Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
tana ya6a mata magana ta fice ko sallama babu. Dama can ba wai tana ganin
mutumcinta bane. Tun suna yara sun san tayi kaurin suna a dangi saboda fitinarta. Yanzu ma
dole ce ta kawota. Zata nemarwa kanta mafita.
*****
Bayan kwana biyu Awaisu yake sanar da ita cewa nan da sati uku su Maamu zasu taho Abuja
domin ta nan zasu tashi. Kuma an kusa fara dibar alhazai. Sanan za'a taho da Rumana tun
yanzu domin taya Laminde zama da su Haris da kuma sabawa ita ma da gidan. Da murnarta ta
dauko takarda tana yi masa list na abubuwan da take so a karo musu na kayan abinci da kayan
masarufi domin tarbar baki. Yadda take yi masa dole duk wani sauran zargi da bacin rai da yake
ransa ya kawar dashi.
Bayan ya fita a gigice ta kira Anti Bebi har ta manta abin da ya faru tsakaninsu. Ita kuwa tana
ganin kiran taki dauka. Sai da ta kira yafi sau biyar sannan ta amsa tana magana da kyar wai ita
a dole anyi mata ba daidai ba.
Gimbi bata yi fushi ba ta fada mata yadda suka yi da Awaisu. Anti Bebi tace idan zata iya ta je
ta sameta a gida washegari su tafi wani kauye a Nasarawa state inda Wangesi na tsangaya
yake.
Da daddare kuwa ta karantawa Awaisu karya da gaskiya saboda kada ya ga bata dawo gida da
wuri ba daga bankin da take aiki. Shi kuwa sanin yanayin aikinsu bai kawo komai a ransa ba sai
addua da yayi mata.
Washegari tana zuwa wurin aiki tayi karyar ciwon ciki ta samu manaja ya yarje mata komawa
gida. Daga nan bata zame ko ina ba sai gidan Anti Bebi. Ko zama batayi ba suka kama hanya.
Dreban Anti Bebin ne ya kaisu. Tayi mamaki sosai yadda taji suna hirar malamin tsibbun tare
dashi. Ashe shine ya hadasu ma. *****
Wangesi ya bata layu da guraye da zata saka a cikin gidan wanda su Maamu suna zuwa zata ji
ta tsani gidan saboda zafin da zaiyi mata. Saboda yarda da shirkarsa da yayi har alkawarin
dawo mata da kudinta yayi idan Maamu ta iya kwana uku a gidan batare da ta matsa a mayar
da ita Fika ba.
Gimbi murna ba'a cewa komai. Tana zuwa gida tayi duk yadda yace ayi da kayan da ya bata ta
zauna jiran lokaci.
Ranar da zasu zo ta kama asabar. Tun kafin asuba ta farka ta shiga kitchen tana ta dafa kayan
tarbar baki. Laminde ma a nan ta sameta. Awaisu kuwa zuciyarsa fes ganin ta sake tana nuna
masa ta fishi murnar zuwansu.
Dama dreba ya tura aka dauko su. Motar na shigowa yaran suka fita a guje suna murnar
ganinsu. Haris tamkar ya shige cikin Harisu don murna. Ba karamin son kawun nasa yake yi ba.
Maamu ce karshen fitowa daga motar. Kafar dama ta fara saukewa cikin sanyin muryarta tace
"Bismillah tawakkaltu alallah" [2/7, 10:42 PM] +234 814 971 0186: *KASHE FITILA*í ½í²¡9
*Batul Mamman*í ½í²–
Awaisu da yaransa duk da murnarsu suka koma cikin gidan tare da su Baaba. Maamu ce
karshen shigowa. Ta tsaya a waje ta karewa gidan kallo. Yau danta wanda ko rabin fuloti bai
mallaka ba shekarun baya da suka wuce shi ne da dankakaren gida irin wannan. Addua tayi
sosai ta neman tsari da kariya gareshi da zuri'arsa da kuma sanya albarka ga samunsa. Sai da
ta gama ta shigo ciki. Nan ta tarar da su Baaba Hure suna ta kalle kallen gida su ma suna
yabawa.
