Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
sanar dashi ba'a kai masa komai fa".
Mama itama da hankalinta ya ɗan tashi, sai zuwa can ta ce.
"Kai ka kwantar da hankalinka, babu abunda ya isa yayi mana, bai dai isa ya ce zai kore mu ba, mun riga da mun zame masa ƙarfen ƙafa babu yadda ya iya damu, ni nasan miye zance masa"
"Yawwa Yaya ai shi yasa ma nazo tuni na ƙara tunasar dake, nasan ku mata akwai dabara sosai, ni bari naje wajan direbobin gidan nan su shirya domin da mota kusan biyar za'a je ɗaukarsa, ai harda ke Yaya ko?".
Murmurshi kaɗan Mama ta saki ta ce.
"Noo da dai Hamda za'aje, amma fa saika kula da ita, kar taje tayi masa wannan shirmen nata Please".
"Karki damu Yaya, ai idan ta gansa ma kwarjininsa kaɗai ya isa yasa ta natsu wallahi, ai Ƴallabai duk yadda take ɗaukarsa ya wuce nan, duk yadda za'a baka labarin kamaninsa bai kai ya ka gansa da idanuwanka ba, yo Yaya ko can Ƙasar wajan fa Mata rububinsa suke bare ace ga nan Ƙasa Nigeria. Yaya fa dole sai mun sake dagewa wallahi, ayi-ayi mu samu Hamda ta auri Ƴallabai Mubarak, idan ta auresa ai mun ƙara warkewa wallahi, domin ƴan matan yanzu kota ina kawo masa hari ake, danma sunga shi ɗin baya son raine, kuma ya daɗe baiyi aure ba kusan shekara arba'in, shi yasa kowa ke kallonsa da ko neman mata yake, ko kuma wai aljana ce ta hanasa auran, basu san shi Matan ne kawai basa gabansa ba, sai kace wadda baya jin sha'awar Mace, wato Yaya ban taɓa ganin mai tsananin kame kansa irin Ƴallabai Mubarak ba, duk tsawon shekarun nan bai taɓa kusantar zina ba, hasalima ya tsani duk wasu masu yinta, yana da wani irin mugun kyamar masu kusantar ta, ni ina gudun ranar da zai gane Hamda.....
Mama tayi saurin ɗaga masa hannu tana zaro ido waje.
"Abubakar wai mi yasa idan ka kama ratatu zance baka iya kwanturorin bakinka ne?, sai zuba kike kamar kanyar data lalace, so kake ƴan aiki ko mutanen dake gidan nan suji ka ne?, a samu wani ɗan baƙin cikin yaje ta bayan fage ya sanar dashi, kuma kake ta wannan ya ma za'ai ya gane cewar ba budurwa bace?, ni nasan ai irin gyaran da zan mata namu na mata, ta dawo kamar budurwa. Kaga mubar zancan nan kamar ma tsautsayi wani yaji mu".
Ɗan dafe bakinsa Abu yayi yana ɗan murmurshi ya ce.
"Ayi hakuri Yaya, kin san bakin nawa ne baida linzami".
"Ni ko na san hakan. Yaa kamata kaje a fara shirin zuwa Airport ɗin nan, domin naga sha ɗaya da ƴan mintoci yanzu kuma sha biyu jirginsu zai sauka".
Mama ta ƙare maganar tana duban agogon dake maƙale a bangon parlon.
Hamda da idonta ke kulle dama tana kwance ne a kujera, ta ɗan mike ganin Kawu Abu ne yasa ta cire abunda ta maƙala a kunnan nata, da duk bata ji shigowarsa bama sai lokacin.
"Kawu Abu ashe kaine ka shigo?".
"Nine Hamda, ya kamata ki tashi ki shirya dake za'a je tarbo Ƴallabai, Please Hamda kisan irin shigar da zakiyi wajan zuwa Airport ɗin nan, kiyi shiga irin ta mutumci dan Allah".
Ɗan taɓe baki tayi kaɗan tana jin an takurata sosai, domin harga Allah bata son sa manyan kaya, kullum cikin ƙananun kaya take, domin yanzu haka ma daga ita sai wando sai wata riga fara ko Cibiyarta bata rufe ba.
