Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
*RAUNIN ZUCIYA*
(*Monday, Feb 10* 2025)
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
*EPISODE 1*
TSOKACI
RAUNIN ZUCIYA, SO shine ya shiga zuciyarta yayi mata mummunan tab'on da harta koma ga Allah bazata tab'a mantawa da wasu abubuwan data sanadiyar So yaja mata ba a cikin rayuwarta, so shine yasa ma Zuciyarta wani irin bala'in RAUNIN ZUCIYA ta yadda ko wanne mutum ya shigo rayuwarta take amsarshi a bisa RAUNIN da ZUCIYARTA ke dashi, tayi so da dama, tayi so kala-kala mai cike da darasi ga wasu jama'ar, sai dai Zuciyarta duk da irin wahalhalun data sha hakan baisa zuciyarta tak'i k'ara son wani ba idan har zai shigo zuciyarta, ya tafi yayi mata mummunan tab'o, ta yadda zata wahala da kyar zata dawo yaccinta, amma RAUNIN ZUCIYARTA shike sake fad'ar da ita ga son wani kuma, tayi kuka tayi kuka a so har bata son adadi ba. Shin yaushe ne zata samu mai sonta na hak'ik'a?, shin sai yaushe ne zata samu y'anci a soyayya?, yaushe ne zata daina shan wahala a soyayya?, yaushe ne zuciyarta zata warke a so?, sai yaushe ne sai yaushe ne?. RAUNIN ZUCIYA labarin ne daya shafi b'angaroro da dama, bazan ce komai game da wannan labarin ba, ku dai kawai ku biyo ni masoya.........
*Unguwar Yammawa Rimaye, Kankia Local Government Katsina State Nigeria*
K'arar saukan ruwan sama mai had'e da tsawa shine yayi nasarar farkawarta daga baccin da bai dad'e da d'aukarta ba. Lumshe idonta tayi da yayi mata wani irin nauyi da wani rad'ad'i da take ji suna mata.
A hankali ta juya d'ayan b'angaran da K'anwarta Halima take kwance wacce suka had'a uba d'aya da ita, ji take inama ita ce ita, mi yasa komai yake zo mata a baibai ne?.
Yau kimanin shekararta ashirin da biyar kenan a duniya, amma har yanzu batai sa'ar samun wadda zai zama jigo a rayuwarta ba. Mahaifiyarta bata raye, shi yasa gidan naso ya zame mata wani irin duhu mai cike da tsananin k'unci da damuwa, Matar Babanta Haj Maryama, wacce take kira da Umma, a hannunta taso ba abunda ta sani a tsakaninsu sai tsananin k'iyayyar Mahaifiyarta wacce tun kan ta zo duniya haka suke zaman doya da manja a tsakaninta Mahaifiyarta, harta haifeta da shekara d'aya Allah ya amshi abunsa, dole Haj Maryama ba dan ta so ba ta bar Ummi a cikin gidanta, ko magana idan zatai ma *AYSHA* wacce taci sunan Mahaifiyarta Baba yayi mata lak'abi da Ummi, ko kallonta bata yi domin wani irin bak'in ciki take ji idan tana kallonta a matsayin d'iyar mijinta, saboda tun asali lokacin da aka auro Mahaifiyar Ummi bata san da auran ba, sai da ana gobe Baba (Malam), zai aureta Umma ta sami labarin auran mijin nata, auran ma tare da wacce bata tab'a tunanin zai auri mace irinta ba, domin tasan yarinyar y'ar wani k'auye ce dake kusa dasu mai suna Hayin kwanta. Asalinsu y'an can ne, tallah ke kawota cikin garin Rimaye, har gidan Haj Maryama tana kawo tallah wani lokacin ta saya wani lokacin ma har shara da wanke-wanke tana tsayawa tayi ma Haj Maryamar.
