Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   16 / 27

45K to 48K   out of 78K words

ya shiga ukunsa".



Dariya Ummi ta saki tana cewa.

"Sannu muguwa ai ko da kinyi zawo, kuma ni bana fatan ƙarshe ace Goman ƙarshe bana sallah ai gara dai tun farkon azumin goman farko data tsakiya ace kayi, amma goman ƙarshe ibada ake sosai saboda daren lailatun ƙaddiri".

"Ke anya ma Daren nan ba'a gansa jiya ba kuwa?".

Umma daga can ta sako masu baki ta ce.

"Tabbas nima naji kamar alamar hakan, saboda wata irin ni'ima da iska da akai jiyan kuma yanayin jiyan tun safe a lullume yake".

"Ai shine Umma Allah yasa dai an gantan jiyan"

"Amin ai hasashe muke, kuma tunda muna raya ko wane dare a cikin goman ƙarshen nan ai Alhmdllhi insha Allahu gata can ma mu gani"

Faɗin Umma.

Sun aikatu sosai a ranar saboda har aka sha ruwa basu gama suyar naman nan ba, dole Ummi ta sakarma Hali sauran, ita kuma ta kama yin abincin buɗa baki, sai da suka makara sosai sai wajen Isha'i kamin ta ƙare abin shan ruwan, Almajiran Baba Mlm sun shigo sun ɗauki abincin shan ruwansu inda Umma ta ɗebar masu nama suma su ɗanɗana kamin aba kowa nasa.

Sunji daɗi sosai danji suke kamar a gida suke, wasu daga cikinsu sun tafi gida sallah wasu kuwa basu je ko ina ba, a nan suka ce zasu yi Sallah saboda sun san sallah a makarantar Baba Mlm ɗin kamar kana gida ne, wani lokacin ma yafi ace ka zauna a makarantar Baba Mlm ɗin daka tafi gidan.

Bayan sunsha ruwa suka ƙarasa ɗora naman Shanun nan suka barsa yayi ta dafuwa sosai.

Hali dai addu'arta bata amsu ba, saboda a Tv suka ji Sarkin Musulmi ya bada sanarwar Saudiyya basu ga watan sallah ba, dan haka gobe da azumi za'a tashi, amma wasu ƙasashen sunce su sunga Watan Sallah dan haka su gobe sallah zasuyi ciki harda Niger da Cameron.

"Kambu lallai ma Sarkin Musulmin nan, na rantse da Allah gobe kuwa bazanyi azumin ba, tunda har Niger sunga Wata nima gobe zanyi sallah Allah"

Faɗin Hali tana wani turo baki tana jin haushin Sarkin Musulmi.

Duka Ummi ta kai mata a cinya tana dariya ta ce.

"Ai ko baki isa ba na rantse sai kinyi azumi gobe kona gaya ma Baba Mlm".

"Hhhhhhh ai nasan bazaki gaya masa ba, kuma kin san Allah gobe ni nayi sallah ta kudai ku biye ma Sarkin Musulmi".

"Kinga fa ko Saudiyya basu gani bafa".

Taɓe baki Hali tayi ta ce.

"Eh na dai naji, ai dai wasu Kasashen sun gani ko, kuma baki ji ma har cikin Nigeriar ba wasu sunce sun ganshi a wasu garuruwan ba?".

"Naji amma dai kin san wasu ƙarya suke yi ko?".

"Duk da haka tunda ance an gani a Niger nifa sallah gobe ba fashi a'ato".

Da safe su Ummi sun tashi da azumi da sauran Musulmi duniya baki ɗaya, saboda Sarkin Musulmi ya riga da ya sanar sai gobe sallah.

Da gaske kuwa Hali tunda safe ta fara cin nama danma Ummi ta shaida batai azumi ba, Umma har faɗa tayi mata ta gaji ta kyale ta.

"Kefa dole yau sallah kikai ko?".

"Kware kuwa gashi ma kin shaida".

"Ai ko zaki rama ɗaya nan ne a'ato".