Tashi tayi tana faɗin.
"Bari to na saka Abaya irin ƴar ƙasar Dubai ɗin nan, saboda bazan iya saka atamfa ba ko Hijab gaskiya".
Mama dake kallonta tana hawa saman benen ta ce.
"Ai ko Hamda da kinyi hakuri kin san kayanmu irin na hausawa atamfar, domin Mubarak yafi son yaga Mace da kayan hausawa wallahi, bare ace kisa kayan masu ɗan duhu haka, saboda yana son kalar baƙi da fari a rayuwarsa".
Bata ma jita ba tayi saurin ƙarasa hayewarta saman.
Mama ta dawo da dubanta wajan Abu tana cewa.
"Waccan yarinya bata da hankali amma ina jin idan ta gansa dole ta gyara dabi'unta. Ni ba wannan bama, ka tabbatar dai an gyara masa part ɗinsa?".
"Haba Yaya ai tun jiya aka gama gyara shashinsa, komai ya zama radi nake gaya miki".
"To yayi zaka iya zuwa ku shirya domin tafiya yanzu nasan itama zata fito".
Da to ya amsa yana ficewa daga parlon...
*Unguwar Yammawa Rimaye, Kankia local government Katsina State Nigeria*
Ummi ce kwance akan katifarta, tana ɗan latsa wayarta sai Halima dake kwance itama akan nata gadon, itama dai wayar take yi da wadda zai aureta.
Ummi ta kalli cikin wayarta Datarta dama a buɗe take tana ɗan kallon photos a cikin facebook da videos data ke cin karo dasu.
Tana cikin kallon auran da Ahmed XM yayi da Safeera, da aketa yayato a social media, kota ina ka shiga maganar dai auran ake, itama bikin ne take kallo yadda ake kashe naira wajan bikin, haɗe da shiga comments ɗin mutane tana karantawa, yadda wasu ke kushe auran nasu, wai yaci amanar matarshi Safiyya da auransu da shekara ɗaya yayo mata kishiya, kishiyarma da tsohuwar budurwarsa, wani idan ta karanta comments ɗin dariya ma yake bata, tana mamakin yadda mutane suka maida hankalinsu ga auran Ahmed XM ɗin, mai makon su maida hankali akan tasu rayuwar, da abunda ya dami tasu rayuwar ko kuma ma suyi magana akan matsalolin ƙasar, yanzu suna nan gashi ƴan bindiga kusan koda yaushe zasu iya shigo masu gari da makwabtan garuruwansu, baka taɓa ji anyi magana akan haka, sai wani abun da baima kamata a maida hankali akansa ba, shine mutane ke tada jijiyoyin wuya akansa, ta tabbata maganar auran da suke yi shi kansa Ahmed XM ɗin da Safirar bama su san anayi ba, koda sun sani sun maida wa'inda suke kushe auran da magana akansa mahaukata, to tunda basu san dai da zamanka a duniyar nan ba, kai wani ma harka mutu baza kaga wani Ahmed XM ba, to na miye kazo kana tada jijiyoyin wuya?.
Tana cikin kallo da tunanin abun, taga an turo friends, ta facebook ɗin, wajanta shiga sai taga namiji ne mai suna Usman, samun kanta tayi da danna masa Confirm itama, hannunta ne ya kuskure ta tura masa hey, da yake da ka danna Confirm ɗin hey da ɗan emos zasu fito.
Dafe kanta tayi da sauri ta shiga wajan chatting ɗin hannunta na rawa ta kai domin gogewa, sai dai kashh tana gogewar taga an turo mata da amsa na Hi.
Huci mai zafi ta firzar kawai ta fita daga facebook ɗin bata maida amsa ba.
Washe gari bayan ta gama duk ayyukan gidan da daddare kamar yadda suka saba kowacce da wayarta, ita Hali tafi yin waya itama ba wani daɗewa take yi tana wayar ba.
