Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   20 / 27

57K to 60K   out of 78K words

son sashi tsaka mai wuya ne?, to Ummi itama yaya zai fara fahimtar da ita?, duk da yasan yarinya ce dama mai haƙuri da fahimta, amma yasan ai abun da ciwo bare ma Hamda da aka je akama kishiya har biyu bata sani ba.

"Kayi Shuru Mubarak shin ko dai abunda na kawo maka yafi ƙarfin kayi min shi ne?".

Mai Gari ya faɗa kawai Mubarak zaiyi magana yaga Mai Gari ya fashe masa da kuka harda jawo babbar rigarsa yana share hawaye.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un".

Mubarak ya faɗa a zuciyarsa.

Da sauri ya kamo hannun Mai Gari yana cewa.

"Dan Allah Baba Mai Gari kayi hakuri ka daina kukan nan Please, ba wai naƙi abunda kace bane, Baba Mai Gari rigimar da zata ɓillo ne a cikin gidan nawa nake hangowa wallahi kasan mata akan kishi".

Mai Gari ya ɗago yana jan lumfashi ya ce.

"Ita Hamda ɗin da uwarta zasu hanaka ƙara aure ne?, idan ma wani abu ya ta so ka kira ni ka gaya min zan taho ne ni ayi rigimar dani tunda ni na saka ka yin auran. Ni dai yanzu abunda za kamin kawai ka yarda yanzu a ɗaura auran nan da kai da wannan yarinyar Habiba, zaka ji daɗin zama da ita baza ka taɓa nadamar auranta ba wallahi".

"Baba Mai Gari a ɗaura yanzu kuma kake cewa?".

"Kware kuwa yanzu nan kuma ka tafi da Matarka, domin nasan kana da inda zaka aje ta ai, kana da kuma arziƙin da zaka iya riƙe Mata har huɗu ma kuwa".

"Hasbilallahu wani'imar wakir Ya Salam".

Kawai Mubarak ke mai-maitawa a ransa.

"Kayi Shuru ko baza kai min wannan alfarmar bane na san matsayina a wajanka tun yanzu".

"Haba Baba Mai Gari matsayinka ya wuce nan, kamar yadda Mahaifina zai bani Umarni nayi haka kaima".

"A'a idan Mahaifinka ne ai da yanzu ka amsa masa zakai masa kai tsaye, ni ko sai wani kauce-kauce kake min".

"Haba haba Baba Mai Gari kayi hakuri na amince".

Ya faɗa yana jin wani iri a ransa. Wai mi yasa ake masa hake ne shi?, sai inda aka san bazai iya gardama ba ake masa haka, bai taso yaga ana raina na gaba dashi ba, bai ta so gaya ana ma babba gaddama ba, iyayensa kamin rasuwarsu sun basa tarbiyyar data dace wacce yanzu gashi duk da basu da rai tarbiyyar nan da suka basa tana anfanar al'ummar Mutane dama na zagaye dashi.

"Mubarak ka amince da gaske?".

Mai Gari ya faɗa fuskarsa cike da wani irin farin ciki, domin yanzu yasan dole ne Mubarak ɗin ya rinƙa waiwayo su, ko banza ya aura masa ƴar cikin garin kuma yarinya mai hankali wacce tasan ya kamata.

"Na amince da gaske Baba Mai Gari".

"Allah Ubangiji yayi maka albarka, ya albarkaci zuri'arka".

Amin kawai ya amsa iya laɓɓansa yana jin wani iri sosai a ransa yana jin bai kyautama Hamda da ita kanta Ummi ba.

Nan Mai Gari ya tashi ya barsa shi kam Mubarak baya jin zai iya zuwa inda za'a ɗaura auranma.

Mai Gari na zuwa Fada duk aka miƙe ana basa girmansa, sai da ya zauna kamin kowa ya koma ya zauna.

Mai Gari ya kalli Inna da kanta ke ƙasa tun lokacin daya zo wajan ya ce.

"Lube mi yasa kike san aurama wannan yarinyar Abba?, wadda duk cikin garin nan ansa Abba baya da mutumci baya daraja kowa, idan kin san mutunan kirki ne mi yasa baki aura ma taki Yarinyar ba?, sai wannan ita dan kin san ba daga cikinki ta fito bane yasa kike ƙoƙarin kassara mata rayuwa?".

