Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 42

3K to 6K   out of 124.7K words

Yaya da an taba shi. Ya hada musu 'yar tsaraba daidai misali sannan ya ja
Harisu gefe.

"Mutumina nayi maka karambani fa, jiya bayan rabuwarmu naje gidan wani tsohon dan
kwangila da nake sayar wa shadda"

"Kana nan da shige shigen ka mutumina" Harisu ya fada yana murmushi.

"Me za'a fasa..yanzu dai mu bar wannan zance. Cikin hira nayi masa bayanin ina da kani da ya
gama karatu yana neman aiki. Sai dai anyi rashin sa'a bansan me ya karanta ba. Shiyasa
bayanin nawa bai cika ba"

Farinciki sosai ya bayyana a fuskar Harisu
" da gaske kake?"

Murmushi yayi ganin abokin nasa yaji dadi "yanzu dai yace sati mai zuwa zashi Abuja wurin
wani kusar gwamnati. Shine yace idan zai yiwu Awaisu ya same shi a can ranar alhamis"

Kati ya dauko mai dauke da sunan mutumin da nambar wayarsa ya mika masa.

"Gashi Allah Yasa a dace. Idan yaje sai ya fada masa cewa shine kanin Saminu Zawachiki"

Harisu ya rike hannuwansa ya ma rasa kalmar godiya "idan munje zaka ce. Ai dole na rakashi.
Allah Ya baka ladan zumunci."

Yafito Awaisu yayi da hannu ya matso kusa dasu ya fada masa halaccin da Saminu yayi musu.
Shima godiyar yake yi kamar zasu ari baki su biyun.
[2/7, 7:09 AM] +234 703 322 0429: *KASHE FITILA*💡4

*Batul Mamman*💖




Ranar laraba da yamma Harisu da kaninsa suka isa Abuja. Da tambaya suka karasa gidan Alh
Mudi Maibuta, dan kwangilan da Saminu ya nemi taimakonsa akan neman aikin Awaisu.

Gida ne babba irin na mutanen da naira ta zauna musu. Daga bakin gate din maigadi ya
tambayi sunansu da abin da ya kawosu. Suna fada ya saki fuska tare da sanar dasu Alhaji ya
bayar da umarnin yi musu iso da zarar sun karaso.

Wurin wata katuwar bishiya ya rakasu inda Alhajin yake zaune yana shan iska. Gefensa 'yan
mata ne guda biyu sanye da kaya iri daya.

Tun tahowarsu Awaisu wurin babbar ciki ta kafe shi da ido tana murmushi. Shi kuwa hankalinsa

bai ma kai gareta ba. Cike da girmamawa suka gaishe da Alh Mudi. Shima fuska a sake ya
amsa musu sannan yace su shiga wani daki kusa da na maigadinsa.

Abinci yasa aka kawo musu aka yi musu tarba a mutumce. Sai da suka ci suka koshi sannan
ya dawo ya karbi takardun Awaisu. Murmushin fuskarsa ya fadada
"Ikon Allah ashe kaima Bauchi kayi karatu. Kila ma ka taba haduwa da Gimbi."

A ladabce Awaisu yace "Wane ne hakan?"

Alh Mudi ya hau dariya "Yarinyar wajena ce, sune a zaune ita da kanwarta shigowarku dazu. Da
yake sunan mahaifiyata gareta shine nake kiranta Gimbiya. To kuma kasan mutane, a hankali
sunan ya koma Gimbi."

Harisu da Awaisu suka gyada kai suna Allah Sarki.

Alh Mudi ya cigaba da bayaninsa
"Shekararnan ta gama ATBU din amma Business admin ta karanta. Nayi magana da wani sun
karbeta a banki zatayi bautar kasa. Shine kaga ina dariya da na ga kaima bangarenka kenan, to
zan tura masa takardunka gobe. Kaga abin ma duk zaizo da sauki"

Godiya da addu'a suka rinka yi masa. Murmushi kawai yayi
"Saminu akwai kirki. Kaya kawai nake saya a wurinsa amma ina jinsa kamar dan uwa saboda
iya mu'amalarsa da mutane"

Harisu yace hakane domin shima shaida ne.