Faɗin Ummi dake zaune suna suyar Dambun naman Shanun da tun jiya ya idasa dahuwa sosai yau da safe suka daka shi a turmi saida yayi yadda suke so sana suka juye shi a kasko har gashi sun kusa gamawa, Hali sai cika hannu take tana ci tana ma Ummi kwalele.

"Uhum sha kumurinki muma gobe iyanzu muna nan bakinmu a buɗe yake".

"Kin san Allah dama ruwa kika sha nifa Sarkin Musulmin nan ko duk shekara haka yake cewa daga baya ya zo ya bada hakuri".

"Ke dai kika sani".

Ummi ta faɗa suka ci gaba da aiki.

Sai kusan ƙarfe biyu suka gama harda miyar Waina da Sunasur ɗin gobe da zasuyi.

Hali ta ce.

"Wai baza mu je ƙonshi da kitsu bane wai?".

Ummi dake juya wayarta ta ce.



"Ke dai zaki iya zuwa, amma ni kin san bazan iya fita ba sai da izinin Hayatyyy ai ko?".

"Hhh wayyo Allah masu aure manya, nifa har mantawa nake da yanzu fa ke aure ne dake, Allahu Sarki har kin bani tausayi, amma dai zan miki kitso tunda na iya, zanje ƙoshi yanzu gidansu Iya a nan bayanmu ta iya ƙonshi zan taho da ita idan ta gama min saita miki kema".

Hararar wasa Ummi tayi ma Hali ganin yadda ta dage sai dariya take mata ta shaƙiyanci.

"Hmmm na dai ji, kema kuma ai kin kusa zama kamar ni ɗin ai ko?"

Tashi Hali tayi tana sanya Hijab ta ce.

"Duk da haka dai, ke dai yanzu tunda kin zama kamar Umma sai dai na ce sai na dawo, zan taho da ita har Umma tayimawa".

"To kitson fa sai dare zaki yi min?".

"Eh sai idan kunsha ruwa saina miki".

Ta idasa maganar tana ficewa.

Koda taje gidan Ƙonshi a cike yake da mutane a hakan ma wai wasu sai gobe za'a masu.

Yadda ake ganin mutumcin gidan Baba Mlm ɗin yasa tana zuwa aka ture kowa mai ƙonshin ta ce dama ta tabbaya tun kamin azumi ya shigo ma, dan haka aka fara yima Hali ƙonshi mai kyau.

Da aka gama Hali taja Iya mai Ƙonshi ta ce dan Allah zata je gidansu tayi ma Umma da Ummi idan babu takura ko damuwa?.

Iya ta ce wallahi babu komai zata zo data idasama wa'innan ko wasu sun zo zata basu hakuri. Saboda hatta gidan su Iya mai Ƙonshi sai da Baba Mlm ya aiko masu da uban neman Shanun da aka raba, domin yanzu hakama shine suke soyawa a matsayin naman sallar su, dan haka duk Mutanan gidan sai nan-nan suke da Halin.

Sai da Hali ta koma gida Ummi taita santin lallen saboda yayi mata kyau sosai har zumuɗin zuwan Iya mai Ƙonshin take itama azo ayi mata.

Sai wajan uku tukunna Iya ta zo, Ummi aka fara mawa saboda zata tashi tayi kayan shan ruwa, kamin ana gamawa aka farayi ma Umma itama.

Sosai tayi masu Ƙonshi mai kyau, da zata wuce Umma tasa Hali ta bata kayan kwalliya da uban wani naman da suka soya.

Na Ummi yana bushewa ya kama wajen biyar na yamma ta cire, Hali sai taga Ƙonshin duk na Ummi ɗin yafi mata kyau, sai yaba lallen nata take sosai.



Tare sukai kayan shan ruwa wannan lokacin Hali ce ƙarfin aikin tunda ba azumi take ba, dan haka ta ce ma Ummi yau dai ɗaya ta huta, dan haka ma rabin aikin Hali ce tayi, sadda Umma ma zata cire ƙoshin har an kira sallah ansha ruwa itama yayi kyau sosai.



