Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
ciwon bai gagaremu ba shine zaka ce zaka fitar da ita?"
"Baki fahimceni bane, ina so ta sami kulaw ne sosai saboda wasu dalilai nawa"
Dariya tayi ganin yadda yayi da fuska da gaske yake.
"To don Allah ka bari ta kara samun sauki sannan ko fitar zakayi da ita sai kayi."
Godiya yayi mata ya koma cikin dakin. Rumana wadda har yanzu bata kula shi tayi saurin
mikewa zata fita.
Girgiza kai yayi ganin da gaske yarinyar nan fushi take yi dashi "Rumana ina zuwa?"
Kamar yayi magana da dutse ko girmansa bata gani ba tayi hanyar kofa. Ai kuwa manyan dake
dakin suka hauta da fada ta fita a fisace tana hawaye. Tasan har abada bazata taba manta
rayuwar gidan Awaisu ba. Idan ta kalli Maamu haushin kanta na barin gidan ita kadai take yi da
kuma na Awaisu da ya gagara kula da ita.
Maamu na kallonta ta kalli yadda ya bita da kallo wai itama ta zama 'yan mata ta iya fushi. Daga
inda take zaune ana bata abinci tace ya bi bayanta ya rarrasheta.
Anti Suwaiba tace ya rarrasheta ko ya zane ta dai "yarinya taki sakawa ranta salama kullum
fushi"
Maamu ta sake kallonsa "idan ka taba min ita zamu sa kafar wando daya da kai da yayar taka
mai bada shawarar"
Anti Suwaiba na dariya ya fita yana cewa yanzu duk duniya ai babu da mai ladabinsa.
Ya dan wahala wurin nemanta kafin ya hangota can wurin ajiye motoci a durkushe tana share
hawaye. Wurin ya karasa tana ganinsa ta kuma tashi sai dai kafin ta fita ya rufe hanyar. Dama
tsakanin wasu motoci biyu ta zauna a wani dan tudu wanda bayansa fence ce babu hanyar fita.
A tsiwace tace "zan wuce"
Yana kada kai yace "Rumana..."
Bai kare magana ba ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Idan da zata tona abubuwan
da Maamu ta rinka dannewa a zuciyarta a zamansu a gidansa bata jin ko ruwa zai kara sha da
dadin rai. Gabadaya komai ya sire mata har tsoro take ji kada itama ta girma duk yadda tasan
Awaisu yana son Maamu ya koma haka itama ta zama hakan.
Tausayi ta bashi sosai ya mika hannu zai rungumeta sai kuma ya fasa. Wannan ba 'yar karamar
Rumanan nan bace. Shi bai san ma yana ina yarinya yar shekara goma sha shida ta zama 'yan
mata haka ba.
Da hannunsa ya nuna kansa ya dan rage murya "nine ko? Kiyi hakuri Umm Ruman Uncle
Awaisunki bazai kara bari abin da ya wuce ya kuma faruwa ba"
Baki ta dan tsuke "ni ba Uncle Awaisuna bane"
"Har kin manta haka kike fada a gida kice naki ne ke kadai? Muje a tambayi su Baaba idan mun
koma gida "
"To na fasa ba nawa bane"
Kwaikwayonta ya sami kansa da yi yace harda yin alamun kuka yace "don Allah kice naki ne ko
na fadawa Maamu"
Dariya yaso bata sai ta wani gimtse fuska wanda ya lura da hakan. Inda ta baro yace tazo su
zauna ta fada masa duk abin da ke ranta ko zata sami sauki.
Dr. Yana da take tsaye a jikin motar Mujahid tun dazu ta sauke ajiyar zuciya ta shiga. Kallonta
yayi yace sannu da shanya ta dan kwanto a jikinsa tana fada masa wani kyakkyawan gamo tayi
wanda dole ma ta ga faruwarsa.
*KASHE FITILA*í ½í²¡34
*Batul Mamman*í ½í²–
Cikin kuka Rumana ta rinka zayyanawa Awaisu wasu abubuwan da suka faru dasu a gidan. Ciki
wasu ya sani har yana mamakin sai yanzu da take fada yake jin haushinsu. Me yasa a lokacin
baiyi yunkurin daukar mataki ba. Ita ce tambayar da yayi ta maimaitawa kansa. Zuciyarsa ba
karamin nauyi ta kara yi masa ba. Ba don a gaban Rumanan bane babu abin da zai hana shi
kukan bakinciki.