Kayan abinci Gimbi da Laminde suka rinka fitowa dasu suna jerawa a tsakiyar katon kafet din
falon. Sai da ta gama sannan tazo ta durkusa har kasa tana gaishesu tana satar kallon fuskar
Maamu. Wangesi dai yace gidan zafi zaiyi mata da kanta zata nemi a mayar da ita inda ta fito.
Wani murmushi tayi sannan ta cigaba da tambayar Rumana yaya mutan gida.
Da yake Maamu banda amsa gaisuwa da kalmomi kadan ita ba Hausa ta iya ba shiyasa bata
shiga hirarsu sosai. Baaba ma yau da gobe tasa Hausarta sai a hankali, ta iya amma sai ka
zata ba bahaushiya ke magana ba. Haka Rumana da Zakiyya su duk da sun dan iya amma ba
kamar Awaisu mai auren bahaushiya da kuma Harisu dan kasuwa ba. Bolanci yafi kama
bakinsu. Hirar dai aka ake yinta wani abin sai kaci dariya. Idan kaga Gimbi a tsakiyarsu sai ka
rantse ko goyo suka nema zata yi musu. Shiyasa basu taba korafi akan ta ba. A ganinsu
yanayin aiki ne yake sawa bata zuwa Fika sosai.
Dakin da aka tanadarwa Maamu nan Baaba tayi masauki tare da Zakiyya. Gado ne kato wanda
zai ishi mutum hudu ma. Ba karamin kashe kudi Awaisu yayi ba. Harda tv ya saka mata da
fridge. Baaba da aka soke zuwanta Abujan itama yayi shirin sake gyara mata nata dakin kafin
su dawo daga Hajji.
Ranar a wurinsu ya yini shi da Harisu. Da safe zai tafi aiki ya bar sallahu cewa drebansa zai
dawo sai ya kai Harisu kasuwa ya ga shagon nasa.
Kwananusu biyu babu wata matsala da ta taso. Ranar laraba Awaisu zai tafi aiki Gimbi take
sanar dashi ta dauki hutu na tafiya Hajji. Ya nuna mata jindadinsa tunda ga baki dama a gidan.
Bayan fitarsa bai dade ba Anti Bebi tazo. Da yake safiya ce babu wanda yasan tazo ta shige
dakin Gimbi. Mayafinta ta cire wanda ya bayyana siraran kitson da akayi mata da karin gashi.
Dama ita da wuya tasa dankwali. Dan mayafi ne guntu shara shara kullum take fama dashi.
"Ke kuma sai naji ki shiru babu wani jawabi game da bakinki?"
Gimbi ta tabe baki "hmmm Anti wannan anya ba kudina yaci ba. Kullum naje dakin sai tayi ta
murmushi babu alamun ta soma gajiya da gidan. Ita fa fuskarta kullum a sake kamar mara
lafiya. Har tunani nake ko aljanun nan ne masu sa dariya basuyi mata kamu sosai ba aka tsaya
a murmushi"
Dariya sosai Anti Bebi tayi "Shegiya Gimbi, ashe kema baki da mutumci, yarinya tayi gadon
uwa. Kuma ina mai tabbatar miki indai zakiyi yadda nake yi to babu wanda ya isa ya taka ki"
Gimbi shiru tayi. Idan da Mama zata ji abin da take yi yanzu Allah kadai Yasan fadan da zatayi
mata. Balle kuma Alhajinsu da ya dauki son duniya ya dorawa Awaisu. Shi a ganinsa ba
karamin dace yayi da surukai ba.
Sai bayan azahar Anti Bebi ta dauki mayafinta
"Tashi muje na ga bakin naki sai na wuce daga can. Idan anyi sati babu chanji da kaina zan
koma wurin Wangesi"
*****
A falo suka tarar dasu harda su Haris sun dawo sun tsaya basu labarin makarantarsu.
