Raunin Zuciya Compelet Book Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 27

33K to 36K   out of 78K words

Sa'ade.

Sauke lumfashi tayi tana tunawa Mai Garin na Auran ƴar uwar Innar su Asabe, amma irin dangin nan na nesa, sai gashi sun zauna a gari ɗaya suna aure kuma.

"Wai ya duk na ganki suku-suku ne?, ko dai Inna ce yau ma?"

"Kema Asabe ai kin san kullum ni Inna ce matsala ta a duniya. Habiba ina cikin tashin hankali wallahi, wai ni Inna take son aura ma Abba ɗan gidan Dije mai markaɗe".

Wani irin dafe ƙirji Asabe tayi tana fiddo ido waje ta ce.

"Na shiga uku na, wane Abban wai kike cewa?".

"Hmmm Asabe wadda dai kika ji na faɗa miki".

"Inah ai wallahi so kawai take ta kashe miki rayuwa, ke Habiba da ki tsaya a aura miki mutum irin Abba gara wallahi ace guduwa ki kai kamin a aura miki shi, kinga ba sai ta nemi wacce zata bashi ba, ni dai wallahi a shawarce gara ki gudu ki bar Mata garin baki ɗaya, domin ni nan ji nake idan ni ce da yanzu na bar garin nan wallahi, ina bazan taɓa iya hakurin da kike da Innar nan taku ba mai baƙar zuciya".

Innar su Asabe ce ta fito jin kamar ƴar hayaniya bayan ta kashe wayar da take yi ganin Habiba ce ga Asabe zaune sai masifa take tana ƙarawa yasa Inna matsowa ta ce.

"Ke Asabe mi ya faru ne sai masifa kike haka?"

"Hmmm Inna ai dole ki ganni ina masifa, yaushe za'ace duk irin muguntar da Innar can take ma Habiba bata isheta ba sai ta haɗa da wargaza mata rayuwa, ta hanyar aura mata mutum kamar Abba, haba Inna ya za'ai bazan masifa ba?, abunda take ma Habiba fa yanzu ya fara yawa gaskiya".

Ai Inna bata san lokacin data kai ƙasa ta zauna ba, tana duban Habiba data yi ƙasa da kanta tana share hawaye yanzu.

Inna cike da tsananin mamakin Lube ta dafa Habiba ta ce.

"Ni ko yanzu ne zan nuna Lube wacece ni a cikin garin nan, ki kwantar da hankalinki kawai Habiba ki bari sai ranar ɗaurin auran ni kuma ranar zan fito dake muje wajan mai gari a gaya masa komai, nasan ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai taɓa bari ki auri Abba ba, ai dama bai san halin da kike ciki ba, saboda abubuwa sunyi yawa a garin nan, to matsalarki ba wani maganarta ake ba, mune kaɗai sai makwabtanku muka sani, shi yasa har yanzu Mai gari bai san tsiyar da take shiryawa ba".

Wani irin sanyi ne Habiba taji a zuciyarta ta ɗago tana sa tafin hannunta ta goge hawayen dake zubar mata ta ce.

"Inna ban san da wane baki zan iya gode miki ba, haƙiƙa idan ki kai min haka kin gama taimakon rayuwata, na gode Inna Allah ya saka miki da gidan aljanna".

Da amin Inna ta iya amsawa tana jawo Habibar ta rungume, tana ɗan bubbuga bayanta.

_____________________

"Asabe ya kamata ki koma tunda gashi har kin raƙo ni kofar gida".

Murmurshi kaɗan Asabe tayi suna ja suka tsaya a ƙofar gidansu Habiba. Asabe zatai magana kawai kamar an faɗo da Bilki suka ganta a gabansu ta fito daga cikin gidan.

Wata irin faɗuwar gaba ce ta riski Habiba amma ta danne tana kallon yadda Bilki ke dubansu tana wani jijjiga.

Asabe ma wata harara ta watsa mata ta dafa Habiba zatai magana Bilki ta wani saka hannunta ta ɗauke hannun Asabe data dafa Habibar.

"Keee dalla can Malama lafiya miye haka?".