A raunane yace "Abin da yasa kika dawo gida kenan? Me yasa baki taba fada min ba?"
Tambayar tasa ta biyu ce taji a kamar wani rainin wayo. Ita fa yanzu daga shi har matarsa tayi
alkawarin dena ragawa kowa sai dai idan tayi a daketa ace mata mara kunya.
Wani kallo ta bishi dashi kafin tace "Uncle a gabanka fa yawanci ake yi"
Ajiyar zuciya yayi "haka ne....hmmmm...tashi ki koma ciki. Komai zai daidaita in sha Allah"
Mikewa tayi tana tafiya yabi bayanta da kallo. Hakuri yaso bata na kasa rikonta da yayi sai
kuma ya fasa kada sauran girmansa ya zube don ya tabbatar yanzu ba wata kima gareshi ba.
Ita kuwa tana tafiya tana tuno wasu abubuwan da kunya tasa ta kasa sanar dashi. Yaushe zata
manta cewa a iya zamanta na gidan kafin tayi rabin shekara ta koma yin gunzugu na mutan da
da dankwalayenta saboda rashin kudin siyan pad. Daga baya ne da suka shaku sosai da Yusra
ta fada mata shine take bata a makaranta. Tsigar jikinta ce ta tashi da ta tuna yadda take
kasancewa duk wata.
Awaisu bai bar wurin ba ya zurfafa a tunanin wannan rikirkitacciyar rayuwar tasa da ya kasa
fahimtarta yaji wayarsa tana ringing. Kyalewa yayi sai da yaji mai kiran ya nace ya dauka.
Muryar mace yaji tayi masa sallama a hankali ya amsa yana tunanin inda yasan wannan murya.
"Shuhada ce, ka gane ni ko?"
Ji yayi hankalinsa ya kuma tashi. Yaushe zai manta da ita, matar da Maamu ta dage sai ya
aureta lokaci guda.
Jin yayi shiru yasa ta kalli Daddynta da yake zaune kusa da Mamansu wadda ta dawo sati biyu
da suka wuce.
Alh Maitama ya mika hannu ya karbi wayar yayi masa sallama.
"Suna na Alh Maitama mahaifin Shuhada"
A mutumce Awaisu ya gaishe shi. A garin Abuja waye bai san wannan sunan ba. Tsoronsa daya
ba dai maganar auren bace zasu sake tayarwa.
Daga daya bangaren yaji Alhajin ya soma yi masa magana.
"Malam Awaisu ina son haduwa da kai ne domin wasu maganganu masu mahimmanci "
"Shikenan" ya fada a ransa yana tunanin tabbas zancen auren ne. A zahiri kuwa ya sanar dashi
baya gari kuma bai saka ranar dawowa ba yanzu saboda rashin lafiyar mahaifiyarsa.
Fatan samun lafiya yayi masa sannan yace "don Allah ka nemi ne idan ka dawo yanzu Shuhada
zata turo maka nambar da zaka sameni. Ina kuma yi maka adduar yadda Allah Ya fitar dani
kaima Ya fitar da kai lafiya. Sai naji daga gareka"
Yafi minti biyu yana kallon wayarsa yana kokarin gano me Alh Maitama yake nufi da maganarsa
ta karshe. Daga karshe ciki ya koma ya sami wuri ya zauna kusa da gadon Maamu. Idan ta
dago kai sai ta ga yana yi mata kallo mai cike da tausayi. Murmushi kawai take yi tana
ayyanawa a ranta ko yanzu ta bar duniya Alhamdulillah. *****
Bayan sun gama wayar Alh Maitama ya mikawa Shuhada wayarta.
Mamanta Haj. Rahama ta ce "Daddy yanzu kana ganin zai yarda idan ka fada masa abubuwan
da matarsa da Bebi suke yi?"