Daga nan Alh Mudi ya yace lallai sai Awaisu ya zauna a Abujan domin idan ya bayar da
takardun washegari mai yiwuwa zuwa litinin a bukaci ganinsa a bankin. Sannan yayi alqawarin
bashi makwanci har zuwa lokacin. Harisu ya rasa bakin godiya. Mutanen kirki basa karewa a
duniya. Sai dai haduwa dasu dace ne. Duk kudin Alh Mudi Maibuta bashi da dagawa da girman
kai.

Da safe Harisu ya koma Fika bayan yaja kunnen dan uwansa akan ya kula da kansa kuma ya
kame mutumcinsa.
*****

Tun tafiyar yayansa baya fita ko'ina. Kullum yana daki sai sallah da take fitar dashi wadda
Alhajin ko wani saurayi da Awaisu bai tantance matsayinsa a gidan ba suke jagoranta. Safe,
rana da dare maigadi zai miko masa abinci ya karba da godiya.

Yau lahadi sun idar da sallar magariba Alh Mudi yace ya shigo falonsa su gaisa da iyalin gidan.
Domin idan har ya sami aiki an barshi a nan Abujan to dole kafin ya sami wurin zama nan zai
cigaba da zama tare dasu.

"Ni kuma ba mazauni bane, shiyasa na ga ya kamata kasan mutanen gidan suma su san ka"

A baya ya bishi suka shiga wani falo wanda aka kawata da duk wani abu na jindadi. Kafin su
zauna wata mace ta shigo sanye da hijabi da alamun sallah ta idar. Sai 'yan matan ranar da
suka zo biyu da wani yaro da suke sallah tare wanda bai wuce shekara goma ba.

Awaisu ya gaisheta ta amsa da fara'arta ta tambayi sunansa.

Kafin ya amsa babbar wadda yake tsammanin ita Alh Mudi ya kira da Gimbi tace "A.S Abali,
Mama shine yayi vice president na S.U.G a makarantarmu"

Da mamaki ya dago yana kallonta. Shi dai bazai iya tuna fuskarta ba amma dai abin da ta fada
gaskiya ne. Kyaunta kuwa tuni yayi tasiri a zuciyarsa.

Maman tace "Gimbi rawar kai, ai ba ke na tambaya ba. Naga yayi shiru ne shine nake son jan
shi da hira ya sake damu."

Ta koma tana kallonsa "Alhaji yayi min bayanin komai game da kai. Allah Ya bamu ikon zaman
gaskiya da amana"

"Amin Hajiya nagode. Allah Ya kara girma"

"Amin, sai dai Mama ake kirana ba Hajiya ba"

Daga nan sun dan taba hira wadda hankalinsa gabadaya yana kan Gimbi. Tunda ta fadi
sunansa dazu zuciyarsa take kawo masa sabon tunani game da ita. Sai dai a wurin ya yakice
shi. Ai ido ba mudu ba amma yasan kima. Ina shi ina 'yar babban gida irin wannan.
*****

Washegari da sassafe ya tashi ya shirya kamar yadda Alh Mudi ya umarce shi. Yana wurin
maigadi suka fito tare da Gimbi. Taci kwalliya tayi kyau sosai.

A bayan mota ta zauna kusa da babanta shi kuma Awaisu yana gefen dreba. Babu inda ya
gane a wurin da suke tafiya sai dai kawai yaga an rubuta Zenith Bank. A reception Alh Mudi ya
barsu shi da Gimbi ya wuce wurin manaja.

Hira suke tabawa jefi jefi saboda shi dai ya kasa sakewa da ita duk kuwa da cewar ya fahimci
sakon da yake boyewa a zuciyarsa itama shine a cikin ta ta zuciyar.

Ba jimawa Alh Mudi ya fito ya bukaci Awaisu ya shiga wurin Manaja. Shi kuma suka shiga wani
dakin daban da Gimbi. A nan ne aka yi mata bayanin aikin da zata rinka yi.

