Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 27

18K to 21K   out of 78K words

da Umma, suna firarsu amma tabbas baka taɓa ganinsu tare da Ummi, Ummi harta saba da hakan, inda Allah ya taimake ta ma, tana da ƴar uwar da Halin ce ta bar mata, da ace babu waya a tare da ita, ƙuncin rashin wani a kusa da ita, da zama ita ɗaya tana yawan shiga tunani mai zurfi, wayar da Halin ta bata ba ƙaramar gudunmuwa ta bada wajan ɗebe mata kewar rashin wani a kusa da ita, wani lokacin ma daga Ummar har Halimar basa yawan zama a cikin gidan, tunda akasa ranar auren Halin, Ummi tasan ba ƙaramin biki za'ai ba, bikin gata za'ai mata, domin yadda ake ta uwar sayayyar nan tun a yanzu, duk da bikin da ɗan sauran lokaci, sai bayan sallah babba, yanzu kuma ana gaf shiga azumi ne.

Ganin ta ƙara faɗawa duniyar tunani yasa Halima faɗin.

"Kinga dama abinci nake so kimin mai daɗin gaske, saboda yau Sulaiman zai zo"

(Wadda zata aure ɗin shine Sulaiman).

A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana amsawa da to insha Allah.

Halin tabi da kallo harta fice daga ɗakin.

Ƙara sauke lumfashi tayi tana kallon cikin wayarta.

Wani kalar murmurshi ta saki na zallar farin cikin samun mutum kamar Usman ɗin.

Saboda ita ya taɓa zuwa har Rimaye a lokacin haɗuwa sukai wani wajan daban abunda taɓa yi ba, Baba Mlm lokacin baya nan sunje Fatawa wani Kauye, sai akai sa'a Umma ta aiki Ummin wani shago dake can bakin hanya, a wani waje suka haɗu, suka gaisa sai lokacin ya fara ganinta itama ta fara ganinsa. Ta tabbaye shi ko mi yasa bazai shigo gida ba kai tsaye?, sai ya ce mata, akwai abunda yake shiryawa ne su yake kawai azo neman aurenta dashi, yanzu kuma baya son zuwa gidansu da sunan zance sai komai ya zama dai-dai.

A ɗan ƙaramin tunaninta ta yarda dashi, har ita kanta tana bala'in mamakin yadda ta koma, kamar wacce ake kwanturorin ɗinta, bata taɓa fita ta haɗu da kowa ba, hasalima kowa ya ɗauka yadda take miskila bata magana ne, shi yasa da yawa mutane na mata kallon marar sun hayaniya, duk da ba wani fita take sosai ba, sai idan Umma tana da aike ne zata fita ta sayo ta dawo.

Sun rabu a ɗan ƙanƙanan lokaci saboda bata ma so wani ya gane ta aje a sanar da Baba Mlm cewa an ganta tsaye da wani mai Mota, shi yasa ma ta sanya liƙaf da zata fito ɗin, saboda ba inda ba'a sansu ba a cikin garin Rimaye, saboda Baba Mlm sananne ne a cikin garin, to hakama yaransa an sansu su duka da kamewa haɗe sa tarbiyya.

A hankali ta aje wayar dake hannunta ta fita tsakar gidan nasu, kitchen ta shiga ta fara kiciniyar ɗora abincin da Hali ta bata umarnin yi.

Abinci biyu tayi saboda Halin ta aje mata komai da take so, tayi fankasu da miyar agusi, sai tayi soyayyar shinkafa wacce taji kayan lambu sosai, saita soya Kaji tayi masu jar soya, haɗe ƴar miya ta jajjage saita juye Kajin data soya a cikin miyar, sai kuma Kunun ayar data yi, wadda yaji madarar iloka, dandanan ta gama gidan ya ɗauki ƙamshin girki, tasa komai a mahallin daya dace, taje babban parlon Umman wadda dama yawanci idan Sulaiman ɗin zai zo a nan suke zama, akan table na tsakiyar parlon ta aje komai.