Inna ta wani ɗago tana duban Habiba da wani irin kallo na gargaɗi kamin ta dawo da dubanta wajan Mai Gari ta ce.

"Mai Gari ni ai ba auran dole zan mata ba, ita ce ta kawo Abba har gida da kanta, idan ƙarya nake kuma ai gata nan ka tabbaye ta kaji".

Inna ta ƙare maganar tana sake kallon Habiba haɗe da kallon da take mata tunda ta zo wajan kallo ne irin na mugun gargaɗin nan.

Habiba tayi saurin yin ƙasa da kanta zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Innar su Asabe dake kusa da ita a hankali ta ce mata.

"Habiba karki sake ki cuci kanki ki lalata rayuwarki akan wannan matar Lube marar imani, karki ji tsoron komai kawai ki sanar ma Mai Gari gaskiyar abunda ke faruwa, idan ma tsoron komawarki gidanta kike ni nan zan ci gaba da riƙe ki har lokacin da wani mai nagarta zai fito ya ce yana son auranki, ni nan zan ɗauki nauyin duk wani abu da yashafi rayuwarki, karki tsorota ki gaya ma Mai Gari gaskiya kai tsaye kawai, karki wani ji tsoron kallon da take miki duk ina ganinta ai ina lura da ita".

Wani irin lumfashi Habiba ta sauke tana jin wata kwarin gwaiwar gaya ma Mai Gari gaskiya, Muryar Mai Gari suka ji yana cewa.

"Yarinyata Habiba ki gaya min gaskiya, idan har kika gaya min abunda ya faru tsakaninki da Allah zan baki Ɗana aure, zan aura miki Ɗana wadda har duniya ta naɗe baza ki taɓa danasanin zamowarsa miji a gare ki ba".

Inna a haukace ta ɗago tana kallon Mai Gari zuciyarta na wata irin muguwar bugawa a ƙirjinta wani irin tashin hankali ta tsinci kanta a ciki lokaci ɗaya jin abunda Mai Gari ke cewa.

Innar su Asabe ko wani maɗaukakin farin ciki ne ya rufeta, tabbas tasan wane ɗana ne Mai Gari yake nufi, idan ko har shine to tayi ma Habibar murna sosai haƙiƙa tayi dace a nan dai gidan duniya.

Ƙasa da kanta sosai Habiba tayi domin yadda taga Inna ke sake mugun mata gargaɗi da ido.

"Baba Mai Gari wallahi Allah ni ba ni ce na kawo Abba ba, hasali ma Baba Mai Gari bana ƙaunar ko ganinsa, amma saboda nayi mata biyayya nake fita idan yazo, idan na ce bazan je bama wani tashin hankalin zan fuskanta a wajan Innar dashi kansa Abban, dan har mari na ma yake idan ina gaya masa bana sonshi dan Allah ya rabu dani do.......

"Wallahi Allah Mai Gari ƙarya take wannan ƴar iskar yarinya, ashe ke Habiba tsintacciyar Mage ce wacce bata Mage?, ni kamar ni Habiba dana riƙe ki tsawon shekaru zaki watsawa ƙasa a ido?".

Inna ta ƙare maganar a tsawace zuciyarta na wani irin zullo na tashin hankali. Ji take da tana da dama jawo Habiba zatai tayi mata dukan da zata kasa moruwa har duniya ta naɗe.

"Ke Lube hattara dai kibi a sannu kina fadar Mai Gari ne ba'a mana rashin hankali a nan".

Faɗin Sallau yana zare mata ido.

Ɗaga masa hannu mai Gari yayi yasa Sallau yin shuru.

"Tunda har yarinya ta buɗe baki tayi magana kuma ta faɗi gaskiya ta faɗi abunda ke ranta, dan haka na gama yanke hukunci".

Bakin Inna yana rawa ta sake cewa.

"Wallahi Habiba nida ko har abada, daga yau ki nemi inda zaki koma amma ba dai cikin gidana ba, kita fi can ki ƙarata bani ba ke".