Anti Bebi kallo daya tayi musu taji babu wanda yayi mata a cikinsu. Duk da cewa zata yi sa'ar
Ummu kulsum 'yar Baaba Hure ta uku domin ita ce autarsu Mama amma daga tsaye ta dan
dago musu hannu
"sannunku"
Zakiyya ta amsa mata tana yi mata wani irin kallo. Wannan mata duk inda ta fito akwai rashin
kamun kai a tattare da ita. Labaran da akeyi a tashar NTA Hausa shine ya dauki hankalin Baaba
Hure ga Rumana ta biyewa su Amir suna ta hayaniya. Remote din tv ta dauka zata karo sautin
yadda zata ji jawabin mai kawo rahoton. Tana cikin dannawa Anti Bebi ta kwashe da dariya
"Mhmmm ashe harda su kaza a cin danko. 'Yata kinyi sa'a su o'o hannu baya gani ya kyale. To
gaskiya a dage a sayo musu computer"
Baaba Hure ji tayi kamar an zuba mata ruwan zafi saboda yadda zuciyarta ta harzuka. Bata
bukatar wani bayani tasan cewa da ita wannan bakuwar take. Ajiye remote din tayi jikinta babu
kwari tana jiran amsar da Gimbi zata bayar sai ji tayi tace
"Waya ga dan wake a hotal"
Zakiyya da Maamu sai dan murmushi sukeyi. Ita Zakiyya duk da tana dan jin Hausa ko kadan
bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba balle kuma Maamu.
Baaba Hure ganin haka itama sai ta biye musu tana murmushin. A iya saninta Gimbi bata san
cewa ita asalin bahaushiya bace. Kuma yanayin da Hausarta ke fita da wuya ace tana gane
karin magana indai ba yarenta bane. Gara ta nuna musu itama bata ji ko don ta ga iya gudun
ruwansu. A lokaci daya kuma tausayim Maamu ya cika mata zuciya. Ashe Gimbi ba son Allah
da Annabi take yi musu ba. Indai hakane kuwa akwai matsala wannan zaman da zata yi a
gidan.
Da yamma da Harisu da Awaiau suka shigo. Baaba taso ta sanar da Harisu abin da taji sai
kuma tayi tunanin kada ta zama uwa mai sa ido. Daga faruwar abu daya bai kamata ta yanke
hukunci akan cewa Gimbi ba mutuniyar arziki bace. Hakan yasa ta fasa cewa komai.
*****
Bayan kwana hudu aka kirasu sune diba na biyu. Awaisu da drebansa sukayi mota biyu aka
kaisu Airport. Basu dawo ba sai da jirginsu ya tashi.
Madina suka fara wucewa. Tun a hanya Gimbi ta soma zazzabi mai zafi da amai. Suna isa aibiti
aka kaita likita yace taci wani abu ya bata mata ciki. Duk rashin kirkin da taso gwada musu sai
ta koma abar tausayi suna jinyarta. Kwanakin Madina kaf bata ji dadinsu ba. Haka suka je
Makkah can ma bata da wani kuzari. Wannan Hajjin dai bata ji dadinsa ba kwata kwata. Daga
zazzabi ya warke sai mura mai zafi da ciwon wuya. Haka sukayi kwana talatin suka dawo da ita
duk ta fige sai mugun nufi a zuciya.
*****
Sai da sukayi sati da dawowa sannan suka koma Fika aka bar Maamu da Rumana. Gimbi ce ta
samar mata makaranta wadda bata da nisa sosai da gidansu. Makaranta ce mai tsada mai kyau
don kawai ta burge Awaisu.
Da taga hankalinsa a kwance yake da abubuwan da take yi ta koma gidan Anti Bebi tana
korafin rashin aikin maganin Wangesi.
"Kwantar da hankalinki naje na same shi. Yace wannan magani ranar da suka je gidan wani abu
ya bata sihirin da yake ciki." Wata leda ta dauko ta mikawa Gimbi.