Ta dawo kitchen ɗin ta ɗan zauna shinkafar data ɗan rage ta idasa cinyewa, sai ta fiddo duk kayan data ɓata ta shiga wankesu.

Tana gamawa ta koma ɗakinta, kamar jira shigowarta ake wayarta tayi ƙara.

Da ɗan sauri ta matsa inda ta aje wayar ta ɗakkota, ganin mai kiran yasata sakin murmurshi tana sake yalwata fuskarta da murmurshi wadda ya ƙara mata kyau sosai.

Ɗaukar kiran tayi tana samun waje ta zauna.

Fira mai cike da shauƙin soyayya suke fara, yana da yawan ban dariya, dan haka dole Ummi ta rinƙa darawa, wani abun yadan yayi mata harda dariya mai sauti take, idan ka kalleta a lokacin zaka shaida ba ƙaramin sone a tsakaninta da wannan bawan Allahn ba.

Kullum idan zasu yi sallama zai ce mata i love you, itama cike da tsananin sonshi zata mayar masa.

Koda Sulaiman ya iso taga dai Hali ta shigo ta sake ɗaukar wanka, tana wani irin ƙamshi ta fita zuwa babban parlon Umma.

Ganin haka yasa Ummi miƙewa taje har parlon kamar yadda duk sadda zai zo zata je su gaisa dashi, yauma da sallama ta shiga suka gaisa ta iske Halin na zuba masa lemo da ruwa a cofi.

Da zata tafi sai da ya tsaida ita ya bata kuɗi masu ɗan yawa, kamar yadda ya sabar masu, idan har zai zo gidan to sai ya ba Ummin wani abu, haka ma Baba Mlm ko Umma, ita Ummi idan ma ya bata Baba Mlm take bamawa, saboda Umma bata amsar kuɗin daya bata ɗin, hakama Hali wannan ba gabansu yake ba, shi yasa ta wani wajan Ummi ke bala'in sonsu, saboda basu taɓa cutar da ita ba, ka barsu dai da rashin harkarta da basa shiga ko abinda ya shafeta, komai zasuyi basa cutar da ita, basu taɓa hanata wani abu ba, ko Baba Mlm ɗin kanshi ya shaida hakan, Umma duk da bata son koda kallon Ummi ɗin ne, amma hakan baya hanata yima Ummi ɗin kyautar wani abu, ko sutura haka ko wasu abubuwan, shi yasa tun Ummi na shiga damuwar rashin kula ta da basa yi sai tayi ta zama ita ɗaya, a lokacin da bata da waya abun yafi damunta wani lokacin har kuka take ita ɗaya, amma shigowar waya a cikin rayuwarta ya taka mahimmiyar rawa wajan fidda ita cikin ƙuncin da take wayan zama ciki, sai dai ta wani wajan kuma ta jefata fara soyayya ada can baya bata san mi ce ce ma soyayyar ba kanta, amma sanadin waya ta fara sanin miye ma so, harta faɗa da yawa, har so ya sa mata wani mummunan tabo, bata taɓa tunanin idan taso mutum haka take shan wahala ba idan ya gujeta, bata iya son mutum kaɗan ba, wani so take masa mai wuyar fassarawa, so ne take da zuciya ɗaya, na gaske-gasken.

Zama tayi bayan ta dawo daga gaida Sulaiman ɗin, tana ganin lokacin da Umma ta fito daga ɗakinta zata je su gaisa da surukin nata, bata taɓa ganin murmurshi sosai akan fuskar Ummar ba sai yau, saboda wadda zai auri ɗiyarta yazo, sai Ummi taji inama ace ita ce da Ummar take ma murmurshi haka, harga Allah tana son Umma, son uwa take mata, tana so watan wata rana Ummar ta canza ta dawo kamar yadda take ma Hali itama ace tana mata.

Kwanciya ta ɗanyi tana jin jikinta na yin sanyi.

Wayar ta ɗauka ta buɗe data ta shiga WhastApp ɗin, ganin har yanzu saƙon data turawa ma Usman bai buɗe shi ba, mamaki ne ya kamata saboda tun safe ta tura masa message amma bai buɗe ba, sharewa kawai tayi tunda sunyi waya da safen.

