Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
duk abubuwan dana ke so na sani ka gano min?".
"Ranki ya daɗe tabbas na gano, amma fa da kyar saboda P'A nasa kamar ya gano ina bibiyar Ƴallaɓai Mubarak hakan yasa koda yaushe yana bibiyata nima, shi yasa ni kuma na sake taku na rinƙa shigar mahaukata har na kauda hankalinsa daga gare ni, a haka har na ci nasarar gano inda Ƴallaɓai ke zuwa yana kwana, akwai wani gidansa dake Ƙofar Sauri shima tabbas yana kwana biyu a cikinsa, amma ban iya gano abunda yasa shi zuwa gidan yana kwana ba. Na daɗe ina bibiyarsa daga baya kuma sai naga can ɗin ma sai idan ya kwana biyu baya sake dawowa sai kwana huɗu, na rinƙa bibiyarsa saina gano sai yaje gidanki yayi kwana biyu kamin ya wuce wani gidan Shaƙatawarsa shima yayi kwana biyu, ranki ya daɗe abun ni kaina ya ɗaure min kai fa, ace sai kace wadda ya aje Matansa a cikin gidanjan idan ba haka ba mi zaisa ya rinƙa kwanaki biyu-biyu a kowanne gida?"..
Runtse idonta Hamda tayi da mugun sauri zuciyarta na zalle a ƙirjinta, wata irin muguwar fargaba da bugawar zuciya suka rufeta lokaci ɗaya da kyar ta iya buɗe baki tsabar tashin hankali da yadda zuciyarta ke wata irin buguwa a ƙirjinta sosai ta ce.
"Ya isheka haka Dauda, bana son ƙara jin komai zuciyata zafi take, aiki ya ƙare naka daga yau zan turo maka kuɗinka, sauran aikin ka barsa a hannuna zan san abunda zanyi".
Tana ƙare faɗar haka ta datse kiran a fusace tana dafe ƙirjinta, wani irin jiri-jiri ta fara gani da sauri ta dafa kujerar dake kusa da ita ta koma a hankali ta zauna, tana jin tashin hankali sosai na sake rufeta, wani irin zargi zuciyarta ke kawo mata da sauri ta girgiza kanta kamar kadangaruwa tana magana a fili.
"Inahhhh wallahi bazai taɓa yuwu ba, Uncle Mubarak bazai taɓa haka ba na sani, yayama za'ai hakan ta kasance? Kai bazan taɓa ɗaukar hakan ba, ba gaskiya bane kawai".
Kamar wacce ta zare haka take maganar, kamar wacce take magana da wani mutum a kusa da ita.
Sake miƙewa tayi a hanzarce ta ɗauki wayarta har hannunta na rawa ta danna number Mama bugu ɗaya ta ɗauka.
Tana ɗaukar wayar kawai Hamda ta sakar ma Mamar kuka, tsabar yadda zuciyarta taƙi yarda da abunda wata zuciyarta tata ke sake kitsa mata, ga wani irin tashin hankali daya rufe mata dukkanin wani jinta da ganinta.
"Innalillahi ke Hamda wani ne ya mutu ne?".
Cikin muryar kuka Hamda ta ce.
"Mama dama wanin ne ya mutu ai da sauƙi da irin tashin hankalin da nake ciki a yanzu, Mama na shiga uku na idan har abunda zuciyata take zargi ne Uncle Mubarak yaje ya aikata min".
"Ke kinfa sani cikin duhu da kuma tashin hankali nima da kokwanto, mi yake faruwa ne ina jinki faɗa min?".
"Mama kin san na gaya miki nasa a rinƙa bibiyar Uncle Mubarak duk inda yake, kin san da baya kwana biyu a gidan nan, ban san inda yake zuwa yayi su ba, sai ma daga baya yazo har kwana huɗu bana saka shi a ido na, abun ya fara taɓa ni haɗe da tashin hankali, shine wadda nasa yake bibiyar tasa ya gano kamar P'A nasa yasan akwai mai bibiyar Ogansa, sai yabi duk wata hanya da zaisa ya gano wani abu ya toshe ta, da yake nayi masa alƙawarin kuɗi masu yawa, bai yi ƙasa a gwaiwa ba wajan sake tako shima, sai rinƙa shigar mahaukata yana bibiyar Uncle Mubarak ɗin, Mama abunda ya gano zaisa zuciyata ta buga wallahi".
