Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
Rumana aka bar
Awaisu da Gimbi. Kasa kallonsa tayi da dukar da danta yana kallon hawayenta suna diga akan
mayafinta. Tashi yayi tsaye a sanyaye yace
"We used to be best friends Gimbi...what happened to us?"
Sai lokacin ta dan dago kanta itama ta mike "son zuciyata ne ya faru Abban Haris, yau Maamu
ko cewa tayi ka sakeni tun zuwanta gidanmu bai halatta na kaita wurin boka ba balle bata yi min
komai ba. Ka yafe min mijina, ka taimakeni kada na nesanta daga rahamar mai rahama saboda
wannan gagarumin sabon da na aikata"
Idanunsa ya rufe sai ga hawaye suna sakko masa baiyi yunkurin tsayar dasu ko sharewa ba.
Hannunta tasa a hankali tana share masa itama yana share nata.
"Ban kyauta mana ba"
"Kaddara ce"
"Baka ce ka yafe min ba"
"Addu'ata Allah Yasa muna da rabon sake zama a matsayin ma'aurata a lahira"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki ta rungume shi tana kuka sosai.
"I love you Abban Haris"
Bai iya bata amsa ba sai bayanta da yake shafawa. Dago kanta tayi tayi masa murmushi "uwa
ba abar wasa bace kuma nayi imani indai muna raye bazaka taba mantawa da yanayin da ka
tsinci Maamu ba lokacin da ka dawo daidai duk lokacin da ka ganni. *Awaisu!* nasan duk
duniya bani da masoyi kamarka amma da bakina ina rokonka ka sauwake min domin zamanmu
bazai taba yiwuwa ba. Daga ranar da na fara kai kafata gidan boka na bata rayuwar aurenmu"
Hannunsa ya dora akan bakinta yana girgiza mata kai ita kuwa ta zame shi tace ya barta ta fadi
gaskiya. Ta tabbatar soyayya dai ta gaske yanzu Rumana yake yiwa kuma bata bakinciki.
Fatanta ya sami nutsuwar da ta hanashi da soyayya ta gaskiya.
A nasa bangaren ya yafe mata dama kullum fatansa ta gane gaskiya sai dai kamar yadda ta
fada bazai taba mantawa ba. Maamu ita ce jigon rayuwarsa ta yaya za'ayi ya manta da
hawayenta saboda soyayya.
Wata takarda ya dauko daga aljihunsa wadda ya rubuta tun ranar da taje asibiti da wannan
izgar dokin ya rubuta. Niyarsa sai ya hadata da limamin nan sannan ya bata.
Hannu na rawa ta karba ta bude. Saki daya ne yayi mata idan aka hada da na baya ya zama
biyu. Kuka ta saka duk da a ganinta ma yayi mata adalci da bai kai biyu ba ya raba tsakaninsu
gabadaya.
"Abban Haris nagode, lallai yau hannu ya girbe abinda ya shuka."
Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace *_la'in shakartum la aziddanahum wala in kafartum inna
azabiy la shadid_*. Yau ga Gimbi da Allah SWT Ya ni'imta da abubuwa marasa kirguwa ciki
harda miji nagari da suruka abar kwatance sai gashi haka nan babu gaira babu dalili ta janyowa
kanta nesanta daga dukkan jindadin rayuwarta.
"Allah mai gafara ne kisa wannan a ranki. All the best....my best friend. Ina miki fatan alkhairi a
rayuwarki ta gaba"
"Kaima Allah Ya baku zaman lafiya da Rumana"
Share hawayenta tayi ta fito tsakar gidan tana kwalawa su Haris kira. Dama sun tashi suka fito
a guje suna murnar ganinta. Dakin da aka sauki su Mama ta wuce tare da yaran ta basu
takardar sakin.
Sun gama hada kayansu tsaf suka fito nan kowa ya san hukuncin da Awaisu ya yanke
tsakaninsa da Gimbi. Sai da taje dakin kowa ta musu sallama sannan ta roki a barsu su tafi da
yaranta tayi kewarsu sosai. Baaba Hure tace ai babu mai hanawa. A mutumce suka yi sallama
Gimbi ta rungume Haj Fanta tana kuka
"Ki bar kuka Gimbiya inda rai da rabo kinji"
Murmushi Gimbi tayi "ina kika baro Gombo kuma Hajiya?"