Da daddare kamar yadda sukeyi Halima na fira da Sulaiman a waya, tana tabbayar ya, ya koma Kano?, da firar da suke taso ta soyayya.

Ummi kuma tana ta kallon sakwannin data sake tura ma Usman ɗin bai buɗe ba, amma sunyi good biyu, alamar yana online ɗin, duk da ba'a ganin yana online. Facebook ta shiga ta nan ta ganshi yana kai.

Mamaki ya sake rufeta, to mike faruwa dashi ne haka?.

Kasa daurewa tayi ta shiga numbers ta lalubo wayarsa ta shiga kiran numbersa, sai dai harya gama ringing ba'a ɗauka ba, ta sake kira na biyu shima ba'a ɗauka ba.

Abun ya so bata mamaki amma sai ta masa azuri tunda bai taɓa bata hakan ba.

Sai dai abun ya fara damunta ainun ganin har safe harta gama gyaran gida, Usman bai kira ta ba.

Tana zaune ɗaki ita ɗaya Hali da Umma na parlo suna kallo a tv.

Ita kaɗai a ɗaki rashin jin Usman ya fara matuƙar damunta fa.

Ta sake kiran wayar tashi again dai zata shiga amma ba'a ɗauka, kuma ba za'a biyo kiran ba.

Message data tura ta WhastApp har yanzu bai buɗa ba.

Abunfa tun tana ɗaukar da wasa har aka kwana biyu, a lokacin har kuka Ummi tayi a ɓoye zata shige toilet tayi kukanta mai isarta, saboda ba ƙaramin mugun sabo dashi Usman ɗin ya riga ya saka mata ba.

Harta fara tunanin ko shima dai gudunta zaiyi kamar dai tasiu, duk da soyayyar taso ba abunda ta tsinta sai zallar wahala.

Sai da akayi sati tukunna Ummi taga message ɗin Usman a WhastApp, baiwar Allah har jikinta na rawa wajan buɗe saƙon nasa.

Inda yake cewa.

"Kiyi hakuri kinji aiki ne yayi min yawa Please".

Abunda ya iya turo mata kenan.

Ko kaɗan bata ji daɗin saƙon ba, mi yake nufi ne wai?.

Ta sake masa uzuri ko aikin ne ƙila.

Sai dai fa abun sake gaba-gaba yake, saboda kwata-kwata dai wayar Ummi Usman yanzu baya ɗauka, kuma bazai taɓa ɗaukar waya ya kira ta ba koda yaga kiranta.

Abun ya so taɓa lafiyar Ummi ɗin, saboda wani irin kuka take fama dashi, tasha tashi cikin dare tana kuka Allah ya juyo mata da hankalin Usman akanta, tsabar damuwa idan tana kukan a ɓoye ma har wani irin tari ke sarƙeta kamar zata mutu.



Sai a kusan sati sana zata ga saƙonsa shima ɗan short amsa ce, ita kuma tsabar yadda zuciyarta ta riga da ta faɗa sonshi na haƙiƙa, bata ƙin buɗa saƙon nashi ta maida masa da amsa mai daɗi, tasha faɗa masa ko dai wani abu tayi masa ne?, sai ya ce shi babu abunda tayi, idan ma tayi masa wani abun ne ai zai faɗa mata.

A ƙarshe sai cewa yayi kin taɓa relationship ne da wani?.

Ummi bata ɓoye masa komai ba, ta faɗa masa ta taɓayi, amma tasha wahala a wancan relationship ɗin data yi.

Sai ya ce ta shima ya taɓa yi, kuma yasha wahala, yama fita shan wahalar, dama can dauriya kawai yake yi, har yake iya faɗawa wata soyayyar.

Wacce suka ɓata ɗin budurwarsa ta baya, yake sanar da ita, a lokacin wai ba laifinsa bane, kawai ta kira shi da rashin hakuri ta ce wallahi sai sun rabu, baza ta iya zama dashi ba, ya bata hakuri amma ta ce sai fa sun rabu.

