Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 27

54K to 57K   out of 78K words

faɗa da wata irin murya har tana shaƙewa, jin yadda ya wani sake kamo mata boobs yana kamo Nipples ɗin yana wani irin murza su.

"Please Hayatyyy ni tsoro nake jiiii".

"Hayatyyy mijinki mabuƙa ci ne a koda yaushe, kinga na jima banyi aure ba. Zanyi miki a hankali kinji?. Kina so naje wajan Hamda ne ta bani?".

Fashe masa da kuka tayi kawai yaga ta fara turesa daga jikinta da sauri ya sake riƙe ta sosai, kuka take bilhaƙƙi da gaskiya tana jin wani irin bala'in zafi a ƙirjinta tunda ya ambaci sunan kishiyarta, dan ita kam idan ba yanzu da ya faɗe ta bama ta ma manta da zamanta a duniyar wallahi.

"Ni ka cika ni na ce, kaje can wajan Hamda ɗin tayi maka".

"Ya Salammmm kiyi hakuri Hayatyyy shhhhhh Please".

Wani irin lumfashi ta sauke jin yadda ya jawota da ƙarfi ya haɗe bakinsu waje ɗaya dole ta haɗeye kukan nata.

Ji yayi ta gartsa masa cizo a harshensa da sauri ya saki bakin nata yana rige bakinsa, kallonta yake sai kuma ya saki murmurshi ganin yadda ta wani yi kicin-kicin da fuska tana sake kwaɓe baki zata sakar masa kukan nata.

"Please bana ce kiyi hakuri ba shine zaki cije ni ko Hayatyyy?".

"Uhum uhum ba kai bane kawai zaka wani ce........

"Shhhhhhhhh"

Ya faɗa yana sake jawota a hankali taji ya sake haɗe bakinsu waje ɗaya.

Dole badan tana so ba ta kamo wuyansa sosai ta tura masa harshenta ya kama yana jinsa yana yawo a sararin samaniya.

Duk da irin fargabar da Ummi take ji dole ta ture komai domin ta faranta masa tunda taji ya ambaci sunan kishiya, gara ta basa kulawa domin idanma bata basan ba zaije wata ne kuma zai samu ne.

A hankali suka faɗa tsakiyar gadon a haukace ya cire mata ƴar rigar baccin tata yayi wurgi da ita a hankali ya shiga sarrafa jikinta yana bin ko wanne lungu da saƙo na jikinta yana lashewa, ba abunda Ummi ke masa sai kukan shagwaɓa wadda ta ƙaranci indai suna irin wannan yanayin yake sake kashesa haɗe da ruɗar dashi sosai.

Wannan karanma taci wuya kam sosai saboda dama ba warkewa tayi ba, an sake fama mata wajan, ai ko kuka ta rinƙa sakar masa harda su cizonsa. Sai da ya dawo dai-dai ya rungumeta yana rarrashinta haɗe da tsokanarta wai harda cizonsa tayi tsabar daɗin data ji, shigewa tayi jikinsa tana sake turo baki tana masa ƙananun kuke-kuke da shagwaɓa, duk ta gama dashi yarinyar tasan lagwansa sosai ta gama kama zuciyar Mubarak.

Washe garin ranar yana rungume da ita sai faman kiran wayarsa ake, Ummi ko bata faɗa ba tasan wace mai kiran nasa, domin taga suna duk da bai ɗauki wayar a gabanta ba sai ma ya kashe wayar gaba ki ɗaya, bata ji daɗin hakan ba dan haka ta tashi daga jikinsa tana cewa.

"Please Hayatyyy kaje parlo ka ɗauki wayarka, ka sani ko akwai wani abun da take son faɗa maka ne".

Wani irin sonta ne ya sake jinsa yana bi masa ko wacce ƙofa dake cikin jikinsa yana kallonta da idanuwansa masu saurin kashe mata jiki ya ce.

"Noo kawai dan taji zanje Ƙauyen Tudun Wulli ne ita da Mama sunbi sun takura karda naje wai, kuma kinga na daɗe banje ba Mai Gari ya daɗe bai sani a idonsa ba, shima yana da haƙƙi a kaina".

