Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   29 / 42

84K to 87K   out of 124.7K words

sannan ya kira cikin yaran
shagonsa yace yazo yana nemansa.

Kayan gidan kaf banda na dakin Gimbi amma komai harda kayan kitchen yace a samo dillalai
masu saya saboda da yawa basu tsufa ba. Kafin ya tafi suka shawarta ina zaije wurin kayan
furniture masu kyau. Sunan wani shago ya bashi a wata babbar plaza. Zama yayi yayi dogon
list na abubuwan da zai saya nasa da Rumana da yaransa. Kayan kitchen da su labulaye da
komai ya gama tsarinsa. Kudi dai zasuyi ciwo amma yadda ya tsorata da kayan tsafin nan ko
bai kara aure ba ya zama dole ya rabu da komai na gidan domin samun kwanciyar hankali.

Yaron shagon sai da yayi kusan awa daya ya dawo gidan tare da masu ganin kaya. Babu bata
lokaci sukayi ciniki suka turo motocin dibar kaya.

Gimbi na dawowa wurin karfe shida ta ga gate a bude motoci biyu manya cike da kaya suna
fita. A gigice ta shiga gidan ta sami Awaisu a falo ya zuba hannuwa a aljihu yana magana da
wani cikin mutanen inda yace duk da yasan zasu chanja kujerun amma suyi hakuri ya farke
dukkansu ta kasa. Kasa magana tayi jikinta na bari tana tunanin ba dai ya ga ajiyar da tayi
masa a daki ba. Ko da ta shiga nata dakin haka ta sami kayanta watse ko ta ina. Zama tayi jiki
babu kwari ta dago jakarta tana tunanin ta ina zata zuba masa wannan maganin da akayi mata
alkawarin karshen duk wata damurta yazo indai yasa shi a bakinsa.
*KASHE FITILA*42

*Batul Mamman*


_Allah Ya tabbatar da alkhairi Ya baku hakurin zama da juna da zuri'a dayyiba. Alhamdulillah_

*U & H*
*Its your dayyyyy*


Aiki su Awaisu sukayi tukura ranar sai bayan isha suka tafi zasu dawo dibar sauran waahegari
sannan shima zaije duba kayan da zai siyo.

Dakinsa ya wuce babu komai sai barguna da ya shimfida a kasa don hatta pillowas yayi waje
dasu. Kayansa kuwa da takardu wasu suna cikin akwatuna wasu ya turasu gefe a dakin. Wanka
yayi ya kwanta bayansa har ciwo yake masa saboda tsabar gajiya. Yana jin yunwa amma baya
tunanin zai iya fita daga gidan saboda ciwon jiki. Wayarsa ya dauko yana ta binciken aikin da
Rumana ta bashi har yau ya kasa gane me take nufi. Zuwa yanzu ma dai gani yake ko kawai
tsokanarsa tayi. Murmushi yake yi shi kadai idan ya tuna rabuwarsu. Bugu yaji a kofar dakin
kamar daga sama ana yi da karfi. Sai lokacin ya tuna ya rufe dakin da mukulli da zai shiga
wanka kada tazo ta saka masa wani abin a cikin kaya don ya tabbatar tunda ta fita babu abin da
zai hanata dawowa da wani maganin. Tashi yayi ya bude mata ta kura masa ido. Yanzu komai
nasa kyau yake mata fiye da yadda ta saba gani. Haushin kanta take ji sosai na wannan
makauniyar soyayya da bata yi ba ko da can da kuruciya da ta tabbatar ta so shi sosai.

"Naga an fitar da kusan komai na gidan nan banda dakunan baki da nawa"

"Sababbi zan siyo ai kinsan nayi aure ko? To amaryar ce zata tare nan ba da dadewa ba" yana
magana yana kallon hannuwanta da take kokarin taba shi dasu. Ja da baya yayi ya hade fuska
ta sauke hannun ba shiri.

