Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
sosai.
A ƙasa suka zauna sai Umma dake saman kujera ita da Baba Mlm ɗin.
Baba Mlm ya dube su a tsanake yana tausayin Ummi haka kawai, saboda yaje ya bada auranta a yau ɗin bata sani ba, ba kuma tasan waye wadda aka batan ba.
Daurewa yayi, yayi gyaran murya ya ce.
"Abunda yasa na tara ku nan shine, dama Ummanku ta bani shawarar na nemarwa Ummi miji tunda ita Halima auranta zuwa bayan sallah ne".
Tunda Baba Mlm ya fara magana ƙirjin Ummi ke bugawa da masifar ƙarfi, lumfashinta kuwa janshi take a hankali amma ji take baya ma shiga hunhunta yadda ya kamata, shi yasa take ji kamar mai cutar asuma.
Umma ma wani tunani ne yazo kanta wadda yasa gabanta faɗuwa, tana addu'a Allah yasa ba haka bane, tana addu'ar ba abunda take zargi bane Baba Mlm ɗin yaje ya aikata akan Ɗiyar sonshi, ita Tata ɗiyar na nan ko ohoo, sai tashi Ɗiyar zaije ya inganta rayuwarta, wadda tasan idan abunda take zargi ne har abada Ummin Bata ba ƙara kukan rashin gata ko ta tsinci kanta cikin rashin madafa.
Muryar Baba Mlm ce ta katse ma kowannan su tunanin daya faɗa, Hali ce kaɗan wani abu bai faɗo mata a rai ba, kawai tana sauraron Baba Mlm ɗin ne taji miye zaice?.
"A haƙiƙanin gaskiya na yanke hukunci ban tabbayi ra'ayinki ba Ummi, ina fatan zaki yafe min, sana ki karɓi abunda nazo miki dashi, naje an ɗaura miki aure, a yau ɗin bayan sallar juma'a, ga sadakinki a nan wajan a hannu na, gasu ki riƙe a hannunki saboda dama haƙiƙƙin ki ne".
Baba Mlm ɗin ya ƙare maganar yana miƙa ma Ummi uban tulin kuɗin dake hannunsa.
Ba Ummi kaɗai kuɗin sadakin daya miƙa ya kashe da mamaki ba hatta Umma ido waje take bin kuɗin da kallo, gabanta ne yayi wata irin faɗuwa, har sai da ta dafe ƙirjinta. Shikenan wallahi abunda take zargi ne ya faru. Lallai yau Malam ya gama nuna mata banbanci da tata Yarinyar, sai Ƴarsa ƴar so ce zaije yayi ma wannan gatan?, dama kuma tunda Mahaifiyar Ummin ta taka cikin gidanta a sunan kishiya bata sake shiga farin ciki ba har iyau, itakam Aysha ta cuceta wallahi ta ruguza mata gida, da ace bata shigo mata gida ba, da yanzu tata Yarinyar ce Baba Mlm zai bawa Baban Abokinsa auranta, ba wai Ummi ba, mi yasa Mahaifiyar Ummi tayi mata shigar bazata?, wani irin dunƙulelan abu ne daya tsaya mata a wuya ta haɗe wani abu mai zafi da ɗaci a maƙoshinta, tana bin Baba Mlm ɗin da kallo kawai.
Ummi ko hannunta na rawa muryarta ma haka, abun jinsa take kamar mafarki take fa, zata tashi taga duk wasa ne ba gaske bane.
Girgiza kanta tayi da kyar tana janye hannunta ta ce.
"A'a Baba Mlm ka riƙe a wajan ka".
Ta faɗa wani irin abu na tsaya mata a wuya. Yau ita aka ɗaura ma aure da wadda bata taɓa gani ba?, kuma da mutum sa'an Baba Mlm?, ina zata kai mutum kamar sa'an Mahaifinta?, kuka ke son kwace mata amma ta danne, sai hawaye dake zubo mata, tayi ƙasa da kanta sosai shi yasa ba wadda yaga irin mummunan halin da take ciki.
Hali ko, ko a jikinta hasalima murna ta taya ƴar uwar tata.