Ummi tafi shiga facebook dama, tunda Whatsapp ɗin nata bata chatting da kowa, duk numbers ɗin dake cikin wayar tata bata fi ta mutum uku ba, daga ta Hali sai ta Tasiu, itama ta tasi'un ta gogeta, yanzu kuma saita halin kawai a ciki sai kuma ta Umma, wacce da wuya ma suyi waya da Ummar, idan ba fita Ummar tayi ba, tana so ayi mata wani abu a gidan kamin ta dawo, shine zata kira Ummin ta bada Umarnin hakan, daga haka kuma zata yanke kiran, dan ko gaisawa ma Ummar bata bari suyi, abunda za'ai mata kawai zata faɗa ta kashe wayarta.
Yanzu ma Ummi sake gani tayi Usman ya sake aiko mata da saƙo.
Shiga tayi, sai taga ashe status ne data ɗora a facebook ɗin na Kuku Mazuru wacce take bada dariya, ɗazo da safe ta ɗora shi, domin tana son Kukun nan tana yawan sata nishaɗi idan tana cikin ƙunci.
Gani tayi ya ce
"Ai ko kunyi kama da ita"
Dariya ta saki kawai ta turo masa da murmurshi.
Sake aiko mata da message yayi na cewa
"Ummi".
Da yake ko a facebook ɗin da Ummi kawai tasa a shafin nata na facebook.
Amsa masa tayi da
"Na'am ykk?"
"Alhmdllhi"
"Masha Allah"
Kawai tace masa ya sake cewa.
"You from?"
Ummi ta saki murmurshi kaɗan ta sami kanta da maida masa reply da cewa.
"Rimaye Kankia local government Katsina State Nigeria"
Murmurshi ya saki haɗe da tabbayarta photonta, samun kanta tayi da tura masan.
"Ah Masha Allah. A Kankia ɗin kike kenan?"
Yayi reply ɗin da photon data tura masa da cewa.
"Kinyi kyaw, thanks".
Shima a kansan saƙon ya turo da photonsa. Kyawawan gaske ne son kowa ƙin wadda ya rasa, domin har yama fi Tasiun data rabu dashi kyau, nesa bama kusa ba.
Wani irin murmurshi Ummi ta saki, lokaci ɗaya taji ta sake dashi sosai.
Ta maida masa reply.
"A'a a Ƙauyen dai Rimaye".
Sai reply na photonsa daya tura mata da cewa.
"Masha Allah".
Ta sake aika masa da reply na sakonsa da ya ce tayi kyau.
"Thanks dear".
Shima reply ya maido mata inda ta ce a Rimaye take, da cewa.
"Ohh Ayya. Thanks"
Ya sake mata reply inda ta ce thanks dear.
"Awwwn" da ɗan alamar kiss.
Ya sake cewa.
"Kina zuwa Katsina amma ko?"
Ta aika masa da reply
"Eh amma ba sosai ba"
Ya ce.
"Ohh Allah sarki
I used to live in kano too ina aiki anan".
Ummi ta ɗan saki murmurshi kaɗan ta maida da amsa.
"Ohhh Allah sarki, ashe Kano kake aiki?"
"Yes Ummi"
"Allah ya taimaka tohm"
Ummin ta maida masa da amsa.
"Ni ki bani number ki to Please?"
Samun kanta tayi ta tura masa number ɗin, shima nan take ya tura mata tashi number.
Ya sake aiko mata da message
"Allah ko kunyi kama da Kuku. Send me morw More pictures".
" uhum uhum Allah bazan yarda ba dear, saina haifa maka irinta kuwa"
Ummi ta samu kanta da maida masa da reply da hakan.
Ta sake tura masa reply.
"Kana WhatsApp da number saina tura maka ta can"
Ya aiko mata da reply ɗin data ce saita haifa masa irin Kuku da cewa.
"Hahahahahahaha maza maza bismillah"
Sai ya sake reply ɗin data ce masa, yana WhastApp zata tura masa photon ta can
"Okay I’ve sent my no already"
Ummi ta yi masa reply.
"Uhum uhum shine ka sake min dariya ko?, da gaske sai na haifa maka irinta"
Yayi reply da
"Auxubillahi kika haifi mage ai munshiga uku ai"
Murmurshi kawai Ummi keyi ta shiga WhastApp ba tunanin komai ta tura masa ƴan photos idanta da wasu bane, ta dawo facebook ɗin ta ce masa.