"Tun jiya na nemeta na rasa sai Gimbiya uwar Harisu nake gani"
Dariya aka rinka yi da alkawarin zumunci sannan Mujahid yaja motarsa shima kanin Gimbi yaja
tasu motar suka kama hanyar Abuja.
Rumana da Awaisu sai washegari suka tafi da sassafe don baya son ta sake fashin makaranta.
******
*Bayan Sati Hudu*
Rumana ta gama girkin dare Daula kuma ta wanke duk abinda suka bata wurin girkin Haris ne
mai jere kwanukan akan dinning table suna ta surutunsu. Bayan sun gama Rumana ta zubawa
kowa sannan ta tafi tayi wanka kafin Awaisu ya shigo.
Shiru bata fato ba suka gama ci suna kallon cartoon har Awaisu ya dawo. Da murna suka tare
shi suna bashi labarin zuwansu gidan Mama yau da sakon Gimbi na gaisuwa gareshi.
"To ina amsawa bari naje nayi wanka na fito. Inna Ammin ku?"
Mu'allim yace itama wanka taje tayi.
Dakinta ya fara zuwa bata nan sai ya wuce nasa dakin. A kwance ya ganta ta rufa da bargo
tana bacci. Kasa shiga wankan yayi sai da yayi kissing dinta ya wuce yana tunanin neman mai
aiki. Ga karatu ga aikin gida yasan abin yana mata yawa.
Har ya fito tana nan kwance ya gama shirinsa ya kula tana yamutsa fuska cikin baccin sai ya
zauna a gefen gadon ya dora hannunsa akan goshinta zai shafa yaga tayi mugun zabura amma
bata bude idon ba
"Don Allah Anti kiyi hakuri"
Abinda yaji tana fada kenan sai ga hawaye ta soma kamar famfo. Jijjigata ya somayi a rude taki
tashi sai kiran Anti da take yi tana kuka. Rasa abinyi yayi kawai ya bude quilt din da ta rufa ya
dagota sai kawai jikinta ya saki jini ya balle mata cikin dan kankanin lokaci ya soma bin gadon.
Firgici da tsoro kan Awaisu ya gama yi. A guje ya dauko jallabiyarsa ya dora mata akan rigar
baccin jikinta ya dauketa yayi falo.
Yaran duka suka taso yace musu bata da lafiya su kula da gidan zai turo azo a daukesu baya
son su zauna su kadai. Duka sun tsorata ganin Ammi kamar yadda suke kiranta bata ko motsi.
Gudu sosai yake yi ya karasa national hospital saboda yana tsoron zuwa private ace babu likita.
Sake daukarta yayi ya shigarda ita emergency nan suka karbeta aka fara bata taimakon
gaggawa.
Awaisu yana reception ya dai kira Nuru ya fada masa yaje ya dauki su Haris. Shiru likitocin basu
fito ba daga dakin da take har Nuru ya kaisu gidansa ya taho shima. Ledar jini uku aka karawa
Rumana. Tashin hankali karshe Awaisu ya gani a wannan daren. Da suka fito ne suka yi masa
bayani cewa bari tayi ya kuma fita duka amma ba shi bane ya daga musu hankali kamar jinin da
take zubarwa. Sai dai suna ganin sun shawo kan matsalar yanzu in sha Allah. Yadda baisan da
cikin ba ya tabbatar da wuya idan Rumanan ma ta sani. Tausayinta yaji ya kamashi ya tafi gida
dauko mata kaya da shirin kwanciya. Amenity ya biya Nuru yace zai turo Kubra ta kwana
Awaisu yace ya gode amma shi zai kwana da ita.
Shabiyun dare ya dawo asibitin har lokacin bata farka ba. Likita dai ya tabbatar masa da cewa
bata cikin hatsari yanzu bacci ne kawai take yi saboda allurai da akayi mata.