Cewar Asabe na duban Bilki.

Bilki ta wani cije yatsa tana kwafa ta ce.

"Yadda akai kenan, wato kece mai hure mata kunne ko?, shine daga fitowarki zance shine ke ƴar son a sani kika kwashi ƙafa kika bar ƙofar gidan nan kika wuce gidan su wannan abar ko?".

Ta ƙare maganar tana wani nuna Asabe a wulaƙance.

Murmurshi kaɗan Asabe ta saki ta ce.

"To sai mi idan taje gidan namu?, ke bari nan gaba kaɗan sai Habiba ta zame maku ƙadangaran bakin tuli, saita zame maku bango majin gina wallahi".

"Ke dalla dakata Malama, ta ina wannan ƙasƙantacciyar zata zame mana bango majin gina?, har abada kuwa wallahi"..

"Hhhhhhh lallai Bilki har zuwa yanzu baki san waye Ubangiji ba, akwai jahilci a cikin ƙwaƙwalwar kanki dan Allah ki daure ki koma Islamiyya ko".

Asabe batai aune ba Bilki ta yunƙuro taci kwalar rigarta, tana faman zare ido ƙirjinta na bugawa na tsantsar masifa ta ce.

"Ke ni kike kallo kike ce ma jahila?".

Habiba hankalinta a tashe ta matsa kusa, tana son kwace Asabe daga hannun Bilki. Bilkin ta wani hankaɗe ta, tana nuna ta da yatsa ta ce.

"Dalla can ke kuma sakarai, ai wallahi yau kin jama kanki, duk abunda wannan banzar ƙawar taki tayi min to ki rubuta a aje Habiba a kanki zan sauke shi, a kanki abun zai ƙare wallahi".

Dama ita Habiba ta san hakan saita faru, shi yasa bata so Asaben ta biyo ta ba, ta so ta taho ita ɗaya amma Asaben ta na ce sai ta yi mata rakiya ko yaya ne, to gashi abunda rakiyar taja mata.

Asabe da ƙarfi tasa hannuta ta yaki ce Bilki data ci kwalar hijab ɗinta.

Asabe ta nuna Bilki da yatsa ta ce.

"Daga yanzu karki kuskura hannunki ya sake gigin cin min kwalar hijabi, na gaya miki".

"Idan kuma aka ƙara cin kwalar hijabin naki wani abu kika isa kiyi ne?".

"Hmmm Bilki kenan ni dai na gaya miki, baki san asalin wacece ni bane, idan rigima kike ji da ita nima fa dai-dai nake dake wallahi".

Fashewa da kuka Habiba tayi tana kamo hannun Asabe ta jata tana faɗin.

"Dan girman Allah Asabe kije gida na gode da irin abunda kika ja min".

Hankali a tashe Asabe ta zare hannunta daga na Habiba tana sake damƙo hannunta yanzu cikin nata ta ce.

"Dan Allah kayi hakuri, ba nayi hakan bane dan naja miki wani abu, amma ai kinga irin cin fuskar data gama min ai ko?, ni kuma wallahi Allah kin san bazan iya kyale ta ba, dama ta daɗe tana ban haushi, duk ba ita ce ke ƙara zuga Inna tayi miki wani abun ba wallahi".

Habiba ta zare hannunta dake cikin na Asaben tana share hawayen dake zubar mata ta ce.

"Amma ai kin san ko miye a kaina zai dawo ko?, sadda ta fara gaya miki maganar da kinyi shuru kawai kin rabu da ita, duk da nasan hakan ma idan kika yi ba tsira nayi ba".

"To kin gani?, ba gara kawai ayi mai gaba ɗayan ba, kinga kiyi hakuri Habiba ina ji a jikina komai ya kusa zuwa ƙarshe".

"Hmmmm"

Kawai Habiba ta saki ta juyawa ta bar Asabe tsaye tana kallonta harta shige zauran gidan nasu, dama tuni Bilki ta shige gidan a fusace.

Tunda Habiba ta tunkari cikin gidan ƙirjinta ke bugawa da masifar ƙarfi, saboda bata san abunda zata je ta tarar ba.