"Kaje WhatsApp na tura Maka"
Yayi reply
"Nagode I’ve seen it"
Ummi tayi reply da inda ya ce idan ta haifa masa mage an shiga uku da cewa.
"Wasa nake yi, Baby zan haifa ma mai kyau, mai kama da kai"
Reply yayi da.
"Mai kama dani? ba zatayi kyaw ba kuwa anshiga uku,
tabiyo mamanta daii"
Reply Ummi.
"Kai Y Salam baka son ta biyo ka. Karfa shiga uku ta kama bakinka fa, ba kyau faɗa".
Ummi ta ɗan waiga inda Hali take ganin har tayi bacci, yasa Ummi dafe kanta tana tunanin miye ya shiga kanta bata san mutum ba haka kawai ta sake dashi.
A tunanin kawai ta kawo ai Allah ne yayi mata canji da Tasiu, Allah ne ya kawo mata wani.
Reply ɗinsa ta gani.
"eh gaskia tabiyo ki nake so ai zatayi kyaw"
Reply Ummi.
"Haka kafi so?"
Reply Usman "Yes Please".
Reply Ummi. "Ni Kai nake so tabiyo, kai ɗin ma ai kana da kyau ai ko?".
Reply Usman. "Touuu shikenan za'a haifi iri na. Next one sai ayi irinki"
Reply Ummi. "Hhhh Allah Hayatyyy farin ciki kake kawai yau ko"
Ta samu kanta da ƙaƙuba masa suna Hayatyyy, ta rasa miya shiga kanta.
Reply Usman. "hmm angodema Allah dai always, sai kuma ta dalilin haɗuwa da ke, please Ummi zaki aure ni?, tunda naga photonki naji kin kwanta min, Please Ummi ki soni".
Wani irin daɗi ne ya rufe Ummi, ko bata faɗa ma tasan itama ta faɗa soyayya lokaci ɗaya, soyayyar Usman saita mantar da ita wani Tasiu, zuciyarta mai rauni ce da saurin kamuwa da son wani, da kuma wuyar mance wani, amma fa idan ta tsani mutum ta manta dashi har abada bata waiwayarsa, tunda tun lokacin data kira Tasiu ta fara jin haushin kanta, ta fara dagewa da addu'a har taji kwata-kwata Tasiun ya fice mata a rai, sai ga Usman kwatsam shima ya shigo rayuwarta, amma fa tana ɗari-ɗari karta taje ta faɗa sonshi da yawa shima wani abun ya zo ya lalata komai.
Sauka kawai tayi daga facebook ɗin ta kashe wayarta ta juya ta kwanta, tana jin wani irin farin ciki haka kawai ya rufe mata zuciya......
*RAUNIN ZUCIYA*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
EPISODE 6
*Kauyen Tudun Wulli, Kankia local government Katsina State Nigeria*
Ganin Innar da Bilki sun shige sun barta ita ɗaya a tsakar gidan, ga hannunta dake mata wani irin zafi haɗe raɗaɗi mai azabar gaske, ga shi hannun lokaci ɗaya ya ɗuri ruwa, hannun na neman ruɓewa, idan har bata neman masa magani ba akwai matsala.
A hankali da kyar kuma ta miƙe hawaye sun mata shaɓe-shaɓe akan fuskarta. Tsoronta ɗaya karya fita, fitar ta zame mata matsala a wajan Inna, bata da zaɓi dole saina fitar taje gidan su Asabe ko ta samu ta samu maganin ƙunar dake hannunta, idan ta ce zata bar hannunta haka tabbas hannunta ruɓewa zaiyi ta zama kuturwa, ko kuma idan hannun ya gaji da wahalar dashi da ake idan aka je wajan masu magani suce sai an yankesa, idan ma an yankesan tasan Inna ko a kwalar rigar ta, kuma bazata fasa yi mata duk wani abun data ga damar yi ba, tasan wacece Inna kamar yinwar cikinta, duk duniya ita ce halitta ɗaya tak da take mugun-mugun shakkarta.
A hankali take tunani mai zurfi harta fice daga gidan, bata so ma Innar tasan ta fita harta dawo addu'arta kenan.