A zaune ya kwana a gefen gadon. Sai wurin takwas na safe ta farka tana rike ciki. Kanta ne ya
nemi juyewa bata gane ina suke ba.
"Son So..."
Da sauri ya taso daga kan kujerar yazo ya duka inda take kwance ya rungumeta yana ajiyar
zuciya.
"Sannu kinji"
"Me muke yi a nan?"
Gabansa ne ya fadi "baki da lafiya ne na kawoki jiya. Ina zuwa zan fadawa dr kin tashi"
Hannunsa yaji ta rike "me ya sameni?"
Bai iya bata amsa ba ya fita can sai gasu sun dawo da likita. Dubata yayi ya gama rubuce
rubucensa ya fita.
Taimaka mata yayi ta zauna ta sake tambayarsa me ya kawota asibiti.
"We lost our baby Umm Ruman"
Zaro ido tayi tare da dora hannu akan cikinta "dama...dama...ina da...?" Sai kuka kuma.
"Shhhh kada ki damu muyi fatan shine alkhairinmu kinji ko. Allah zai kawo mana wasu masu
albarka"
A hankali ta gyada kanta ya rungumeta yana rarrashinta. Suna zaune a haka ya kira Harisu ya
fada masa. Nan da nan duka gidan suka sani. Maman Rumana ta shiga damuwa sosai har
Baaba ta kula da hakan ta fadawa Harisu gobe idan zasu tafi lallai a tafi da ita ta ga 'yarta.
Yinin ranar Awaisu baya fita daga dakin sai sallah. Daga gidan Nuru aka rinka kawo musu
abinci. Washegari da yamma su Maamu suka iso. Kafin su wuce asibitin da kanta ta yiwa
Rumana girki. Miya ce ta ganyen alayyahu, ugu, shuwaka wadda taji wanki sosai babu daci sai
zogale ga hanta, bushasshen kifi da koda anyita da manja. Kana ganin miyar kasan girkin ya
sami kulawa daga maiyi. Tuwon semo ta tuka mai kyau da ya dahu taje yin wanka Maman
Rumana ce ta kulle a leda suka shirya suka tafi.
Abin nema ya samu tana ganin iyayenta da Maamu sai shagwaba ta karu. Abincin ma cewa tayi
bazata iya ci ba Maamu kuwa tace Awaisu ya zauna ya bata. Kunya kamar ya nutse ganin
idonsu Harisu. Maamu ta soma fada idan bazai tashi bane ita sai tayi. Yana mikewa kuwa
Mama da Harisu suka kusa karo suna neman hanyar ficewa daga dakin suma kunyar suke ji.
Rumana da ta janyo abin daskarewa tayi a zaune tana takaicin me ya hanata ci da kanta.
Maamu ta kallesu duka tace "gulmammu". Nuru da Kubra me zasuyi in na dariya ba.
Bayan kwana uku aka sallameta su Harisu suka koma Fika. A satin Awaisu yace a nemo masa
'yar aiki aka samo wata mata zatayi kusan shekara arba'in Hanne. Ita take kula da shara da
goge gogen gidan banda dakin Rumana da Awaisu. Sai taimakawa wajen girki da kula da yara.
Zamansu suke cikin farinciki da kwanciyar hankali.
Wata biyu a tsakani Rumana ta sake samun ciki. Wannan karon ma basu sani ba saboda baifi
sati hudu ba. Tana wanka Awaisu yana aiki a dakin yaji kamar ta fadi. Bai san lokacin da ya ture
laptop din ba ya tashi da sauri ya bude kofar. A kwance ya sameta gefen baho ga jini yana bin
kafafunta.
Tsoro sosai yaji ya dagota da sauri yana kiranta. Shiru kamar wancan lokacin sai Anti da take
kira cikin galabaitacciyar murya. Wannan karon banda fargaba harda mugun bacin rai. Wancan
lokacin baya son saka zargi a ransa amma yanzu tabbas abin ya zauna masa a rai.
Maamu ce tayi zaman jinyarta don sai da aka hada da wankin ciki. Tasha wahala sosai akayi
sa'a cikin sati daya ta sami sauki.