Har ciwo ya kwanta a asibiti akanta, sai yanzu kuma ta sake dawo masa cikin rayuwarsa, wai dan Allah yayi hakuri wallahi wancan lokacin ɓacin raine yasa tayi masa hakan.

Shi kuma sai ya ce mata ai bazai taɓa dawowa gare ta ba.

Ummi najin abunda yake faɗa sai kawai ta samu kanta da ƙaryata zancen nasa, sai kawai ta samu zuciyarta da ƙin yarda da cewa bai yarda ya koma wajan tsohuwar budurwarsan ba, shi yasa kenan yake ƙin ɗaukar wayarta, saboda ya samu tsohuwar budurwarsa ta dawo masa?, shine zai gujeta ita kenan?, bayan ya gama da zuciyarta, ya gama lalata tunaninta da tsananin sonshi.

Kashe wayar tayi kawai ta fashe da wani irin kuka tana ɗuƙewa ƙasa kuka take mai ƙarfi tama manta da kar a jita.

Wani abu taji yana biyo mata ta hanci, kai hannunta tayi tana taɓo abunda taji yana bi mata hanci, dubanta ta kai akan hannun data taɓa hancin dashi sai taga jini ne ke biyo mata ta hanci, bata wani damu da jinin data gani ba, saboda dama tana yawan Haɓo dama wani lokacin, amma tunda Baba Mlm ya bata wani magani ta daina Haɓon kwata-kwata sai yanzu tsabar tashin hankali yasa Haɓon nata dawowa.

Hali ce ta shigo ɗakin da sauri ita kaɗai ce a tsakar gida, Umma dama ta fita, jin kukan Ummi yasa cike da mamaki ta shigo ɗakin.

Ganinta duƙe ƙasa tana wani uban kuka sai kace wacce aka sanarma da mutuwa.

Jin motsin mutum akanta yasa Ummi miƙewa da sauri tana saurin share hawayen dake zubo mata.

Girgiza kai Hali tayi cike da mamaki akan fuskarta ta ce.

"Ummi ƙalau kike kuwa?, wannan uban kukan na miye haka?".

Girgiza kanta Ummi tayi tana ƙoƙarin matsawa tana kuma so tayi magana kawai wani irin jiri ya ɗebe ta tafi zata faɗi da mugun sauri Hali ta tarbo ta a jikinta.

"Kai innalillahi, a haka kike faɗin ƙalau kike?".

Ummi na jikin Halimar ta sake rushewa da wani irin kuka, tana rirriƙe Hali da ƙarfi kamar zata ɓallata.

Da sauri Hali ta matsa suka zauna akan gado, sai da ta barta tayi mai isarta kamin ta kalleta ta ce.

"Wai kukan nan na miye ne wai?".

Ɗagowa Ummi tayi tasa hannunta ta ɗauke hawayen dake zubar mata kamar an boɗe fanfo, ta girgiza kai cikin muryar data gaji da kuka ta ce.

"Ba komai Hali, kawai na tuna da Umma ta ne".

Wani irin kallon rashin yardar abunda ta ce mata ɗin Hali ke jefa mata.

Zuwa can kuma kamar zatai magana sai ta fasa tana ɗan taɓe baki ta miƙe ta ce.

"Sai ki rinƙa mata addu'a idan kina cikin halin tunowa da ita ɗin, duk da nasan ba haka bane, amma Allah ya yayema kowa abunda ke damunsa".

Ta ƙare maganar tana ficewa daga ɗakin.

