Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
kudi a
hannunsu yasa Shuhada tace ya zauna kawai har a koma hutu ya cigaba da karatunsa .
Daga dakinta ta fito zata kwaso kayan shanyarta don mai wankin gidan daga na Alhaji sai Anti
Bebi yake wankewa.
Daya daga cikin malaman karyar ne ta gani da Anti Bebi a wani karamin falo suna magana a
hankali ta lallaba ta tsaya a gefe babu mai ganinta. Daga ciki take jiyo muryarsa a hankali
"Wannan maganin Wangesi yace ki zubawa ita babar taki a abin sha. Yadda zata shanye haka
duk wani fushi ko bacin ran da zaki haddasa mata zata shanyeshi tas"
Juya maganin tayi tana dan murmushi.
"Shi Alhajin yace na barshi haka ko"
"Yaji tsoron kada yawan asirin ya haukata shi shine yace a saka masa ido na dan lokaci"
Dafe kirji Shuhada tayi don tasan da babanta ake. Barin wurin tayi niyar yi taji mutumin ya
ambaci sunanta.
"Ita yarinyar nan Shahada take ko me ga nata maganin. A abinci zaki zuba taci. Da zarar taci
yace ko sunan mutumin kika kira sai taji gabanta ya fadi sonsa ya karu a ranta. Ki kwantar da
hankali bazata yi musu ba har ayi auren"
Karbar wannan magani yasa Anti Bebi nishadi da murna sosai.
"Sai na koya musu hankali su duka. Awaisu dama nasa matarsa ta gama juya masa tunani.
Abin da ya rage bai wuce na aura masa Shuhada ba kuma na tsaya mata har sai ya saki Gimbi.
Ni da ka ganni nan bana yafe rashin mutumci ko kadan"
"Kiyi yadda yace zaki ga biyan bukata"
Daga haka ta karbi maganin kafin su fito Shuhada ta bar wurin da sauri.
Dakinta ta koma ta hau kuka. Ta rasa wace irin mutum ce Anti Bebi. Share hawayenta tayi ta
shiga tunanin neman mafita. Wurin rabin awa ta kwasa a dakin kafin ta fita.
Kitchen ta dosa dauko abinci ta tarar da Anti Bebi a falo.
"Ke ina zuwa?"
"Abincina zan dauko ko shima an hana ne?"
"Aa Shuhada, ni bana jindadin yawan rigimarmu kamar ba mata ba. Ga abinci can akan dinning
table kije kici."
Ba musu Shuhada ta wuce ta diba ta cika plate har yayi tsororo. Hanyar dakinta ta nufa Anti
Bebi tayi dariya
"Shegiya mai cikin zani. Baki iya komai ba sai ci da kashi. Ji wannan tulin abinci kamar mai aikin
karfi"
Shuhada tayi kamar bata ji ba ta wuce. Leda ta samu a gabanta tana juye abincin cokali cokali
kamar ci take. Ba zato taji an turo kofar dakinta. Anti Bebi ke son tabbatarwa ko taci.
Ita kuwa Shuhada sai ta wayance tana kokarin kai cokalin baki. Anti Bebi bata ce komai ba ta
juya ta fita. Shuhada ta juye fiye da rabin abincin a leda sannan ta mayar da sauran kitchen.
Anti Bebi ce ta biyota har kitchen ta dafa mata kafada. Shuhada don tsoro kamar ta saki fitsari.
Bata kaunar hada inuwa da ita. Ji tayi Anti Bebin tace
"Kina son Awaisu mijin yar nan tawa Gimbi?"
Da kyar ta iya hadiyar yawu kafin ta tattaro hankalinta ta nutsu. Kai ta sunkuyar ita a dole kunya
take ji tayi murmushi
"Kai Anti har kin gane"
Anti Bebi tayi wani juyin farinciki sannan ta sake maimaita tambayar. Wannan karon Shuhada
hannu tasa ta rufe idanunta tana wani fari
"Ni dai Anti kunyarki nake ji"
Daga haka ta kwasa da gudu ta bar kitchen din.
Anti Bebi taji dadi mara misaltuwa ta kama dariyar mugunta. Da Shuhada zata wargaza rayuwar
Gimbi.
