Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 27

36K to 39K   out of 78K words

ma kowa nashi, saboda suma Almajiran sai da asubar zasu zo su karɓa.

Koda suka kwanta bacci Ummi ta kasa baccin kirki tsabar zumuɗin ɗaukar azumi da za'ai gobe.

Baccin nata rabi da rabi ne, saboda a kunnanta aka fara kiran sallar farko ta asuba, ai ko ita ce wacce ta fara tada kowa a gidan.

Zaune suke bayan Baba Mlm ya fita ya kira Almajiran sun ɗauki abincin Sahur ɗinsu. Ita da Hali ne zaune a ɗakinsu, suna nasu Sahur ɗin.

"Ke Ummi anya yau kinyi wani baccin kirki kuwa?".

Faɗin Hali tana kai lomar abinci bakinta.

Murmurshi kaɗan Ummi ta saki ta ce.



"Hali wallahi ni kaina ban san irin ƙaunar da nake ma watan Ramadan ba, ina masa wani irin so ne, da har idan ya zo nake kasa iya yin bacci, har ya zo ya wuce, banƙi nifa ace wata biyu Ramadan yake mana ba".

Wata dariya Hali ta saki tana cewa.

"Sannu muguwa, tabɗi jam, ai ko wallahi wasu har ƙagara suke yazo ya wuce su kam, nikam kinga babu ruwa na ina ɗokin sallah idan aka zo goman ƙarshe, kinga goma ta wuya ɗin nan, da Malam Bahaushe ya riga da ya chaffata wallo da gaske wahalar ake sha fa, wannan dama goma ta marmari zamu shiga ai".

Itama Ummi dariya tayi ta ce.

"Ni wallahi abun dariya yake bani, wai goma ta marmari goma ta wuya goma ta ɗokin sallah, ni wallahi gaba ɗaya gomomin ina sonsu kuma basa ban wahala".

"Hhhh wai gomomi, sannu Ummi".

Cewar Hali tana sake kwashewa da dariya.

Cike da wani irin nishaɗi suke Sahur ɗin nasu, wadda tunda suka shirya da ƴar uwarta Hali take jin wata irin kaunar Ummi ɗin har cikin jininta, data aje komai ta ture duk wani abu a ranta, duk sai taji kamar ta aje wani gungumemen dutse ne a zuciyarta, ashe ma idan kasa baƙin cikin mutum a ranka, kaine zakai ta shan wahala, ko kuma kasa tsanar mutum a ranka, ko kana masa tsawa da hantara duk kaine abun zai rinƙa saka ciwon kai, amma idan ka cire komai a ranka sai kaji ka sayau. Tana fatan Umma ma ta sauke komai dake a cikin zuciyarta akan Ummi ɗin kota samu natsuwar zuciya kamar dai yadda ta samu.

Washe garin da suka tashi da Hali suka haɗu suka wanke kwanukan da aka ɓata da Asuba.

Wajan ƙarfe biyu haka Hali ce kwance akan gadonta, sai juyi take tana waya da kyar take iya magana tsabar yadda azumi ya fara bata wahala, ga wata irin rana da ake zubawa a garin harta innalillahi, danma gidan masu akwai iska ga inuwa, ɗakinsu ma akwai sanyi, shi yasa su da ɗan sauƙi, amma wasu gidajen zaki ga duk azumi idan gidansu nada zaure a nan suke zama, saboda ɗaki baya zaunuwa bare tsakar gida, dan wasu tsakar gidan ma babu rana ko kaɗan shi yasa dole sai zaure daka wuce zaka rinƙa hango mata, Maza kuwa ana waje a samu gindin bishiya ya kwanta.

Kashe wayar tayi tana sakin tsaki kaɗan, Ummi ta ɗago daga karanta Al'qur'anin da take yi bayan ta idar da sallar ƙarfe biyun.

"Hali ya dai, ko duk azumin ne?".