"Wai Hamda dan ubanki har yanzu fa baki idasa sanar dani abunda ya gano ɗin ba, zaki gaya min ne ko nima sai kin sa hawan jini na ya hau ne?".
Mama ta ƙare maganar a tsawace itama tana jin yadda gabanta yake faɗuwa.
Hamda ta wani ja majina a hanci tana kuka ta sake faɗin.
"Mama ce min yayi wai gidansa dake Ƙofar Sauri a can yake kwanaki biyun, daga baya sai ya ƙara fahimtar idan ya kwana biyu yana sake zuwa gida na yayi kwana biyu sai kuma yaje gidan Shaƙatawarsa shima yayi kwana biyu. Dan Allah Mama idan ba Matansa ya aje a cikin gidajan ba mi zaisa ya rinƙa raba kwanaki har biyu-biyu, Mama na bani na shiga uku".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, kai kaiiiiiii yaya za'ai hakan ta faru Hamda?, kai mtsww gaskiya ban yarda ba, bazan kuma taɓa yarda ba, ki ma daina saka hakan a cikin tunaninki, ya ma wai za'ai Mubarak yaje yayi wani auran ban sani ba?, ina a matsayin uwarsa a yanzu".
"Mama yau-yau ɗin nan zanje gidajan nasa wallahi Mama sai naga uwar mi ya aje a ciki da har zai rinƙa raba kwanaki a can".
"Bari yanzu zansa driver yazo ya kawo ni gidan naki daga nan ya wuce damu gidajan nasa, bari yanzu zamu iso".
Au ko ba'a daɗe ba su Mamar suka karaso tunda dama unguwa ɗaya suke tazarar kaɗan ce a tsakaninsu dama.
Jikinsu na rawa suka shiga Motar bayan Mama ɗin ta shiga gidan Hamda ɗin ta fito da ita.
Tunda suka ɗauki hanya suka gaya ma driver inda zai kaisu kowanne zuciyarsa cike da tsananin tashin hankali na gaske, sunyi shuru zuwa can Mama ta ce.
"Kina ganin mu fara zuwan Ƙofar Saurin yayi".
"Mama can nake so muje kawai ɗayan koma minene shima dole yau dai asiri zai tonu".
Shuru kawai Mama tayi tana sake jin tashin hankali na sake rufeta.
Dai-dai ƙofar get ɗin gidan suka ba driver umarnin yayi parking ɗin Motar, su kuma suka fito suna kallon uban gidan da haɗuwarsa, duk dai kusan gidan da Hamda ɗin take kusan kyansu ɗaya kamar ma ginin na kama da juna.
Tunda suka tunkari ƙofar get ɗin gidan zuciyarsu ke sake buguwa da ƙarfi, jan ƙafa kawai suke tashin hankali kwance akan fuskokinsu.
Mai gadi ganin baƙin fuska ganin kuma ƴan gayu ne sai ya ɗauka ko bakin matar gidan ne dan haka kai tsaye ba tare da tunanin komai ba ya buɗe masu get suka shige gidan.
Ƙofar babban parlo suka tsaya ƙofar shiga cikin gidan suna ɗan bubbugawa.
Jim kaɗan Ummi dake zaune daga ita sai wata dogowar riga bata kai mata ƙasa sosai ba saboda tasha iska ta sata cikinta da ya girma sosai ya sakata ya wala saboda duk yawanci kayanta sunyi nata kaɗan saboda cikin yasa ta ɗanyi ƙiba ba laifi.
A hankali taje bakin ƙofar tana tafiya tana kallon cikinta hannunta ɗaya na akan cikin, kawai ta sami kanta da buɗe ƙofar.
Gabanta ya yanke ya faɗi ganin baƙin fuska, ta so ta gane Hamda saboda wata rana sau ɗaya Mubarak ɗin ya taɓa nuna mata photonta amma bata wani tsaya ta ƙare mata kallo ba a lokacin, Mama ko bata ma santa ba a fuskar, dan haka ta ture tunanin komai tana sake kallonsu zatai magana taji Hamda na nunata da yatsa tana faɗin.
"Mama kinga mi nake gani kuwa?, Mace ce fa ɗauke da ciki a cikin gidan Uncle Mubarak".
"Shittttt muje ciki".
