Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   25 / 27

72K to 75K   out of 78K words

da wai Matarka ce, kai ko kunya ma baka ji ba?, yaushe ma akai hakan banda labari?, ashe har na kai lalacewar da zaka je kayi aure ban sani ba?".

Wani lumfashi Mubarak yana sake kallonsu a yanzu baya jin zai iya yin abunda Mamar ke so dan haka kai tsaye yau yayi niyar komai ya zo ƙarshe ya ce.

"Mama ita wannan ɗin da kike gani kware Mata ta ce, kuma bana jin kunyar faɗin hakan ko ina a duniya, ita ɗin jinin Baba Mlm ce amini na. Sana Mama ba ita kaɗai bace wacce na aura baku sani ba, akwai ƴar asalin garin Mahaifana Habiba wadda itama Mai Gari ne ya ɗaura min aure da ita, yanzu haka tana gida na itama a matsayin Matata, ita kanta Ummin ta sani amma ita mi yasa duk batai wannan haukan ba sai Hamda?".

"Na shiga nahh Kai Mubarak wai miye kake cewa ne ban gane ba?, zuwanka Tudun Wulli ɗin Mai Gari yayi maka aure banda labari?, shima Baba Mlm ɗin ya haɗa da Ƴarsa tsabar kwaɗayin dukiya ko mi?, na shika uku na lalace sun gama ɓata min komai nawa, sun gama ruguza duk wani buri dana gama ci akanka Mubarak Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un".

Mama ta faɗa kamar wacce ta samu kwancewar kai.

Hamda ko a zubure ta miƙe daga jikin Mama da take tana sake nuna Mubarak da kyar ta fisgo magana a bakinta ta ce.

"Uncle Mubarak baccin wannan da nake gani akwai wata ma itama kuma Matarka ce?".

Ɗaga mata kai kawai yayi, ai tana ganin haka ta dafe kanta tana jin wata irin hajijiya a saman akanta, zubewa ƙasa take neman yi a ƙaro na biyu da azama Mubarak zai nufi inda take ya tarbo ta jikinsa Mama tayi saurin tarbo ta, Hamda ta faɗa jikin Mama tana sake wani suman, Mama tana ɗaga ma Mubarak ɗin hannu idonta jawur na tashin hankali ta ce.

"Karka kuskura ka matso kusa da Ƴata, Ka gani ko ta sake suma duk saboda kai?, so kake ka kashe ƴar uwarka da kanka?, to wallahi Allah bazan yarda ba, sai dai ka zaɓa ko ni ko shegun Matan nan naka wa'inda aka je aka maka tushensu dan kawai kwaɗayin abun duniya".

Mama ta faɗa tana sake riƙe Hamda ta kwalama Doctor kira aka sake shiga da Hamda ɗakin da za'a bata taimako, Doctor sai faɗa yake danmi za'a bari dama daga farkawarta ta tashi taje inda za'a sake gaya mata wata maganar da zata ɗaga mata hankali, idan suka sake ta sake wani suman bayan wannan to tabbas ɓarin jikinta na iya shanyewa ta farka ba'a dai-dai ba.

Tashin hankali iya tashin hankali Mama taji ya rufeta tana addu'a Allah yaba Ƴartata kwarin gwaiwar fuskarta wannan gungumemiyar jarabawar da suke fuskanta a yanzu.

Ta kira Kawu Abu ya zo sai kyarma yake tana sanar dashi abubuwan da suka faru a yau ɗin, sai da yaja wata ashar yana tsine ma Mai Gari da Baba Mlm, dama shi ya daɗe yana zargin wani abu akan Mubarak ɗin.

A wajan Mubarak suna fita Ummi ta sake fashewa da kuka domin ita kwata-kwata bata buƙatar tashin hankali a yanzu.

Runtse idonsa yayi da ƙarfi yana jin kukan nata na masa zafi a zuciyarsa.

Da kyar ya lallasheta tayi shuru yana kiran Mai Gari ya sanar dashi abunda ke faruwa ya kamata shida Baba Mlm su taho zuwa gobe a warware komai a kuma tsawatar ma Mama akan furicin da take ta nanata masa.

Dan baya jin zai iya rabuwa da duka Matansa akan Hamda ɗin, zai iya dai rabuwa da ita idan tana son hakan, amma kuma baya son rabuwa da Mamar saboda ko ba komai a matsayin uwa take a wajansa a yanzu.......

