Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
azumin nan ya ƙare shegiyar sai dai ta rinƙa cin tuwo".
Habiba duk tana jinsu, bata wani ji wani abuba, tunda dai har zata iya cin tuwon kuma ta rayu ai da sauƙi sai kawai ta cire rai da cin wani abu mai daɗi da a cikin azumin.
Suna zaune tsakar gidan Yaro yayi sallama wai ana sallama da Habiba inji Abba.
Habiba ji tayi zuciyarta na zafi, shi wai wane irin maye ne wai?, jiya fa sai da tayi masa rashin mutumci haka kuma baya gajiya da kwaɗa mata mari idan tayi masa rashin kunya, haka kuma bazai gaji da zuwa gobe ba.
Tana ji har Yaron ya tafi bata da niyar miƙewa domin zuwa kiran nasa, dan haka Inna ta rarumo wani kwano da suka gama cin abinci dashi zata kwaɗa mata shi Habibar ta gani tayi saurin miƙewa tana jin wasu hawaye na taruwa a cikin idonta.
"Kaga shegiyar yarinya ana magana kin wani maida mutane shashashu sa'anninki".
Ita dai Habiba ƙofar gidan ta fita tana aiyana irin ɗibar albarkar da zatai masa a yau ɗin.
Sai dai tana fitowa ta ci ƙaro da Asabe a ƙofar gidan. Kalle-kalle ta fara yi tana son gano inda Abban yake, sai taga Asabe ta kamo hannunta tana damƙa mata wani abu a bakar leda, Habiba ta kasa haƙuri ta ce.
"Wai dama ba Abba ke kira na ba, ke ce wacce kika ce na zo?"
Sauke lumfashi Asabe tayi ta ce.
"Kware ni ce na ce ma Yaron ya ce Abba ne ya kiran ki, domin nasan idan na shiga gidan ko na ce inji Asabe ke kiran naki baza su taɓa bari ki fito ba, kuma abun zai zame miki matsala, shine yasa kawai na kawo shawarar bari na ce Abba ne ke sallama dake. Kinga Inna ce ta ce na kawo miki kayan buɗa baki gashi nan , saboda tasan ba lallai su baki abincin buɗa baki mai ɗan maiƙo ba".
Buɗa ledar Habiba tayi ganin Doya ce data ji Kawai harda Kosai a ciki, mai yawa dan haka bata san lokacin data ji hawaye sun zubo mata ba ta ce.
"Wallahi ban san miye zan ce miki ba Asabe, haƙiƙa keda Inna kune mutum ma farko dake sona a cikin garin nan, nagode dan Allah ki ce ma Inna na gode sosai".
Ta ƙare maganar bakinta na rawa.
Da sauri Asabe ta saka hannunta tana share mata hawaye, kamin ta zaunar da ita ta ce ta zauna a gabanta ta cinye yanzu nan.
Zaman tayi kuwa ta cinye tas tana sake gode ma Asabe da Inna, inda Asabe ta ce karta damu har Azumi ya ƙare zata rinƙa kawo mata abincin buɗa baki insha Allah........
14
*House No: 11, Ahmadu Belloh Sardauna Estate, Katsina State Nigeria*
A hankali ta miƙe jin jikinta yayi mata nauyi wata irin kasala ta kwana da ita, yau kusan sati biyu kenan da kawota cikin gidan Uncle Mubarak ɗinta, amma har zuwa yanzu bata san miye matsayinta a garesa ba, wani irin kwarjini yake mata duk sonta da mitar kasancewa tare dashi abun na son yafi ƙarfinta.
Wani irin yanayi yake saka ta a ciki, zai zo mata wani irin mutum daban saiya gama jagwalgwalata kamin komai nasa ya dawo dai-dai, baya taɓa kusantar ta har kawo yanzu bata jin akwai abunda ya shiga tsakaninsu bayan rikita mata jiki da yake da salonsa mai rikitar da kwanya.