Ɗan rungumesa tayi duk da itama sai yanzu take jin tafiyar tasa tana jin wani irin ba daɗi game da tafiyar itama ta ce.

"Yau zaka yi tafiyar ne?".

"Yes Hayatyyy".

Jikinta ne ya ɗanyi sanyi sai kuma ganin yadda yake binta da kallo tayi ƙoƙarin kauce komai da take ji a zuciyarta game da zuwan nasa ƙauyen itama ta ce.

"Karka damu kaje Ubangiji Allah ya tsare mana kai ya dawo da kai cikin amincinsa".

Rungumota ya sake yi yana amsawa da amin sake ɗan zamewa tayi tana kwantar da kansa akan cinyarta tana wasa da gashin Sajensa dana gemunsa tana ɗan sosa masa sumar kansa wacce ba wata bace, hurhura harta fara fito masa ma ƴan kaɗan akan gashin kansa da ƴan kaɗan a gemunsa.

"Ohhh Hayatyyy na an tsufa dai".

Ɗagowa yayi yana murmurshi ya ce.

"Hhh ai a haka nan kuma ake son tsohun kuma ba".

Dariya ta saki itama ta ce.

"Allah ka tsufa jifa furfura duk ta cika kanka fa".

Tashi yayi yana sake roƙo ta ya ce.

"Ke yarinyar nan tsokana ta kike yi ko, bari to na nuna miki ƙarfin tsohun mutum yanzun nan ki gani".

Da sauri ta zame tana dariya ya sake kamota yana faɗin.

"Baki isa ba wallahi saifa na sake nuna Miki"

"Wayyo Hayatyyy wallahi na hakura, ai ba sai ka sake ba na shaida tuntuni fa".

"Haba yarinya a'a na sake dai shaida mikin".

Zarya suka farayi a tsakiyar gadon tana jefa masa filo yana caɓewa yana murmurshi, ta bayanta yayi nasarar kamu ƙugunta yana dariya yana cewa waya kama?.

Dariya ta saki tana sake riƙe hannunsa, yana daga bayanta ya saƙalo da fuskarsa akan wuyanta, hannunta tasa ta bayan tana shafa Sajensa tana dariya, a hankali ta waiga bayan jin yana sakar mata lumfashinsa mai ɗumi akan wuyanta, tana waiga da fuskarta ya ɗago, murmurshi take masa shima ya sakar mata wadda yasa Ummi lumshe idonta ta sake buɗesu akansa, a hankali suka matso da fuskokinsu gaf da juna, a hankali kuma suka haɗe bakinsu waje ɗaya suna sauke ajiyar zuciya a tare, zubewa sukai a tsakiyar gadon.

Sai da komai ya lafa a tare suka shiga wanka wajan wankan ma sun ɓata lokaci mai tsawo a toilet ɗin kamin da kyar Ummi ta lallaɓasa ya fito tana sake tuna masa da tafiya fa zasuyi.

Tsaye take kansa tana fesa masa turare haɗe gyara masa zaman rigar shadda da yasa ruwan ƙasa tayi masa wani irin kyau sosai.

Kallonsa Ummi kawai take tana saka hannunta ta shafo Sajensa dake kwance luf-luf akan kyakkyawar fuskarsa, shima a hankali ya ɗago hannunsa yana riƙe hannunta da take shafa Sajen nasa ya kai ɗayan hannun nasa ya riƙe ƙugunta yana jawota jikinsa gaba ɗaya.

"Uhum ya da wannan kallo haka Hayatyyy?, nayi miki kyau ne?".

Murmurshi kaɗan ta saki a hankali ta ɗaga ƙafafunta tayi ɗan tsawo zuwa fuskarsa dai-dai kan lips ɗinsa ta sakar masa kiss sana ta sakar masa akan goshinsa da kan hancinsa sai kuma ta koma tsaye sosai yadda take ta ce.

"Koda yaushe ai kyau kike mi, ji nake kamar karka fita yau ɗin".

"Ohhh really?".

"Yes Hayatyyy".

"Karki damu zan dawo miki da tsarabar ƙauye uhum?".

Lumfashi kaɗan ta sauke kawai tana sake dubansa, wayarsa ce tayi ƙara a hankali yasa ka hannunsa yana ɗakkota ya amsa wayar ganin PA nasa ne.