Koda taje gidansu Asabe Innar su Asaben hankalinta yayi mugun tashi ganin irin izayar da Habiba kesha a wajan Matar ubanta.
Jawota tayi cike da tausayi Asabe na riƙe da ita, Innar su Asaben ta kamota sosai tana kallon hannun nata, hankalinta a tashe tsigar jikinta har tashi take ganin yadda hannun marainiyar Allah na son ruɓewa a banza saboda rashin magani.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, Habiba yanzu Innar taku ce take miki izaya da wuta?, wake azaba da wuta idan ba Ubangiji ba?, wannan matar anya akwai zuciya a ƙirjinta kuwa?. Ni banga abunda yasa take kishi dake ba, tunda wacce take dan ita ta mutu ta bar mata duniya, ke hatta Mlm ɗin mahaifinki Habiba danshi dai ake tada jijiyoyin wuya, Mata dan namiji suke kishi, to shima baya duniyar, banga dalilin da zaisa ta tsaneki har haka ba. Wai mi yasa wasu Matan kwata-kwata basu da imani a ransu ne?. Ni Asabe ta gaya min ban taɓa yarda ba ashe dai da gaske tana miki azaba da wuta?, kai jama'a".
Asabe na hawaye itama tana duban Habiba ta ce.
"Wai Habiba komawar gidan da kikai daga wajan tallarmu ta ƙara ƙuna miki hannun har haka? naga ya sake chaɓewa ƙunar tafi wancan wacce na gani dazo?".
Habiba cike da dauriya bata iya magana ba ta ɗaga mata kai kawai, saboda idan ta ce zatai magana kuka ne zai kwace mata, domin yanzun ma hawaye take tana damtse da bakinta hawayen ne kawai ke zubar mata akan kwakwalwar fuskarta, wacce ta gaji da wahala, kyan nata ma baka taɓa shaida shi, saboda tsantsar wahalar data ke sha duk ta ɓoye kyan nata, har wani duhu-duhu ta ɗanyi, duk da fara ce tass amma yadda kasan ruwa biyu haka ta koma, ga fuskarta data ɗan zurma ta rame duk fuskar tata saita wani irin mugun faɗawa can ciki, alamar yinwa tayi mata mugun kamu sosai.
Innar Asabe da gudu taje ɗakinta ta ɗakko wani maganin ƙuna ta fito, dama kuma tana yawan ajesa saboda da irin hakan.
Tana zuwa ta kamo Habiba ta zaunar da ita akan tabarmar da suke zaune zuwanta yasa suka miƙe hankalinsu a tashe.
Saida ta ɗan gyara mata hannun da ruwa ya fara taruwa na ƙunar, saboda rashin magani da kula da ba'a bashi har ƙunar ta fara jan wani irin ruwa.
Tana yi tana faman mata sannu ji take kamar ciwon a jikinta yake, hakama Asabe dake riƙe da itama sai hawaye take, ita ake ma magani amma yadda kasan su ake sama maganin, yadda suke runtse idonsu suna faman mata sannu motsi guda zatayi sai sun tabbayeta da zafi sannu kinji?.
Kallonsu kawai take tana ɗan murmurshi mau haɗe da hawaye, duk duniya sune mutum na farko da suka fara nuna mata ƙauna haɗe da kulawa.
Sai da aka sama mata maganin ta miƙe zata koma gida, Innar su Asabe ta tsaida ita da cewa.
"Ki tsaya kici abinci, nasan yau da wuya ta baki abinci ki tsaya kici dan Allah"
Habiba ta haɗe wani miyau dama yinwa take ji, amma tana bala'in tsoron tsayawa ɗin, saboda taga lokaci harya ja zuwanta gidan.
A hankali ta shiga girgiza kanta ta ce.
"A'a Inna ki barshi kawai, kinga na ɗan daɗe a gidan nan, gashi kuma bata san nazo nan ɗin ba, kar na ƙara ma kaina wani laifin".
A hankali cike da wani irin tausayin Habibar ta sake jawota ta ce.
"Bazan taɓa bari ki fita daga gidan nan baki ci abinci ba, gara idan zaki tafi ni naje na raka ki, ai dama babu wadda ya taɓa mata magana akan azabar