Harga Allah ta gaji da irin abunda ke faruwa da ita akansa, wani lokacin zai tafi ya barta da wata muguwar sha'awarsa ne, sai da kanta zata zauna ta idasa biya ma kanta buƙata, saboda ta riga da tayi wani irin sabo da abun, bata da hakuri ko kaɗan akansa, shi yasa watan azumin nan da aka shigo yanzu kwata-kwata ma baida time ɗin yi mata kamar yadda yake mata a da can baya.
Duk shima taga abun ya dame sa, bai taɓa kawowa ashe bai da cikakkiyar lafiya ba sai da yayi auran komai ya fito fili, baya taɓa jin wata sha'awar Mace, yayi iya baƙin ƙoƙarinsa wajan bata haƙƙinta amma abun ya gagara, dan haka rana ta biyu yaje ya dara ganin Doctor, inda suka fara bincike suka kuma ɗorasa akan magani.
Sauke lumfashi tayi tana duban window ganin rana tayi sosai yasa ta miƙe tana duba wayarta kusan ƙarfe sha ɗaya na rana. Wanka ta shiga sai data fito kamin ta shinfiɗa sallaya ta data sallah wacce sai yanzu take samu tayi ta asuba ƙarfe sha ɗaya (Allah ya shirya)
Tana idarwa ta ɗakko wayarta tana ɗan jujjuyata a hannunta, tabbas dole Mama ta sani dole asan yadda za'ai bazata iya hakurin zama a haka ba gaskiya akwai matsala.
Tana kiran Mamar bugu ɗaya biyu ta ɗauka.
"Mama, there is something you don't know about Uncle Mubarak's life". Mama ashe duk tsawon lokacin nan ko na ce shekarun nan ashe Uncle Mubarak baida cikakkiyar lafiyar kasancewa da Mace".
Mama muryarta cike da zallar mamaki ta ce.
"Ban gane mi kike ƙoƙarin faɗa min bafa Hamda?".
"Mama abunda kika ji daga farko dai shine gaskiya, I know you know what I mean. Haba ni dai Mama ace mutum tsawon shekaru bai taɓa kawo yin aure ba a rayuwarsa bai taɓa sha'awarsa ba, ni dama na ɗora ayar tabbaya akansa wallahi"
"Nima na fara tunanin haka fa, amma da naga kusan sati baki kira ni ba na ɗauka komai ƙalau ne ai, to gaskiya duk da haka Hamda bance ki koma gidan jiya ba, karki sake ki kice zaki rinƙa yawon banza dan kawai mijinki baida cikakkiyar lafiyar ɗebe miki ƙishirwarki, karki dawo mana da aiki baya na magungunan da na samu na baki"
Wani lumfashi kaɗan Hamda ta saki tana ayyanawa a ranta aiki tun nawa kuma data ɓata tunda duk sadda zai zo ya tayar mata da fitina zai barta ne zata biya ma kanta buƙata, komai ai ya lalace, kawai dai lokacin data fahimci ya samu lafiya bazata bari ya kusance ta a ranar ba, zata je tayi shiri na daban domin bata so ya gane wani abu dake tare da ita.
Mama ce ta katse tunaninta tana faɗin.
"Kina jina kuwa sai magana nake kinyi shuru?, kinga watan azumi ma muke dan Allah Hamda ki kiyaye".
Hamda kamar tana gabanta ta ɗaga mata kai kawai, kamar Mama tasan abunda Hamda ɗin tayi sai Mamar ta sake cewa.
"Yawwa Hamda, amma abunda nake son ji shin ya fara neman magani ko kuwa, ni na fara nemar masa, na nufe sa da maganar".
Da wani irin sauri Hamda tayi saurin girgiza kanta tana cewa.
"Noo noo noo Mama karki ma bari yasan kin san abunda ke damunsa, honestly, I don't know what eye to look at, tunda kinga sirrinsa ne bai kamata ma ace kina surukarsa ace kin sani ba, even though I know he is your son, but the matter is here between us, nasan tabbas dole ya nemi Doctors ina da tabbacin hakan".