Ummin ta faɗa tana danne dariyarta, domin tun wajan ƙarfe goma Halin ta fara juyi-juyen da faɗin cikinta harya fara ƙugin yinwa, ko sallah ta kasa tashi tayi, wai Ummi ta fara sallar kamin ta gama ta tashi tayi, shine tana kwanciya bayan ta ɗauro alwala Sulaiman ya kira wayarta da kyar ta ɗauka take magana, maganar ma wahalarta take ji.

"Hmmm Ummi Allah ko bana son ko magana ni kaɗan nasan yadda nake yanzu fa, nifa gaskiya duk wata soyayya ko waya aje gefe har Watan nan ya wuce".

Murmurshi Ummi ta saki mai sauti ta ce.

"Lallai ma Hali, wai tun yanzu kike faɗan haka?, ƙirfe biyu fa Hali har yanzu da sauran lokacin shan ruwa saura kusan awa biyar fa"

Kwalkwal da ido kawai Hali tayi tana kallon agogon wayarta ta ce.



"Matsa min nayi sallah bacci ma zanzo nayi, kar ki tashe ni sai karfe huɗu, dan naga ke fa ko a jikinki har yanzu Azumin bai fara gwala ki ba, koda yake kefa Azumi baya baki wahala na sani".

Dariya kawai Ummin ta saki tana ɗan tashi ta bata waje, tana kallon yadda da kyar ta iya tsayawa sallar kamar ma juyawa take gani.

Tana idarwa ta zube akan sallayar tana sakin wani nishi tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa.

A hankali Ummi ta dafata ta ce.



"Sannu Hali".

Tana jin tausayinta, dama duk azumi yana bata wata irin wahalar gaske, wani lokacin ma ranga-ranga take kai azumin, amma tana shan ruwa zata wartsake, akwai sadda Baba Mlm ya taɓa cewa ko zata aje ne ta ɗan huta, daga baya ta rama, amma sai ta ce ina gara a haka a haka dai tayi, ramawar nan daga baya shima wani aikin ne, gara ace ramuwar da zatai wadda tasha ne dan dole idan jinin al'ada yazo mata, shima wallahi badan tana so bane dan ya zama dole ne.

Ɗagowa Hali ce tayi daga kwancen da take tana gyara kwanciyarta akan sallayar ta ce.

"Hmmm yawwa Ummi, kinji yadda nake jin wata juwa na ɗiba ta kuwa?, da kyarfa na idar da sallar nan Allah".

Ta ƙare maganar tana sakin nishi sai kace wacce ke naguɗa.

Itafa Ummi idan tana nishin nan dariya ke kamata, dannewa kawai take.

A nan bacci ya kwashe Halin, ita kuma Ummi ta fice domin rage uban aikin dake gabanta.

Yau Doya Umma ta bada Umarnin a soya da kwai da kuma Kosai, dan haka Doyar ta fara ferewa kusan guda biyar manya-manya.

Tana gama ferewa sai kawai ta fara jajjagen kayan miya da zatai ƴar miyar da za'a haɗa a ci Doyar da ita, abinci dama shinkafa ce zatai da miya itama, amma miyar ta markaɗe ce sai zuwa anjima idan Al'majire sun shigo zasu kai niƙan Kosai da zata soya shi na tiya biyu shima, saima yanzu ta tuno harda Kosai za'ayi dan haka Surfen waken ta soma yi shima, tana gamawa ta wanke sa shima tasa wani faranti mai girma ta baza waken yasha iska kamin zuwa yamma akai markaɗen.

Sai data gama rage aikin kamin ta koma ɗaki, lokacin har uku tayi, dan haka itama ɗan kwanciya tayi tana son hutawa kamin huɗu tayi.

Tana kwanciya bacci bai daɗe da ɗaukarta ba ta fara jin kiran Sallah, dan haka da kyar itama ta miƙe tana jin kanta na ɗan sarawa, saboda baccin dara fara kaɗan ta farka, shi yasa bata cika son baccin rana ba ciwon kai yake sakata.