Page 25

Zaune suke gaba ɗayansu a babban parlon Mama. Su Baba Mlm ne da Baba Mai Gari sai Mamar da Kawu Abu sai Hamda dake jikin Mama kwance lokaci ɗaya duk ta rame ta zafge kamar wacce ta shekara tana ciwo.

Kowanne ka kalli fuskarsa cike take da magana dan Mama ko kaɗan babu fara'a a akan fuskarta.

Suna zaune aka buɗe kofar parlon.

Ɗaga kanta Hamda tayi idonta ya hasko mata Mubarak tare da Matansa Habiba na gefensa sai kuma Ummi da ya ɗan roƙo hannunta saboda ya taimaka mata wajan tafiya, dan tafiyar ma da kyar take iya yinta, saboda cikinta yadda kullum yake ƙara girma shi yasa duk ta zama ƙatuwar karfi da yaji, idan ka kalleta sai ta baka tausayi.

Tunda Hamda ta ɗora idonta akansu zuciyarta ta shiga soya tana haɗe wani abu a maƙoshinta mai zafin gaske, Mama ko zan iya cewa saura kaɗan ta haɗiyi zuciyata, tsabar tashin hankali ganin itama Habiba ga ciki nan ƙarami ya fara tasowa a cikinta, idan ka ƙura ido zaka shaida lokaci ɗaya itama ciki ne da ita.

Ita kanta Hamda ɗin taga tabbas wannan ɗayar ma da ake kira da matar Uncle ɗinta gata nan da juna biyu.

Wai mi ma yasa itama bata ɗauki cikin bane?.

Kin manta zugar ƙawa kika ɗauka?.

Wata zuciyar ta bata amsar tabbayar data jefa kanta.

Girgiza kai tayi hawaye masu zafi na zubo mata, tabbas tayi kuskuren bin shawarar Ƙawa, yanzu ba gashi sai ririta su yake ba akan suna da juna biyun, dole ta sake taku itama, amma bata jin zata iya zama da Uncle Mubarak tare da wa'innan Matan nasa masu kama da aljanu.

Da kyar Ummi ta zauna a ƙasa tana gaida su Baba Mlm, Habiba ma ƙasan ta kai ta zauna kanta ƙasa ta gaisar dasu.

Saboda tunda tayi ma Hamda da Mama kallo ɗaya taga suna mata wani mugun kallo ta ɗauke idonta daga kansu, koda gigin wasa bata sake kai dubanta kansu ba.

Kusan tare Ummi da Habiba suka shiga gaisar da Mama, amma idan dutse na magana to Mama ta tanka su.

Shuru kawai sukai suna jin babu daɗi.

Baba Mai Gari ne ya dubi Mama ransa ya som ɓaci da lamarinta ya ce.

"Wato ke dai Sakina baƙin halinki har zuwa yanzu yana nan tare da ke ko?".

(Ya kira ainafin sunanta).

Turo baki tayi gaba tana ƙunƙuni, kamar wata Ƙaramar yarinya.

Baba Mai Gari ya sake faɗin.

"Ke yanzu fisbilillahi miye laifin wa'innan Yaran dan kawai sun auri Ɗanki?. Baki duba kika gani bane rabo ne mai tsanani ya haɗa su da Mubarak ɗin ba, gasu nan kowaccen su da rabon haihu a jikin Mubarak, ina zaki kai wannan rabon iye Sakina idan kika hanashi auransu?, ko so kike Allah ya ɗauki rayuwarki saboda da dole sai rabon nan yazo duniya?, ko kuma so kike aje ta hanyar babu aure a haifi wa'innan rabon dake jikinsu ko yaya kike nufi?".

Nanma Mama bata ce komai ba, sai wani baƙin ciki dake sake rufeta.

"Ina so ki sani ni ne nan na bashi auran Habiba, Ummi kuwa Baba Mlm ne ya ɗauki ƴarsa kyauta ya damƙa masa, ko so kike da ya bashi kyautar Ƴa guda ya ce baya so?, saboda rashin ta ido irin naki, ai zumunci bai ce haka ba, kuma nima kin san ina da haƙƙi akansa".

Sai yanzu ne Mama ta buɗe baki cike da rashin kunya a zuciyarta ta buɗe baki ta ce.