Innar su Asabe cike da fara'a ta dubi Inna ta ce.

"Ashsha Lube wai da alama baki ji Mai Gari abunda ya ce bane, yanzu nan za'a ɗaura auran Habiba da mijin da idan kika gansa sai zuciyarki ta buga saboda baƙin ciki in.....

Mai Gari ne ya katse ta da cewa.

"Ya isa haka nan".

Ya sake kallon Inna ya ce.

"Tunda kince haka kinga yanzu gidan da kike zaune ai na Mahaifin ita Habiba ne, dan haka yanzu bashi a raye dole a saida shi bata gadonta tunda dama ba'ai rabon gadonsa ba".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un na shiga uku na ni Lube".

Inna ta faɗa hankali a mugun-mugun tashe sai zufa take tana zare ido.

Habiba da kanta ke ƙasa ta ɗago ta kalli Mai Gari ta ce.

"A'a Baba Mai Gari na bar mata gidan kawai idan har akwai gadon nawa na bar mata bana buƙatar komai ni".

Mai Gari cike da son wannan yarinya mai halin manya ya ce.

"To kin dai ji da kunanki, amma baccin ta ce ta bar miki da yau-yau ɗin nan sai an saida gidan da kike taƙama dashi naki ne an bata haƙƙinta itama, amma tunda da kanta ta furta hakan shikanan".

Mubarak dake gefe wadda tun hayaniyar Inna ta farko ya sami kansa da fitowa, daga gefe yake tsaye sai P'A ɗinsa daya matsa a kusa dashi yana sake basa labarin su Habiba da tausayinta da yaji shima, Mubarak ɗinma yana kwallon yarinyar yadda take komai cike da sanyin jiki da natsuwa kawai yaji ta kwanta masa a rai zai aureta kodan ya ciro ta daga ƙangin rayuwar da daɗe tana ciki.

Ɗan shafa kansa yayi kamin ya kalli P'A ɗinsa ya ce.

"Uhmmm P'A Mai Gari fa ita yake son aura min yanzu da kike jin yana faɗa".

"Wai da gaske kake ranka ya daɗe?".

"Hakane kamar yadda kaji na faɗa, hmmm akwai rigima fa a gida na nake gaya maka, ban san yadda zanyi da Ummi da kuma Hamda ba".

"Eh to ranka ya daɗe bazan baka shawarar karka ƙi amincewa da ƙudurin mai Gari ba, saboda shima kamar mahaifi yake a wajanka, ita kuma Ummi tana da fahimta ranka ya daɗe kamar dai Mahaifinta Baba Mlm, kuma ai idan tayi tunani itama kusan hakanne aka aura maka ita, so duka an baka so ne kawai ba dan wai kaine ka gansu ka ce kana so ba, sai daga baya ne soyayyarsu ta ɗarsu a ranka hakama suma, dan haka ni ina ganin bazaka samu matsala ta bangaren Ummi ba, matsalar da tashin hankalin tana wajan Hamda saboda yadda Yarinyar nan take nuna tsananin kishinka fa harta fara zargin ina kake zuwa kake kwana biyu kana kake dawo mata gida, duk da tasan yanyin aikin ka wata rana dama kana kwana a waje amma ranka ya daɗe abunda baka sani ba nake so kuma na gaya maka yau da safe shine, Hamda fa na ƙoƙarin saka masu saka maka ido so take ta gano ina da ins kake zuwa ka kwana".

Wani irin duba na mamaki Mubarak yake ma P'A ya ce.

"Lallai aikin ka na kyau, dana saka kake saka mata ido sosai, da ba haka ba da yanzu ta gano inda Ummi take ƙila, amma ka ci gaba da saka mata ido komi ake ciki ka rinƙa sanar dani da wuri, itama wannan Baba Mai Garin ya ce a tare zamu tafi zan aje ta ne a gidan hutawa na kawai ya kasance nan ne gidanta".

"Kaga kuwa hakan yayi kowaccensu tsakanin unguwannin da suke akwai tazara mai nisa a tsakani, Allah dai ya baku zaman lafiya da fahimtar juna".

Iya laɓɓansa ya amsa da amin kawai.