"Ni da na yarda a yanzu nasan ba komai bane illa karfin addua da ikon Allah. Gabadaya jina
nake kamar rayuwar da nayi da ita a mafarki ta faru. Lokaci yayi da matan nan zasu fuskanci
hukuncin laifukansu. Dubi Shuhada duk irin son da mijinta yake mata Bebi ta shata musu layi
bazasu kara zama tare ba idan har ba wani auren ta kuma ta fito ba. Kina ganin akwai iyayen
da zasu so a rinka kirgawa 'ya'yansu aure ne?"
Haj Rahama ta girgiza kai. Ita kanta Allah ne Yayi da sauran zama tsakaninta da masoyinta
uban 'ya'yanta. Saki uku Anti Bebi tasa yayi mata daga shigowarta gidan. Fushin da tayi akan
wannan sakin yasa tana gama idda tayi aure don ta nuna masa tana da sauran daraja. To da
yake bata son mutumin zaman nasu yaki dadi ga kishiya can ma ta matsa mata. Auren bai jima
ba ta fito.
"Waccan ledar yaya za'ayi da ita ne" ta nuna ledar da aka kulle da tarkacen layoyi, guraye, ruwa
kala kala a robobi da kananun tukwanen kasa duka dauke da sunayen Alh Maitama da iyalinsa.
"Munyi magana da wani malami a islamiyar da su Shuhada sukayi. Yace zai zo karshen sati ayi
addu'o'i sosai a gidan sannan a konasu."
'Yarsa ya kalla tana gefe tayi shiru sai ta kara bashi tausayi.
"Ki kara hakuri kinji 'yar Daddy. In sha Allah da sannu Allah zai baki miji nagari. Jiya shima
Tajuddeen nayi ta masa nasiha akan yayi hakuri ya fawwalawa Allah komai. Ni da kuka ganni
duka abubuwan da suka faru kara min imani sukayi da sanin cewa lallai Allah Shi kadai Ya
cancanci a bauta maSa."
Sun jima suna hira wadda kusan dukkanta akan yanayin da suka tsinci kansu ne bayan zuwan
Anti Bebi. Basu tashi ba sai da yayi musu alkawarin tafiya wurin Suhail cikin wata mai kamawa
sai su jira ya kammala jarabawa su taho gida tare. Kudi kuwa ba kadan ya tura masa ba yace
ya biya duk abubuwan da ake binsa na makaranta da bashin abokai idan yaci.
*****
Yau Harisu ya tsaya a daya daga cikin shagunansa sunyi lissafi da yaron wurin. Yana dawowa
Baaba Hure dama a shirye take ta fito su tafi asibiti cikin Damaturu. Sun kusa fita daga layin
gidan nasu ta hango ta yi saurin cewa Awaisu ya tsaya. Juyowa yayi yana kallonta ta waiga
baya
"Wata na gani a motar can da ta wuce kamar Gimbiya"
Ransa har ya baci jin sunanta yace "Gimbiya kuma Baaba me zai kawota yanzu?"
"Juya mu koma gidan dai. Na tabbatar ita na gani"
Ba musu suka koma. Ai kuwa suka hadu da Gimbi da yaranta a waje suna fitowa daga mota.
Harisu da Baaba suka kalli juna ganin yadda ake ta fito da kaya daga boot. Kwalayen juice ne
kala-kala da kayan abinci irin su shinkafa, maggi, taliya, mai da sauransu. Motar wata
hadaddiya ce amma mai mazauni uku.
Tana ganinsu Baaba ta dena yamutsa fuska musamman ganin yaranta sunyi wurinsu da gudu
suna murna. Harisu yaji dadin ganinsu domin jinin Awaisu ne don yana kin babarsu baya jin
akwai dalilin da zai sashi kin yaran.
Gimbin ma da sauri ta karaso wurin Baaba ta fada jikinta tana ta murna.
"Baaba mun sameku lafiya? Yaya gida ?"
"Da kin bari mun shiga ciki sai gaisa sosai" Baaba tayi gaba yaran na biye da ita.
Suna shiga ciki Gimbi ta nufi dakin Maamu tun a tsakar gidan take kwala mata kira kai kace 'ya
tazo ganin babarta ne bayan sun jima basu hadu ba.