Wayar yake a hankali ya ɗan rankwafu yana sakar mata kiss shima a bakinta kamin a hankali ya shiga rarrashinta a ido kuma a aikace, duk yana wayar kamin daga ƙarshe ya kashe wayar yana faɗin gashi nan fito yanzu.

Yana kashe wayar ya sake jawota jikinsa yana wani haɗe bakinsu waje ɗaya ya ɗan daɗe yana shan bakinta kamin ya sake ta ya juya ya fice daga bedroom ɗin yana jin tana masa addu'a yana amsawa da amin, cikin da zallar farin ciki da samun mace kamar Ummi ɗin, shi kam Baba Mlm ya gama masa komai a rayuwa tunda har ya haifa masa Mata kamar Ummi ɗin haɗe da basa ita halak malak....

*Ƙaunyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*

"Wai ko Lube ina wannan yarinyar Habiba ta shiga ne fisbilillahi ana yau ɗaurin auranta, ace tun safe bata a cikin gidan nan?".

Gaban Inna ne ya ɗan faɗi jin abunda wata kawarta Saude data gayyato da ƴan tsirarun mutane a gidan, wai yau zata aurar da Habiba take faɗa.



"Ina ga duk inda taje bazai wuce gidan su Asabe ba ai ko".

Faɗin wata Mata dage gefen Saude suna maganar suna cin tuwon masara da miyar taushe.

Inna ta miƙe tsaye tana ɗan duban su zatai magana Saude ta sake faɗin.

"Wai ni ina Bilki take ne?, itama ban ganta ba tunda muka shigo gidan nan".

In'ina Inna ta farayi sai zuwa can ta fisgo magana a bakinta ta ce.

"Wai Bilki?, ai ko tana cikin gidan nan bari naje naga ko tana ɗaki".

Inna ta faɗa tana fatan ace Bilki na cikin ɗakin, domin tasan idan ma bata nan tana can wajan ɗan iskan Yaron nan Shamsu, domin ɗazu da safe ta kamata ita dashi suna waya da ƴar ƙaramar wayar daya bata wacce duk zamansu da Bilkin Innar bata san da ita ba, sai yau data kamata da kunnanta tana wayar cewa gata nan fito zata zo su haɗu. Da yake ta raina ta saita tayi mata shuru kawai, tana mata maganar dawa take yin waya?, kuma ina ne zata je?, waye ma ya bata wayar dake a hannunta?.

Koda ta shiga ɗakin babu kowa a ciki, gaban Inna ne ya sake faɗuwa rass haka kawai data ga Bilkin bata a cikin gidan har banɗaki ta leƙa amma babu Bilki, duk da ba tun yau take nemanta ta rasa a cikin gidan ba, amma haka kawai yau data ga bata a cikin gidan sai duk hankalinta ya kasa kwanciya da fitar tata a yau ɗin.

Gashi kuma Habiba itama tun safiyar data fakaici idon jama'a sai ta fice daga gidan, ta tabbatar bata wuce gidan su Asabe, amma ai har gargaɗin hakan tayi mata, wato bata ji ba ko?, zata dawo ne kamin a fitar da ita zuwa gidan miji saita lakaɗa mata na Jaki duk karshenta ko.

Wani Yaro ne ya shigo da gudu cikin gidan, ya ɗan tsaya yana haƙƙi kamar wadda mutuwa ta biyu a baya.

Inna ta dube sa a mamakance ta ce.

"Kai Yaro lafiya zaka faɗo ma mutane cikin gida?, ko wani ya aiko ka ne?".

Sauran Ƙawayen nata suka miƙe tsaye suma suna jin miye yaron zai ci domin sunga akwai magana sosai a bakin Yaron, dama gasu da son jin gulma.

Yaron ya buɗe baki ya ce.

"Wasu motoci ne na gani a ƙofar gidan mai gari, kuma naga Innar su Asabe da Habiba a Fadar Mai Gari, kuma kamar an aiko da masu zama Fadar Mai Gari su zo nan domin tafiya da matar gidan nan".

Wani iri zaro ido waje Inna tayi ido waje gabanta ya yanke ya faɗi.