Faɗin Mama wani abu na taso Mata.
Matsa masu Ummi tayi ta kasa gane maganar da Hamda ɗin ke faɗi, duk da jikinta ya bata wa'innan bayin Allah ba alkhairi ya kawo su ba.
Ciki suka shiga zuciyoyinsu na wani irin soya sosai suna ƙarema gidan kallo ga wani ƙamshin daɗi da gidan keyi ko ina tsaf-tsaf dashi gwanin sha'awa.
Hamda zuciyarta har zuwa yanzu bugawa take da ƙarfi ta fuskanci Ummi data tsaya a bayansu tana jin wata faɗuwar gaba haka kawai.
"Mama ki ce wani abu mana, Mama wallahi zuciyata bugawa zatai na mutu kawai".
Wayar dake hannun Ummi haka kawai ta danna number Mubarak dan magana ta biyu da Hamda ɗin tayi ta gano tabbas ita ce Hamda kishiyarta, tashin hankalin abunda zai iya biyo baya da irin abunda zasuyi Mata yasa ta danna kiran.
Hamda gadan-gadan idonta ya rufe ta matsa kusa da Ummi tana zuwa batai wata-wata ba ta kamo gashin kan Ummi da ƙarfi tayi baya da kayan tana zare mata ido haɗe da cewa.
"Ke ƴar iska Karuwa ki faɗa min ubanda kike a cikin gidan miji na?, waye ya baki lasisin zama a cikin gidan miji na?. Wai tsaya ma cikin nan na uban waye?".
Hamda ta faɗa cikin fitar yacci dan nema take ta haukace masu.
Ummi wata zufa ce ta keto mata a jiki, Yaron cikinta ne ya motsa tana dafe cikin nata ta runtse idonta da ƙarfi.
Ganin tayi shuru kawai hamda ta jawota ƙiiiiiiii dai-dai wani table dake tsakiyar parlon tana zuwa ta buga kan Ummi a saman table ɗin, nan take table ɗin ya fashe haɗe da goshin Ummi daya fashe ya fara zubar da jini, wata irin ƙarar azaba Ummi ta saki wacce bata fita sosai saboda yadda ta shake mata wuya a yanzu tana sake zare ido tana cewa.
"Na rantse da tsarkin mulkin Allah idan har baki yi magana ba yau ni ce zan zama ajalinki shegiya munafuka Karuwar banza kawai".
Mama tana kallon komai bata motsa ba dan itama so take kawai Ummin ta ce wani abu ko sun tabbatar da zarginsu, duk da tuni zuciyarsu ta gama hasaso masu wannan ɗin da suke gani kamar matar Mubarak ɗin ce, amma sunƙi yarda da hakan saboda idan suka ce zasu yarda da hakan zuciyarsu na iya daina aiki a nan take.
Ummi na jan lumfashin azaba bata da niyar magana domin bata san ma miye zata ce masu ba.
Hamda iya ƙarfin ta ɗaga hannunta ta ɗauke Ummi da wani kyakkyawan mari mai ƙarfin gaske.
Da wani irin sauri Ummi ta runtse idonta tana sakin ƙara hawaye suka shiga bin fuskarta tana sake jin yadda Yaron cikinta ke harbin mararta yana wani irin juyi a cikin cikin nata, wata zufa ce ta sake keto mata kota ina a jikinta.
*Mubarak Pov*
Tunda Ummi ta danna masa kira ya ɗauki wayar kuma duk yana jin abunda ke faruwa.
Hankalinsa a mugun-mugun tashe ya baro Office ɗinsa, yadda P'A nasa yaga Ogan nasa ya fita ya hau Mota a haukace yaja Motar ita kanta, yadda yake faska gudu da Motar yasa P'A ɗin shima hawan tashi motar yana bin bayansa.
Sosai ya cika da mamakin irin uban gudun da Mubarak ɗin keyi akan titi ikon Allah ne kawai ya kaishi gidansa dake Ƙofar Sauri.
Bai bari Mai gadi ya buɗe masa get ɗin ba kawai ya ture mai gadin daya buɗe ƙaramar ƙofar get ɗin ya shige gidan a hanzarce yana jin tashin hankali na rufesa abu ɗaya yake gudu karsu Hamda da Mama su cutar masa da Mata tana ɗauke da ciki.