Tana fita Ummi ta sake sakin wani kuka marar sauti tasa hannunta tana toshe bakinta, zuciyarta take ji tana mata wani irin zafi haɗe da wani irin haushin kanta, mi ma yasa ta fara sakewa dashi har haka ne?, mi yasa tayi saurin manta abunda tasiu yayi mata ne?, mi yasa zuciyarta ke ruɗarta da faɗawa son masu wani ne?, mi yasa Usman bai sanar da ita tun tuni wannan maganar ba?, sai yanzu da ya riga da ya ɓata komai, mi yasa Maza da yawa basu da tausayi ne?, mi yasa Maza da yawa suke karya zuciyoyin Mata da dama ne?, mi yasa Maza suke wasa da hankalin ƴan mata da soyayyarsu ta ƙarya ne?, sai suje suna soyayya dake ashe ba kece suke son aure ba, ta auran tana gefe, keta soyayya ce kawai, ko kuma ta soshalewa, idan har baki da yawo kinje kin bada jikinki a wajan Saurayi ya gama lalata rayuwarki, ko kuma ya gama sanin jikinki kuna ƴan taɓe-taɓe idan kuka haɗu, yana miki daɗin bakin cewar yana sonki kice zai aura, ke kuma tsabar gidadanci ki yarda nan take, tsabar rashin hankali, kina ɓata lokacinki ne kawai domin bazai taɓa auran irinki ba, yana can ya aje ta kirki ita ce zai aura, kamin kiyi aune sai dai kiji an ɗaura masa aure da wata bake ba. Inda Allah ya taimaki Ummi bata taɓa bari ko ɗan yatsa wani ya taɓa, taɓa mata ba, kai ko a chatting bata taɓa tura masa wani abu wadda ba dai-dai ba, wadda da yawan ƴan mata ko ba'a taɓa haɗuwa da Saurayi ba, sai yayi maki daɗin baki ya ce ki turo masa tsiraicinki ata waya, ke kuma da yake ƙaramar kwakwalwa ce dake, ki ɗauka ki tura masa, idan abu ya kwaɓe ko dai ya tuna miki asiri, ko kuma ya gujeki domin bazai taɓa auran irinki ba kema kin sani, giyar soyayya ta ɗibe ki ta kaiki ta baro ki.



Sauke lumfashi Ummi take tana gode Allah da irin tarbiyyar da Baba Mlm ɗin yake basu, domin duk irin wannan nasihar bai jin nauyin ya zaunar dasu yayi masu, saboda yasan sharrin zamanin nan da muke ciki. Ke Uwa ko Uba kina can hankalinki kwance kina tunain ai kinba ɗiyarki tarbiyyar data dace, bari kawai ku barta ai kun bata tarbiyya.

Uhum da yawansu tabbas iyaye suna iya bakin ƙoƙarinsu, to amma fa sai ka dage wajan kula da yaranka, bare idan akace Allah ya baka Mata, ba ƙaramin aiki bane kula da tarbiyyar Ɗiya Mace wallahi, saika kula ka saka ido, kasan da waye da waye take ma'amula dasu, sana ka rinƙa zama da ita kana janta a jiki, haɗe da rinƙa nusar da ita abunda baida kyau, da illar samarin yanzu. Karki ji kunya ke Uwa ko Uba, wajan faɗa ma Ƴaƴanka gaskiya, gudun faɗawarsu halaka.

Ummi taja lumfashi tana sake kaunar Mahaifinta sosai, saboda ya taka mahimmiyar rawa a cikin rayuwarta, duk da ta taso babu Uwa, babu kuma wacce ta zame mata kamar Uwar, sai shi, shine ya koya mata komai ya kula da ita ya bata tarbiyya kamar dai wacce Uwa ke ba ƴaƴanta, shi yasa akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninta da Mahaifinta.........

*RAUNIN ZUCIYA*

*©Zahra Royal Star*

*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*

EPISODE 8

*Kauyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*

"An faɗa, ko gani kike bazan iya tuɓewa mu dakun bane?".

Innar su Asabe zatai magana Habiba ta miƙe cike da ƙarfin hali ta ce.

"Dan girman Allah Innar su Asabe kiyi hakuri ki tafi dan Allah".

Innar su Asabe ganin yadda Habiba ke kuka tana roƙonta yasata cizon yatsa cike da tausayinta ta juya ta fice daga gidan.

Tana fita kamar jira Inna take ta wani ci kwalar hijab ɗin Habiba tana kallonta, ta shiƙe mata wuya da hijab ɗin dake jikinta.

Wani irin tari Habiba ta farayi domin shaƙar taji ta har lumfashinta na shirin daukewa, tsabar yadda ta shaƙeta sosai.

"Wato zuwa kike ko ina

7 / 27