"Ba zuwa nayi ka fada min bakar magana ba mijin Rumana mai budurwar zuciya. Nazo yi maka
tuni ne akan kayan fadar kishiya da ban ga kana da niyar yi min ba tunda kayan dakina banda
hargitsawa ko tsinke baa dauka an fitar ba"

Yatsansa ta ga yana kadawa a gefen kansa "Gimbi kin fara shaye shaye ne? Ni kike tambaya
kayan fadar kishiya? Idan har sai na baki zaki saka kaya to ki fara shirin yawo tsirara. Ke bari na
fada miki wannan hannun da kika shafowa kayan tsibbunki idan kikayi gigin tabani dashi sai na
karya shi. Sauran tarkacen da kika ajiye a lunguna da sakon gidan nan ma na konasu
gabadaya kuma in sha Allah kin gama samun nasara a kaina da 'yan uwana na."

Borin kunya ne ya kamata amma dayake ta kware ta daga kai tana hura hanci "ni ba damuwa
zanyi da sharrin da aka cusa maka yarda dashi daga gidanku ba. Idan ma ka tsinci wani abu
baya wuce wanda aka bawa Rumana ta binne a gidan nan don ka aureta. Kuma gashi
bukatarsu ta biya sai su zuba ruwa a kasa su sha"
"Kinga na gaji idan kin gama abin da ya kawoki sai anjima" kofar ya janyo ya rufe ya barta a
tsaye daga waje.

Shu'umin murmushin da yanzu take yi idan ta sami nasarar aiki tayi ta juya ta tafi. Indai itace sai
ya dawo bata hakuri don tun kafin ya bude kofar ta shafa maganin a jikin hannun kofar dakin.
Fatanta idan ya taba yaje ya dauki wani abu yaci da hannun ta samu maganin ya shiga cikinsa.

Sai bayan wurin rabin awa da tafiyarta ya bude kofar ya fito rike da karamin towel jike da ruwa.
Bismillah yayi ya goge kofar tun daga sama har kasanta. Duk da bai ganta ba amma yaji a
jikinsa yanzu ko ta wane hali Gimbi zata yi kokarin hadashi da magungunanta. Ji yayi kamar ya
saketa tun yanzu sai ya fasa. A kalla ta zauna ko na wata daya ne da Rumana ta kwashi
guzurin bacin rai ta tafi dashi.

Rumana ya kira Iman ta dauka tace masa tayi bacci. Ya kula tana kwanciya da wuri shiyasa
yake kiranta da farkon dare. Yau da bai kira ba ta sami kanta da jiran wayar tasa har bacci ya
dauketa. Gashi ita kuma tana kunyar kiransa da kanta.
*****

Washegari Rumana da wuri tayi wanka saboda Mama tayi mata waya tace taje gidansu Hajiya
Umma tana kiranta. Tana shiryawa Iman tazo ta zauna a kan gado

"Rumana kina kiran Uncle Awaisu kuwa?"

Ta madubi ta kalli Iman din "bangane ba?"

"Naga kullum sai dai yayi ta kiranki a waya. Jiya ma ya kira kina bacci. Ke ko dan text dinnan
bana jin kina masa bare su chatting a whatsapp."

Juyowa tayi da kyau ta kalleta "Iman, Uncle ne fa. Sai in yi masa text don rashin kunya."

Dariya Iman din ta yi taje ta kamo hannunta suka zauna "Jiya Ummanmu ta tambayeni ko kina
masa waya nace kuna waya dai don ban san dalilin tambayar ba. Shine tace in fada miki ki
rinka sakin jiki dashi gidansa zaki koma. Kuma dai Rumana baki gani mu masu samari ma ko
babu kudin kira mukanyi text balle ke da mijinki. Mijin ma kamar Uncle dan gayu dan boko"
Rumana tayi shiru jikinta ya danyi sanyi "tsakani da Allah ina son yi amma tsoro nake ji kada ya
fassarani yace sonsa nake yi"

Wani mugun duka Iman ta sakar mata a baya saki kara tare da mika hannu tana shafa wurin.
Iman tace "Wai kada yace kina sonsa. To da bazaki so shi ba bayan ya zama mijinki? Ko don
kinga babba ne" ta kare da sanyin jiki.