Toilet ta shiga ta ɗauro alwala ta fito sai da ta idar da sallar kamin ta miƙa hannunta ta fara tayar da Hali tana baje a ƙasa, Tana jin matsin Umma a tsakar gidan.

Da kyar da kyar ta samu Hali ta miƙe tana faman dafe bango domin wani jirin take gani data miƙe, da kyar taje tayo alwala tana faɗin.

"Washh Ummi anya ba'a zaune zanyi sallar nan ba kuwa?".

Ummi ta aje charbin dake hannunta ta shafa addu'ar da takeyi ta ce.

"A'a ai kuwa a tsaye zaki daure kiyi ta, da ranki da lafiyarki, marassa lafiyar ma so suke suga sun zama kamar ke suyi sallar su a tsayen amma ba damar hakan".

Jikin Hali ne yayi sanyi ta miƙe da kyar, tabbas da gaske take ganin juwa idan ta miƙe tsaye, amma a haka ta ɗaure da kyar tayi sallar, tana idarwa ta sake kwanciya tana son ɗan hutawa kamin ta miƙe dan tana son taya Ummi aiki dake gabansu mai yawa, danma duk yawan aikin Ummi ce dama mai yinsa.

Sai wajan biyar saura suka miƙe suka nufi kitchen ɗin gidan, Umma na tsakar gidan tana yanka su Kankana da Ayaba.

Ummi ce ta gaida ita tana aikin bata kalleta ba ta amsa, taji daɗi tunda har ta amsa mata kuma yau taji muryar Ummar ba kamar sauran ranakun da ba, da kyar take amsa mata ba.

Hali ce ta matsa tana magana da Ummar tana fama shagwaɓar cewa dama bata azumi ita ce farkon cin KanKanar nan da Ayaba, idan tana kallonsu ji take kamar ta saka hannu ta ci, take ce mata Ummar ɗazo ta kusa shan ruwa ma ta manta kwata-kwata da azum ake, sai lokacin Umma tayi dariya tana ce mata ragguwa kawai.

Ummi na daga kitchen tana iya jiyo hirar ta su, sai taji inama tata uwar na raye suyi haka da ita, duk sadda zata ga Hali da Umma a haka tana jin wani irin miƙi na taso mata, ko taga wasu tare da Mahaifiyarsu suna raha duk sai taji wata irin kewar rashin tata mahaifiyar.

Harta fara ɗora Doyar akan wuta da ɗan dahu kaɗan kamin ta sauke ta fara soya ta da Kwai a cikin mai amma man kaɗan take sakawa a cikin Kaskon.

Hali ce ta zauna bayan ta shigo kitchen ɗin tana faman yima Ummin sannu ta ce.

"Yawwa dami zan kama miki aikin amma fa wadda zanyi ana daga zaune, wallahi saifa kinyi hakuri dani, idan ba bazan iya wani aiki a tsaye ba".

Ummi ta juyo tana dariya ta ce.

"Tabɗi anya Hali idan kikai aure waye zai miki duk wannan aikin to?".

Ɗan taɓe baki Hali tayi ta ce.

"Idan ba sai dai duk azumi ya rinƙa ɗakko min ƴar aiki, domin Allah bazan iya ba, nayi dai wadda naga zan iyan".

Shuru kawai Ummi tayi tana tunanin ai mai kuɗi ne zai iya ɗakko ko mai aiki nawa ce, amma ita dai kam bata jin zata iya barin ƴar aiki tayi mata girki, ace ba mai kuɗin mutum zai aura bafa ayi yaya?, girgiza kanta tayi ta ce.

"Ki dama min Kunu to ga ruwan zafi nan na ɗora yanzu zai tafasa".

Da to ta amsa ta ɗan miƙewa ta buɗe tukunyar da ruwan zafin yake, tayi Sa'a kuwa ya tafasan, dan haka ta ɗakko tsumma tasa ta kama tukunyar ta sauke daga saman Gas ɗin ta sheƙa ruwan zafin a wani Bokitin fenti da Ummi ta dama ruwan Kunun data haɗa komai dama ruwan zafin kawai zata sheƙa Kunun ya damu.