Ai ko tana shigowa ta iske Inna a tsaye da Bilki kamar ita suke jiran shigowarta dama.

Wani murfin sulba ne a hannun Inna ta ɗaga shi iya ƙarfinta ta saita goshin Habiba ta sauke mata shi a saman goshin.

Da wani irin sauri ta dafe goshin nata, tana jin wani raɗaɗi da yayima kwanyar kanta dirar mikiya, dandanan goshin ya haye ya kumbura, saboda ba ƙaramin kwaɗa mata shi tayi ba.

Habiba bata san lokacin data ɗuke ƙasa ba dafe da goshin tama ƙasa kuka sai azabar da goshin ke mata.

"Wato ke isassa shine kika kwashi ƙafa kika je gidan su Asaben dana hane ki zuwa, wato kince ga ƴar iska ai wallahi bazan taɓa iya daina zuwa gidan su Asabe ba ko?"

Da sauri Habiba ta shiga girgiza kanta.

Wani shegen tsaki Innar taja tana sake cewa.

"Magana zakayi munafuka, shine kika jawo ita Asaben marar kunyar banza take ma Bilki rashin kunya, to wallahi ba kunyar zuwa gidan Furerar nake yi ba, data ji mata ciwo kota sake ta gaya mata maganar daba shikenan ba, wallahi da yau Ƴan Sadda ne kaɗai zasu iya shiga tsakaninmu da ita daga ita har Ƴar Tata".

"Inna kiyi hakuri dan Allah".

Da wani irin sauri Inna ta ɗaga hannunta tana kaima Habiba wani uban dundu a gadon bayanta, wadda yasa Habiba sakin ƙara tana gantsarewa.

"Makira ni ki daina haɗana ni da Allah ki cuce ni, da anyi magana dan Allah Inna kiyi hakuri, baki san na tsani wannan hakurin naki ba, wannan shegen hakurin naki sake sawa ma yake na ƙara jin haushinki, yawwa danma ki sani".

_______________________

*House No: 23, Ahmadu Belloh Sardauna Estate Katsina State Nigeria*

Sai da ta tsallake jama'ar dake parlon kamin taje inda Mama take.

"Mama wai har zuwa yanzu Uncle Mubarak bai dawo ba?".

Mama ta ɗan waigo tana kamo hannun Hamda suka shiga wani ɗaki ta ce.

"Wai ke yaushe ne zakiyi hankali ne?, ina ruwanki da rashin dawowarsa da wuri?, kina neman wane abu ne a wajansa?, ke dai ba gidansa kawai za'a wuce dake ba zuwa anjima kaɗan"

"Nifa Mama Party ne fa Ƙawaye na suka shirya mana a Munaj event Santa, shine fa lokaci ya kusa na tafiya wajan Partyn kuma Ango bai dawo ba".

"Kinga Hamda koda Mubarak ya dawo tofa bazai taɓa zuwa wajan Partyn nan naku ba, dan haka kawai garama ku wuce ku kuje kuyi abunku ku kaɗai. Ni bana so ma kuyi dare saboda da wuri nake so a miƙa ƙi gidansa".

"Amma Mama ba cikin Estate ɗin nan bane ba, ina ganin ai ko an kai dare ba wani abu bane tunda unguwa ɗaya ce ai lafiya lau ne"

Wani duba Mama tayima Hamda ɗin kamin ta ce.

"Na fiki sanin ai cikin unguwar nan ne, ni ce nake so a kai ki da wuri dan haka garama kiyi maza kuje ku dawo daga wajan Partyn idan lokaci ya ƙure kuma Allah baki zuwa, sana Hamda akwai abunda zan sanar dake, Hamda ki daina shan maganin hana ɗaukar ciki, saboda yanzun ne nake so ki haihu tare da Mubarak".

Gaban Hamda ne ya ɗan faɗi, amma tunowar firarsu da babbar ƙawarta Raihan inda take ce mata.