P'A ma daya saka daga Motarsa yayi parking nata a kusa data Ogan nasa, Yadda ma yayi parking ɗin Motar kaɗai zaka san akwai babbar matsala kwata-kwata baya cikin natsuwarsa ma.
"Ranka ya daɗe Oga lafiya na gansa a ruɗe haka?".
Faɗin mai gadi yana sake duban cikin gidan.
P'A yana idasa shigowa cikin gidan ya kalli Mai gadi ya ce.
"Akwai wa'inda suka zo gidan nan ne?".
"Kware kuwa ranka ya daɗe basu ma daɗe da zuwa ba ai".
Runtse idonsa yayi kai tsaye ransa ya basa su Hamda ne wallahi, dama yasan da wuya idan Hamda zata bari bata haka kawai bata gano inda Ogansa yake zuwa ba, tunda ta fara zargin akwai wani abu dama yasan rana irinta yau sai ta zo ne. Ya dubi Mai gadin ya ce.
"Mi yasa ka buɗe masu gidan kai tsaye ba kai wani bincike ba?, ka taɓa ganin wani daga wani waje ya zo gidan nan ne?".
Jikin Mai gadi ne ya soma rawa jin yadda P'A ɗin yayi maganar a tsawace.
"Ranka ya daɗe kayi hakuri, amma ni wallahi gani nayi suma ƴan gayu ne kamar dai Madam ɗin gidan nan, shine ma yasa ya na buɗe masu ƙofar kai tsaye suka shigo gidan".
Wani dogon tsaki P'A ya saki yana harɗe hannuwansa a ƙirjinsa yana sake kallon ƙofar parlon yadda Mubarak ɗin ya barta buɗe. Bazai shiga parlon ba dan bai san halin da zai iske su ba ya tsaya nan ne dai gaya abunda zai faru.
A wajan Mubarak ko yana banga ƙofar parlon idonsa suka hasko masa yadda Hamda ta damƙe gashi kan Ummi tana shirin sake ɗauke Ummi da wani marin banda wadda ta sharara mata ɗazo kamin shigowarsa.
Ai bai san lokacin daya idasa kawowa inda suke ba, yana zuwa ya saka hannunsa ya riƙe hannun Hamda bai tsaya wata-wata ba wajan ɗauke Hamda da wani gigitaccan mari ba, yana fisge Ummi daga hannun Hamda ɗin.
A ruɗe yake taɓa fuskar Ummi ganin yadda take lumshe ido tana neman zubewa a jikinsa a sume yana faɗin.
"Hayatyyy Hayatyyy please ki buɗe idonki gani a kusa dake, ba abunda zai same ki Hayatyyy Please gani a kusa kinji".
Haka kawai yake faɗa a ruɗe kamar wadda ya zare.
Wani irin ja da baya Hamda tayi tana jin kanta na juya mata nuna su take da yatsa tana sake waigo Mama data riga tayi suman tsaye ido waje take kallon Mubarak riƙe da wata a matsayin Matarsa da kuma ciki dake jikinta, ba makawa nashi ne kenan?.
Da kyar Hamda take jan lumfashinta da take kokowa dashi yana neman ɗaukewa daga gangar jikinta.
Baki na kyarma take faɗin.
"Mi naji kana faɗi Hayatyyy fa naji ka ce?, wacece wannan ɗin a wajanka Uncle?".
Kallonta yayi ransa a mugun ɓace ya nunata da yatsa yana cewa.
"Kiyi min shuru Hamda, kuma ita ɗin Matata ce sai akai yaya?".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Mubarak ka kalli tsabar ido na kake faɗin wannan shegiyar Ƙaruwar Matarka ce?".
Faɗin Mama a tsawace zuciyarta na dukan kirjinta.
Hamda ko basu lura ba tunda ya buɗe baki ya ce wannan Matar matarce gashi da take ganinta da ciki kenan ma har cikin nasa ne?, Hamda tayi baya-baya kawai sai karar faɗuwarta suka ji, ta faɗi ta sume a wajan.
Wata irin ƙara Mama ta saki tana faɗin shikenan Mubarak zai kashe mata Ɗiya.
Mubarak duk ya ruɗe ga Ummi itama data idasa sumewa a jikinsa dan haka da mugun sauri ya ƙinƙinme ta sai waje ko Hijab baya jin zai iya wani ɗakkowa bare ya saka mata.