Shi kuma Awaisu takardu ne aka bashi yayi ta cike cike. Bayan ya gama aka sanar dashi zai
dawo washegari interview sannan yaje Lagos sati na sama training na wata daya daga nan ya
jira posting.
[2/7, 7:09 AM] +234 703 322 0429: *KASHE FITILA*💡5

*Batul Mamman*💖



Abu kamar wasa sai gashi komai ya kankama dangane da samun aikinsa. Awaisu ya koma Fika
sanar da mutan gidan halin da ake ciki da tafiyar da zaiyi Lagos.

Kafin ranar tafiyar Maamu ta tura shi wurin yayanta ya karbo rago biyu cikin tumakin da ake yi
mata kiwo ya sayar. Da kudin wanda ko sisi bata cire a ciki ba tace yayi kudin mota da guzuri.

Kamar kullum kyakkyawar addua yayi mata tare da godiya.
"Ba godiya zakayi min ba. So nake idan kaje ka dage yayi abinda ya kaika. Lokaci yayi da ya
kamata ace kana da iyali kaima sannan ka fara ragewa dan uwanka nauyi. Ga zuri'a Allah Ya
bashi sosai. Kaga yanzu cikin yaran sai ka rinka biyawa wasu kudin makaranta idan ka fara
daukan albashi"
"Maamu kenan, Allah Ya bani iko. Nifa babban dana ma sunansa Haris. Tun yanzu ya kamata ki
fara kirana Abu Harith irin na Larabawa"

Neman abin da zata buga masa tayi saboda rashin kunyar da yake yi a gabanta. Ba shiri ya
tashi ya gudu.

Bayan kwana biyu Harisu ya raka shi tasha ya wuce Lagos. Watansa daya wurin induction din
sababbin ma'aikatan banki. Ana gamawa ya koma Abuja domin jiran posting. A wannan lokacin
ne kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsa da Gimbi. Tun yana ja da baya har ya amince. Ji
yake yafi kowa sa'a. Mace kamarta tana soyayya da talaka irinsa.
Da taimakon Alh Mudi ya samu aka barshi a Abuja maimakon Ilorin da aka tura shi da farko.

Ganin yana da kwanaki goma kafin lokacin fara aikin ya hada kayansa sai gida. Gimbi harda
kuka da zai tafi saboda sonsa take da gaske. Alkawari yayi mata cewa bazai wuce sati ba zai
dawo sannan suka rabu.

Yana isa gida yara suka fito ana ta murnar dawowarsa. Ya shiga ciki nan ma su Baaba sai
murna aiki ya samu. Nan yake jin kwanaki hudu da suka wuce matar Harisu ta biyun ta haihu.
Kai kace shi aka yiwa haihuwar ya fita neman dan uwanansa yana murna.
*****

Washegari suna zaune a bakin shagon Harisu suna hira Awaisu yace ya zabawa jaririya suna
Ummu Ruman. Amma Rumana za'a kirata.

"Kai kuma a ina kaji wannan sunan" Harisu ya tambaya yana kallonsa.

"A littafin tarihi"

"Idan munje gida sai kayi mata huduba dashi" cewar Harisu

Duk da cewa ya riga yayi mata da suna Aisha amma baya son batawa kaninsa. Shima kuma
Awaisun da yasan da hakan bazai taba kawo wani sunan ba.

Sai yamma suka koma gida. A bakin kofa ya tarar da dansa na biyu yana shirin fitowa.

"Sarkin yawo ina zaka da yamman nan"

"Baba kayi bako daga Kano. Shine aka ce na kirawo ka"

Harisu ya shiga ciki dakin Baaba inda suke yana tunanin waye yazo.

Abin mamaki Saminu ya gani tare da matarsa da yaransu biyar. Tsabar murna ya rungumeshi
suna dariya.

"Bala dreban tifa ne ya fada min haihuwar nace to lokacin tada zumuncin mu fa yayi. Dole mu
hada kan iyalinmu."

"Sosai kuwa, sannu yaya hanya"

Matar Saminu mai suna Amina da yaransa duk suka gaishe da Harisu. Ana ta barkwancin
yadda zasu rinka magana tunda Hausa a gidan bata zauna sosai ba. Baaba da Awaisu sune
masu Hausar sosai. Awaisun shima ya shigo suka gaisa. Fita yayi sauran kudin hannunsa yasa
ya siyo lemo, kaji da kwai ya bawa Maman Antu uwargidan Harisu domin karrama baki. Yaushe
zai manta Saminu a rayuwarsa.