"Ga wannan yace ki dafawa mijinki abinci dashi. Daga ranar a hankali duk wani so da kulawa da
yake yiwa uwar tasa zai fara fita daga zuciyarsa. Sai kiyi amfani da wannan damar ki gasa mata
aya a hannu. Da kanta zata kwashi kafarta ta gudu gashi an daure bakin"
Karba tayi jindadi ya bayyana a fuskarta
"Ina fata wannan karon a dace. Idan ba haka ba kuma zanyi maganinta da kaina. Shiru shirunta
irin na munafukai shi nafi tsana. Kinsan irinsu abin tsoro ne. Ga wannan yarinyar da suka zo
tare mai cin tsiya. Ina tsammanin horon yunwa zan fara yi musu a gidan"
[2/7, 10:43 PM] +234 814 971 0186: *KASHE FITILA*í ½í²¡10
*Batul Mamman*í ½í²–
Ranar laraba da daddare Gimbi da kanta tayi girki sabanin yadda ta saba saboda yanayin
aikinta Laminde ce take yi. Maganin da aka karbo mata ta juye shi tas a miyar Awaisu ta kara
maggi.
Da ya dawo dakin Maamu ya fara zuwa ya gaisheta tare da zama zai fara hira ta dube shi duk
da alamun gajiya a tare dashi
"Ka tashi kaje kaci abinci ka huta na yafe hirar nan"
"Maamu ni sai kiyi ta korata. Da Yaya Harisu ne ai sai kin gama sauraronsa"
"Sannu baban kishi. Yanzu dai ka tashi, ka ga matarka itama ba zama take yi ba. Dan lokacin
naku kuma bazan so na hanata sakewa ba. Ni ban zo gidan nan don takura muku ba. Abokan
hirar nawa ma abinci suka tafi ci. Yanzu zaka ga sun dawo"
Tashi yayi rike da coat dinsa a hannu yace zai dawo bayan yaci abinci yayi wanka. Har ya fita
tana cewa ta yafe hirar yau.
Wanka yayi Gimbi ta biyo shi da abincinsa daki wai falon hayaniya tayi yawa. A haka tana yi
masa hira ya cinye tuwon da ta zuba masa harda neman kari. Dadi ya kamata kuwa. Yanzu
abin da ya rage kawai shine ta fara gwada aikin maganin.
*****
Washegari saboda fitarsu aiki da zuwan yara makaranta tun asuba suke tashi ranakun aiki.
Kitchen ta shiga ta aunowa Laminde shinkafa sannan ta fito da kazar da ta tafasa tun dare.
"Kiyi min jallof din shinkafa taji alayyahu da busasshen kifi. Wannan kazar kuma pepper chicken
nake so kiyi. Kiyi komai cikin sauri kinsan Abbansu Daula baya son jira."
Laminde ta gyada kai "To Hajiya, amma shinkafar bazata ishemu har su Hajiya Babba ba da
'yan makaranta"
Gimbi ta koma store din da yake cikin kitchen din ta dawo rike da wata karmasasshiyar doya.
"Shinkafar ki dafa mana ni da yara da babansu. Wannan doyar kuma fate zaki yi muku ke da
sauran mutan gidan"
Laminde ta kalli doyar ta kalli uwargijiyarta. Ita dai tunda take a gidan ba'a taba yi mata
wulakanci akan abinci ba. Wani lokacin ma ita Gimbi take barwa zabin abincin da za'a dafa.
Kasa shiru tayi ta dan rausayar da kai tana kara kallon doyar da ta bushe
"Wai Hajiya nace ba, uhmm ita Hajiya Babba nake nufi ki karo shinkafar saboda ita"
Daure fuska Gimbi tayi "sunanta Maamu ba Hajiya Babba ba. Wannan so kike yi wani yayi
zaton ni da ita uwargida da amarya ne. Anyway, itama faten zaki zuba mata naji ance tana son
doya. Ga langa can da na karbo wurin Mama. Kinsan mutanen da suna son komai irin na
zamaninsu. Shine na nace har sai da Mama ta bani cikin nata tun na aure. A ciki zaki rinka zuba
mata abinci. Kuma kiyi sauri tare zamu fita zan aike ki"
Kasa hadiyar yawu Laminde tayi domin tsananin mamaki. Langa ce da gaske ga kuma doya da
akace ta zuba mata. Ko ita da take aiki yau tasan anso wulakanta ta bare uwarmiji. Magana
take son yi amma sam bakinta ya kasa hada kalma ko daya. Tana ji Gimbi tace ita zata yi musu
nasu girkin wanda suke tafiya dashi wurin aiki yaran kuma suje dashi makaranta. Ita kuma tace
tayi sauri tayi faten kada su makara.