Shuhada na shiga daki rufe kofar tayi tana numfashi da kyar. Tunda ta tari Anti Bebi da wannan
karyar ya zama dole tayi amfani da wannan damar wurin sanin sirrinsu da kwatarwa kanta da
duk wanda suka kafawa takunkumi 'yanci.
*KASHE FITILA* 23
*Batul Mamman*í ½í²–
_*Waiwaye*_
_Shuhada ta nunawa Anti Bebi asirin da akayi mata domin ta kamu da son Awaisu ya kamata.
A bangaren Gimbi kuma tana nan tana cigaba da wulakanta Maamu._
Ladabin karya da biyayya Shuhada ta cigaba da nunawa Anti Bebi. Ita kuma dadi ya isheta ta
sami hanyar ganin hawayen Gimbi cikin ruwan sanyi.
Bayan kusan sati biyu tana sanya ido akan Shuhada wadda ta dage sosai wurin nuna ita idan
ba Awaisu ba yanzu sai rijiya. Hakan yasa Anti Bebi fara tunanin hanyar da zata bi domin ganin
sun hadu ta fara aiwatar da kudirinta.
******
Kiran sallar magriba akeyi Rumana ta shigo gida da sauri rike da ledar kosai. Kitchen ta wuce
inda take jin muryar Gimbi tana tashi taje ta mika mata ledar.
Gimbi ta karba ta bude hade da zaro idanu ita ta ga abin mamaki.
"Yanzu wannan kosan dari ne? Lallai wake ya soma arha. Wannan kosan ya yiwa Maamu yawa
ai. Cikin tsofaffi sai ana sa ido sosai"
Plate din roba ta dauko ta debi kosai guda bakwai 'yan miri-miri ta mikawa Rumana.
"Maza ga kunu ki dauka ki kai mata an sha ruwa tun kina hanya."
Rumana ta kalli dan siririn kofin da ko cika baiyi ba da plate din kosan sai ji tayi hawaye na
barazanar kwace mata. Wai yanzu wannan ne abincin shan ruwan Maamu a gidan danta.
Gimbi na kallon yadda yanayinta ya chanja a ranta tace mayu masu zuciyar kare. Zaman gidan
sai kace dole sunki tafiya.
Haka Rumana ta tafi dakinsu ta ajiyewa Maamu abincin shan ruwanta wanda yasa idanunta
kawo ruwa itama. Kunun kansa bai wuce kurba hudu zuwa biyar ba kwarara bare kuma kosan.
Rashin wadatuwa da abinci ya sanya Maamu azumin dole kusan kullum yanzu shi take yi.
Abincin da aka basu rana da dare sai su hada su ci lokacin shan ruwan don su fi koshi. Wani
lokacin Rumana tana yi itama. Yau kamar gaske ganin idon Awaisu da safe Gimbi tace zata yi
mata kayan buda baki. A yadda ta nuna kamar ranar Maamu ta fara azumin shi kuwa ya fita
yana kara jin babu macen kirki sama da matarsa.
Maamu na kallo Rumana ta shige bandaki taci kukanta na tsantsan bakinciki da nadamar zuwa
Abuja. Da ta fito wayar Maamun ta dauka tana shashshekar kuka ta kirawo babanta. Da yake
wayar ba'a ji sai an sakata a speaker Maamu tana jin muryarsa ta karbe wayar daga hannun
Rumana kafin ta tona asiri.
"Harisu"
Dadi yaji na samun kira daga garesu saboda kwana biyu idan ya kira ta wayar Awaisu baya
rasa uzurin da zai fake dashi a matsayin dalilin rashin bata waya su gaisa. Ita kanta muryarta
raunana tayi da taji yace
"Maamuna"
"Harisu yaushe zaka zo ka kaini Fika? Kewar mutanen gida nake yi sosai. Ina Baaba da sauran
mutan gidan?"
Dadi yaji domin suma suna kewarta yace "Zanyi magana da Awaisu sai ku taho idan anyiwa su
Rumana hutu. Ko nazo da kaina mu taho tare"
Za tayi magana ya katseta ta hanyar yi mata tambayoyi akan lafiyarta da kuma kula da cin
abinci akan lokaci.