Maganar Inna Saude taji tana ce ma Yaron.

"Kai dalla can bar cikin gidan, yara sai gulmar tsiya, ce maka akai ka shigo ka sanar damu to faɗi ba'a tabbaye ka ba iyee?".

Yaro ya juya da sauri yana ƙunƙuni ya fice daga cikin gidan.

"Ƙawa ta anya yaron nan maganarsa akwai ƙamshin gaskiya fa a cikinta, domin kin san dama Innar su Asaben ƴar uwarta na auran Mai Gari fa. To amma abun maganar shi ne mi ya kai Habiba Fadar Mai Gari ne?".

Faɗin Saude riƙe da baki.

Ɗayar ce ce ta amshe da cewa.

"Zai wuce ƙararta ta kai a Fadar Mai Garin na cewa zatai mata auran dole".

Saude ta wani juya tana duban wacce tayi maganar tana faɗin.

"To Lare faɗi ba'a tabbaye ki ba kema, uban wani ya ce miki auran dole zatai ma Habibar iyee?".

Wacce aka kira da Lare ta wani ƙanƙance ido tana duban Saude ta ce.

"Ke Saude abun fa a buɗe yake a'ato, waye bai san aminiyar taki ba, yadda take gallazawa Habibar ba iyee, dan haka daga magana baza ki koma kaina ba ehee, kuma magana ta akan gaskiya take sai ku jira jiran kiran Mai Gari, domin wallahi Allah wannan yarinyar ƙararta ta kai ko ku yarda ko kar ku yarda".



Innar zatai magana idonta jawur na tsananin masifar da Habibar take son janyo mata, ga wata irin tsanar Habibar data ƙara cika mata zuciya, ji take da ace tana kusa da ita ba abunda zai hana yau bata ƙarya yarinyar nan ba wallahi.

"Assalamu alaikummmm".

Aka kwaɗa sallama a ƙofar gidan.

"Kin ji ko na rantse da Allah masu Fadar Mai Gari ne fa".

Faɗin Lare ta ƙare maganar tana son fita wajan.

Saude ce ta take mata baya sai kuma Innar.

"Bayin Allah lafiya da sallama haka?".

Faɗin Inna.

Wani daga ciki mai suna Sallau ya kalli Innar ya ce.

"Mai Gari ne ya ce azo a tafi dake".

"Azo a tafi dani mi nayi?, da har za'a zo har gida na ace za'a tafi dani, tsabar tozarci ma a rasa wacce rana za'ai min haka sai ranar da nake da taron jama'a a cikin gidan nawa".

"Kinga Malama bamu zaki tsaya kina gaya ma magana haka ba, tasa ki zamuyi har Fadar Mai Gari idan kika je can sai kiyi masa bayin duk wannan".

Faɗin Sallau yana mata kallon rashin mutumci domin tun a can Innar su Asabe ta gama basu labarin abunda ya faru da irin gallazawar da take ma Habibar wacce basu da labarin hakan sai kuma auran dolen da take son ƙaƙubama mata.

"Kinga Lube kifa bisu ku wuce Fadar Mai Garin nan, koma miye a can zaki ji ai, karki sake magana da wa'innan domin na lura kamar cike suke da haushinki, koma miye an riga da an gama kitsa masu fa".

Faɗin Saude tana raɗa ma Inna a kunnanta.

Ba yadda ta iya haka suka tasa ta gaba kamar wacce tayo sata suka nufi Fadar Mai Gari da ita, zuciyarta cike da baƙin cikin wannan abu da akai mata.....

Page 19-20

Tunda Inna ta doso faɗar Mai Garin gabanta ke faɗuwa sosai, saboda Irin jifga-jifgan motoci data gani a Fadar Mai Garin anyi perking ɗinsu.

"Zauna a nan"

Faɗin Sallau yana nuna mata wajan zama.

Cike da masifar dake ci mata ciki ta nemi waje ta zauna, tana ɓallama Sallau harara ji take kamar ta fallama Sallau mari take ji. Ganin Mai Gari baya ma wajan sai su Innar su Asabe da kuma Habiba dake zaune daga gefensu yasa ta duban Habiba tana mata wani irin kallo.