****
Kwanansu hudu a gidan duk an saba kamar sun dade tare. Yaranma kowa da abokin sa ban da
babbar wadda ta girmi duka yaran gidan.

Ana gobe zasu tafi ne Harisu da Saminu sun zauna hira da daddare Harisu ya sako zancen da
yake ta son yi.

"Mardiya shekararta nawa ne yanzu?"

"Ka ganta tayi tsayi ko? Shabakwai zatayi da azumi. Badi zata gama sakandire in sha Allah"

Harisu yayi murmushi "To Allah Yasa abin da zan zo dashi yayi maka. Nace mai zai hana mu
hadata da Awaisu?"

Saminu ya kalle shi sosai "da gaske kake yi?"

"Indai ka amince. Wallahi Saminu ban taba ganin mutum irinka ba. Halayenka abin koyi ne ga
wasu. Idan na bari damar nan ta wucemu ai na cuci zuri'ar Awaisu. Mai alkhairi irinka dole a
kyautatawa 'ya'yanka zato"

Saminu ya kama hannunsa kam "in dai haka ne na bawa Awaisu Mardiya halak malak inyi
maka ta yara"

Dadi ya kama Harisu suna dariya "in sha Allah Awaisu bazai bamu kunya ba. Dama watan da
ya wuce na gama biyan su Zakiyya kudin gidan Malam da ya fada rabonsu a gado. Gyara shi
zanyi sosai kafin shekara mai zuwa shima Awaisun ya tara abin da ya tara sai su zauna a ciki.
Ba munyi maganar a Abuja zaiyi aiki ba? To muna sa rai zai sami muhalli kwanan nan. Kaga sai
su koma can ya sa ta cigaba da karatu ma"

Saminu farinciki ya cika zuciyarsa. Shi yana yiwa Harisu kallon mutumin kirki. Shima Harisun
kallon da yake yi masa kenan.

Sun yanke shawarar sanar da Mardiya babbar 'yar Saminu da Awaisu shawarar da suka yanke
domin jin ta bakinsu da kuma basu hakkinsu don kada a zalinci kowa.

Awaisu wanda yake bayan kofa tun bayan yaji an ambaci sunansa ya fasa karasawa wurinsu. Ji
yayi kamar an dora mada dutse a kansa. Shi kadai ya soma magana a hankali "yanzu wannan
yarinyar da bata gama zama mace ba za'a bani? Wallahi da sake. Ko ban hadu da Gimbi ba
babu inda zan kai wannan yarinyar"
*KASHE FITILA*💡6

*Batul Mamman*💖



Tun daga wannan rana Awaisu yake wasan buya da Harisu. Duk inda yasan zasu hadu su kebe
guduwa yake yi. Ranar da zai koma Abuja ma kamar ana korarsa don sauri. Haka ya tafi tasha
kafin Harisu ya dawo daga shagonsa inda ya ajiye masa kayan amfani kamar su madara da
ganyen shayi da yake son bashi guzurin tafiya.
Baiyi sati da komawa ba Alh Mudi ya dawo daga Kano. Wata rana da yamma ya tura karamin

dansa ya kirawo Awaisu. Da ya zo ne ya tabbatar masa da Gimbi ta sanar dasu abin da ke
tsakaninsu. Karshe yace yana so ya sanar da yayansa cewa su same shi a Kano shi da Saminu
idan har da gaske yana sonta da aure suyi magana.

"Ban yarda da bata lokaci ana soyayya ba indai akwai halin yin auren gara ayi kowa ya huta."

Gaban Awaisu ya fadi jin Alh Mudi ya ambaci ganin yayansa da Saminu. To da wane idon zai
kallesu ma. Shi dai Alh Mudi bai san me yake faruwa ba. Albarkacin Saminu yake ganin lallai
Awaisu ma mutumin kirki ne kamar yadda ya kula a dan zaman da yayi dasu.