"Bana so ki sake kwanciya kamar wancan karon"
A ranta tunani take yi idan ba a yi saurin mayar da ita cikin dangi ba kila gawarta za a kai Fika.
Bayan duk sun gaisa da 'yan uwa domin Harisun kashewa yayi ya sake kiransu Maamu rokon
Rumana tayi akan ta rufawa kawunta asiri har Allah Ya kawo karshen zamansu a gidan. Ita dai
Rumana ko magana ta kasa yi saboda bacin rai. Maamu na gama magana ta fice daga dakin ta
nufi kitchen. A yau dole ta dauki shawarar Yusra ko don ta huce takaici.
Inda ake ajiye kayan kadi na miya ta bude ta debo karkashi ta zuba a kofi wanda rabinsa ruwa
ne. Tana juyawa da yatsanta bata sani ba ashe Daula ta ganta. Dakin Awaisu ta nufa inda suke
hira da Gimbi ta fada musu ga Rumana tana kwaba milo da ruwa zata sha.
Da sauri Gimbi ta tashi tana kallon Awaisu.
"Kana ji dai da kunnenka yarinyar nan ta fara sata duk irin kokarin da nake yi akansu ita da
Maamu"
"Ki kyaleni da ita zanyi mata magana" shi tashin hankali ne baya so musamman da yake ya
kwaso gajiya.
Bata saurare shi ba ta bi bayan Daula. Yau sai ta koyawa Rumana hankali kila da safe ta bar
mata gidanta.
A bakin kofa suka hadu Rumana zata je dakin Gimbi ta juye kwabin karkashin a bakin kofarta.
Ba karamin tsorata tayi ba da suka hada ido da Gimbi. Kofin ta fizge tayi wurgi dashi abin ciki ya
watse don ma na roba ne. Sannan ta kwashe Rumana da mari.
"Barauniya kawai kwadayayyiya. Wato dama kece kike karar min da madara da milo ban sani
ba"
Rike kumatu tayi tana kukan sharrin da akayi mata sai ga Daula ta yo kan Gimbi santsin
karkashin da ta taka ya kwasheta tana neman faduwa. Garin haka bata kula ba tana kokarin
rike 'yarta itama ta taka suka yi sulu a kan tiles duk su biyun suna ihu. Daula tsoron faduwa
yasa ta damki kan Gimbi wanda aka yiwa kananun kitson barebari. Jela ukun da ta damko tana
ja yasa Gimbi sanya wata muguwar kara, hakan yayi daidai da cizgewar kitson sai gasu a
hannun Daula. Su duka biyun suka fadi a kasa jikinsu dame da karkashi.
Rumana kuwa me zatayi banda dariya. Kana kallon kan Gimbi sai kayi dariyar yadda ya
kwashe. Sai fada take yiwa Daula. Da kyar suka iya tashi santsi na kara dibarsu. Sai da
Rumana ta ji tahowar Awaisu yana tambayar ihun me akeyi ne ta durkusa ta rike ciki. Duk da
bukata ta biya amma tsoron hukuncin da zaiyi mata take yi.
"Me ya sameku haka, ku duk kun zube a kasa ke kuma kina rike ciki"
"Abba faduwa mukayi da wannan abin da Rumana ta hada" cewar Daula
Taimakawa Gimbi yayi ta tashi amma kafarta kamar bazata iya daukanta ba don buguwa.
Runtse ido kawai take yi ta kalli Rumana
"Uban mene kika hada a kofin nan"
Fuska Rumana ta kwabe ita abar tausayi
"Cikina ne yake ciwo tun a makaranta shine wata tace min ana jika karkashi da kanwa"
"Karkashi da kanwa kuma Rumana? Baki da lafiyar bazaki fada min ba sai ki hada wani
karkashi"
Awaisu yana magana yana kallon Daula mai kawo rahoto.
"Na zata fa milo ne" ta fada kai a kasa. Dama ita ce mai zuwa hada milo da madara ta sha duk
dare. Lokacin da ta ga Rumana ma abin da ya kawota kenan.