A bude kofar take saboda an ajiye kayan wankinta da safe baa rufe ba. Ganin babu kowa kuma
dama tasan babu din ta fito tana gaisawa da matan gidan. Su mamakin kayan da ake shigowa
dasu sukeyi. Harisu ta kalla tana murmushi
"Yaya Harisu shine daga zuwa ka dauke mana Maamunmu ko? To kafata kafarta tare zamu
koma kuma mu hada da Baaba Hure kaga mun koma 'yan gata ko ta ina. Tana ina ne?
Maamu???" Ta kare da daga murya tana kiranta.
Murmushi Baaba Hure tayi wanda Gimbi tayi zaton na murnar tace zasu tafi da ita Abuja ne. A
zuci tace kwadayayyu. Ita kuwa Baaba Hure tsabar mamakin rashin kunyar Gimbi take da
gogewa a kissa. Tana kallonta tace
"Su Makiru manya"
Gimbi a razane ta kalli Baaba ba dai da ita take ba ta dan hade rai da tsoron kada a dagota.
Baaba ta fahimce yadda fuskarta ta sauya ta daga kai tana kallon sama tana magana cikin
kulawa da sassauta murya
"Makiru shegen tsuntsu, idan baka iya takunka ba da ranka da lafiyarka sai ya sunkuce maka
da ya barka da ciwon zuciya. Tsuntsaye da dama tsoronsa suke yi. Gimbi kuna dashi a Abuja? "
Harisu ne yayi saurin magana saboda tsoron kada daga nan Baaba ta fadi maganar da zata
janyo rikicia take a wurin don bata da hakuri indai an taba nata bisa rashin gaskiya. Yafi so cikin
ruwan sanyi su shayar da Gimbi mamaki akan abin da tayi.
"Babana ina Abbanku ne" ya dafa kan Mu'allim yana tambayarsa. Yayi sa'a babu kowa a wurin
sai shi da Baaba kada wani yayi saurin cewa Awaisun yana nan.
Gimbi tayi saurin cewa yaran "kai ku shige ciki"
Bayan taga shigarsu dakin Maman Rumana ta dan tabe baki "Yaya Harisu lamarin kaninka sai
addua kasan yadda ayyuka suke masa yawa. Tare muka so zuwa tun farkon tahowarku da
Maamu sai aka tura shi Lagos. Na kasa hakurin jiransa ne nace bari na taho kawai kewar
Maamu ta dameni. Shi kuma kwana biyar ban sami wayarsa ba ma, ina zaton aikin can din ne
yayi masa yawa ko an sace wayar."
Ikon Allah, wato da haka ta taho zata nuna bata san me yake faruwa ba kenan ta mayar da
laifin kan mijinta. Girgiza kai yayi kawai yace "Allah Ya kyauta. Kuci abinci ku dan huta sai mu
tafi Damaturu. Dama asibiti zamu je wurin Maamu muka ga shigowarku shine muka dawo"
Jakar hannunta mai mugun tsada ta saki a kasa ta dafe kirji "asibiti kuma? Me ya sameta?"
Bai kai ga bata amsa ba ta soma kuka harda daga murya. Nan da nan kuwa aka fara fitowa
daga dakuna kallonta. Su Haris ta kira tace su zo su tafi asibiti Maamu babu lafiya.
Wadanda ke wurin manya mamakin diramar Gimbi suke yi yayin da ta zamewa yara abin kallo.
Tare da Baaba suka sake fita ta shige tasu motar da 'ya'yanta wsu Harisu na gaba suka dauki
hanya.
*****
Kana shiga dakin Maamu zaka san cewa akwai soyayya da shakuwa tsakanin ma'abota cikinsa.
Maamu zuciyarta ta sanyaya har tana ganin ya kamata a sallameta ta karasa jinyar a gida. Ga
su Anti Baraka da 'yan uwanta ana ta wasa da zolayar juna. Lokaci lokaci sai ta kalli Awaisu
wanda ya kasa dena yawan kallon Rumana.
