Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 27

27K to 30K   out of 78K words

ma Tudun Wulli".

Ɗan taɓe baƙinta Hamda tayi ta ce.

"Na rasa gane Uncle Mubarak komai shi dai ƴan uwansa, baya jin wani abu ma kamar shi ace a rinƙa ganinsa irin Ƙauyukan nan, haba dan Allah".

______________________

Tun safiyar juma'ar da suka tashi daga Hamda har Mama kwacaniya kawai ake a cikin gidan, a ƴan kwankin nan gyaran jiki ciki da waje kawai Hamda ke sha, bata yawan zama a gidan, ita ce zuwa can sayo kaza ita ce zuwa can gyaran jiki, Mama kuwa sai dirka mata magungunan mata take, gidan cike yake da Kewayen Hamda da kuma wasu wadda Mama ke mutumci dasu a cikin garin Katsina, masu hannu da shuni ne duk wacce ka gani nan take zaka shaida naira da hutu sun zauna mata a jiki, Mama bata harka da ƴan tagajan-tagajan, shi yasa masu naira ne duk suka cika gidan, za'ai bikin gata.

A wajan Mubarak baya jin auran a kansa, domin a safiyar ranar tunda safe ya shirya yayi ma PA ɗinsa wayar cewa daga shi sai P'A ɗin zasu tafi zuwa Rimaye, baya buƙatar zuwa da kowa, Kawu Abu jin haka baiji komai tunda Mubarak ɗin ya ce masa a ɗaura auran nasa kawai tunda ga Kawu Abu nan ya barsa a matsayin waƙilinsu shida Hamda ɗin, dama kuma an bugo Invitation na biki, Mubarak bai turama kowa ba, amma duk da haka saida aka samu wa'inda suka taso tun daga wata uwa duniya suka zo, shi yasa abun ya basa mamaki, a hotel wasu suka sauka, PA shike kula da komai sai Kuma Kawu Abu da aka dawo masa da kula da komai na ɗaurin auran.

Daga shi sai P'A suka ɗauki hanyar zuwa Rimaye.

*Unguwar Yammawa Rimaye Kankia local government Katsina State Nigeria*

Ummi ce zaune tsakar gida ita kaɗai, gidan yayi shuru da alamar mutanan gidan basa nan, sai Ummi ita ɗaya, sai Baba Mlm dake zaune a waje yana ba Almajiransa karatu.

Jikinta a sanyaye take duk aikin, tun safiyar juma'ar yau ta tashi jikinta a sanyaye, saboda dama tun jiya data ci ƙaro da abunda ya kusa sama zuciyarta bugawa, status ɗin Usman taci ƙaro dashi na Invitation ɗin bikinsa, da kansa kuma ya ɗorasa bare ta ce a wajan wani ta gani, ko ƙarya ne, amma a wajansa ta gani kuma da kansa ya ɗora a status nasa, tayi mamaki ainun, tayi kuka kuma a daren jiyan kamar zata mutu, duk da tun lokacin da sukai waya yake sanar da ita wai tsohuwar budurwarsa ta dawo ta yanke kiran, tun lokacin bai sake nemanta ba, haka itama ta taushi zuciyarta bata sake kiransa ba, duk wani son kiransa da zuciyarta ke azalzalar yi da sun kasancewa tare da shi, da zafin da zuciyarta tata ke mata na rashinsa, amma haka ta daure ta cije har zuwa lokacin data ci ƙaro da Invitation ɗin bikinsa daya ɗora, tunda ta gani tayi kuka kamar ba gobe, haka kawai taji wata irin tsanar Usman ta rufe mata zuciya, nan take tayi blocked ɗinsa a WhastApp ta je ta goge numbersa kuma.

Baba Mlm ne ya shigo gidan da sauri, hakan yasa ta katse tunanin data lula tana dubansa ganin duk a ruɗe ya shigo yasa Ummi miƙewa a ɗan mamakance take kallon Baba Mlm ɗin ta ce.

"Baba Mlm lafiya na ganka a haka?".