Haka rayuwa taci gaba Awaisu na kula da iyalinsa sosai sai dai ya kasa cire abubuwan da suka
sami Rumana. Ko da ya tambayeta me take gani kafin tayi barin cewa tayi bata iya tuna komai.
Karo na uku da ta sake yin barin kiransa akayi yana wurin aiki yazo makarantarsu. Kafin yaje
sun kaita asibiti saboda irin jinin da take zubarwa. Tana zaune a aji kawai ta kwantar da kanta
kamar mai bacci wadda ke zaune a bayanta ce ta sanar da malamar dake ajin tana bleeding.
Da yake basu san tana da aure ba duk anyi zaton wata matsalar ke damunta.
Awaisu bai bata lokaci ba ya isa asibitin abinda yaji tsoro ne wato ta sake yin bari. Jikinsa har
wani tsuma yake yi yana tabbatarwa ta sami kulawa ga Maamu a kusa ya tafi gidan Alh Mudi.
******
Cikin girmamawa ya gaishe da Mama yace yana neman Gimbi. Tana daki da yake yanzu can
tafi zama tana karatu saboda masters da ta koma Mama tace Awaisu yana kiranta. Karamin
hijabi ta saka ta fito falon.
Ko zama batayi ba Awaisu ya tareta cikin bacin rai
"Gimbi me nayi miki haka da zafi ne?"
Kallon rashin fahimta tayi masa ita kuwa Mama jin ya daga murya ta kasa karasa barin wurin ta
tsaya daga bakin kofar falon
"Bangane ba?"
"To bari nayi miki kashedi gwaro gwari. Wannan ya zama karo na karshe da zaki zubarwa da
Rumana ciki. Na rantse miki idan irin haka ya sake faruwa zan kawar da duk wani sauran
mutumcin da yake tsakaninmu na dauki mataki"
Kirjinta ta dafe da yake neman bugawa saboda ciwon da yake yi mata. Wannan mugun son da
take yiwa Awaisu har yanzu da tuni ta gama iddah bai barta ba sai ma abinda ya karu.
Hawaye ta soma yi "Abban Haris wani ne yace maka na zubar mata da ciki?"
Yatsunsa uku ya daga a gabanta "sau uku kenan Rumana tana bari. Ko yaushe idan abin zai
faru sai dai ta kwanta kamar mai bacci tayi ta ambaton sunanki daga nan bazata sake farkawa
da cikin ba. Na dauke kai iya yadda zan iya amma bazan zuba ido ki nakasa min mata ba"
A fusace ya fita tana kiransa ko waige babu. Ta juya ta koma daki taji saukar maruka masu
radadi har uku a kuncinta. Mama ce tsaye tana hawaye tana hucin bakinciki
"Gimbi ashe tuban muzuru kika yi mana dama? Zubar da ciki har sau uku don rashin imani. Irin
haka fa kika yiwa Dr. Yana gashi ita har yau shiru kake ji "
Gimbi na kuka take ta rantsuwar ba ita bace amma a banza. Alh Mudi Mama take jira ya dawo
ta fada masa.
Da ta koma daki Dr. Yana ta kira ta tambayeta yanayin da ta shiga lokacin da tayi bari. Ta kasa
fahimtar dalilin tambayar gashi Gimbin kuka take yi ta fada mata. Tana ji hankali a tashe ta
dauki mukullin motar da take amfani da ita a gidan ta tafi gidan su Ovi.
Ita ce kuwa ta bude kofar tana mata murmushi "gaskiya Awaisun nan naki yana da hakuri indai
sai yanzu kika sami sakona"
"Me kike nufi Ovi?"
"Ina nufin duka zubewar cikin matarsa bai taba nuna yasan kece ba sai na yau ko." Dariya take
yi ta shige ta bawa Gimbi hanya ta shiga cikin gidan.
Ovi da kanta ta fadawa Gimbi ita ke sawa boka ya zubar da cikin Rumana kuma ya tabbatar
yayi yadda za'a zargi Gimbi.