Murmushi tayi domin bai dade da fada mata cewa yana tsoron dasa kiyayyarsa a zuciyarta ba
duba da cewa yarinya ce kada abubuwan da suka faru su kasa gogewa a ranta. A lokacin
Maamu cewa tayi kada ya damu indai Rumana ce zata hakura. Yanzu ma ganin yadda ciwo
yaci karfinta ne yasa ta zama haka har take ganin tamkar laifinta ne na dawowa ita kadai. Da ta
fada masa haka cewa yayi yadda ta bashi labarin abubuwan da suka faru a gidansa yasa
jikinsa yayi sanyi. Yasan Girmansa ya fadi tana masa kallon wanda ya kasa rike mahaifiyarsa
bai cancanci a ga girmansa ba.
Maamu gani tayi abin ba komai bane Rumana yarinya ce mai ladabi da hakuri komai zai wuce
nan gaba. Amma yadda Awaisu yake ta jan maganar da nuna damuwa yasa tace masa to
yasan yadda zaiyi ya dawo da kimarsa a idon Rumana tunda abin ya dame shi haka.
Jin ta fadi haka yasa shi saurin mikewa "Maamu ba fa wani abu nake nufi ba abar zancen nan
dai".
"Dawo dai mu karasa sai ka fada min me kake nufi"
Matsar da kujerarsa yayi can gefe cikin 'yan uwansa shi kadai namiji a cikinsu yana dariya. Sai
dai duk motsinsa a idon Maamu tana kallon inda idanuwansa suke yawan sauka.
Wasu ne suka zo dubiya daga Fika dangin Baban Awaisu maza da mata dakin ya dada
kaurewa da hayaniya da gaishe gaishe. Rumana da ta kasance karama duka dakin sai ta matsa
can gefe bayan ta gaishesu. Sallamar Babanta taji ta tashi karbar kayan da yake hannunsa
idanunta suka sauka akan Gimbi. Nan take jikinta ya hau bari tsoro ya kamata ta kasa motsin
kirki a wurin. Awaisu na ganin yadda ta tsorata don bai ma ga Gimbi ba ya taso yazo gabanta
ya tsaya tare da rage tsaho ya hura mata iska a fuska.
"Umm Ruman are you okay?"
Hawaye ne taf ya cika idonta duk yadda ta rinka tsara rashin kunyar da zata yiwa Gimbi ranar
da duk suka sake haduwa ji tayi abubuwa da dama sun dawo mata a lokaci guda sai
matsanancin tsoro da fargaba.
Ledar da ta fara karba a hannun Harisu ya karbe ya ajiye a kasa yace mata ta wuce su fita daga
dakin. Daga kan da zaiyi ya mikawa Harisu hannu su gaisa ya hada ido da Gimbi wadda tayi
mutuwar tsaye.
A zuciye take da yadda ta ga yayiwa Rumana. Harda wani sabon salo wai Umm Ruman. Sunan
da rabon da taji ya ambata tum farkon zuwansu Abuja kafin Wangesi ya fara aiki a kansa ita da
Maamu ya manta da lamarinsu ballantana sunayensu. Kishi ne ba bala'i a cikin idanuwanta da
suka kada sukayi jazur. Me yasa boka yace kada ta biyo mijinta washegari? Me ya faru a
kwanaki biyar dinnan da ya dawo Fika?
Daga kan gadonta Maamu ta gama kallon komai tsaf ta kuma gano ta inda in sha Allahu zata
nunawa Gimbi nata ikon na mahaifiyar Awaisu. Tun da ta fara samun lafiya ita da Baaba Hure
suka saka shi a gaba da fada akan sakaci da azkar. Sun karfafa ko ma meye ya same shi da
yadda ya damu da neman kudi kawai batare da yawaita yiwa kansa addu'ar neman tsari ba.
Yaransa ne suka rungume shi suna murnar ganinsa shima yayi murna domin yayi kewarsu.
Gimbi da duk abubuwan da take yi tun zuwanta shawarwarin Ovi ne ta rasa me yake mata dadi
saboda ganin da tayiwa Awaisu da Rumana yana nuna damuwarsa a kanta. Kenan asirinta ya
soma karyewa tunda har ya damu da wata karan kada miya Rumana. Kula da tayi dakin ita
suke kallo yasa ta mayar da idanunta ga Maamu wadda kallo