"Wane irin haƙƙi ne akansa naka Baba Mai Gari?. Shi kuma Baba Mlm ɗin ai kwaɗayin abun duniya ne ya kaisa basa ƴarsa kyauta idan ba haka bane kuma ya musa mana, kai kuma Baba Mai Gari miye muka haɗa da kai ne wai?, ba dai gari bane shin?, shima fa garin nan tun asali ba'a nan iyayenmu suke ba a Ƙanƙara muke, idan ka manta bari na tuna maka, ko ka manta shi kansa Mubarak ɗin da wane suna yake anfani?, Mubarak Khabeer ƙankara ko ka manta da hakan?".

Zan iya cewa gaba ɗaya mutunan parlon kowa kallon Mama yake yadda ta fitar da kunya ta zage sai tafko magana take son ranta, Baba Mai Gari harma Baba Mlm runtse idonsu sukai suna mamakin furucin Mamar, lallai Sakina ba kunya a zuciyarta ba kuma tsoron Allah a ranta dan haka Baba Mlm zaiyi magana Baba Mai Gari ya ɗaga masa hannu alamar yayi shuru kawai, sai shi ya ce.

"Uhmmm tabbas Sakina kin nuna min yau ba kowa bane ni a wajanki, kin kuma tuna min bana ɗaya daga cikin Ahalinku, to amma karki manta nida Ubanki abokai ne na sosai wadda muka riga muka zama tamkar ƴan uwan juna na jini ɗaya sosai, tunda muke dashi bai taɓa nuna min cewa ni ba ɗaya daga cikin ƴan uwansa bane, saboda abotarmu ta wuce duk yadda kike tunani, shi yasa ma har kika ga na ba Mubarak ɗin aure kuma ba gaddama ko wani abu ya amsa, saboda shi yayi gadon Mahaifinsa shima wadda shima matsayin aboki yake a gare ni, amma ke nayi mamakin yadda lokaci ɗaya kika canza hali kamar ba ƴar cikin Ahalinsu Mubarak ɗin kika fito ba".

Mama ta wani taɓe baki tana girgiza ƙafarta, tabbas abunda zata furta dole fa ayi ɗaya ko dai ya sakar mata Ƴa ko kuma idan yana son zama da Hamda dole ya saki wa'innan shegu matan nasa.

Ummi da kanta ke ƙasa tsabar bakin ciki da abunda aka gaya ma Mahaifinta yasa ta jin hawaye kawai nabi mata fuska, gefen hannunta tasa tana sharewa. Mubarak na gefe yana kallonta zuciyarsa ta shiga masa zafi sosai da irin ɗibar albarkar da Mamar kema Manyan Mutane haka. Da yana da dama da zuwa zaiyi ya rungume Matarsa ya lallasheta, saboda dama yanzu saurin kuka Ummin ke gareta tunda ta sami juna biyun nan da anyi abu kaɗan sai hawaye ko kuma ta fara masa kukan sangarta.

Muryar Mama suka sake ji tana faɗin.

"Ni dai kawai yanzu ya zaɓa ko ni da Hamda ko kuma wa'innan Matan nasa Matan tushe, dan gaskiya ni ƴata bazata iya zama da wa'innan a matsayin kishiyoyi ba, ama rasa abunda za'ai mata sai kishiya har biyu?, ina laifin ma ace kishiya ɗaya ce amma har biyu?, ina gaskiya kowa ma yaji wannan zancan yasan ba'a kyauta ma Hamda ba ko kaɗan. Kuma tsabar munafurci ba'a gaya mata ba har saida asiri ya tuno, da bai tuno ba haka za'a barta cikin duhu tana zaune da kishiyoyi har biyu, gasu nan kowaccen su da ciki tsabar dama anzo a haihu ake su daga zuwa ta yadda za'a samu dukiya mai tarin yawa idan babu Mubarak ɗin a doran duniya".

"Ya subhalallahi Sakina wai mi kike son zama ne?, kai Abubakar baka saka baki bane kasa ta daina wa'innan maganganun ne?, tunda mu mun zama mutanan banza a wajanta, munfi karfin mu ce tayi abu tayi sa ai, wata ƙila kai taji taka maganar".