*****
Rumana cikin sauri ta gama shirinta tsaf saboda bata so a jirata. Tun fara zuwa makarantarta
kwanaki biyu da suka wuce tare suke fita da yaran gidan da Gimbi. Dreba ne yake kaisu
makaranta ya wuce da ita wurin aiki. Tunda a banki take shiyasa suke yin sammako sosai.
Ko da ta fito falo Mu'allim ne kawai Gimbi take bashi abinci a baki yana ta rigima shi bacci yake
ji. Har kasa ta durkusa ta gaisheta sannan ta nufi dinning table inda kayan tea suke zata hada.
"Dakata Rumana me zakiyi a nan?"
Murmushi tayi ta kirata yadda yaran gidan suke kiranta "Mummy tea zan sha kafin su Haris su
fito"
"Kinga daga yau ki rinka zuwa wurin Laminde ki sha tea din a can."
Bata ji komai a ranta ba tayi hanyar kitchen. Sake dakatar da ita Gimbi tayi "Kiyi sauri kisha ki
fito kada ki makara"
Dayake bata san sunan dreban ba sai tace "Mai kaimu makarantar har yazo ne? Bari na fadawa
su Amir suyi sauri su ma"
"A'a kina jina ko Rumana, makarantarku ba wani nisa gareta ba. Ki rinka shiryawa da wuri kina
tafiya. Tafiyar da mukeyi da ke tasa ina makara kwana biyu. Gashi ba'a gama abinci ba. Idan kin
dawo sai ki ci. Tea din ma ruwan zafin aka juye a girkin sai an dafa wani"
Sai a lokacin Rumana taji wani iri a ranta.
"To Mummy bari na tafi, sai kun dawo"
Gimbi harda murmushi "yauwa Rumanan Abba. Allah Ya kiyaye kinji."
Rumana ta dan tsaya jim ko zata bata kudi tunda sai hudu da rabi suke tasowa. Gimbi ta
fahimci dalilin tsayuwar ta dan sake fuska "ko akwai wani abu ne Rumana?"
"A'a babu komai. Na tafi"
Fita tayi tana tafiya a hankali. Allah Yasa makarantar a bakin titi take kuma babu wuyar ganewa.
Tafiyar minti shabiyar zata kaita idan tayi sauri. Iyayenta ne suka fado mata a rai taji kamar ta
fashe da kuka. Bata san yadda zata fassara abin da Gimbi tayi mata ba. Tayi kamar minti biyar
tana tafiya taji mota ta tsaya a gefenta. Horn da akayi yasa ta kalli motar. Mace ta gani tasha
lullubi sai wata yarinya mai uniform irin nata. Da ta sake kallonta ta tuna ajinsu daya duk da
bata san sunanta ba. Gaishe da matar tayi cikin hausarta.
"Shigo mu karasa kin fito cikin sanyin nan ko rigar sanyi babu. Kada kiji tsoro ga Yusra ajinku
daya tace min"
Bayan motar ta shiga ta sake gaisheta sannan Yusra ta juyo "Sunanki Ummu Ruman Abali ko"
Rumana ta gyada kai tana murmushi. Hira uwa da 'yar suka cigaba da yi har suka iso kofar
makarantar.
"Umma baki bani kudin break ba fa"
"Yusra bana son wannan kashe kudin da kike son koya. Ga abinci nan a jakarki"
Yusra ta sake kwantar da kai "Umma ko hamsin ce saboda siyan ruwa"
Dari biyu maman ta mika mata "gashi ku raba da Rumana idan kun fito. Allah Ya bada sa'a"
Rumana tayi mata godiya suka jera cikin makaranta tare da Yusra wadda take yi mata
tambayoyi akan makarantar da ta baro. Da haka ta manta da bacin ran da ta fito dashi.
*****
Duk sun gama shiri sun fito Awaisu ya tambayi ina Rumana. Gimbi tace
"Ta tafi, wai makarantar babu nisa zata rinka tafiya da kanta."
Bai ce komai ba suka fice saboda ya leka Maamu tana bacci.
Bata farka ba sai karfe tara da kusan rabi. Sabanin yadda ta saba ganin tray din