Aysha macece mai kirkin gaske kwata-kwata bata da damuwa a rayuwarta, tana da bala'in sauk'in kai, ga dad'in zama bata d'auki rayuwarta a komai ba, tunda dama ta sani ita y'ar k'auye ce kuma marar gata gaba da baya. Abunda ya faruwa har Mlm yaji yana buk'atar auranta, Y'an Bindiga sun addabi yankin k'auyikansu kusan kullum sai sun shiga Hayin kwanta, wani tsautsayi ya fad'awa kakaninta dama su kad'ai suka rage mata ciki da bai, domin ta dad'e batai aure ba, domin har girma ya fara tasar mata, tun kakanin nata na damuwa har suka barwa Allah komai, a ranar da y'an Bindiga suka shigo Hayin kwanta harda gidan su Aysha tsautsayi ya fad'a masu, suka shigo suna jidar y'an mata a lokacin kakan Aysha yana kuka ya taimakawa Aysha ta haura katangar dake gidansu wacce ba wani girma ne da ita ba, saboda yasan idan suka jidi y'an Mata zuwa suke su zube su, su rink'a lalata dasu, su zame masu kamar Matansu na aure. Dai-dai lokacin da Y'an Bindiga ke shigowa gidan sunga lokacin daya taimaka mata ta haura katangar ta fice daga gidan da gudu, nan take suka sakar masa Bindiga shida matarshi, ogan y'an Bindigar ya bada Umarnin aje a kamo Aysha duk inda take.
Aysha tasha kuka tana gudu, tana kuka kamar ranta zai fita ga wani azababben zafi da k'irjinta ke mata tana dafe k'irjin nata tana gudu tana jin yadda k'arar tashin Bindiga ke k'ara karad'e cikin garin nasu. Da kafa ta iso Rimaye duk da akwai tazara sosai a tsakanin Hayin kwanta da Rimaye amma tsabar tashin hankali bata san lokacin data kawo Rimaye a k'afa ba, dama can kuma a k'afa take tahowa idan zata zo tallah, to wannan lokacin tashin hankali yasa da gudun masifa ta iso cikin garin Rimaye.
Lokacin data iso Rimaye dare yayi sosai a lokacin ne kuma ta had'u da Baba Mlm dake dai-dai karya kwana da Mota zai koma gida dawowarshi kenan daga Kankia Kasuwa, da yake duk ranar da Kasuwanni keci yana zuwa, d'an Kasuwa ne sosai.
Sosai hankalinsa ya tashi domin saura kad'an ya bigeta, hasken kwan Motar ne yasa yayi saurin gane wacece.
Hankali a tashe ya fito bai san lokacin daya ja hannunta ba ya tayar da ita daga k'asan data fad'i daya d'an bigeta kad'an ta fad'in.
Yadda ya ganta a firgice, a tsananin rud'e shima yake tabbayar miya kawota garin nan cikin daren nan?.
Tana wani irin bala'in kuka take sanar dashi abunda ke faruwa a Hayin kwanta.
Sosai shima hankalinsa yayi mugun tashi domin a kwanakin dama Y'an Bindigar sun addabi K'auyukan Rimaye, Rimayen abunda yasa itama suka gagari shigowa cikinta akwai Malamai masu yin addu'a koda yaushe duk asubar duniya sai anyi addu'a sosai domin Allah ya kare garin, shi yasa duk abunda zai faruwa sai dai suji wajen garin Rimaye, amma dai a shigo a kashe wani ko su jidi jama'a ba'a tab'a yi ba a Rimayen, shi yasa da yawan Y'an K'auyen dake kusa dasu wasu duk sun dawo cikin garin Rimaye saboda tsira da rayuwarsu da kuma gudun wahala.
A lokacin ya rasa ina ya kamata ya fara taimaka mata da inda ya kamata ya fara kaita, domin yasan ko karan hauka ya cije sa bazai tab'a kaita gidanshi ba, duk da yasan tana zuwa can d'in, amma yasan Haj Maryama bata da yarda ko misik'ala zarratin, yanzu zata fara masa y'an tuhume-tuhume.
Shawara d'aya ya yanke akan kawai zai kaita gidan wani abokinsa dake cikin garin.
A cikin daren ya d'auketa a Mota suka nufi unguwar Dokoki ba wata tazara bace a tsakaninsu da unguwar Yammawa d'in da Dokoki, dan haka dandanan suka isa.