"Lafiya lau Ummi na, wallahi wani baƙo nayi ne wadda muka daɗe rabon da mu haɗu, yana can na ajesa shagon dake waje, kin san na gyara wajen ya koma kamar parlon tarbar baƙi dama saboda irin haka. To na shigo ne duk na rasa mima ya kamata na fara tarbarsa dashi wallahi, zuwan bazata yayi min shi yasa".

Ummi da jin haka tasan baƙon yana da mahimmanci a wajan Baba Mlm ɗin, dan haka da sauri Ummi ta ce.

"Baba Mlm ba matsala bari yanzu na ɗora sanwa, bazan jima ba zan gama, akwai lemoka a cikin firizar Umma ka ɗauka idan ta dawo sai na gaya mata ko kai kayi mata bayani".

Da to kawai ya amsa Ummi ta shiga kitchen ta ɗakko filet guda biyu taje ɗakin Umma ta ɗebo lemoka da ruwa na roba da Umma ke yawan ajewa, ta kawo ma Baba Mlm ya amsa yana ficewa domin zuwa ya kai ma su.

Yana fita ita kuma ta ƙarasa kitchen ɗin, da yake akwai komai ta fara ɗora sanwa, haka nan kawai ta samu kanta da fere doya, ta fara dafata, sai da ta dahu sosai ta juye ta turmi ta dakata sosai tayi danƙo ta luliyata a cikin leda, (sakwara) tayi kuma ba karamin kyau tayi ba a ido, tana gamawa ta sake ɗora miyar agusi wacce tasa ganda da naman Kaji da bushashshan Kifi, dandanan gidan ya buɗe da ƙamshin girki, dama Ummi gwana ce ta ɓangaran girki.

Bata daɗe da gamawa ba, saiga Baba Mlm ya sake shigowa gidan, ganin ta gama komai ta juye a kula, ga farantai duk aje yasa Baba Mlm ɗin sakin murmurshi yana sa mata albarka yana cewa.

"Gaskiya kinyi sauri, mi kika dafa ne haka?".

Murmurshi ta saki ta ce.

"Baba Mlm Sakwara nayi da Miyar agusi".

"Kai Masha Allahu, ai ko kamar kin san abunda Mubarak yafi so kenan a cikin abinci, amma gaskiya na gode miki Allah yayi miki albarka Ummi na".

Da amin ta amsa tana jin sunan daya kira Mubarak, har bata san ta mai-maita sunan nasa a saman laɓɓanta ba.

Baba Mlm da kansa ya ɗauki abincin, Ummi ta so ɗauka ta kai ya hanata, yana fita kuma Musa Almajiri ya amsa yana kamama Baba Mlm ɗin suka shigar da abincin inda su Mubarak suke zaune.

"Haba Baba Mlm yanzu sai da na saka aiki da ɗawainiya haka?".

Zama Baba Mlm yayi yana murmurshi ya ce.



"Ba wata ɗawainiya fa wallahi, yaushe rabon dana ganka bare nayi maka haka?, ai wallahi banma yi komai ba, dan ban san da zuwanka bane ai".

Murmurshi kawai Mubarak yayi yasan Baba Mlm ɗin zaiyi abunda yafi hakan ma, saboda yana da matuƙar kirki sosai fiye da zaton mai tunani.

Sosai ko Mubarak yaji daɗin abincin yana satin waye haka yayi girkin nan mai daɗi haka?.

Baba Mlm yana murmurshi ya ce.

"Ummi ce wacce tun lokacin daka bar Ƙasar nan ba'a daɗe da haihuwarta ba".

Mubarak nashan ruwa ya aje yana duban Baba Mlm ɗin ya ce.

"Wai Allah sarki Ummi ai bana nan ma aka haife ta Baba Mlm".

Baba Mlm ya kalli PA ɗin Mubarak ganin ya gama cin nasa abincin. Mubarak ganin Baba Mlm yabi PA da kallo yasan yana son basu waje ne su tattauna, ƙila akwai abunda yake son sanar dashi wadda daga shi sai shi ne yake son yin maganar.

Mubarak ya dubi P'A ya ce.

"PA Please ɗan bamu waje zan gana da Baba Mlm".

Cike da girmamawa PA ya amsa yana ficewa daga shagon.