Bai sami damar komawa gida ba sai bayan sati biyar ana hutun Good Friday da Easter Monday.
Haka ya tafi jiki babu kwari saboda rashin sanin yadda zai tunkari dan uwansa da maganar
auren Gimbi. Gashi Alh Mudi yace su same shi a gidansa na Kano. A son ransa ayi bikin bayan
sallah karama tare da na babban dansa wanda suke a Kanon tare da babarsu uwargidan Alhaji. *****

Kwanansa biyu da dawowa ya rasa abin da ke masa dadi kuma ya kasa fadawa kowa. Maamu
tayi fadan da magiya duka yaki cewa komai. Gashi yana matukar son Gimbi baya fatan rasata.

Da daddare yana kwance a dakinsa Harisu ya shigo. Ya tashi zaune amma ya kasa cewa
komai.

Harisu yayi murmushi yana kallonsa. Sai da ya zauna a gefen katifar dakin ya soma magana.

"Yanzu ni kake gudu saboda ka soma aiki a Abuja kayi kudi ko. Kana ganin kafi karfinmu."

Awaisu ya zaro ido a razane "Yaya me ya kawo wannan zancen kuma? Wallahi ba haka bane.
Allah Ya kiyaye. Bana fatan abin da zai kawo min tunani makamancin haka"

Harisu ya daure fuska "haka kawai za ka fara guduna ne idan ba kana tsoron a ganka tare da
talaka irina ba."

Idanun Awaisu tuni suka yi ja saboda rashin jindadin kalaman yayansa. Shi da ya dauki Harisu
uba yaushe ma irin wannan tunanin zai zo masa.
"Wata matsalar ce daban Yaya"
Ya fada a raunane.

Harisu yayi dariya a zuci domin ya samu Awaisu ya fada tarkon da yayi masa na son jin
damuwarsa.

"Ina jinka, menene matsalar da take hanaka walwala a gidan nan?"

Babu amfani cigaba da boyewar shiyasa ya fada masa maganar da yaji sunyi da Saminu da

kuma wadda suka yi da Alh Mudi.

Wani dogon numfashi Harisu ya ja. Ya jima yana tunani kafin ya soma magana cikin nutsuwa.

"Kai ba yaro bane da zan ce baka san abin da kake yi ba. Sannan ka wuce ayi maka auren
dole. Duk yadda nake son ka auri Mardiya ba ni zan zauna maka da ita ba. Saboda haka
nagode da ka fada min da wuri kafin ayi auren muji kunya. Zanyi kokarin fahimtar da Saminu.
Kuskurena ne da ban fara maganar da kai ba na fada masa"
Ko bai fada ba yasan ransa a bace yake kawai ya danne ne "Kayi hakuri Yaya. Itama Gimbi
tana da kyawawan halaye idan ka ganta ....."

Bai karasa ba Harisu ya mike batare da yace komai ba yayi hanyar fita. Tunaninsa bai wuce
yadda zai fita kunyar Saminu ba. Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba yace
"ka shirya muje Kanon gobe kafin lokacin komawarka aiki."
*****

"Zancen banza kai, ina Awaisu ina 'yar masu kudi. Ko kuwa so yake ya janyo ace yayi auren
jari? To ma a ina yake tunanin ajiyeta idan anyi auren. Yaushe ma ya fara aikin da zai jajibo
aure irin wannan"

Maamu ce take ta fada bayan Harisu ya sanar da ita da Baaba batun tafiyarsu Kano neman
aure. Haka tayi ta fada yana bata hakuri da nuna mata magana kawai zasu je yi ba auren za'a
daura ba.

Ranar da suka isa Kano Saminu jiki a sanyaye ya tarbesu. Wannan ya dagawa Harisu hankali
ko har Alh Mudi ya sanar dashi komai. Baya son abin da zai taba alakarsu ko kadan. Shi
Awaisu dama ya kasa kallonsa ma. Tunda suka zo yake sunkuyar da kai.

Bayan sun dan huta ne suka zauna tattaunawa. A nan Saminu ya dubi Harisu "Alh Mudi yazo
gidan nan da kansa akan yana son na bawa dansa auren Mardiya. Sanin cewa munyi magana
da kai nace na bayar da ita ga Awaisu. Shine yayi min wani bayanin daban da ban gama
fahimta ba "
A kunyace Harisu ya fada masa abin da

2 / 42