"To ai shikenan tunda kince hakan, zamu zuba ido ne muga har zuwa wane lokaci ne zai samu lafiya, yanzu ma yana ina ne?".
"Mama ai kin san tunda aka shiga Goman ƙarshen nan baya taɓa kwana a gida, he is in the mosque until the day of prayer and he will return".
"Hakane hakane fa na manta to Allah yasa mu dace".
Da amin kawai Hamda ɗin ta faɗa tana sauke wayar ta kashe tana tashi ta fice daga bedroom ɗin.
*Unguwar Yammawa Rimaye, Kankia local government Katsina State Nigeria*
A ɗan ruɗe ta tashi daga baccin daya ɗauke ta, har yanzu idonta na sake hasko mata Mubarak da yau zuwansa garin kwana biyu kenan kamin a shigo goman ƙarshe, har gashi anyi na biyu a gamon karshe ɗin. Ya zo ne domin sauke nauyin daya rataya a wuyansa na Ummi ɗin, ya taho mata da kayan sallah masu ɗunbin yawan gaske haɗe da kayan lefenta kusan akwati goma sha, abun har ya so bata tsoro, kai hatta Umma abun da mamaki take sake kallon uban kayan da duk yanzu na Ummi ɗin ne, Hali a ranar tayi tsallan murna kamar zata maida Ummi ɗin ciki, duk rabin kayan sallar daya kawo sai data raba su rabi taba Umma da Hali, duk da suma ya kawo ma kowanne dake cikin gidan, hakama Baba Mlm ɗin shima da nasa kayan sallar kai hatta Almajiran Baba Mlm ba'a barsu a baya ba sai da yaba kowannen su kuɗi kusan dubu goma-goma, ya ce kowa yaje yayi ɗinkin sallah, bayin Allah a ranar wasu harda kuka tsabar jin daɗi, ranar yasha addu'a kamar mi a wajan Baba Mlm ɗin da Ɗalibansa, yasa jama'a farin ciki dama shine burinsa, dan haka ranar fuskarta cike take da wani irin annuri sosai.
Shi yasa koda aka kaisa parlo Ummi zata fito su gaisa, saboda sai a ranar ko wannansu zai fara ganin ɗan uwansa.
Ummi tunda ta doso parlon wani irin mayen ƙamshinsa yayi ma hancinta dirar mikiya, wadda lokaci ɗaya ya sakar mata wata irin kasala mai kashe jiki.
Dan hakama jikinta a mugun sanyaye ta idasa shiga parlon, kanta a ƙasa jikinta ne ya soma rawa jin wata murya bayan tayi sallama ta amsa mata sallamar tata, har bata san lokacin data wani irin ɗago da kanta tana zuba masa idanuwanta ba.
Wani irin jiri ne ta fara gani tunda idonta yayi tozali da Mubarak, zata iya cewa tunda take a duniya bata taɓa ganin mutum mai cikakkiyar natsuwa haɗe da wata irin haiba da wani irin kwarjini a jikinsa ba kamar wannan mutum ɗin da take gani a gabanta, hasken fatarsa har wani ɗaukar ido take, tayi wani irin fresh da ita, ga wani irin gemunsa daya haɗe da Sajensa wadda ya sake ƙawata kyakkyawar fuskarsa, gashin gemun nasa har wani kyalli yake tsabar yadda ake kula dashi, idonsa kuwa nan ƙarshen kwarjinin yake. Tunda shima ya zuba mata idonsa bai ɗauke ba, hakan ya sake bada gudunmawa wajan rikita Ummi jikinta ya sake ɗaukar rawa dan neman zubewa ma take a wajan ga zuciyarta data dameta da bugawa a ƙirjinta da ƙarfi.
Ƙafafuwanta ne suka soma yin rawa tana neman zubewa ƙasa, lura da hakan yasa Mubarak ɗan sakin murmurshi kaɗan yana ɗauke idonsa daga kallonta, tabbas yasan shima indai zai zuba ma mutum idanuwansa to tabbas mutum ruɗewa yake ya rasa natsuwarsa, wannan baiwa ce da Allah yayi masa tun yana yaronsa.