Wani lildai ta ɗakko mai tsawo ta juya Kunun da yayi kauri ya haɗe jikinsa, yayi kyau yayi haske sosai ƙamshin Tsafiya sai tashi yake a cikinsa.

"Kinga Kunun yayi kyau kamar nasha".

Murmurshi Ummi tayi ta ce.

"Dama wasu idan suna azumi da sunga abinci sai su rinƙa ji kamar su ci, amma kinga ni abinci baya birge ni har sai idan ruwa aka sha tukunna".

"Tabɗi ai ke daban ce Ummi".

Ita dai Ummi dariya kawai tayi tana girgiza kanta kawai.

Sai da ta gama soya Doyar kamin azo akai Markaɗen Kosai dana miya. Ba'a daɗe ba aka kawo, saida za'a Soya Kosan tukunna Hali ta sake kama mata suka soya a tare. Sun debarma kowa nashi har Almajiran Baba Mlm, sai ta ɗora miyar shankafa kamin bayan ansha ruwa ta ɗora shankafar saboda kusan ta Sahur ce ita dama.

Zaune suke an jera kayan shan ruwa masu yawan gaske, a parlon Umma kusan dama duk shekara tare ake haɗuwa asha ruwa a tare, Baba Mlm ɗin ya roƙi Umma data rinƙa fitowa ayi shan ruwan da ita a parlon, da kyar ta amince da hakan, saboda da bata taɓa fitowa tasha ruwa dasu a ɗaki take shan nata ruwan, daga shi da sai ƴaƴanshi suke buɗa baki a parlon, amma wannan lokacin ta amince ne zata fito dan ya roƙeta da kansa.

Ummi ta kalli yadda Hali keta kallon ruwan data haɗa a kofi mai sanyi, so kawai take taji an kira sallah kota kai ruwan a bakinta ta ce.

"Hali yaya dai".

Tana danne dariyarta.



Hali ta wani shagwaɓe fuskanta ta ce.

"Wai liman ɗin nan bazai je ya kira mana sallah ba haba dan Allah, so yake har sai mun bushe tukunna"

Ummi zatai magana aka kira sallah, tana jin yadda Hali ta wani saki Alhmdllhi, tana ɗaukar kofin ruwanta har hannunta na rawa wajen kaiwa baki.

Ummi ta saki murmurshi tana ɗaukar dabino da Baba Mlm ya shigo ya basu kamin ya fita zuwa masallaci dan a can waje zai sha ruwa ya wuce masallaci kamin ya shigo shan ruwa gida, yanzu su biyu ne zaune sai Umma da kiran sallar yasa ta fito parlon yanzu.

Ummi da kanta aje mata komai tana mata barka da shan ruwa.

Cike da ƴar sakewa ta amsa, hakan ba karamin faranta ran Ummi ɗin yake ba, Ummi taga tunda aka shigowa watan Ramadan ɗin Ummar ta ɗan fara sake mata kaɗan.

Suna shan ruwa suka miƙe kowa yaje domin yin sallah, sai da akai har isha'i kamin Baba Mlm ɗin ya shigo suka haɗu a parlo aka fara shan ruwa su Ummi na masa barka da shan ruwa, Almajiran Baba Mlm ma tun ɗazo suka shigo suka ɗauki kayan shan ruwan su.



__________________

*Ƙauyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*

"Ke wai wacce irin banza ce ne, ace har an kusa shan ruwa baki gama yi mana kayan shan ruwa ba?"

Habiba kanta a ƙasa tana kallon Bilki dake tsaye a kanta, yau tunda aka ɗauki azumin daga ita har Inna take shan faɗa da zagin daya fi na kullum a wajansu, koda yake kamar yinwa ce kesa su yawan faɗan, tunda aka wayi gari an ɗauki azumi rana ta take sosai, abu kaɗan Inna saita ɗura mata ashar.