Bayan sunsha ruwa a Tv suka sake jin anga watan sallah amma kamar ba tsayuwar yau bane, inda Sarkin Musulmi ya bada hakuri harda ita kanta Saudiyyar saida ta biya Diyya.

Ai ko Hali taita dariya tana faɗin dama ai ta faɗa duk ƙarshe dama haka za'a ce, ai tunda wasu Ƙasashen suka ce sun gani magana ta ƙare kuma, shi yasa kawai tasha ruwa.

Cikin daren Hali tayi ma Ummi kitso harda ma Umma, ita kuma Umma itama ta iya kitson dan dai su duka ba wani yi suke ba, sunfi zuwa Kankia suyi Salon kawai, Umma ce tayima Hali itama ba wani mai yawa sukai ba, shi yasa da wuri suka gama.

Washe gari dubbanin jama'ar Musulmi suka tashi da murnar Sallah, kota ina murna ake haka ce ta kasance a gidan su Ummi.

Tunda safe suka fara ɗora tuyar Waina da Sunasur harda ma Chincin da Samosa, sai suka raba aikin Ummi ke Waina da Sunasur sai ita kuma Hali ke jigilar yin Chincin dasu Samosa.



Basu je sallar Idi ba saboda ayyuka sun sha masu kai, dama ko za'aje sai dai Hali ce zata je ita ɗaya, dan haka itama ta ce tana gida aiki yayi yawa.



Tun safen suka fara ganin baƙi kota ina shigowa ake shi yasa Wainar kusan ta tiya nawa akai amma gashi harta kusa ƙarewa, sai wajan sha biyu na rana suka gama komai aka rabama Almajiran Baba Mlm nasu kowa ya zo ya ɗauki nashi a ciki Umma ta raba naman kowa ta saka masa, suna shigowa su ɗauka sai godiya suke haɗe da addu'a kowa yasha kayansa masu kyau.

Su Ummi sai da suka huta suka ci abinci sana suka samu sukai wanka. Wasu irin kaya masu shegen kyau Ummi tasa cikin kayan da Mubarak ya kawo mata, itama Hali Sulaiman ya kawo mata kayan sallah amma saita sa cikin wadda Mubarak ya basu itama, Umma ma anci gayu sosai.

Baba Mlm ma ba'a barsa a baya ba, shi tun za'a tafi Idi ya ci nashi wankan da wata shidda ruwan hanta tayi masa kyau sosai su Ummi da Hali sai wasa suke da dariya dashi inda basu bari ya fita cikin jama'ar dake jiransa ba a waje sai da suka yi Pictures masu kyau dashi sosai, sana suka barshi ya fita, so kuma suka ci gaba da yin nasu photon, Hali ta so Umma ta taso suyi amma fufur taƙi dole ta kyale ta.........

Page 16

*UMMI POV*

Tsaye tayi a tsakar gidan tana jin ƙamshin turaren da har duniya ta naɗe bata jin zata manta da mamallakinsa, a wajansa ta fara jin wannan mayen ƙamshin. Zuciyarta ce ta fara bugawa a ƙirjinta, duk da bai shigo cikin gidan ba, amma gangar jikinta da ruhinta da wannan mayen ƙamshin nasa ya tabbatar mata da yana gaf da isowa gareta.

"Ummi naga kin tsaya?, ki ɗebo mana kunun ayar ko mun gama cin abincin nan".

Faɗin Hali data ɗan leƙo jin Ummi shuru, tana fitowa ta iske ta tsaye kamar gunki.

Ɗan dubanta Ummi tayi tana jin wani irin yanayi a jikinta tun kan ta gansa ma, lumshe ido tayi tana buɗewa ta ce.

"Hali ji nake kamar Hayatyyy ne ya zo garin nan fa".