A lokacin da abokin nasa yaji wayar da abokin nasa ke kiransa a tsohon daren yayi mamaki yama d'auka ko wani abu ne ya faru, shi yasa hankali da d'an tashe ya bud'e gidansa ya fito domin harsun k'ulle gida ma, tunda har goma ta wuce yawanci y'an garin da goma tayi na dare zaka tadda garin yayi tsitt yayi shuru saboda gujewa y'an Bindiga, domin suna wucewa ta cikin garin wani lokacin suna harbe-harben Bindiga ko kuma su tsaya a bakin hanyar garin duk wani shago dake bud'e su shiga su kwashe duk wasu kaya dake cikin shago, shi yasa dole suke rufe shagona da wuri suke wucewa gida a kulle gidaje da wuri.
"Mlm lafiya na ganka cikin tsohon daren nan haka?".
Mlm ya kalli abokin nasa da yake da yawan jama'ar garin haka suke kiransa da suna Malam tunda da yawansu ya koyar dasu a primary ko secondry, shi yasa suke basa girma bamai kiran sunansa sai dai suce Mlm koda a cikin abokansa ne.
Nan ne Mlm ya kwashe komai ya fad'a masa, sosai ya tausaya mata, inda ya ce masa babu wani abu zai aje masa ita har aga abunda Allah zaiyi.
Yaji dad'in hakan sosai. Sai dai ba'a je ko ina ba zaman gidan abokin Mlm d'in ya gagara, saboda Matarshi itama ta tada hankalinta sosai wadda takai ta kawo har fad'a mai tsanani ya shiga tsakaninsu, ganin hakan yasa Aysha da Mlm yazo tana kuka take sanar dashi kawai ya barta ta tafi.
A lokacin yaji bala'in tausayinta ya sake rufesa, yanzu idan ya barta ya zatayi?, ina zata fara nufa?, bata da kowa daya rage mata a yanzu, domin har Hayin kwanta sunje babu wadda yayi saura a cikin danginta, dama kakaninta ne kawai ta sani to suma an kashesu, sai gidan da suke zaune dama na haya ne ba nasu bane.
Bazai tab'a bari ta shiga duniya ba ta sanadinsa, baccin yana da abunda zai iya taimakonta dashi.
Kai tsaye ya gaya ma abokin nasa zai aureta insha Allah ya zame mata gata ko bayan ransa yasan hakan da yayi zai same mata gata ko a nan gaba.
Shima abokin ya basa goyan baya domin shi niyyarsa ma idan baida yadda zaiyi da ita shine zai auretan yaga yadda Matarshi zatai, domin Aysha irin Matan nan ne masu shiga rai dandanan su zauna, shi yasa kai tsaye da ya yanke haka, sai gashi Mlm d'in ya rigasa fad'a.
A washe garin ranar aka d'aura auren Mlm da Aysha.
A ranar kuma yasa aka gyara d'ayan d'akin dake kusa dana Haj Maryama.
Haj Maryama ta d'auka ko gyara yayi domin ya zuba mata wasu kaya.
Sai dai abunda ya tada mata hankali shine lokacin da aka kawo wata Mace wai a matsayin Matar mijinta, ya fad'a mata, amma ita ta d'auka ko wasa yake, Haj Maryama ba macece ita mai hayaniya ba, ko son magana wani lokacin, dan haka bata d'auki maganar da wani mahimmanci ba, amma lokacin da aka kawo mata wata wai a matsayin kishiya kuma watan ma Aysha wacce tasanta tasan k'ask'antacciya ce wacce bata wuce ta goge mata takalmi ba, ko ta zama y'ar aikin ta ba, amma wai ita ce a matsayin kishiyarta.
Zuciyarta ta k'asa d'auka a lokacin sai da aka kaita asibiti, domin wani hawan jini ne yayi mata mummunan kamu lokaci d'aya, had'e da wani ciwon zuciya. Tama kasa cema Malam d'in komai domin ko ci kanka bata ce ma Malam d'in ba, kuma hakan da tayi shi ya sake sa Mlm cikin tashin hankali, gani yake bai mata adalci ba ya bata hakuri har ba adadi, amma bata tab'a d'aga kai ta kalleshi ba.