Faɗin Mai Gari yana duban Kawu Abu da ya juya ƙeya alamar bazai tanka ba, ai maganar bama tashi bace.

"Uhmmm ina ruwan Abu a cikin wannan zancan, ni kawai ya sakar min ƴata idan har ba zai rabu da wa'innan alaƙaƙai ɗin ba". Mama ta faɗa tana nuna su Ummi.

Mubarak ya runtse idonsa da ƙarfi yana jin wani irin abu na taɓa ransa.

Hamda ko sai kallonsa take tana jiran taji abunda zai ce, zuciyarta sai bugawa take a ƙirjinta tsabar fargaba da tashin hankalin abunda Uncle Mubarak ɗin zai iya cewa.

Baba Mai Gari ne sake nuna su Habiba yana faɗin.

"Sakina wai tuwu ne a cikin idonki ne?, baki duba kika ga abunda suke ɗauke dashi bane da zaki ce ya sawwaƙe masu?, ke da daɗi a saki taki ƴar a irin wannan hali da suke ciki?, kinyi adalci kenan?".

Mama tana duban Mai Gari babu ko kaɗan kunyarsu a cikin idonta, idonta ya riga da ya rufe kanta da kuma Ƴarta kawai take gani ta ce.

"Ai Baba Mai Gari wallahi Allah yau da ace ni da kaina na Mahaifi Mubarak ni ce ya fito daga ciki na, to da wallahi yau idan har bai saki wa'innan Matan nasa ba to sai na tsine masa albarka, sai ya zaɓa ko ni dana haifesa ko kuma so".



Ido waje kowa ke duban Mama hatta su Ummi da kansu ke a ƙasa sai da suka ɗago a razane suna kallon Mama dake wannan furucin, ai ko suka samu rabon wani mugun kallo data watsa masu.

Baba Mlm ne ya buɗe baki ya ce.

"Subhalallahi subhalallahi Allah ya kyauta to".

Abunda ya iya cewa kenan danshi kam yanzu bai san abunda zai iya cewa akan Mamar ba, domin yaga tayi nisan kiwo bazata ji kira ba a yanzu.

Yana ganin lokacin data wani taɓe baki ta amsa da amin.

"To Mubarak gaka ga Sakina yanzu kam kaine mai wuƙa da nama a hannunka, kaine ya kamata ka yanke hukuncin da duk ya dace da rayuwarka, muna jiran jin abunda zaka yanke akai yanzu. Idan kuma sakar mana Yaran zakai sai mu sani mu kwashi ƳaƳanmu muyi gaba dasu, mu muna son Ƴaƴanmu ai".

Cewar Baba Mai Gari ya faɗa yana duban Mubarak sosai.

Mubarak ya ɗago yana jin ransa duk ɓace da maganar da Mai Garin, yayi ya ma za'ai ya fara sakin Matansa?, wa'inda suka riga suka zame masa aljannar duniya, yana samun farin ciki daga garesu a koda yaushe, dai-dai da rana ɗaya bai taɓa samun koda digon farin ciki ba a wajan Hamda ɗin, wa'innan data raina dai sune ya samesu da mutuncinsu, ya same su a matsayin shine kaɗai wadda ya fara saninsu a matsayin Ƴa Mace, itafa Hamda dan kawai ya rufa mata asiri bai gaggaya mata maganganu ba akan abunda taje tayi masa, bai kuma ɗauki mataki ba shine har suka sami kwarin gwaiwar fuskantarsa da maganar wai ya saki Matansa, hmm ina ai ko marar hankali ƙila yaji haka ya yanke hukuncin daya dace.

Buɗe baki ya ce.

"Mama bazan iya rabuwa da su Ummi ba, haka zalika bazan Saki Hamda ba gaskiya".

"Ohhh ni Sakina naga duniya, yau ni Mubarak kake faɗa ma magana kai tsaye?, baza ka iya rabuwa dasu ba ka ce?, to ka sakar min Ƴata na ce Mubarak".

"Itama bazan iya sakinta ba". Ya sake faɗa mata kai tsaye.

Baba Mai Gari yayi wani murmurshin gefen baki irin na manya ya ce.

"Hmm yaya za'ai bazai miki magana kai tsaye ba, ke baki ga irin ɗibar albarkar da kikai mana ba a gaban Ƴaƴanmu ba yanzu?, ai dama masu iya magana sunce abunda kayi kaima sai an maka kwatankwacinsa, dan haka kinji dai da bakin ki ya ce bazai iya rabuwa da Matansa ba har taki Ƴar ma".