Fitowa gaba ɗaya Hali tayi sai ma yanzu ne itama take jin wannan mayen ƙamshin nasa, a hankali ta sake matsowa tana wani murmurshin tsokana ta ce.

"Ahh lallai Ummin Hayatynta har kin riƙe ƙamshinsa da komai nasa?. Ina ganinfa yana cikin gidan nan, yana shagon nan na baya wajan Baba Mlm ƙila, idan ko hakane maza ki zo ki sake kayan nan nayi maza na shirya parlon can".

Da sauri Ummi ta ce to, ta koma ɗakin nasu tana jin wani irin maɗaukakin farin ciki na rufeta.

Hali ta gyara parlon tasa turaren wuta mai ƙamshin daɗi, tana gaf gamawa Umma ta fito daga ɗakinta tana kallon Hali ta ce.

"Yawwa yanzu Baba Mlm ya kira ni a waya, ya ce a gaya ma Ummi ta shirya ga mijinta nan ya zo, a shirya tarbarsa. Zuwan bazata dai yake yi Mubarak dai".

Murmurshi Hali ta saki ta ce.

"Ai Umma dama kamar taji a jikinta shine yazo, shi yasa ma nake gyara parlon nan gashi har na jera abinci ma da komai, ita kuma gata can tana shiryawa".

Ɗan murmurshi kaɗan Umma tayi tana ɗaga kanta kawai ta koma ɗakinta bata ce komai ba.

"Yawwa kin shiry...... Maganar Hali ce ta maƙe shigowarta ɗakin nasu ganin yadda Ummi ɗin tasa wani leshi ruwan fari da gwaldin, sai ta koma kamar wata amaryar da aka ɗaura ma aure a yanzu.

"Kai kai kai wai Allah na, Ummi wai kinga yadda kika koma kuwa?, kamar Amarya fa, anya bazaki ruɗa bawan Allahn nan ba kuwa?, kinga yadda kikai kyau?".

Murmurshi mai sauti Ummi ta sakar mata tana sake duba kanta a madubi itama kanta tasan tayi kyau ba ƙarya.

"Wai kin manta bani kaɗai ba ce?, kinga ko dole ne na zage nima na rinƙa ɗaukar hankalinsa".

Dariya Hali ta sheƙe da ita tana kaima Ummi dukan wasa tana cewa.

"Naga alamar kefa ƴar nan a shirye kike da wannan kishiya taki wacce ko haɗuwa baku taɓa yi ba, ke nifa har mantawa ma nake yi da wai bake kaɗai ba ce wallahi".

"Ai bana tunanin ma zamu haɗun Hali, saboda naga alamar kamar har zuwa yanzu basu san ya aure ni ba, akwai dai wata ƙullaliyar dake faruwa a cikin family nasu kawai, tunda auran zumunci ne aka masa da ita".

"Ohhh na fahimci hakan nima, to Allah dai ya zaunar daku lafiya amma kishiya dama bata da daɗi ko kaɗan".

Murmurshi kaɗan Ummi ta saki tana amsawa da amin kawai.

Suna haka wayar Ummin saƙo ya shigo mata, duk dama sunji alamar shigowarsa suna gaisawa da Umma, dan haka Hali ma fita tayi taje har parlon suka fara gaisawa, ta dawo tana santin wannan bawan Allahn ba dai iya ɗaukar wanka ba, duk kayan daya saka kyau suke masa.

"Kai Ummi na rantse da Allah dana gansa sai naga duk wankan da kikai ya dishashe wai kin gansa kuwa?, shima yasha fararen kaya kamar kun san abunda ɗan uwanku ke so?".

Murmurshi kawai Ummi ta saki dan ita haka kawai tasa kayan bata san dai kalar daya fi so bace, kawai dai ta karanci yana son baƙar kala sosai, to ƙila harda kalar farin ma yana so.

Ficewa tayi zuwa parlon da aka sauke shi, tana jin yadda ƙirjinta ke bugawa ji take kamar yau ne zata fara saka shi a idonta.