Tana zaune ne da Aysha amma ko gaisu bata had'asu, Aysha kullum bata fasa gaisheta amma Haj Maryama bata tab'a amsawa ba koda sau d'aya ne, kai koda inda Aysha take bata kalla, idan tana wajan kuwa Haj Maryama zaka sameta ta mik'e daga wajan, ko inuwa d'aya bata san suna zama, abun na damun Aysha sosai amma ba yadda zatai dole take dannewa, itama sosai take ganin laifin kanta data amince da auran mutum kamar Malam d'in, wadda tasan nesa bama kusa ba yafi k'arfinta, bare Matarshi harta had'a kishi da ita.
A d'an K'ank'anin lokaci Aysha ta sami ciki, karsu ganin irin farin cikin da Mlm ya shiga, Haj Maryama ko bazaka tab'a gane miye a cikin ranta ba, ita kad'ai tasan yadda take ji a cikin zuciyarta, tasha yak'ar shaid'an akan Aysha da abunda ke cikinta, domin kar Allah ya bata ikon cutar da ita, amma kam ko magana har tsawon lokacin basa yi, sai ita Ayshar ke d'awauniyar yin hakan, sai dai a banza, shi akanshi Mlm yayi-yayi domin gidan nasa ya dawo dai-dai amma abun ya gagara.
A lokacin da Aysha ta haihu a asibiti ta haihu kusan satinta biyu a hospital amma ko sau d'aya Haj Maryama bata zo domin ganin ya jikinta da ganin abunda ta haifan ba, ta sami D'iya Mace a nan take kuma Mlm ya rad'a mata suna Aysha kamar yasan Mahaifiyarta Ayshar bamai tsawon shekaru bace, tun lokacin data haihu ta k'ara sarewa da lamarin Haj Maryama, ko barka bata jin tayi mata, a lokacin tayi kuka tayi kuka tana jin wannan zaman da suke yana bala'in damun zuciyarta, kwata-kwata bata jin dad'in zaman gidan Mlm d'in, kullum cikin k'unci suke su duka, duk saboda Haj Maryama ta kasa sakin zuciyarta ta amshi Ayshar a matsayin abokiyar zamanta, shi yasa gidan ya zama kamar wadda kullum ake zaman makoki, shi kanshi Mlm d'in duk ya rame tsabar cikin gidansa babu fahimtar juna tsakanin matan nashi.
An haifi Ummi da shekara d'aya Allah ya amshi Aysha, sosai mutuwar Aysha ta daki zuciyar Mlm wadda saida ciwon zuciya ya kamashi shima, aka kwantar dashi a asibiti. Haj Maryama ko baka tab'a gane yaya yanayin da take ciki.
Tun Ummi na shekara d'aya ta fara sanin lallai tayi rashin uwa, domin ana yin addu'ar arba'in komai Mlm d'in ke yima Ummi idan ya tafi wajan aiki kuwa haka zai dawo ya tadda ita a yadda ya barta, domin Haj Maryama bata tab'a d'aga kai ta kalli ya yanayin yarinyar take ciki ba, bare ta taimaka mata da wani abun, wani lokacin ne idan taso take mata wanka shima sau d'aya a rana, idan ta k'ara b'ata jikinta sai dai idan Mlm d'in ya dawo ya sake mata wani wankan ya gyara mata jikinta, tun bata fahimtar mike faruwa a gidan harta taso ta fara girma tasan wane irin matsayi take dashi a gidan, tana da shekara biyar Haj Maryama ta samu ciki, itama ta haifi d'iya Mace, aka Saka mata suna Halima, Ummi na kiranta da suna Hali.
Ummi na son Hali sosai sai dai Haj Maryama wacce tun tasowar Ummin take kiranta da Umma take hana Ummi zuwa inda Hali take kwata-kwata ta hanata sakewa da K'anwarta, bare har su sami wata shak'uwa.