Baba Mlm ya sake dubansu ya ce.
"Haƙiƙa zaki ji abun a bazata kamar ba gaske ba, na yanke hukunci ne saboda na inganta rayuwarki, wadda na bawa auranki bazai taɓa cutar dake ba, baban abokina ne wadda yau yazo min a bisa zuwan bazata da yayi min, ya sake kasheni da wata bazatan da karɓar auranki a yau ɗin ya ce a ɗaura sa, saboda yana son goge duk wani laifi na yayi min, da na so ba yanzu ba tukunna amma yaƙi hakan, domin yana ganin idan yayi min haka shine kaɗai abunda zai iya sakamin dashi, sana yau ɗin bake kaɗai bace wacce aka ɗaura masa aure da ita ba, can danginsa an basa wata ƴar uwarsa, kuma duk a yau akayi ɗaurin auran, Ummi kiyi hakuri nasan kamar laifi nayi miki, amma zan ƙara jaddada miki nan gaba zaki ga abunda nake hango miki".
Tunda Baba Mlm ya furta ba ita kaɗai aka ɗaura auranta ba, da shi wadda aka aura matan, kenan dai kishiya gareta?, yanzu Matansa biyu kenan?.
Kukan da take dannewa ne ya kwace mata, da sauri tasa hannunta ta toshe bakinta.
Hali ce ta riƙeta itama haka nan taji tausayin Ummi ɗin. Baka san mutum ba an aura maka shi, haka zalika baka sonshi, kuma a haɗa maka da kishiya, abun da ciwo sosai ai.
Umma ko duk da taji maganar Mata biyu aka aura masa, ita hakan bai wani dameta ba, kawai ji take Baba Mlm ɗin ya nuna tsantsar son kai, daya hana Ƴarta auran mutum kamar Mubarak ɗin.
Amma a fili da yake ita mutum ce marar shiga sabgar da babu ruwanta, tashi tayi kawai tsaf ta ce Allah yasa alkhairi.
Baba Mlm yayi saurin tsaida ita da cewa.
"Umman Yara babu abunda zaki ce ne?".
"Mi kake so na ce maka Malam?"
"Amma ai...
Ɗan ɗaga masa hannu tayi ta ce.
"Na ce Allah yasa alkhairi, to banga abunda zai iya ƙara cewa ba, saboda sadda aka yanke hukuncin wadda za'a aura matan ba'a sa dani ba, haka kuma ko sadda za'a kawo mahaifiyarta shima ba'a shawarce ni ba, dan haka ni suwa da zan saka baki?".
kalmar data iya furtawa kenan tabar wajan. Baba Mlm ya bita da kallo kawai, dama yasan ba lallai ta tanka ba, abun nan na masa ciwo.
Umma ko ciwon abun da baƙin cikin da ke taso mata ne yasa tayi saurin barin wajan, tana saurin korar shaiɗan da yake son bijiro mata wani tunanin marar kyau, har abada bata jin zata iya cutar da wani bare kuma Ummi, ta dai shanye baƙin cikin da Baba Mlm ɗin ya daɗe yana ƙunsa mata akan Mahaifiyar Ummi da kuma ita kanta Ummin.
Ta rantse da Allah ko hannunta baza ta sa ba wajan hidimar bikin Ummi ɗin, tunda lokacin daya yanke hukuncinsa ai bai sanar da ita ba, bai kuma nemi shawararta ba, yaje yayi abunsa, haka kuma sadda yaje ya auri Mahaifiyar Ummi ɗin ai baiyi shawara da ita ba, sai dai kawai ta ganta a cikin gidanta a matsayin kishiyarta, shi yasa duk wani abu daya shafi Ummi bata taɓa sa hannunta a ciki, yanzu ma tunda ya nuna mata banbanci ƙarara baza ta taɓa cewa komai ba, mima yake so ta ce masa to?. Hmm inda Allah ya taimaketa itama Halima wadda zata aura ɗin ba baya ba wajan nagarta da kuma dukiya, amma fa baka taɓa haɗashi da Mubarak Khabeer ƙankara, Mubarak ɗin ƙarshen komai ne, a hasashenta kenan.