Baice komai ba ya tallabo Gimbi suka tafi daki ciwo a kafarta ta hagu ya isheta. Daula sai
harara take dokawa Rumana ta tafi dakinta. Ita kuwa da murna ta tafi harda danewa jikin
Maamu. Bacin ranta duk ya kau saboda dadin da take ji a lokacin. Maamu bata san me yake
faruwa ba amma canjin yanayin da ta gani wurin Rumana ya dan kwantar mata da hankali. *****
Daren nan Gimbi batayi baccin kirki ba saboda ciwon kafa ga kanta yana zugi. Gari na wayewa
kafar ta kumbura suntum daga wurin gwiwa. Awaisu da kansa ya tashi Rumana tayi abincin
safe zai kai Gimbi asibiti.
Ta dan ji faduwar gaba ko a dalilinta wani abu ya sami Gimbin. Amma da ta tuna gasuwarsu a
gidan sai ta share. Da kyar ya taimaka mata suka fita waje tana jan kafar. Kwakkwaran motsi
idan tayi sai taji kamar ana soka mata wuka.
Bayan fitarsu Rumana ta shiga fadar Gimbiya matar Awaisu inda ake horasu ta dafa shayi ta
soya kwai ta zubawa su Daula nasu ta hada mai yawa a flask ta kaiwa Maamu. Ga kwai ga
bread.
"Rumana wannan daga ina?"
"Allah ne Ya bamu Maamu. Kiyi sauri ki ci kafin su dawo daga asibitin"
Dan fito da ido tayi "waye babu lafiya?"
Rumana tana dariya ta labarta mata yadda sukayi jiya. Maamu ta soma yi mata fada akan kada
ta kara. Amma Rumana ta kula fadan bai kai zuci ba don har dan murmushi tayi.
Ranar sun ci sun koshi suna gamawa taje ta dora na rana da wuri kafin goma ta gama ta sake
zuba musu mai yawa. Sai da ta koma gyara kitchen Awaisu ya dawo ya sanar dasu an kwantar
da Gimbi a asibiti kashinta ne ya goce ga buguwa kafar tayi tsami.
Haka nan yaji yana son ganin Maamu bayan kusan sati ko hanyar dakin baije ba. Yana shiga ta
fito daga wanka. Ji yayi jikinsa duk yayi sanyi saboda wata muguwar rama da Maamu tayi.
Hankalinsa yayi mugun tashi yace
"Maamu baki da lafiya ne?"
So take tayi kuka sai ta dake "Ka kaini Fika"
Muryarta ma ta kankance kamar yadda ta rame. Duk yaji ya tsani kansa da rashin kulawa da
ita.
"Kiyi hakuri a dan kwana biyu ki kara warkewa sai na kaiki. Amma a haka kowa ya ganki yasan
baki da lafiya"
Daga murya tayi ta soma fada
"Ubanka ne ya samin ciwon da zaka ce bani da lafiya? Ka mayar dani inda ka dauko ni tunda ka
gagara kula dani da yar amana Rumana"
Jin kansa yake kamar wanda ya tashi daga bacci a lokacin. Me ya faru tun tafiyar su Baaba ya
dena bibiyar halin da Maamu ke ciki bayan yasan yadda Gimbi take wulakanta masa dangi .
Kamar wani yaro ya soma hawaye a gaban Maamu amma ya rasa me zaice mata. Tausayinsa
ya kamata itama sai kukan.
*KASHE FITILA*í ½í²¡ 24
*Batul Mamman*í ½í²–
Sai da suka yi mai isarsu sannan tace ya tashi ya fita bata son ganinsa. Jiki a sabule ya fita
ransa yana kuna. Mamakin kansa yake yi da yadda yake sakaci da mahaifiyarsa. Shi Awaisu
manajan banki kuma babban dan kasuwa shine Maamunsa take wadannan kasusuwan kamar
wadda ta shekara ciwo.
Tun shigarsa daki tunani kawai yake yi karshe bacci mai nauyi ya dauke shi.