Kuka Rumana ta soma yi mata ta girgiza kanta "kunyarsa kawai nake ji har cewa yake yana
sona Iman. Idan ya fada sai naji har tsigar jikina na tashi. Wai ni yake so. Ta yaya zamu zauna
idan aka kaini Abujan? Don bakiji yadda gabana ke faduwa ba."

Duk da Iman ba wata babba bace amma tafi Rumana wayewa ta wannan fannin "ina jin fa kema
kin fara sonsa ne tunda kike jin haka. Ki rinka yi masa text ko waya kice gaisheshi zaki yi zaiji
dadi."

"Idan nayi niyar yin abu sai naji tsoron kada yace bani da kunya ko kuma idan banyi ba yaji
babu dadi. Shiyasa cikin biyun nake zabar rashin yin"

"Cikin kudin da ya aikowa Ummanmu da tace yace a baki ki karba kisa kati mana ki kirashi"

"Ya saka min kudi yafi 5000 a ciki shiyasa nace mata ta barshi bana bukata"

Harararta Iman tayi "kina da wannan kudin shine kika gagara kiransa. To yanzu kafin ki fitan nan
tura masa text na gaisuwa kawai"

Da taimakon Iman ta rubuta text don duk wanda tayi sai Iman din tace baiyi ba. Karshe
tambayarta tayi ko tana missing dinshi. Murmushi Rumana tayi ai kuwa Iman ta rantse sai ta
rubuta tunda abin da ke ranta kenan. Tana turawa ta kashe wayar ta saka a yar jakarta. Bata
ma son jin me zaice idan har yin text din laifi ne gashi Iman ta sakata rubuta abin da batayi niya
ba.
******

Yanayin gajiyarsa ta jiya ya sanya shi tashi a makare. Shima wayarsa maigadi ya kira ya fada
masa masu kwasar kaya sun dawo. Umarni ya bayar a bude musu gate yana zuwa. Alamun
sakonni text ya gani da yawa ya dan bude ya duba sunayen wadanda suka turo ko akwai masu
mahimmanci sosai ya fara cin karo da suna *SS* wanda a haka yayi saving din sunan Rumana
wato son so. Cikin sauri ya bude saboda yau ce rana ta farko da ta taba turo masa.

_Uncle ka tashi lafiya? Yaushe zaka dawo ne? I miss you._

Ya karanta yafi sau biyar bakinsa ya kasa rufuwa saboda farinciki. Karshe dai screenshot
yayiwa text din yasa shi a screensaver. Da ya kirata yaji a kashe yasan kunya taji shiyasa ta
kashe.

A gurguje ya tafi wurin masu kwasar kayan aka ci gaba da gyaran gidan.

Gimbi na ganin shigarsa daki ta koma nata dakin tsabar murna harda tsalle tayi. Bokan Ovi
bashi da wasa tasan indai anyi yadda yace bukata kuwa zata biya.

Rabuwa tayi dashi sai dare bayan ya dawo daga zabar kayan gida da zai saya ta shiga dakin
tayi kwalliya tasha turaruka tana zuba kamshi.

Karar ruwa taji daga bandaki tasan wanka yake yi ta sami wuri ta zauna. Yana fitowa ya ganta.
Dauke kai yayi ta danyi murmushi

"Kaga ba fada ne ya kawoni ba. Magana nake so muyi"

"Ina jinki"

"Ba wani jan zance zanyi ba yarinyar nan da ko sunanta bana son fada nake so ka saki"

Fuska ya saki ya ce "shikenan bukatarki?"

Bokan nan ba dai iya aiki ba ta fada a ranta "sauran komai mai sauki ne indai ka saketa"

"Miko min takarda da biro zaifi akan na tura text"

Jiki na rawa tana sauri ta dauko masa takarda da biron daga cikin jakar da yake zuwa office da
ita. A kasa ya zauna yace ta matso ta rinka gani. Da ta tashi harda shigewa jikinsa.

_Ni Awaisu Kabir Fika na saki Gimb.._

Wata muguwar wawura Gimbi tayiwa takardar. Kafin ya farga ta nadeta ta cusa a baki tana
tauna iya karfinta.