Baba Mlm ya sauke lumfashi yana duban Abokin nasa lokaci ɗaya fuskarsa ta canza daga fara'a zuwa ta ban tausayi.

Hankali a ɗan tashe Mubarak ya sakko ƙasa kusa da Baba Mlm yana kamo hannunsa ya ce.

"Abokina mi yake faruwa ne?".

Baba Mlm ya sake sauke lumfashi kamin ya ce.

"Ummin da nake gaya maka kasan Mahaifiyarta ta rasu tun lokacin data zo duniya, nasan kasan irin yadda na auri Mahaifiyarta Uwar gida na bata sani ba, hakan yasa har gobe take ganin na cutar da ita, shi yasa har abun ya shafi ita Ummi, kwata-kwata Ummi bata da mai jawota a jiki, ita kaɗai take rayuwa a cikin gidan nan, sai kuma ni idan na samu lokaci zan zauna da ita naji damuwarta, Ummi ni kaɗai ta sani a matsayin uwa da uba, ta taso cikin ƙuncin rashin uwa. Na so na bawa Ummi ilimi mai zurfi na boko, sai dai kashh karayar arziƙi ce ta same ni, wadda hakan yasa komai nawa tsayawa, harta kai ta kawo mai ɗakina uwar gida na, ita ce ke iya ciyar da gidan nan, sai idan naje karatu wani wajen ko wa'azi nake ɗan samun abunda zan kawo gida na, ita uwar gidan tawa tunda Ummi ta gama secondary school ta ce bazata iya ɗaukar nauyin karatun ta na gaba ba, ciyar da mu ma da take kaɗai ya isheta, na mata uzuri tunda bata taɓa Cutar min da Ummi ba, rashin sakewar da take da ita ne kawai. To a nan dai Kanwar Ummi Halima mai bi mata, ta samu miji bayan sallah za'ai bikin, shine ta ce na samo ma Ummi miji ko cikin almajire na ne, domin bazata iya zama da Ummi ba idan har Halima tayi aure, gara kawai kowaccen su ta tafi ɗakin mijinta komai ya wuce. Mubarak bazan ɓoye maka ba, bazan iya ba kowa auran Ummi ba, zuciyata kai tsaye ta kawo min kai, nasan har yanzu ba kai aure ba, shi yasa kawai na yanke cewar zan baka Ummi, nasan baza taɓa ƙin jini na ba Mubarak".

Tunda Baba Mlm ya fara bashi labarin irin matsalolin daya rinƙa fuskanta a rayuwa bayan barinsa ƙasar, kai tsaye ya ɗora ma kansa laifin mi yasa bai mai da hankalinsa sosai ba wajan kula da zumuncin su da Baba Mlm ɗin?, kawai ya sakankance da su Kawu Abu suna kula da Baba Mlm ɗin, ashe ba haka bane, sai gashi suna zuwa Rimayen suka tabbaya aka nuna masu gidan Baba Mlm ɗin da dai shine ya sani tun asali bai wani sake gida ba, bare har ya tashi daga garin.

Cike da wata irin kunyar Baba Mlm ɗin Mubarak yayi ƙasa da kansa ya ce.

"Baba Mlm kayi hakuri, haƙiƙa nayi kuskuren barin komai a wajan su Kawu Abu, wallahi duk watan duniya sai nayi aike da kayan abinci haɗe da kuɗi masu yawa domin a kawo maka, ashe saƙon da nake bayarwa kwata-kwata baya ƙarasowa inda kike ma, haƙiƙa laifina ne, ace kana da kamar ni har ka shiga halin karayar arziƙi ban sani ba?, miye anfanin dukiyar tawa to idan ban taimaki na kusa dani ba?, gaskiya nayi takaicin kai wallahi".

Baba Mlm yayi saurin girgiza kansa yana cewa.

"Ko kaɗan banji haushinka ba Mubarak, nasan tabbas dama akwai abunda ya hanaka zuwa inda nake, nasan abubuwa sun maka yawa a can ɗin, ai ba wai yawan shaƙatawa kaje yi ba, aiki ne ya kaika ƙasar waje, karka wani damu wallahi kaji?".

Girgiza kansa Mubarak yayi yana jin cewa babu abunda Baba Mlm gidan duniya zai roƙe shi ya kasa masa shi, kai tsaye ya ce.