P'A a ruɗe shima ya nufi inda Ogansa yake ganin yadda ya fito da Ummi a hannunsa kamar wacce babu rai a tare da ita.
Da sauri ya fito da ita inda yayi parking ɗin Motarsa a waje, da sauti P'A ya shiga wajan driver shima kuma Mubarak ya shige baya da ita suka ja suka bar wajan.
Mai gadi da drivern su Hamda dai zare ido suke yana tabbayar kansu lafiya kuwa?.
Mama ce ta ɗakko Hamada da kyar ta fito da ita rungume tana tsine ma Ummi da Mubarak ɗin kansa wai zasu kashe mata Ɗiya babu gaira babu dalili.
Sai da ta danƙarama Mai gadi zagi kamin ya buɗe mata get ta fice da Hamda riƙe da ita a jikinta drivernsu a ruɗe shima ya buɗe gidan baya Mama ta saka Hamda kamin ta shiga tana basa Umurnin yabi bayan su Mubarak asibitin da duk zasu je can suma zasu je, yau-yau sai ya zaɓi ko ƴar iskar matar da ya ke ikirarin Matarsa ce ko kuma su.
Da yake asibitin anyi masa farin sani yana isa aka amshe Ummi da sauri aka shiga bata taimakon gaggawa.
Sai zarya yake da kyar P'A ya riƙesa ya zaunar dashi, amma yana zama ya sake tashi kamar wadda aka tsikara yana sake zarya a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga Ummi domin duba lafiyar ta.
Lokacin da su Mama suka shigo asibitin suma aka amshe su aka shiga da Hamda ɗakin duba marassa lafiya itama. Tana kallon su Mubarak ɗin amma ko inda take da drivernsu tsaye bai kalla ba.
Mama baƙin ciki duk ya gama kasheta. Wato tata Ƴar ta mutu ma kenan ko a jikinsa?, tashi Matar da yake kira Matarsa ta rayuwa kowa ma ya mutu.
Girgiza kanta kawai take tana ayyana irin tashin hankalin da za'a sake shiga bayan farkawarsu Hamda ɗin.
*Bayan awa biyar*
Tsaye yake bakin gadon da aka kwantar da Ummi riƙe da hannunsa a cikin nata, ta farka tana kallonsa ɗayan hannunsa kuma na akan cikinta da yake jin motsinsa alamar yana cikin ƙoshin lafiya.
Hawaye ne Ummi suka shigo bi mata gefen fuska, da wani irin sauri ya girgiza mata kai alamar ta daina baya so.
Ba alamar zata bari dan haka ya rankwafa yana saka harshensa yana ɗauke mata su, da sauri ta lumshe idonta tasa hannunta akan wuyansa.
Suna cikin haka kamar an jefo su Mama da Hamda da bata daɗe da farkawa ba, ta tasa Mama tana rusa mata kuka ita saita kaita inda aka kwantar da ƴar iskar matarsa ko kuma ta haɗiyi zuciyata ta mutu, a kaita ya zaɓa ko Matarsa ko kuma ita, yadda suka banko ƙofar yasa Ummi ƴar firgita tana zare jikinta daga roƙon da Mubarak yayi mata, shi ko duk da yaji shigowarsu kuma yasan babu mai masu hakan sai su ɗin tunda yasan suna cikin asibitin, bai fasa abunda yake yi ma Ummi ba, hasalima sai ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya shiga kiss ɗin bakin Ummi ɗin da gangan.
Zan iya cewa saura kaɗan Hamda ta sake zubewa ta suma da kyar Mama ta riƙeta a jikinta, sai kawai Hamda ta saki kuka mai cin rai, Mama tsabar baƙin ciki ta buɗe baki ta ce.
"Yau Mubarak ka nuna min ba ni ce asalin wacce ta haife ka ba".
Sakin Ummi yayi yana kallonsu idonsa sunyi jawur na ɓacin ran su Hamda ɗin a yau zaiyi magana Mama ta ɗaga masa hannu tana cewa.
"Yau ba sai gobe ba ka zaɓa ko wannan Matar taka ko kuma Ƴata, ka zaɓa ko mu ƴan uwanka da ni wacce muka fito gida ɗaya da Mahaifiyarka ko wannan ƴar iskar Matar da kike kira