"Mijinki ya bata min rayuwa duk iskancina ban taba kwana a cell ba sai dalilinku ke da shi. Ki
dauka ramuwa ce kawai nayi amma bana jin zan taba bari ta haihu yadda kanwata bata shiga
ba ita bari zata rinka yi mai ciwo ke kuma ayi ta zarginki"
Mari Gimbi ta sharara mata ta dafe kunci tace ta kiyaye abinda zai biyo bayanta. Fada sosai
suka yi na cacar baki sannan Gimbi tazo fita tayi saurin jiyawa gefen kujera inda ta hango wata
bakar tukunyar kasa. Dama tasan bokan Ovi ayyukansa yawanci da tukunyar tsafi ne tuni
zuciyarta ta bata dashi ake tsafin zubar da cikin. A guje ta ruga ta daga tukunyar Ovi tana ihu ta
rotsata da kasa. Kanta Ovi tayo ta fita da gudu ko takalmi bata saka ba Ovi na bayanta ta
hankadata kasan benen gidansu dama a sama suke.
Duk abinda suke yi Rita tana daki tana jinsu kawai bata son shiga ne. Gudun da taji ne yasa ta
fito daidai lokacin da Ovi ta hankada Gimbi. Duka sun rikice Ovi ta gudu daga gidan ita kuma
Rita wayarta ta laluba ta kira Awaisu dama tana da numbarsa.
Yana tsaye gaban Rumana yana jin kamar yayi kuka sai ga Mama ta shigo tana share hawaye
tana basu hakuri. Ko da Rita ta kira kamar kada ya daga sai kuma ya daure yasa wayar a
kunne. Don kada ya ajiye yaki sauraronta fada masa Gimbi na gidansu ta farayi sannan tayi
masa bayanin komai. Bai iya magana ba sai salati ya sake kwasa sai gidansu Ovi yana bin
kwatancen Rita.
A kasa ya sami Gimbi bata motsi shima da hawaye baya masa wuya sai gashi sun zubo. A
bayan mota ya sakata Rita tabi bayansa a taxi. Emergency aka kaita suka duba ta sannan aka
bata gado kusa da na Rumana. Rita gwiwa a kasa ta rokesu gafara sannan ta fada musu duk
abinda Ovi tayi.
Mama na rungume da Gimbi tana kuka Rumana ta farka. Lokacin Awaisu ya kira abokinsa DPO
ya fada masa duk inda Ovi take su kamata.
Sai gashi Rumana ta tashi amma Gimbi sai yamma ta farfado. Likitan da ya dubata yace ta
sami sauki buguwa ce dama da karaya a hannu wadda suka gyara.
Waahegari haka su Awaisu suka sake biyo hanya shima Alh Saminun Kano yazo duka suka
hado a asibitin ana yiwa juna jaje. Shuhada da iyayenta ma duka sunje.
Rumana bacci take yi lokacin likita yazo dubasu kowa ya fita. Wurin Gimbi doctor din ta tsaya
"Yanzu bazaki yarda na fadawa 'yan uwanki ainihin ciwon da yake damunki ba?"
Gimbi ta girgiza kai tana hawaye "ko kin fada bashi da magani. Na rasa wace irin soyayya ce
nake yiwa tsohon mijina"
"Har fa aman jini kike yi, ki bari a taimaka miki" doctor ta fada tana tausasa murya.
"Kada ki dami kanki ina bakin kokarina wurin cire sonshi daga zuciyata. Akwai kunya mai girma
idan nace zan zauna dashi. Labarin darasi ne ga mata. Ke dai duk yadda zakiyi a rayuwa ki
tabbatar baki cuci kowa ba, mafi alkhairi gareki shine a cuceki Allah sai Ya isar miki"
Hawaye ne ya gangarowa Rumana amma tayi dif kamar bacci take yi. Zantuka masu ban
tausayi Gimbi take yi a take taji mugun tausayinta kuma ta kara sonta domin taji komai game da
yadda ta fasa abinda akayi mata tsafi dashi.
Da daddare Rumana ta kafe babanta Harisu da ido idan zai juyo sau biyar sai sun hada ido.
Hawaye ya gani fal idon sai yaji tace ya kaita waje tasha iska.
Awaisu da bai san ta