Awaisu baiyi magana ba ta tashi a fusace ta fita harda buga kofar dakin da karfinta. Sai a
lokacin yayi dariya don ya fuskanci abin nata ya soma zama hauka. Wato ta saka masa magani
ne nan a tunaninta yayi aiki a kansa.
*****

A can Fika kuma da Rumana taje gidan kakaninta nasiha suka yi mata sosai da shawarwari
akan zaman gidan miji tunda abu ne yazo musu duka babu shiri. Anti Umma tata shawarar
harda yadda zata kula da kanta da kuma canza salon yadda take gabatar da kanta a gaban
Awaisu domin kuwa yanzu mijinta ne shi kuma wannan matsayin ya danne duk wata alaka da ta
san suna da ita a baya. Wasu abubuwan dai ji take sun girmi tunaninta musamman da yake ita
ba mai kwashe kwashen kawaye bace bata tashi da lallai sai ta koyawa kanta ilimin da komai
dadewar lokaci indai mace tayi aure zai zo gareta ba. Anti Umma tace mata lokacin kunya ya
kare tunda an shafa Fatiha, yanzu sai karatun yadda za'ayi zaman. Ranar a nan ta wuni sai
yamma likis ta koma gidan Anti Ummukulsum.

Bata jima da tafiya ba kayayyakin da dangin Mama suka tura kannensu biyu Kano su siyo suka
iso. Yawanci kayan kitchen ne kuma sunyi kokari sosai don an mata siyayyar da ta dace duk da
kurewar lokaci. Su Anti Umma ne suka kai kayan gidan Harisu a matsayin tasu gudummawar.
Lokacin yake sanar dasu yadda sukayi da Awaisu akan yi mata siyayya.
Anti Umma tace babu yadda zasu aurar da 'ya ko tsinke babu. Aure daban zumunci daban.
Basa fata ko da wasa nan gaba wani abu ya taso gori ya biyo baya.

*****

A hankali kowane bangare ya cigaba da shiri. Rumana tana can tana shan gyara a wurin
Antinta. Awaisu kuma ya wadata gidansa da duk kayan bukata don har fenti aka sake yiwa
gidan. Kayan kitchen ne Harisu yace ya dakata har sai an kawo wanda gidansu Mama sukayi
don sunyi rawar gani kada ayi ta asara wurin sayan wasu.
Gimbiya bata sake shiga sabgar Awaisu ba don ba karamin tsorata tayi da sakin da ya kusa
auna mata ba. Yanzu jira take yi Rumanan ta iso gidan ai ba sai da Boka kadai zata iya sawa ta
bar mata gida ba. Har nawa take da zata yi kishi da ita.

Yau alhamis Awaisu ya tashi daga wurin aiki ya wuce gidan Alh Maitama. Sun dade suna
magana da shi akan halin da Gimbi da Anti Bebi suka sakasu.

"Babu abin da yake damuwa Mal Awaisu kamar kashewa Shuhada aure da tayi. Wallahi da
mijin nata yazo gidan nan ya shiga wani irin yanayi. Kuma gashi saki uku ne"

Awaisu ya jinjina kai. Mutanen nan sunyi nisa. Yanzu dole sai dai ta auri wani anyi mata katanga
da masoyinta. Shuhadan ya nemi gani bayan sunyi sallama da mahaifinta. Sun gaisa a
mutumce har yake bata labarin abubuwan da suka faru da Maamu har zuwa aurensa da
Rumana.
Baki da rike tana dariya "Kaga ikon Allah ko. Allah sarki Rumana yaushe zata tare muzo yiwa
Gimbi dannar kirji?"