Habiba zatai magana Inna ta faɗo wajan tana faɗin.

"Wai har yanzu abincin da ba wani bane kin wani tsaya iyayen tsiya da feleƙe ace har zuwa yanzu baki gama ba, ke ga muguwa so kike mu kai azumin bamu ci komai ba?"

Ita dai Habiba hakuri ta basu, saboda tun safe take aikatuwa, ita ce surfa waken da za'ai ma su Inna Kosai harda awara da Kokon da za'a dama masu duk ita tayi har surfen geron da za'a dama masu Kokon, sai tuwan Sahur da kusan shine ƙarshe.

Ta gama soya awara ta dama Koko Kosai ne kawai take soyawa yanzu sai ruwan miyar tuwo data ɗora shi Yanzu, shine suka shigo suna mata bala'in bata gama ba har yanzu, basu ga irin uban aikin data sha ba a yau ɗin, ba godi bare na gode, Habiba tama saba da hakan, sai dai itama ba ƙaramar wahala tasha ba bare Azumin farko, amma da yake ta riga da ta saba da wahalar gidan da kuma zama da yinwa shi yasa kwata-kwata yau da aka ɗauki azumin bata wani sha wahala har kawo yanzu ɗin gara ma idan ta miƙe tsaye tana ɗan ganin jiri, saboda surfen Masara da na Gero data yi da yamma shi ya sake wahalar da ita sosai.

Kiran sallar da akai ne yasa Bilki sakin hamma tana furta.

"Wai Allah na, ƴar baƙin ciki to ai har gashi an kira sallah baki gama mana abunda zamuyi buɗa bakin dashi ba".

Inna data juya ta ɗebo ruwan randa ta kai baƙinta Habiba na kallonta bata jin ta tsaya wata addu'a bare Bismillah ruwan kawai takai bakinta, Bilki ma kofi ta ɗauka ta fara shan ruwan har yana zubar mata a jiki.

Habiba tasan bata isa ta miƙe ta ce zata sha ruwa ba, har sai ta gama uban aikin nan gashi itama tana baƙatar shan ruwan.

Da hanzari take komai domin itama jikinta yayi liƙis sosai.

Tana kallo suna ɗeba suna ci har Kosan da take soyawa sai da suka kusan cinye rabinsa kamin ta gama ta jera masu a gabansu, sai lokacin ta samu ta sha ruwan itama.

Tana komawa gefensu tana kallon yadda suke shan ruwa suna cin abincin data gama ta basu, amma har lokacin basu ce mata gashi ba ta ci itama.

Sai haɗiyar miyau take.

Harta gama tukun tuwo da miyar Kuka data yi, sadda zata kwashe tuwon har sun gama cinye awarar nan da Kosai data soya, basu bar mata ko tsinke ba, Habiba ta haɗe miyau tana jin wani irin abu na tokare mata maƙoshi, tabbas ta saka rai ko kaɗan ne su bata.

"Ke dalla can mayiya kin wani tsare mu da kallo lafiya?"

Faɗin Inna tana kallon Habiba dake ta kallonsu har suka gama ci.

Ƙasa tayi da kanta ta ce.

"A'a Inna ba komai dama yinwa nake ji".

"To yinwa kike ji baga tuwo nan ba ki zuba mana ki ci, ko nufinki dama abincin nan da muka gama ci zamu baki dama?"

Da sauri Habiba ta girgiza kai, tana miƙewa ta zubo tuwon data yi mai ɗan yawa ta koma gefe ta fara cusa shi a cikinta, danma sauƙin ita tayi shi ba laifi kuma yayi daɗi, ita dai indai zata ci ta ƙoshi Alhmdllhi, taci kuma ta ƙoshi sosai ta sha ruwa, ɗan haka tayi hamdala tana jin Bilki na cewa.

"Itafa da nufinta mu tsaya mu bata namu taci".

"Ai ko tana da aiki wallahi, ai har

13 / 27