"Baba Mlm idan har auran Ummi shine zai zaka ka farin ciki, to na amince, na amince a yau ɗin nan da an sallamo daga sallar masallaci a ɗaura auranmu da ita. Amma fa Baba Mlm yanzu haka a can gida Katsina ma Mama ta haɗani aure da Hamda, nasan zaka santa".

"Mubarak daka bari tukunna dai, ai kamar yayi sauri da yawa, tunda yau za'a ɗaura auranka da wata, ka bari idan aka kwana biyu sai ayi da Ummi ɗin".

Girgiza kansa Mubarak yayi ya ce.

"A'a Abokina ba za'ai haka ba, yau nake so a ɗaura, idan ya so zan zo daga baya na ɗauki Matata, bana so yanzu dai su Mama su sani, saboda mutanen nan da kake gani Baba Mlm sai a hankali babu abunda baza su iyayi ba, duk da suna ƴan uwana na jini, sun cika son kansu da yawa, shi yasa gara a ɗaura kawai hankalinka sai yafi kwanciya, kuma zan goge laifin da nake ganin nayi maka, na rashin zuwa inda kake har tsawon shekarun nan, da rashin saka ido hakan abubuwan daya shafi rayuwar abokina wadda muka taso tun yarinta".

Wasu irin hawayen daɗi ne su cika idon Baba Mlm, bai iya cewa komai ba saboda bai taɓa tunanin Mubarak ɗin zai amince a ɗaura nan take ba.

Kamar yadda ya ce masallacin dake kusa da gidan Baba Mlm dake bayan gidan, ana sallame sallar juma'a mutane da yawa sun cika da ɗunbin mamakin jin shelar ɗaurin auran ɗiyar Baba Mlm ɗin, ana gama ɗaurin auran Kawu Abu ya kira shi yana shaida masa suma yanzu aka ɗaura auransa da Hamda.

Wani irin abu yaji ya tsaya masa a zuciya, tunda aka sanar da ɗaurin auransa da Ummi yaji wani irin sanyi na shigar masa jiki, wata irin natsuwa mai daɗi na rufesa, sai ga kiran Hamda ma ta zama Matarsa, bazai iya cewa ga abunda yaji ba daya ji hakan. Lokacin ɗaya wai yau shine da aure har mata biyu?, Allah kenan bai taɓa kawo haka a ransa ba, shi kansa PA ɗinsa ya cika da mamaki kware da gaske, amma yana taya Ogan nasa murnar samun mata har biyu, bare ma jinin Baba Mlm, sosai yayi masa murnar haɗa jini da babban abokinsa kamar Baba Mlm ɗin. Dama ance wani jinkiran auran alkhairi ne, gashi dai lokaci ɗaya ya sami Mata masu nagarta har guda biyu...........

*Washhhh Allah jama'a na gaji fa hannuna🤧🤣. A nan na kawo karshen Free pages masoya. Akwai daru fa a cikin wanga book. Tabɗi jam, jama'a Mubarak da aure har mata biyu, kai yaya Hamda zata yi idan ta sami labari wai?, Mama yaya zata ji idan taji cewa ba ɗiyarta kaɗai ɓace Mubarak ɗin ya aura a rana ɗaya?. Kai wai tsaya ma ina labarin Habiba yake ne?, shin itama zata auri Abba ne kuwa?, miye abunda zai faru idan Mubarak yaje garin da Habiba take ne?, mi yasa Mama taji bata ƙaunar zuwan Mubarak Tudun Wulli?, tabbas akwai fa abunda zai faru, tunda har Hamda taji bata son zuwansa Rimaye, ashe baiwar Allah kishiyarta ce acan🤧🤭*.

*To duka-duka a nan zamu dakata, nima fa ina buƙatar sanin yadda zata kaya fa. Karka bari ayi tafiyar nan babu kai wallo domin akwai kallo fa*

Idan ka shirya biya ga account number nan a ƙasa.