"Sai ki taho da yan sanda saboda na tabbatar bazaku rabu lafiya ba" shima yayi maganar yana
dariya.
"Shuhada nagode sosai da taimakon da kika yi min duk da a lokacin ban san me yake faruwa
ba. Kuma ina so don Allah mu cigaba da zumunci. In sha Allah har gidan nan zan kawo miki
Rumana kafin kema Allah Ya kawo mana suruki musha biki. Alhaji yace akwai kaninki da zaku
je gani ba don haka ba da na gayyaceki biki har garinmu"
Murmushi tayi "in sha Allah zumunci yanzu muka fara. Sai dai batun aure sai dai zuwa nan
gaba. Yanzu dai masters zan nema in sha Allah"
*****
Ranar Juma'a yana ta murna zai je Fika da sun tashi sai dai wannan karon da dreba zaije
saboda ya sha wahalar tuki wancan zuwan. Rumana tun da tayi masa text dinnan bata sakewa
dashi sosai sai ya kyaleta yana jiran su hadu.

Yau ma baiyi nasarar gano aikin nan da ta bashi ba gashi har ya kusa tafiya Fikan. Yayi ta
browsing akan sign language bai ci karo da wannan alamar ba. Hakura yayi kawai yace zai sa
ta fada masa da bakinta. Idan tsokana ne kuwa yasan maganinta don ta bashi wuya.

Wurinsu Haris ya fara zuwa ya kaiwa su Mama kudi duk da basu karba ba yayi musu alkawarin
yana gama gyaran gida zai mayar dasu. Sai dai ya kula suna jindadin gidan sosai kuma ga
chanji sosai a yanayin tarbiyarsu. Daula ce mai tsiwa ya kula tafi kowa nutsuwa duk da ba wai
ta dena wasa ko harkokinsu na yara ba.
Anti Ummukulsum ya fadawa tun safe yana hanya bayan ya tashi daga aiki amma yana so tasa
Rumana yi masa girki duk da bai fada mata ya taho ba. So yayi ta ganshi kawai.

Da taimakonta Rumana ta dafa tuwon shinkafa da miyar taushe wadda aka sawa ganyen ugwu
da alayyahu don tasan yana daga cikin abincin da yake so. Sai lemon kankana da apple mai
dadi.

Anti Ummukulsum ta tafi amsa wayar maigidanta shima washegari zai dawo Rumana tana cin
cingam ta ciro shi ta sake dandana miyar a karo na barkatai. Miyar tayi mata dadi sosai amma
sai taji kamar da dan tsami wanda dandanon cingam din bakinta ya saka mata.

Fridge ta bude ta dauko soyayyen jajjagen attaruhu da albasa ta kamfata a cokali daidai yadda
take jin zai daidaita miyar ta zuba cokali biyu. Ta sake debowa taji Anti Ummukulsum na tahowa
tayi saurin ajiyewa don ita tace miyar tayi.

"Rumana ba dai karawa kika yi ba?"

A tsorace tace "yanzu zan zuba naji kamar da tsami"

"Ba dole kiji tsami ba kina ta fama da cingam mai tsami sosai. Kunfi so kuji miya ana ci ana
shhhh da baki. Kije kiyi wanka ki shirya ina jiranki yanzu"

"Fita zamuyi?"

"Zamu je gida ne amma kiyi sauri kada yamma tayi"

Rumana ta tafi ta shirya tana saukowa ta ga Anti Ummukulsum ta hada kwanukan abincin a
cikin wani kwando mai kyau. Kwandon tace ta dauko su tafi.

Suna zuwa gidan da murnarta ta shiga dakin Maamu don tayi kewarta sosai. A guje ta shiga
tana kiran Maamun. Kamar yadda ta saba fadawa tayi jikinta tana tambayarta yaya jiki.

"Jiki da sauki Rumana ina maman taki?"

Sai a lokaci ta kula ita kadai ta karaso. Ashe Anti Ummukulsum din ta tsaya a falon Harisu inda
suke hira da Awaisu yana masa fadan yaki cin abinci.

"Rabu dashi na amarya yake jira. Ta shige dakin Maamu bari nace ta kawo maka abincin"

Harisu ya kalla yana yar dariya "Yaya anyi min izinin tashi"

Harisu yace nan da sati biyu zaku bar min gida ni dai. Dafe kai Awaisu yayi ya fita yana dariya
Anti Ummukulsum na tsokanarsu su biyun.

Rumana tana jikin Maamu

29 / 42