"Ai saboda ba ni ce na zuƙƙunna na haifesa ba shi yasa duk yake min haka, da ace yau ni ce nayi naƙudarsa wallahi bai isa ina faɗa yana faɗa ba".

"Ahh Sakina ai da ace ke ce kika haifesan ai da yanzu babu ma aure a tsakaninsa da Hamda ɗin ko kin manta na tuna miki?, dan naga ilimin addininki kamar baya aiki akanki yanzu".

Faɗin Mai Gari.

Tashi sukai gaba ɗayansu Baba Mlm ne farkon miƙewa yana cewa.

"Ya kamata Mai Gari muje ko?, zaman ya isa haka nan, tunda dai shi Mubarak ɗin ya yanke hukuncin daya dace, yake ganin kuma hakan yayi masa".



Mai Gari shima ya miƙe kamin gaba ɗayansu suka miƙe Habiba ce ta taimaka ma Ummi wajan tashi tsaye.

Hamda tun ɗazu take hawaye tana sake kallon su Ummi ta rushe da kuka tana jin wani irin baƙin ciki na sake rufe mata zuciya, Mama da sauri ta jawota jikinta tana sake sakin maganganu masu zafi akan su Ummi ɗin da Iyayensu.

Tsaye suke a harabar gidan Baba Mlm ya kalli Mubarak ya dafasa ya ce.

"Hukuncin da ka yanke yayi dai-dai kayi aiki da hankali da baka saki ko ɗaya daga cikin Matan naka ba, Allah ya baku fahimtar juna ya kuma dai-daita kanku".

Da amin ya amsa.

Baba Mai Gari ma yayi masu addu'a, inda yasa Mota biyu kowacce ta maida su gida, haɗe da kayan masarufi da kuɗi masu yawa da ya basu, Baba Mlm da kyar ya amsa sai da Mubarak ya nuna ɓacin ransa, har ya fara cewa kodai maganar Mama ce tayi tasiri a zukatan su ne?, da zai bashi abu ya ƙi amsa, ganin haka yasa Baba Mlm ɗin ya amsa yana masa godiya, suka shiga Mota ta fice dasu daga cikin gidan.

Sai ya dawo da dubansa inda su Ummi suke tsaye, Ummi ji take inama tabi Baba Mlm ɗin zuwa gida, duk sai taji ma garin Katsinar ya isheta itakam.

Driver yasa ya miƙa Habiba zuwa nata gidan yana mata kiss a goshi bayan Ummi ta shiga Mota wadda shi Mubarak ɗin tare zasu koma da Ummi saboda yau ma sai ya kasance a wajanta zai kwana tunda Hamda bata nan sai lokacin da suka gaji dan kansu yasan zata dawo ne.

Bayan an wuce da Habiba ya shiga Motar da Ummi take da kansa yake tuƙa Motar Ummi na zaune daga gefe.

Hannunsa ya kai a saman nata hannun yana ɗan murzasa.

Lumshe idonta tayi tana ɗan kallo kyakkyawar fuskarsa ta ɗan faɗa a ƴan kwanakin.

A hankali ta ɗan kwanto jikinsa tana saka hannunta a saman kirjinta tana ɗan shafawa.

Murmurshi kaɗan ya saki yana faɗin.

"Karfa kisa na kayar damu Ummi".

Murmurshi itama ta saki kawai tana jin damuwar data kwaso tana yayewa, dama idan har zata kasance daga ita har shi manta komai take da kowa sai su kaɗai.

***************A wajan su Hamda suna fita Hamda ɗin ta sake sakin kuka mai cin rai tana jin wani irin baƙin ciki na rufe mata zuciya.

Cikin Muryar data gaji da kuka Hamda ta ce.

"Mama da Uncle Mubarak ya sake ni mutuwa zanyi wallahi, yaya ma zan fara rayuwa ba tare da shi ba?, Mama yanzu yaya zanyi Ni?".

"Karki damu dole ya zo ya sake ki fa, ni auran naku ma ya sire min, tunda ga ƴan banzar Matansa can zasu haifa masa Ƴaƴan da zasu riga

25 / 27