"Ai wallahi ƙawata karki sake daga zuwanki ki buɗe ciki ki haihu, domin kina haihuwa ɗaya ma ba wata haihuwa ce mai yawa kikai ba, zaki ga namiji yazo ya daina sonki, ya tsane ki, sai kiga yana shirin ƙaro miki kishiya. Ni dai na baki shawara ki bari sai kin shekara irin goma ko biyar haka sana ki bari ki haihun, idan ma kika haihu saiki sake yin wasu ƴan shekaru haka kamin ki sake, Ƴaƴa uku ko biyu ma sun isheki Rayuwar nan".

Hamda ta kalli ƙawar Tata ta ce.

"Amma Raihan kina ganin Mama zata bari hakan ta faru".

Wacce aka kira da Raihan ta ce.

"Ke sakaran ina ce?, bari zakiyi ta sani ne?, ko kuwa idan ya tashi ƙaro miki wata ita ce zata zauna miki da ita ko ke?, kefa irin miji irin naki Hamda samun kamarsa sai anci wuya kuma sai an tona, dan haka wallahi idan baki yi da gaske ba, kina nan zaune zakiji yana can yana neman auran wata, ke kuma kina gida kina fama da ɗawainiyar Yaransa, kinga ya gama yayinki kenan kin zama tsohuwa, a'a bari yaje ya sake ɗakko wata, domin kin san babu inda Mijinki bazai je neman aure aƙi basa ba kema kin san da gudun tsiya za'a basa, dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya".

Wani irin huci Hamda ta saki ta ce.

"Please Raihan ki daina danganta Mijina da auran wata, domin yanzu haka zuciyata zafi take min maganar nan da kike danganta wata da mijina, idan kuwa yaje ya auri wata da gaske wallahi Allah Raihan kasheta zanyi, ina bala'in son mijina, ina kuma bala'in kishinsa, gani na farko da nayi masa naji duk duniyar nan shine nafi so, daga Mama sai shi ne kaɗai a duniyar nan nake ma son da baki ma bazai iya faɗarsa ba".

Girgiza tan da Mama tayi ne ya katse mata tunanin data faɗa.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana cewa.

"Shikenan Mama ai dama kin san ba sake sha zanyi ba"

"Yawwa to, ni bari naje naga da waye da waye ya kamata suje miƙa ƙi gidan naki".

Tana faɗar haka ta raɓa ta gefenta ta wuce, tabar Hamda na tunanin tabbas bazata taɓa ɗaukar shawarar Mama ɗin ba. Tana jin cewar Raihan abunda ta gaya mata shine gaskiyar halin Mazan yanzu, dan haka baza ta taɓa bari ta haihu dan yanzu ba, duk da Mamar tasha gaya mata yadda shi Uncle Mubarak ɗin yake da son yara da yawa, yana kuma son gaya Ƴaƴansa masu yawan gaske ace duk shine ya haife su.

A fili Hamda ta ce.

"Hmmm Uncle Mubarak zan haifa maka Yara amma ba yanzu ba, yanzun abunda yafi tsunkular raina da ruhi na shine kawai na ganka a kusa dani kana nuna min soyayyarka mai shiga rai da zuciya, ina sonka Uncle Mubarak ɗina".

Ta ƙare maganar tana wani ƙanƙame jikinta...........

Page 13

Rayuwa na wata irin tafiya tana gudu idan safiya ta waye kamar jan lokacin ake haka zaka ga dare yayi, haka kuma kwanaki ma sai suka zama kamar dai kwana ɗaya ne, watanni kamar sati ɗaya, shekara ta zama kamar wata, game tsoron Allah dole rayuwar yadda take gudu so kawai take kamai yazo ya wuce duniyar ma ta tashi kowa yasan makomarsa, dole abun yaba mutum tsoro.

Hakan ce take kasancewa a wajan Ummi, domin tun ana ƙirga azumi saura wata kaza, har gashi ana shirin ɗaukar azumi daren ranar juma'a.