Mai Gari bai bari Inna ta tafi ba sai da aka ɗaura auran Habiba aka kuma bata goran ɗaurin aure da Mai Gari yasa aka sayo shi yanzu.

Zuciyar Inna ta cika da baƙin ciki sai haɗeyar zuciya take.

Bata tashi gane waye aka aura ma Habibar ba sai da Mai Gari ya ce Mubarak ya matso sai miƙa masa hannu ake ana masa murna yana amsawa da murmurshin yaƙi kawai.

Habibar ma da Innar su Asabe zata wuce da ita zuwa gidanta kamin a wuce da ita, data hangi wadda Mai Garin yaba wai aurenta sai da gabanta ya faɗi zuciyarta ta shiga harbawa da masifar ƙarfi, tana mamakin wannan wai yanzu shine a matsayin mijinta?, anya Mai Gari ya duba mata kuwa?, wannan bawan Allahn ai yafi ƙarfinta ita kuwa, ina zata kai wannan ɗan gayun mai ji da kuɗi da kansa ga naira kuma, jikinta ne ya sake yin masifar sanyi jin Innar su Asabe da Asabe na bata labarinsa yana da Mata har biyu kuma su duka ba'a daɗe da yin auran nasu ba, ita kam ina zata kai Matan nashi?, yaya zata fara kishi da su ma?, suna ƴan gayu wa'inda suka tashi a waye, ita fa mita sani idan banda wahala ta ta so a cikin Ƙauye karkara?, ita Mai Gari da yayi shawara da ita wallahi da bai aura mata wannan kyakkyawan mutunan da take gani ba a matsayin miji a gareta, daya barta ta kawo dai-dai da ita, wannan iya tunaninta yafi ƙarfinta yafi ƙarfin duk wani tunaninta.

Inna ko tunda tasa idonta akan wadda take jin wai shine mijin Habiba, ta fara ganin wata irin hajijiya na son kayar da ita. Habiba dai data sani ita ce yau ɗaya ta mallaki mijin da ko a mafarki bata taɓa kawo ma kanta wata Habibar banza ta sami miji koda irin Shamsu bane wadda suke watsewarsu da Ɗiyarta Bilki, sai gashi rana tsaka kawai ta sami mijin nunawa a duniya baki ɗaya, shin wai ko dai duk mafarki take yi ne ba gaskiya bane?. Ɗan marin kanta tayi wai ko zata dawo yaccinta amma ina hayaniya kawai take ji a saman kanta tana sake hasko mutunan dake a matsayin wai mijin Habiba dai?.

Tunda Mai Gari ya sallameta take tafiya zuwa gidanta take haɗe hanya tsabar tashin hankali ko ganin gabanta bata iyayi.

Lokacin data shiga gidan Ƙawayenta suka rufeta da tabbayar miya faru a Fadar Mai Garin?.

Itafa sama-sama take jin maganganun nasu suna mata shawagi.

Sai da Lare da Saude suka girgiza ta kamin ta ɗago tana binsu da kallo, kawai ta sami bakinta da fara basu labarin abunda ya wakana a Fadar Mai Gari.

Wani irin salati Lare ta ɗauka tana faɗin.

"Kai kayyasan nan Ke Lube kin ko san waye Mai Gari yaba auran Habiba?, ko kin san irin Matsayi da kuɗin da Allah ya basa?, kin san irin ɗaukakar da Habiba zatai a cikin Garin nan baki ɗaya, ai Habibah gata can ta zama tauraruwa a cikin Garin nan dama kewayensa, tabɗi jam wani Lube baki gane Mubarak wadda iyayensa suka daɗe da rasuwa bane?, wadda da can yake zuwa har yana gina masallatai da islamiyyu harda su Fanfo da ruwa, duk wani ɗan ci gaba da ake yi mana shekaru masu ɗan dama da suka wuce duk shine to yake yinsu in gaya miki. Ashe ya dawo ƙasar ma?, ai da bashi ƙasar shi yasa aka daina ganinsa a garin nan, ita Kanwar Mahaifiyarsa ai tana tare dashi".

Saude ta amshe da cewa.