Tunda Habiba ta kalli Inna ganin wani shegen kallo da Innar ta jefeta dashi, yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta, gabanta na faɗuwa. Tana tunanin yau idan har ta koma gidan Innar kasheta ne kaɗai baza tai ba.

Mai Gari ne zaune a wani ɗaki shida Mubarak tunda ya zo garin kota ina zuwa ake ganinsa duk wadda ya zo ganinsa saiya koma tare da tarin alkhairi shi yasa yau fadar mai garin cike take da jama'a daga wannan ya zo sai wannan ya tafi, har Mai Gari ya ce ya kamata su keɓe shida Mubarak ɗin zasuyi wata magana.

"Mubarak!"

Mai Gari ya kira sunan Mubarak ɗin cikin muryar wacce bata tare da wasa.

Mubarak ya sake natsuwa yana fuskantar Mai Gari saboda babban mutum ne a wajansa, kuma abokin nasa Mahaifin gashi ɗan uwane a cikin Ahalinsu.

"Mubarak sai yanzu ita Mamar taku ta baka umarnin zuwa inda muke?. Ashe har aure kayi Mubarak bamu da labari? taje ta haɗaka aure da Hamda jininta, wato mu ko ohoo ko?, komai tabi ta handame daga ita sai Iyalanta".

Mubarak kunyar duniya ta cika sa, shima kansa yasan kwata-kwata bai kyauta ma su Mai Garin ba, saboda rabonsa da garin tun ranar da yazo tafiya da su Mamar lokacin da suke zaune a garin, amma babu ranar da zata zo ta wuce bai tabbaye su ba a wajan Kawu Abu, haka kuma babu Watan duniya da zai zo ya wuce baiyi masu aike ba, sai yanzu ya fahimci kwata-kwata dai aiken da yake yi baya zuwa inda suke suma, kamar dai na Baba Mlm ɗin, ransa sosai ya sake ɓaci ainun da lamarin su Mamar da Kawu Abu ɗin.

Sauke lumfashi yayi jin Mai Gari ya sake magana yana faɗin.

"Uhum baka da abun cewa ne Mubarak?, wato duk abunda na faɗa gaskiya ne kenan?".

"Wallahi Baba Mai Gari kwata-kwata yadda kake ɗauka ba haka bane, ban so hakan ta kasance ba, amma ba laifi na bane, ayi hakuri dai".

Gyara zamansa Mai Gari yayi yana sake duban Mubarak kamin ya ce.

"Ba sai ka ce komai ba ai, ita Mamar taku duk ita ce mai baƙin halin ai, idan ka tafi yanzu kuma sai mun sake shekara ƙila goma bamu ji ɗuriyarka ba, dan haka muma zamu baka iri daga cikin Garin nan, kaga idan akai haka ai dole ka rinƙa waiwayo Mahaifar iyayenka, dama naji Baba Mlm dake Rimaye shima ance ya baka yarinyarsa duk ina da labari, hala ita Mahaifiyar Hamda bata san da auran yarinyar Baba Mlm ɗin bane ko?, saboda nasan halinta ciki da bai saina rubuta labarinta".

Gaban Mubarak ne ya ɗan faɗi har bai san lokacin daya ɗago yana duban Mai Gari ba. Fuskar Mai Gari fa babu alamar wasa yake a maganarsa dan haka Mubarak cikin kwantar da murya ya ce.

"Mai Gari ban fahimci abunda kake ƙoƙarin nayi ba?".

"Bari na fito maka a mutum, muma nan zamu baka yarinya ka aura a cikin garin nan, yanzu haka tana nan fadar tawa, koba komai Mubarak zaka sami lada, Marainiya ce ka taimaketa tana cikin wani hali, uwar roƙonta auran dole zatai mata kuma da wani ɗan iska ɗan shaye-shaye wadda duk garin nan ya fitini kowa, na kuma yanke hakan ne saboda muma koba komai ka auri tsatson Mahaifiyarka toshenta har guda biyu da ita Hamda ɗin da Habiba".

Mubarak jin maganar yake kamar a mafarki yanzu ina zai kai rigimar Hamda data Mama idan har suka gane aure yaje yayi har guda biyu?, tayaya zai fara masu bayani ne wai?, ya mai Gari yake

19 / 27