Shi yasa ko ina gidan hidima ce ake. Kusan zan iya cewa Ummin ce mai yin hidimar ɗora abincin da za'a ci da Sahur harma na buɗa bakin, harda na Almajiran Baba Mlm ɗin, wa'inda suma Iyayensu suke aiko masu abinci, saboda indai kana makarantar Baba Mlm baka taɓa zama da yinwa, baya ƙarbar almajirai har sai iyayen Yaro sun kawosa da abincin da zai ishesa har zuwa lokacin da zasu sake yi masa aike, sana zai bar ko wanne almajiri yaje neman sana'a amma itama sana'ar saiya bincika yaga idan mai kyau ce tukunna zai bar Yaro ya ci gaba da yinta, ba'a Bara a makarantar Baba Mlm ɗin saboda komai akwaisa babu abunda suka nema suka rasa. Kowa daga cikinsu ma wasu harda rushu ɗinsu suke zuwa domin dafa abinci da kansu, wani shago mai girman gaske ne a ɗaya bangaren dake gidan Baba Mlm ɗin, kamar gida yake, saboda gidan Baba Mlm na kallon inda almajiran ke kwana, kusan ɗaki uku ne a ciki, banɗaki biyu, shi yasa komai suna da shi, sai da azumi ya zo, wasu ke shigowa suna riƙon Ummi tayi abincin Sahur dasu, duk da sun san dama indai Azumi ya zo Baba Mlm ɗin yana cewa kowa ya aje abincinsa shine zai rinƙa ciyar dasu har watan azumin ya ƙare, to tunda ya samu karayar arziƙi shikenan ko wanne azumi suke dafa abincin buɗe bakinsu, to yanzu kuma buɗi ya zo ma Baba Mlm ɗin saboda dawowar abokinsa, shi yasa ya gaya ma al'amaran nasa kowa ya aje abincinsa har zuwa sadda za'a kammala azumi wannan shekarar shine zai ciyar dasu har watan ya ƙare, sosai Almajiran suka ji daɗin haka, saboda ba ƙaramin abinci mai daɗin gaske bane Baba Mlm ɗin yake sakawa ayi masu, yadda Iyalan Baba Mlm ɗin zasu ci abinci haka ake ba kowanne almajiri abincin buɗa bakin, shi yasa dukkanin Almajiran nasa suna bala'in ji da Baba Mlm ɗin ƙauna ce mai tsananin gaske a tsakaninsu.

Ummi ta so tayi aikin zuwa asuba amma Baba Mlm ɗin ya ce mata gara tayi shi cikin dare, a juye abincin a kuloli da asuba ɗin kawai ci za'ai, saboda baya so a makara da yawa, duk da tasan dama su gidan basa yin abinci da asuba, dafa sa ake a aje tun cikin dare.

Sai da aikin yayi nisa kamin Hali ta fito ta fara kama mata, sosai taji daɗin hakan, saboda kwana biyun ita ke sake kwantar mata da hankali akan auran da Baba Mlm ɗin ya ɗaura mata, shi yasa yanzu Baba Mlm ɗin baya yarda a aiketa, idan ma aiken ne zai aiko almajiri yaje aiken a maimakonta, saboda aure ne a kanta ba kamar da ba. Umma ko har mantawa ma take da wani aure dake akan Ummi ɗin. Ummi ma yanzu ta sake ganin yadda Ummar ke sake ja baya da duk wasu al'amuranta, sosai ta ƙara kame kanta itama tunda taga haka Ummar ke so, amma sosai abun ke damunta, itama har mantawa take da wai yanzu aure ne a kanta, itafa ba kamar da ba ce, ita fa gani take kamar ba gaske ba, shi yasa kawai ta aje komai ta ci gaba da rayuwarta, bare wannan watan da ake shirin shiga na Azumi tana wani irin mugun son watan Ramadan har zuciyarta wani irin zumuɗin shigowar watan azumin take, shi yasa idan ka kalli fuskarta a ƴan kwanakin da ake ta ƙirga saura kwana biyu saura kwana uku azumin kullum cike take da annuri.

Har suka gama abincin mai yawan gaske aka zuba al'majiran Baba Mlm a wata uwar kula mai girman gaske, sana ta ware ma Umma nata da Baba Mlm sai kuma nasu ita da Hali a kula ɗaya.

A nan suka aje

12 / 27