Murmurshin daya saki ne ya ƙara kashe zuciyar Ummi ɗin tana tasbihi ga Ubangiji. Da ɗan hanzarinsa Mubarak ya miƙe cike da takunsa na ƙasaita ta tako har inda take saboda da dai da gaske yaga neman faɗuwa ƙasa take.
Tarbota yayi a jikinsa wadda ya idasa Ummi zarewa gaba ɗaya jikinta ya sake ɗaukar rawa jinta a jikinsa ga uban ƙamshin nan nasa da ƙara hautsina ƙwaƙwalwar kanta, ga wani mugun taushi data ji a jikin nasa, su duka sai da suka ji wani iri da jikinsu ya haɗu yadda kasan sun taɓa wayar wutar nepa, hatta shi kansa da kyar ya dai-daita natsuwarsa yana sake matseta a jikinsa, wai a tunaninsa ta samu natsuwa a cikin jikinsa, bai san hakan da yayi mata ba ya kusa haukatata gaba ɗaya, ƙaramar kwakwalwarta bata saba da irin wannan karatun ba, duk da baida cikakkiyar lafiya amma akan Ummi ɗin sai da yaji wani irin abu ya motsa masa tun daga ƙwaƙwalwar kansa har izuwa tafin ƙafarsa, duk da yasan dama Doctor ya ce indai yana yawan shan maganinsa akan lokaci baya mantawa, to kowanne lokaci zai iya dawowa dai-dai, dama matsalar ba wata mai yawa bace, domin matsalar bata wani jima a jikin nasa sosai ba, saboda shi ya sani tun can da baya yana da wata irin muguwar sha'awa, shi yasa yake yawan azumi sosai dan gudun gujema aikata zina, Allah ya karesa sai dai tun sadda ya daina jin abubuwan da abu kaɗan zaiji sha'awarsa ta motsa sai kwata-kwata ma ya daina jin sha'awar ko wacce Mace, shi yasa ya ƙara shantakewa baiyi aure ba har kawo lokacin, bai san da ciwon a jikinsa ba har sai da yayi auran nan, lokacin yasan tabbas baida cikakkiyar lafiya, shi yasa baiyi ƙasa a gwaiwa ba ya tafi ganin Doctor saboda yasan yanzu akwai wa'inda suke da haƙƙin hakan a tare dashi wato Matansa dole ya nemi lafiya cikin gaggawa domin gujewa fushin Ubangiji akansa.
Ganin yadda ya sake wani riƙeta sosai a jikinsa yasa Ummi ƙarfin halin tattaro sauran ɗan ƙarfin daya rage mata ta fara ƙoƙarin ture sa daga jikinta.
Sai lokacin ya dawo daga duniyar tunanin daya wulla yana sake kafeta da ido ya ɗan sake ta kaɗan yaja baya.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana lalaubar ƙasa ta zauna har lokacin jikinta rawa yake, ƙamshinsa ya gama kama mata jiki yadda kasan ita ce ta sanya turaren yadda take jin ƙamshin nasa a jikinta sosai.
A hankali muryarta na rawa ta gaida sa cike da sanyin jiki.
Komawa yayi ya zauna shima ya sake dubanta ya amsa gaisuwar tata. Ba wani sabo a tsakaninsu dan haka daga gaisuwar data masa sai godiyar uban kayan daya kawo mata haɗe sa masa addu'a sosai yana amsawa da amin, tabbas yaji daɗin addu'ar sosai ba kaɗan ba, domin har murmurshi yake saki, yana sake jin wani irin abu na masa yawo akan Ummi ɗin ganinsa na farko da ita.
Ummi dake zaune ƙasa ko mata taɓa tunanin zata gansa a haka ba, yo wannan yama za'ai ace wai abokin Baba Mlm ne?, kodai sun sha'afa ne ƙila ɗalibinsa ne kawai?, ai ita dai iya kallonta dashi bata ga wasu alamar shekaru sun nuna ba a jikinsa, tsayayyen namiji ne kuma ƙaƙƙarfan gaske ne, ga wani irin kyan halittar jiki dana fuska da Allah ya zuba masa kamar shine yayi kansa.