Baba Mlm tunda yabi Umma da kallo harta fice parlon sai yanzu ya dawo da dubansa wajan su Ummi.
"Halima ki rarrasheta dan Allah. Ummi ko dai auran ne baki so?, nasa a warwaresa".
Da sauri ta girgiza kanta, har abada duk abunda Baba Mlm ɗin ya bata tasan bazai taɓa cutar da ita ba, dan haka har gaban abada bazata taɓa watsa masa ƙasa a ido ba, ta ce.
"A'a Baba Mlm ko kaɗan duk abunda ka yanke a kaina wallahi ya yanku, kuma na amsheshi hannun biyu-biyu, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a cikin rayuwata".
Wani irin daɗi ne ya rufe Baba Mlm ɗin yana alfahari da samun Ɗiya Mace kamar Ummi ɗin, mai hankali da tawakali kamar dai Mahaifiyarta.
"Allah yayi maku albarka tashi kuje. Amma tarewarki sai bayan sallah za'a haɗa ayi taron bikinku keda Halima insha Allah, nina yanke hukunci nan kawai".
Halima tayi murmurshi kaɗan ta ce.
"Kuma Baba Mlm ai hakan yayi ma wallahi".
Kallon ɗiyar tasa yake Halima yadda bata nuna komai ba, a yanzu dama tuni ya lura ita ta fara sakkowa daga irin share ƴar uwarta da take yi a baya, ba laifi yanzu tana ɗan shiga harkar Ummi ɗin, Umma kuma ganin haka yasa kawai ta kyaleta tunda tasan dai ba tare zasu dawwama ba, tunda dai Halimar aure zatai dole su rabu ai.
Tunda suka shigo ɗaki Ummi ta zube tana sakin wani irin sansanyan Kuku, mai tafe can ƙasan zuciyarta.
Bata taɓa tunanin hakan zai kasance da ita ba, aure a nan kusa, kuma da wadda bata taɓa tozali dashi a duk cikin rayuwarta ba.
Hali ta kalli yadda Ummin ke kuka, haƙiƙa dafa ciwo, kuma harda kishiya ba ita kaɗai bace, dole kam tayi kuka.
Kuma tasan Ummi akwai kishin abunda take so, akwai saka abu a ranta, bare idan tana son mutum wani irin so take masa na gaske.
Dafata Hali tayi ta ce.
"Dafa kin daina wannan kukan Ummi, saboda idan kika ga wadda aka aura mikin da wallahi baza ki taɓa zama kiyi wannan kukan ba, baƙin ciki ɗaya nake miki shine dana ji cewar bake kaɗai ba ce, amma ai kowacce da halinta take zama, dan haka banga abun tada hankali ba, ai wallahi Baba Mlm ba ƙaramin gata yayi miki ba, uhum bafa zaki gane ba Ummi sai lokacin da kikayi ido huɗu da Mubarak Khabeer ƙankara, nifa a photo kawai na taɓa ganinsa amma nake gaya miki hakan, wani abun ma sai kin sakashi a ido, wata miyar ai sai a maƙota kinji Ummi, kawai ki share hawayenki ke kam ai kin gama dace a nan dai gidan duniya sai kuma ki nemi aljannarki a gidan mijinki, ta hanyar yi masa biyayya kawai".
Shuru kawai Ummi tayi, tana son hasasoma ranta yadda Mubarak ɗin yake, jin yadda ake ta wani kuranta shi, duk iya hasashenta ta kasa gano yadda zata suffanta shi a zuciyarta. Duk da haka tana jin wani irin zafi-zafi a zuciyarta, ta rasa na miye?, shin na auran da akai mata ne bata so, ko kuma najin cewar ba ita kaɗai bace?, ko kuma na anyi auran amma ko yazo ya ga wacece ma Matar tashi, amma da yake bai damu ba, kuma ba sonta yake shima, shine yasa kawai yayi tafiyarsa ya barta da auransa akanta.
*Ƙauyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*
Inna ta yaye labulan ɗakinta tana fitowa gaba ɗaya, ta dubi Habiba dake surfen masara ta ce.
"Wai ke tun ɗazu tsabar son jiki irin naki ace baki gama surfen nan ba?".
Bakinta na ɗan rawa ta ce.
"A'a Inna na kusa gamawa".
"Ke wai tsaya ma ba tun ɗazu naji Abba ya aiko kiranki ba?, ina ɗaki bacci ya ɗan ɗauki ni, naji Yaro ya zo kiranki ba?, kar dai baki je ba?".
Da wani irin sauri Habiba ta girgiza mata kai alamar a'a taje. Bata je ɗin ba, saboda ko inuwa ɗaya bata fatan su sake haɗawa da Abba, bata fatan abunda zai haɗasu, idan ko Innar ta sani to ta bani ta shiga ukunta.
Inna zatai magana Bilki ta shigo gidan dama bata gidan.
Bilki ta dubi Habiba ta ce.
"Wato ke isassa shine tun ɗazu kika bar Abba a ƙofar gida yana faman zaman jiranki har yanzu bai tafi ba".
Innalillahi Habiba ta furta tana taune lips ɗinta da ƙarfi tana saurin runtse idonta, gabanta ya yanke ya faɗi tana jiran hukuncin da Inna zata yanke a kanta yanzu.
A kamin ba ta gama tantancewa taji saukar kwano akanta, Innar ta ɗakko wani kwanon shan ruwa ta dage iya ƙarfinta ta buga mata shi a kai.
Da sauri Habiba ta saki tabaryar da take daka da ita, ta matsa nesa da Innar tana zare ido waje bakinta na rawa ta ce.
"Dan Allah Inna kayi hak.....
"Keee dalla can rufe min baki algunguma makira, da ni zakiyi ma ƙaryar cewa wai kinje tun ɗazu?, tsabar kin iya shirya ƙarya da munafurci?"
"A'a Inna wallahi....
Ƙara katse ta tayi tana ɗaga mata hannu, idonta rufe tsabar masifa ta nuna mata hanyar waje ta ce.
"Zo ki wace, ko yanzun nan nayi miki dukan da zaki kasa moruwa wallahi".
Sumi-sumi Habiba ta fice daga gidan da gudu domin gani take kamar Innar zata kamo ta ne tayi mata dukan da take kirarin yi, tasan ba ƙaramin aikin Innar bane.
Inna ta dawo da dubanta ga Bilki ta ce.
"Kaga ƴar banza, wato ni zata maida shashasha ko?, cewa fa tayi wai taje tun ɗazo ma harya tafi, tsabar ta iya munafurci".
Tsaki Bilki taja tana neman waje ta zauna ta ce.
"Hmm rabu da ita, da bana waje sai dai ya ƙarashe zamansa ya tafi, danma Abban ne da baƙar zuciyata yaƙi tafiya shima, domin nima saura kaɗan ya makeni akan ana sane aka ƙi barinta fita wajansa wai".
Zama Inna tayi ta ce.
"Ai ko wallahi idan ma ya bige ki sai anjimu dashi, domin har wajan uwar data haifeshi zanje, yabar ganin zan bashi Habiba ya ce kuma zai rinƙa taka ni yadda take so ba. Kinga ba wannan bama, ina kika je kika daɗe haka wai tun safe fa kika fita".
"Inna yaushe kika fara min titsiye ne?".
"Kefa daɗi na dake baki iya magana ba, daga tabbaya?, tabbaya ce fa nayi miki kawai?".
"To Inna wajan Shamsu naje".
"Innalillahi baki rabu da Shamsun nan ba dai ko wato?".
"Ai wallahi Inna bazan taɓa iya rabuwa dashi ba, nifa dole Shamsu saiya aure ni, tunda ya riga ya sanni a ɗiya Mace na rantse da Allah sai ya aure ni, kuma duk duniya shine kaɗai nake so".