👇



8130479973 Fatima Rabiu Opay bank

Saika turo shaidar biya ta wannan number ɗin👇

08130479973

11

Sadda su Umma suka dawo yanayin wajan gidan Baba Mlm da yawan jama'ar dake ta miƙe masa hannu suna masa Allah yasa alkhairi, abun yaso ɗaure ma Umma kai.

Koda suka ƙarasa cikin gidan ganin Ummi zaune tayi jigum da ita, dan itama tunda aka sallamo sallar juma'ar kamar tasan abunda ke faruwa haka kawai jikinta yayi sanyi haɗe da ƴar faɗuwar gaba, wacce motsawa kaɗan sai taji ta.

Hali ce ta aje jakar dake hannunta ta kalli Ummi tana faɗin.

"Ummi Baba Mlm baƙi yayi ne?".

Ummi tabi Umma da kallo ganin ita tayi saurin shigewa ɗaki ta barsu.

"Eh baƙi yayi wai wani abokinsa Mubarak tun na yarinta ne yau ya zo".

"Kai wai Uncle Mubarak Khabeer ƙankara?, ai na sanshi nasan maganarsa a wajan mutane da dama, sai kuma Baba Mlm ɗin da ya taɓa kiran sunansa a gidan nan, ashe da gaske dai abokai ne?, Allah sarki".

Hali ta ƙare maganar cike da mamaki.

Ummi ko kallonta take, dan ita bata wani san waye shi ɗin ba.

Umma dake cikin ɗaki a parlo tana iya jiyo hirar da suke, haka kawai tunda taji Mubarak ɗin yazo Rimaye tabbas akwai muhimmin wani abu da ya faru a yau ɗin tafiyarsu, amma ko ma dai miye bari Baba Mlm ɗin ya shigo zasuji abunda yasa aketa masa Allah yasa alkhairi da iyayen mutanen da aka tara a kofar gidan.

Sai wajan dare tukunna Baba Mlm ya shigo gidan, domin su Mubarak ana gama ɗaurin aure suka juya suka koma Katsina, ya su ganawa da Ummi, amma ya ce dole ya koma da wuri dan kar ma su Mama suyi zargin wani abu can daban.

Yana shigowa gidan yasa Almajiransa su rinƙa shigo da kayan da Mubarak ɗin ya lodo masa na kayan masarufi, yadda kasan wani ɗan ƙaramin shigo, harda su lemoka kayan lambu ne duk gasu nan, gashi ya cika sa da kuɗi masu tarin yawa yaja jari, wadda kuɗin daya narka masa sunfi ƙarfin jan wani jari, ai kawai sana'a ce zai fara gadan-gadan, sai kuma kuɗin Sadakin Ummi dubu ɗari uku daya damƙa shi a hannun Baba Mlm ɗin domin aba Ummin.

Hali da Ummi dake ɗaki jin hayaniyar Almajiran Baba Mlm suna shigowa su koma su sake shigowa yasa su fitowa suna kallon uban kayan abincin da aketa shigowa dasu wadda sunƙi ƙarewa ma.

Umma najin komai kuma tana kallon komai ta window ɗin parlon amma bata miƙe ba bare taje tsakar gidan.

Sai da aka gama shigowa da kayan Baba Mlm ya umarci su Ummi su shiga dasu kitchen inda ake aje kayan abinci, tare da Hali suka rinƙa jidar kayan suna kaiwa har suka gama.

Bayan sun koma ɗaki wayar Hali tayi ƙara, ganin sunan Umma ne yasa ta ɗauka da sauri.

"Ku zo ke da Ummi Baba Mlm na san ganinku".

Daga haka ta yanke kiran.

Hali ta waiga inda Ummi take kwance akan katifarta, amma haka nan yau ɗin take jin idonta ya bushe bama tajin wani bacci, sana motsi kaɗan sai taji zuciyarta ta buga, har sai ta dafe saitin zuciyar tata, tana mamakin abunda ya kawo mata hakan, ga wani irin nauyi da take ji a ƙirjinta.

"Ummi ki ta so Baba Mlm na son ganinmu a parlon Umma".

Ummi ta tsinkayi muryar Halima na faɗin haka.

A hankali ta miƙe tana jan ƙafafunta, suna tunkarar parlon gabanta na tsananta faɗuwa, jinin jikinta na gudu

10 / 27