Agogon hannunsa ya kalla ganin har karfe huɗu da wani abu baya son dare yayi masu akan hanya ko susha ruwa akan hanya dan haka ya miƙe a hankali yana kallon agogon hannun nasa.
Saukar Muryarsa taji wadda tasa itama miƙewa again bata harda ta sake haɗa ido dashi ba koda gigin wasa domin kanta a ƙasa yake sosai.
"Well, I'm going to pass, what's my wife going to give me?".
Wayyo Allah ji Ummi tayi kamar ta ruga da gudu ta ganta ɗaki ita ɗaya, domin wata irin murya yayi anfani da ita, dan ji tayi yana sane yayi hakan shi kam bata san iya gaskiyarshi ya faɗa mata ba, bai ma san yayi ma muryar tasa hakan ba da take ji wai yana sane yayi mata haka ba.
Ummi tama rasa miye zata ce masa ita, sai wasa take da ƴan yatsun hannunta tana so ta furta, ita miye zata basa, amma ta kasa faɗar hakan sai wani mis-mis take da baki.
Bata ankara ba taji shi gaf da ita domin a jikinta taji shine ya matso inda take, saboda wannan mayen ƙamshinsa turaren nasa data jisa ya sake rufe mata ƙofofin hanci.
Bata taɓa kawo hakan ba kawai taji yasa saka hannunsa ya kamo ƙugunta da gaba ɗaya hannunsa, so yake ta ɗago ta kallesa, Ummi ji tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige kota huta, jikinta da zuciyarta na narkewa akansa da samun kusancin da suka samu.
Wani irin mayen abu take ji yana tsarga mata tun daga kanta har izuwa tafin ƙafarta.
Da ƙarfi ta rufe idonta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa a ƙirjinta.
Yana iya jin yadda jikinta ke rawa sosai.
Dan haka ya saki wani irin murmurshi kaɗan ya ɗakko hannunsa yasa shi akan fuskarta kaɗan ya ɗago da fuskar tata kawai taji ya sakar mata kiss a goshinta, yana yin haka ya sake ta ya matsa baya kaɗan, saboda ba abunda yayi niyar yi ba kenan, dan kawai ana azumi ne baya son ɓata mata azumi, tunda shi dai ba wani abu yake ji ba, garama akanta ya ɗan fara jin canji sosai akanta.
Yana sakinta Ummi tasa hannunta ta dafe ƙirjinta tana sake yin ƙasa da kanta ta sake jin maganarsa ya ce.
"You have nothing to do for me that I will go and I am happy to have a woman like you, zan tafi da tunaninki har zuwa lokacin da zan dawo?"
Innalillahi kawai Ummi ke faɗa wai dama haka Mubarak ɗin yake ne dama?. So kawai yake ya kasheta da kalmomin nan nasa, ita wai mima yake so ta ce ne?.
Ƙarfin hali ta aro dole ta yafama kanta domin tana iya jin yadda kaifin idanuwansa ke yawo a jikinta, domin kafeta yayi da kallo kawai yana son jin abunda zata ce, so yake duk Matan nasa ace sun sake dashi, dole ne ma ya cire mata kunyar nan tata, duk da kunyar nan da take nunawa ba ƙarimin birgesa hakan yayi ba.
Samun kanta tayi da wata irin shagwaɓe murya tana cewa.
"To ni Yaya, ban san abunda zanyi maka ba ai".
Sake matsowa yayi sosai kusa da ita, saura kaɗan Ummi ta faɗi wajan taja baya, bai taɓa ta ba hannunsa kawai yasa ya ɗago da fuskarta tana kallonsa ba dan ta so ba, dan har wasu hawaye taji na neman zubo mata, saboda kwarjinin idonsa akanta da wani irin kaifin masifa da suke dashi.
"Look at me, I don't want any Yaya from now on, choose a name for me if you want me to go now, idan ko