Duk wani wankin Halima dana Ummar Ummi ce ke yinsa, tun bata iyawa harta koya da tsiya, duk wani aikin gidan ya dawo kanta ne, tun bata sababa harta saba da Hakan.
K'aryar arzik'i ce ta sami Mlm, wadda hakan yasa sai Haj Maryama ta ciyar dasu suke samun abunda zasuci, ita dama can tana kasuwacinta bata zama shi yasa yanzu ita ke da kud'in, shi yasa Ummi na na gama secondary school ta ce bata da kud'in da zata kaita wata kuma, dan haka dole Ummi ta aje karatun a gefe, sai zaman gida da uban aikin da take yi, ta koma kamar wata y'ar aiki ba y'ar gidan ba, shi dai Mlm kullum cikin jawo d'iyar shi a jiki yake, da ita da Hali.
Amma Halima ta taso itama da irin halayyar Mahaifiyarta na tsananin tsanar Ummi domin basa jituwa ko kad'an tun asali an nuna mata tsanar Ummi d'in, sai dai kamar uwar tata bawai kyararta sukeyi ba, a'a babu sakin fuska ne, basu zama da ita bare wata shak'uwa ta shiga tsakaninsu, ta tasu ba abunda ta sani sai rayuwar k'unci da tsananin kad'aici da kuma uban aikinsu kawai da bautar da take masu.
Hatta kayan sakawa sai Hali ta cire sana ake bata kwancen kayan Halin da su take sakawa ta d'an samu sutura, amma bata tab'a yin kaya sababbi nata na kanta ba, sai dai idan Hali ta cire ta gama yayinsu sana a bata kwance ta saka, Mlm na kallo amma baida yadda zaiyi tunda a hakan ma ya gode tunda bata tab'a cutar masa da Ummin ba, shi a hakan ma yaji dad'i.
A haka rayuwa take ta tafiya har girma ya fara zuwarma su Ummi kusan kansu d'aya da Hali saboda ta tasu mai jikin girma sosai shi yasa har tazo tafi Ummin ma.
Kota ina manema ke zuwa auran Ummi sai dai ba'a zuwa ko ina lamarin ke lalacewa, gashi yanzu har an saka ranar auran K'anwarta Hali, wadda dangin Umma da bakwafta har sun fara yada mata magana ana cewa tayi bak'in jini tak'i auruwa, duk da Umma b'ata tab'a gaya mata hakan ba a fili bata dama lokacin da zata tsaya tayi magana da ita, bare har ta tsaya ta goranta mata, domin ko kallon arzik'i bata samu daga wajan Ummar babu wata magana mai tsawo dake had'asu, amma a aikace take ganin kamar ta gaji da ciyar da ita ne itama, domin abunda take mata na rashin son ganinta da rashin bata mahimmanci a gidan ya sake dawowa sabo sosai.
Kowa ya shigo rayuwarta daga baya sai yazo ya gujeta bayan ta fad'a tsananin sonshi.
Yanzu ma soyayya suke ita da wani mai suna Tasiu asalina d'an Kaduna ne sun had'u ta hanyar Facebook tana yin Facebook da y'ar k'aramar wayarta Vivo, wacce ta Hali ce wadda ta gama yayinta ta tsofa da kyar ma Haj Maryama ta bari Halimar ta bata ita, sab'anin Hali dake da Babbar waya mai tsadar gaske.
Ta saba dashi ta soshi kamar zata mutu da k'aunarsa, haka take idan taso mutum wani irin bahagon so take ma mutum da zuciya d'aya, shi yasa take wata irin wahala a soyayya idan har aka gujeta, yanzu ma kusan hakan ce ke son kasancewa da ita.
Domin ta fara ganin canji a tare dashi saita kira wayarsa yafi sau nawa bazai d'auka ba bare ya biyo kiran, shi yasa yau da kuka ta kwanta tasha kuka kamar mi har idonta suka kunbura sosai.
Sauk'e lumfashi tayi yafi a k'irga tana jin yadda take tunano rayuwarta ta baya, mi yasa komai yake zuwar mata a haka?, ko bata zo duniya a sa'a bane?.