin kofa dan murmushi Alhaji yayi yana kallonshi trying to read something yace  ohh that s new zama yayi kusada Zayn din yana kallon farin glasses din da akamai na hospital dayake sanye dashi shi, glass din yamai kyau ba kadan ba, baki yabude zaiyi magana Zayn yarigashi ahankali yace  Papa yay maganan yana ijiye glass na milk din kan coffee table sanan yadago, ahankali Alhaji daya tattaro duka natsuwanshi yace  Na am Zayn menene me kakeso ? Dan juyowa Zayn yayi yakalli Baban nashi kallon daya dade baimaiba murya chan kasa yace  Dad am I being immature ? Yanayin fuskanshi kadai Dad yagani yagane he s serious da tambayan baki yabude zaiyi magana cikin yanayi na baison yamai karya Zayn yace  don t you dare lie to me Dad kafada min gaskiya please, I don t have anybody, you are my best friend Dad, am I being immature ? Tsayawa Alhaji yayi yana kallon Zayn kalman best friend daya kirashi dashi wanda Zayn baitaba kiranshi dashiba yasa yaji kaman yay kuka, gently ya gyadama Zayn kai yace  yes! But just a little Son, I guess u just 26 still a kid that s why girgiza kai Zayn yayi tareda dan juya idanu irin na sangartattun yaran nan yace  no Dad, I think I am being incentive Dad, I am selfish and extremely rude dasauri Dad yace  noooo Zayn kada ka kara kiran kanka haka, Zayn you are one sweet Human da duk wanda zai zauna dakai saiya soka, you are just being yourself, chasing your likes abubuwan dakakeso, and you are one reserve person baka shiga rayuwan kowa, shiru shiru, you are just the way you are, and being the way one is doesn t mean he s rude or incentive or even selfish, you are Zayn, my only son, abin alfaharina, kyautan da Allah yamin yay maganan yana kama hannunshi mai lafiya trying to assure him abinda yafadamai gaskiya ne, shiru Zayn yayi yana kallon Babban shi na kusan 2min kaman yanda Baban nashi ke kallonshi, ahankali yace  Dad ahankali shima Alhaji yace  na am Zayn dina meke damunka haka nafara shiga damuwa wlh, menene talk to me, kome kakeso consider it done dan ijiyan zuciya Zayn yasauke sanan yakalli hannunshi dake nan adaure yana kallon igiyoyin dan kwallin Farrah data dauremai hannunshi dashi, yatsanshi yakai kan igiyan yana tabawa murya chan kasa kaman mai tunani yace  When those goons kidnapped me Dad I went through a whole lot, I lost all hopes, was thirsty, hungry, ga karaya ga idanuna ga lot of spiders Dad at that point everything was a thing for me, I looked up to the sky nace Allah ya taimaken, then that gurl came from nowhere kaman daga sama aka jefota yadanyi shiru yana kallon hannun nashi still in a very very low tone yace  Dad that girl protected me with all she got, at first I thought she was an angel, Dad kasan dan kwalinta tayaga ta dauremin hannun nan yay maganan ahankali yana shafa hannunshi saikuma yadan yatsine fuska ahankali yace  Dad kasan I couldn t thank her, whenever I looked at her sainaji she s too small nace mata thank you and I am not use to thanking anybody yadanyi maganan yana murmushi iya lebe kafin ahankali yace  Dad jikina is telling me I need to do morethan a thank you, she saved my life nima I should save her life and even give her a better life, education, da sauransu, Dad ina Uncle dinta kasa an daukoshi? Dad na kallonshi right in the eye ya gyadamai kai, ahankali yace  tun around 3 chopper su yasauka, suna biyeda ni maybe ma yanzu haka sun shigo gidan nan shiru Zayn yayi yana kallon mahaifinshi, lips dinshi ne yashiga rawa kaman yana fighting da abinda yakeso yafadi dan lumshe idanu yayi sanan yabude su yadaura su kan Dad ahankali yace  Dad can you adopt the girl please? ! Shi kanshi Alhaji saida yakara kallon Zayn maganan tazomai wani bagtatan bawai adopting yarinyar ne matsalan shiba ko kadan but this is the first time in history Zayn yacemai please kan wani abu mamaki ma hanashi magana yayi, ahankali Zayn yakai hannunshi yadaura kan na Alhaji yace  Dad lokacin da Mami tace the girl has been abused I felt so so guilty, bansan anything akanta ba but I know batada iyaye, and I know her uncle ran away they don t like the girl, she s like a burden, let s call our lawyer muyi adopting nata idan ma so suke mukara musu wani kudi zamu kara, Dad I want to sponsor her education with my money not your own just to repay her kaji Dad yakarashe maganan yana jijjiga hannun Alhaji, wani kalan sassanyar ajiyan zuciya Alhaji yasauke yana kallon fuskan Zayn din sanan yace  duk wanda cannot see beyond this your face da ake gani kaman u are rude is blind cus this your heart Alhaji yakai hannunshi kan kirjin Zayn yace  is made from gold dan murmushi Zayn yasaki, dan hararanshi Alhaji yayi yace  what are you waiting for, jeka saka kaya karakani nayi adopting yarinya ta Farrah dan murmushi Zayn yayi yatashi glass cup nashi yafara dauka ya shanye milk din ciki sanan yawuce sama bai wani dade ba wani dark blue hoodie yasaka da gajeren wando iya gwuiwa milk, ya sanya eye glasses dinshi sanan ya feffesa turare yafito kafafunshi sanye cikin wasu navy blue designers crocs simple kayan zZama gida but still ka kalleshi saika kara kalloOnshi suka fito daga side din Zayn din tare..2?? 0??
Side din Mami suka wuce, Mami na zaune a falo tana magana da Mama awaya suka shigo ganinsu tare yasa ta hararesu tacigaba da wayanta zama kusada Mami Alhaji yayi yana kallonta sabida tai kyau taci gayu sosai cikin kace kai kyau, katse wayan tayi takalleshi tace  ne kake kallona haka cikeda tsokana yace  wai ke baki tsufa ne jibeki saikace ba kene kika haifi wannan gansamemen saurayin ba yanuna Zayn, dan dariya Mami tayi tace  I take that as a compliment  ina Farrah ? Alhaji ya tambayeta anatse, murmushi tayi tace  tana sama nabarta cartoon take kallo a IPad dina, you need to see yanda maganan ta ke improving Alhaji, one thing I like about her is she is fearless tanada kwazo da jajircewa murmushi Alhaji yayi yace  kiramin ita tashi Mami tayi tai sama bata wani jimaba suka shiga saukowa tareda Farrah, tana sanye da doguwan riga na atampa brown dinkin yamata das das ajiki sai dan kwalinshi data daura aka kanta na kasa wani kunya taji tanaji ita Mami tafiso da Mami kawai tasaki jiki saukowa kasa sukayi Mami ta zaunar da ita kan kujera kusada ita kasa zama tayi tazame jikinta ta zauna akasa da sauri kanta na kasa tashiga wasa da yatsunta Dan dariyan manya Alhaji yayi yace  Farrah yaya jikin? Wajen dinkin yadaina zafi ? Gyadama Alhaji kai tayi ahankali cikin zazzakan muryanta tace  eh& ..Ab&

13 / 48