A asibiti sai shabiyu likitan kashi yazo aka gyara kafar Gimbi. Tasha azaba gumi ya rinka bin
jikinta saboda ciwo. Ga kanta inda Daula ta tsige mata kitso ya tashi sosai kafar gashin da ya
fita ta kumburo shima ciwon yake mata. Duk wannan ya taru da rashin dawowar Awaisu daga
cewa zaije gida ya dawo. Tayi ta kiran wayarsa shiru baya dauka. Nan fa ta damu sosai ta fara
tsoron ko aikin Wangesi ya soma rabuwa dashi ne yau daya da batayi masa turare ba. Abu
kamar wasa har azahar bai dawo ba kuma babu waya. Ganin haka hankalinta duk ya tashi har
ta fi damuwa da rashin dawowarsa akan ciwon da jikinta yake yi. Takurawa wata likita tayi akan
lallai sai an sallameta suka ki. Da ta rasa abin yi sai ta kira Anti Bebi.
"Gimbiya ta Awaisu yaya akayi ne?" ta fada tana dariya
Gimbi ta amsa mata da kyar ta labarta mata halin da take ciki. Kamar gaske Anti Bebi ta nuna
damuwarta ta shirya ta taho asibitin.
Da tambaya ta gane dakin ta shiga. Tana budewa ta ga kan Gimbi sai dariya har ta kusa kaiwa
kasa.
"Gimbiya wannan kyan ki hoto wallahi a kafa shi a kofar gidan Awaisu."
Daure fuska Gimbi tayi "wannan ciwon fa ba na wasa bane Anti Bebi"
Da gayya ta kaiwa kafar da aka nade duka cikin wasa ita kuwa Gimbi ta saki kara har tana jin
fitsari na barazanar fita saboda azaba.
Anti Bebi ta dauke kai kamar bata kula ba "nima ban ce na wasa bane, wai.... wannan kai naki
kamar na budurwar zabuwa a lokacin da ta fara kora. Awaisu ya caba da Gimbiyar mata"
Ran Gimbi in yayi dubu ya baci har ta fara dana sanin kiranta.
"Idan dariya zakiyi min ki tafi kawai na nemi taimakon wani"
"Dadina dake tsiwar tsiya. Me kike so dai yanzu"
Tunanin yadda zatayi maganin Gimbi a nan gaba take yi. Dauriya ce kawai yanzu take kafin
lokacin da zatayi dariya.
"Saboda wannan ciwon yau banyiwa Abban Haris turaren nan ba. Kinga tun fitarsa har yanzu
shiru. Ina tsoron kada hankalinsa ya fara komawa kan uwarsa"
Anti Bebi ta murmusa "Gimbi Allah dai Ya baki suruka irinki. Nasan ba karamin dadi zaki ji ba ke
me 'yan maza har uku su auri mata masu jajircewa akan mazansu kamar ki"
Gimbi ta dafe kirji jin wannan muguwar addua daga bakin Anti Bebi.
"Ba Amin ba wallahi, wai me nayi miki ne haka kike min mugun baki?"
"Auuuuu, ashe babu dadi kike yiwa Maamu baiwar Allah? To maida wukar wasa nake yi. Amma
ni kam gaskiya da ina da da namiji wallahi bazan bari ya aureki ba."
Ganin cewa cin fuska Anti Bebin take yi mata tace ta tafi kawai ta fasa. Anti Bebi taji dadi ga
dama ta samu na hada Shuhada da Awaisu tace tayi hakuri. Kwantar da kai sosai tayi tana bata
baki Gimbi na hura hanci ita a dole ta isa. Bayan sun gama magana akan cewa Anti Bebi za ta
je har gidan da sunan dauko mata kaya tayi masa turare ta dauki jakarta.
"Ki jirani da kansa zai zo har nan ya sameki ki sille shi ciki da waje."
******
Gidanta ta wuce kai tsaye tana murmushi. Da yake ita ke tukin motar ko yaya ta tuna irin mugun
tanadin da ta yiwa Gimbi sai ta daki sitiyari tana dariya. Da isarta Shuhada ta umarta da ta
shirya zasu fita. Ita kanta wanka ta sake yi tamkar kanta zata kaiwa Awaisu ta saka riga da zani
na mutumci harda hijabi. Shuhada ma doguwar riga ta saka mai kyau yalwatacciya da hijab
wanda ya wuce kirjinta da kadan. Ganin shigar da Anti Bebi tayi abin ya daure mata kai sosai
tuni ta