"Anya Bilki kina da hankali kuwa?, karfa kije ciki ya shiga tsakaninku in bani an shiga uku, asiri na tonu a bainar nasi. Ai wallahi ba ƴan jaraba ba ko ƴan miye ƴan gidansu Shamsun tunda ya lalata min Ƴa na rantse ba sai kince komai ba, dole ne ya aure ki, ko sama da ƙasa zasu haɗe, lokaci kawai nake jira, amma fa Bilki na haneki zuwa inda yake, na hanaki Bilki".
Inna ta ƙare maganar tana nunata da yatsa.
Bilki kuwa taɓe baki tayi, domin bata jin zata ɗauki gargaɗin Innar, ai tunda Shamsun ya ɗanɗana mata daɗin abun bata taɓa kwana ɗaya bata je inda yake ba sun jone, abun na damun Inna kamar tayi kuka, saboda tsoronta ɗaya kar Bilki ta kwaso mata ciki asirinta ya tonu, ta so ace Habiba ce lalace haka take bin Maza ba wai Bilki ba, sai dai ba'ai ma Allah wayo, saboda sadda Bilki ta lalace ma bata sani ba bata ankara ba, sai da abun yayi nisa sosai, ta so hanata amma Bilkin tayi nisa bata jin kira.
Shi yasa Innar Abba na zuwa ya ce yana son auran Habiba ta ce faɗuwa ta zo dai-dai da zama, domin dama hanyar da take nema ta yadda za'ai ta wargaza rayuwar Habibar...........
12
A hankali ta tsaya a zauran gidan tana sauke lumfashi, wasu ƴan guntun hawaye ne suka zubo mata, tasa hannunta ta share.
A zauran ta tsaya ta sami waje ta zauna, danta rantse da Allah baza ta fita wajan Abba, ba.
Ta ɗauki lokaci mai tsawo a zauran tana addu'a kar da Allah yasa Bilki ko Innar su fito har Abban ya ƙarashe zamansa ya wuce.
Wani yaro taga zai shigo gidan da sauri ta miƙe tsaye, yaron na ganinta da sauri ta rufe ma yaron baki tana faɗin.
"Wani ya aiko ka ne?".
Sakin bakin yaron tayi yana dubanta ya ce.
"Wai ance ana sallama da Habiba, ya ce a gaya mata shi zata shanya?"
Wani lumfashi ta sauke tana duban Yaron a hankali ta ce masa.
"Kaje ka ce ance wai bata nan, ance tun ɗazo ta fito bai ganta bane?".
Yaro ya juya ya fice abunda ta ce ma yaron haka yaje ya faɗa, tana leƙe daga zauran gidan tana kuma jin abunda yaro ya faɗa masa kamar yadda ta ce dashi, ganin yadda Abban ya wani miƙe kamar zai shigo gidan, yasa gaban Habiba faɗuwa tana komawa baya kaɗan tana dafe da saitin zuciyarta, tana addu'ar Allah ya rufa mata asiri, domin tasan ba ƙaramin aikin Abban bane shigowa har cikin gidan.
Can lingo ta ɓoye tana zare ido, sai da ya leƙo zauran kuwa ya shiga dubawa, baiga kowa ba, hakan yasa shi sakin tsaki yayi kwafa ya bar kofar gidan kwata-kwata.
Wata wawar ajiyar zuciya ta sauke tana fitowa daga inda ta ɓoye, kai tsaye gidan ta fice tana son zuwa gidan su Asabe.
Da sallama ta shiga gidan ganin Asabe bakin murhu tana murza dambu, ganin Habiba ce ta shigo gidan yasa Asabe aje dambun da take murzawa.
"Lahh Habiba ki ce dama tafe?".
Zama tayi akan wata tabarma dake shinfiɗe a tsakar gidan nesa da inda ake sanwar.
"Ni ce Asabe, ina Inna?".
Asabe ta waiga ƙofar ɗakin Innarsu ta ce.
"Yanzu nan ta bar min murza dambu nan, ta shiga ɗaki amsa wayar Mai Gari, wai Matarsa ƙanwar Inna ce ai kin sani, shine suke waya tun jiya Innar taje gidan bata da lafiya, shine yau ta kira shi baya kusa, sai yanzu ya kira ta taji ya jikin Inna