Tunda tayi sallama a parlon ya ɗago yana amsawa a can ƙasan maƙoshinsa, waya yake tayi tunda ya zauna, amma ganin tauraruwar tashi ta shigo ta haska gaba ɗaya parlon, bai san lokacin daya datse kiran ba.

Yana zuba mata gaba ɗaya idanuwansa masu matuƙar kwarjini da haifa a cikinsu.

Ummi a hankali ta shiga ɗagowa tana son kallonsa, kawai ɗagowar da zatai idonsu ya sarƙe dana juna, so take ta janye nata amma kamar yasa wani maganaɗisu ya hanata hakan.

Ummi wani irin duba take masa yadda yayi wani mahaukacin kyau mai ɗaukar hankali.

Sanye yake da wata ɗanyar shadda har wani maiƙo take, tayi ma farar matarsa kyau sosai, ya ɗan rame kaɗan saboda azumin da ba'a daɗe da gamasa ba, ramar ma tayi masa kyau, idonsa daya zuba mata cikinsu fari ƙar kamar an zuba madara, Sajen nan nasa kamar ƙara masa kyau ake saboda yanzu Ummi gani tayi ya ƙara yawa an gyara shi yadda kasan ɗora masa shi akai yadda ya wani zauna masa ya haɗe da gemunsa ya sake haska farar fuskarsa.

Kyan fuskarsa dana jikinsa da Allah ya zuba masa har wani fisgar mutum yake dan Ummi ji tayi tana neman zubewa a ƙasa saboda idanunsa idan suna yawo akanta ji take bata iya tsayuwa da ƙafafunta.

A hankali take takowa yanzu kanta a ƙasa so take ta samu waje ta zauna kota samu natsuwar zuciya yadda take bugawa a ƙirjinta ya hanata sukuni.

Batai aune taji sa a kusa da ita wannan ƙamshin nasa ya cika mata ƙofofin hanci har maƙoshinta take jin ƙamshin nasa na shiga, ta rasa wane mayen turare ne yake amfani dashi haka?, ga ƙamshi mai kwantar da hankalin mai shaƙarsa ga kama baida hawa kai kwata-kwata.

Ji tayi kawai ya ɗaga ta sama yayi kujera da ita bai sauke ta a ko ina ba sai akan cinyarsa bayan ya zauna. Wayyo Allah Ummi ta ruɗe ta rasa yadda zata yi ma, zuciyarta na faman duka a ƙirjinta kamar zata fito.

Zaro ido waje tayi bata san lokacin data kallesa ba a mugun shagwaɓe tana wani narke masa ta ce.

"Wayyo Hayatyyy ka sauke ni kar wani ya shigo fa"

Ta ƙare maganar tana taɓe bakinta, wadda hakan data yi yasa Mubarak ɗauke wuta, wani irin shegen Feeling yake ta so masa akanta, saboda tun kamin azumin nan ya wuce ya fahimci kamar ya samu lafiya, amma lafiyar tasa tafi aiki idan yana tare da wannan baiwar Allahn.

A hankali yasa hannunsa ya kamo ƙugunta yana sake matsowa da ita cikin jikinsa sosai, saura kaɗan fuskarsu ta haɗe waje ɗaya.

Ƙasa da kanta Ummi tayi tana jin wani irin baƙon yanayi wadda tunda take a duniya bata taɓa jin irinsa ba, ga wata shegiyar kunya data rufe ta, jikinta ya mutu murus tama kasa komai sai binsa kawai data keyi.

A hankali yasa hannunsa ya ɗago da fuskarta suna kallon juna, fuskarsa ya matso da ita sosai zuwa ga tata, hancinsu ne ya haɗe dana juna yana wani goga mata shi akan nata hancin. Lumshe ido tayi tana jin ƙirjinta na yin sama da ƙasa,

A hankali ya fara goga mata gashin gemunsa akan fuskarta, haba Ummi bata san lokacin data damƙe riƙesa ba sosai tana sake shigewa jikinsa itama.



16 / 27