"Ke dan Allah Lare wai Mubarak dana sani dai shine mijin Habiba a yanzu tabɗi jam?, ai kin san fa Kanwar uwar tashi bata son abunda ke haɗata da Garin nan, ta tsani Garin nan yanzu, dan naji ana cewa mafa wai duk ita ke hanashi zuwa cikin Garin nan ya taimaki ƴan uwansa da jama'ar cikin Garin nan, danshi ance yana da kirki sosai".

Duk maganganun da suke yi basu san sake hargitsa ƙwaƙwalwar Inna suke ba, sosai tashin hankalinta ya sake hauhawa wadda har yafi na da ma data shiga a Fadar Mai Gari, wani irin jiri take gani ji take kamar zata faɗi.

Suna cikin haka wani Yaro yayi sallama da gudunsa kuma ya shigo, hankalinsu ne ya koma kanshi jin abunda Yaron ke faɗin.

Abunda Yaron ya furta ne yasa Inna sakin wata irin ƙara mai ƙarfi kawai suka ga ta zube a wajan a sume.

Wani irin salati suka ɗauka Saude na faɗin.

"Innalillahi wai wace irin baƙar rana ce a wajan Lube haka ne yau?. Kai Yaro a ina a iske Bilkin a cikin jini da kake cewa?".

Yaro ya sake cewa.

"A wajan wata bola na ganta kwance jini yana bi mata kafafu, shine na rugo nazo na faɗa ma Innarta tana can kamar wacce babu rai a jikinta".

Yana idasa faɗar haka ya fice daga gidan da gudunsa.

"An shige su ni Lare, ita ko Bilki ina taje haka?, waye yayi mata haka to?".

Sa sauri Saude ta yafa mayafinta tana jan wata Mata suka fice jim kaɗan sauka dawo rungume da Bilki wacce take a sume itama ga jini har lokacin na bi mata kafafu da cinyoyi.

"Kai jama'a kamar fa ciki ne ke shirin zubewa a jikin Bilki jama'a ku duba da kyau".

Faɗin Lare tana ƙara duba jikin Bilki da kyau.

Tofa ƙananun maganganun kawai kake ji a cikin gidan ga mutane wa'inda suka zo bikin Habiba da Abba.

Wadda Innar ta gayyato.

Saude ta ce.

"Dan Allah Lare ki daina irin haka mana, ki miƙo min ruwa a watsa ma Lube tukunna"

Ruwan ta miƙa mata Saude ta shiga watsawa Inna ruwa, kusan sau uku ana watsa mata amma shuru kamar wacce bazata tashi ba, ana huɗu ne taja lumfashi mai ƙarfi.

Wani sabon tashin hankali haɗe da tsantsar mamaki ya rufe Inna da su Lare ganin Inna dai ta farka amma rabin jikinta baya aiki, ɗaya kawai ke aiki na ɓarin damarta.

Ai Inna na fahimtar haka ta sake fashewa da kuka tana kallon yadda Bilki jini ke mata zuba, sake shiga wani tashin hankalin tayi dandanan jikin Innar ya soma rawa da ɗayan hannunta mai lafiya ta shiga tattaɓa jikin Bilki tana kuka tana son tayi magana amma baki ya karkace ya jirkice babu dama.

Lare ce ta amshi kofin ruwan dake a hannun Saude ganin ta tsaya sai kallon Inna take yadda lokaci ɗaya Allah ya maida ita abun tausayi, wani irin tsoron Ubangiji ne ya rufe duk wani dake a cikin gidan wasu harsun fice sun fara haɗa ƙarya da gaskiya a cikin garin.

Sadda Lare ta watsama Bilki ruwa ta farka a firgice tana wasu irin sabbatu tana faɗin.

"A'a a'a Shamsu ni dai tsoro nake ji, kar na zo na mutu wajan zubar da cikin nan dan Allah karka....

Maganar ce ta maƙale jin yadda aka girgizata da ƙarfi.

Wata irin zubara tayi tana miƙewa tsaye, da da sauri ta koma ta kwanta ƙasa jin wani irin bala'in raɗaɗi da mararta ke mata, kwanciya tayi ƙasa ta shiga juyi-juye take kiran wayyo

20 / 27