Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   31 / 42

90K to 93K   out of 124.7K words

dan shafa hoda sannan ta dauki miya ta fita. Addua Mama tayi
mata don yanzu kam ta wuce duka ko murde kunne an zama matar aure.

Da taje kofar dakin tayi ta sallama bai amsa ba sai ta murda kofar. Dakin a bude yake amma
yana can waje tare da Harisu dawowarsu kenan daga masallaci. Shiga tayi ta ajiye miyar ta
dauko wancan plate din zata tafi dashi sai gashi ya dawo. Da murmushi tayi masa sannu da
zuwa sannan ta duka gaban flask din.
"Mama ta koya min na sake wata miyar da waccan din. In zuba maka?"

Kirjinsa ya dafe yana tuna azabar da yasha dazu. Yau naga ta kaina.

"Ki bar tuwon kinji my sweet SS. Tea zan sha kawai ya isheni"

Bata ji dadi ba ta bude harda tura masa shi kuwa ya matsa yana mai fargabar sake zuba yajin
nan a bakinsa don gaskiya bai yarda da girkinta ba.

"Wannan tayi dadi sosai kuma na dandana"

"Bakinki dinnan bana yarda dashi"

Cokali ta dauko ta debi miyar ta saka a baki tana kallonsa "ka gani da gaske wannan babu yaji"

"Sai na dandana nima zan yarda"

Diba ta sake da cokalin ya rike hannunta ya mayar cikin flask ya janyota tsaye
"Bude bakinki na tabbatar kin hadiye"

Tana budewa ya saka nasa. Ya kuma yi mata riko mai wuyar kwacewa. Dama abin da yake so
kenan.

Da ya saketa ne yace "yanzu na yarda babu yaji zuba min yunwa har ta cinyeni"

Kasa kallonsa tayi saboda yadda yake mata abubuwan dake sakata jin kunya ta zuba masa
abincin ta fita kafin ya ankara.
*****

Gimbi sai kai kawo take a daki duniya tayi mata zafi. Ta kira Ovi yafi sau goma ba'a daga ba.

A nasu bangaren Rita ta kalli Ovi ganin yadda take murmushin mxugunta.

"Sis wai me yake faruwa ne kinki daukar wayar Madam Gimbi"

"Kinsan a da naso ne ki auri mijinta saboda mu sami rabonmu a gidan. Amma Boka yace idan
akayi auren nan daya daga cikinmu zata rasa ranta. Shiyasa nake ganin gara muci kudinta
kawai muyi gaba. Ko maganin da ta karbo last a wurinsa ruwan datti ne kawai nace ya bata "

"Ba kya tsoron kada ta gane?"

"Zata gane amma sai mun gama da ita. Bani wayar naji me take so. Nasan yanzu haukane
kadai batayi ba tunda aiki yake ta baci ga aure yayi"

Kafin wayar tayi Gimbi ta dauka rai a bace "Ovi kina kokarin cuta ta nr ko me. Yaya zanyi ta
sakin kudi babu biyan bukata"

"Kiyi hakuri Madam Boka yace akwai inda aka sami kuskure wurin aikin da kikayi da maganin"

Da a gabanta take yadda ranta ke kuna kila sai ta kai mata shaka "sai kace wata sabon shiga
zaku ce matsalar amfani da magani aka samu? Sau daya aka samu hakan da Maamu tana
asibiti"

Ovi jin zata cika mata kunne da fada tace "haba ni nasan akwai inda aka kuskure. To boka yace
ko waye silar bata aikin a wannan lokacin sune suke bibiyarki suka hanaki sakat"

Gimbi tayi shiru tana son tuna sunan wannan shegiyar likitar da ta hanata shafawa Maamu
magani. Kwafa tayi taja tsaki "akwai wata likita da nake zargi don ta saka min ido lokacin. Ki
fadawa Boka yayu min maganinta. A rabata da abin da tafi so duk duniya yadda ta taimaka
wurin nesantani da mijina. Zan turo miki 200k yanzu ayi komai a gama da wuri. Ita kuma
Rumana idan Awaisu ya dawo garin nan da igiyar aurenta Ovi zan baku mamaki. Bani da kirki
ke kin sani. Shi kanshi ba don wannan azababben son da na rasa dalilinsa ba da bai isa ya sha
daga hannuna ba"

Bayan sun gama waya Ovi ta cewa Rita ya zama dole wannan karon a biyawa Gimbi bukata
saboda kada ta dena yarda dasu. A cikin daren babu fargaba bare tsoro suka tafi wurin Boka.
Kayan tsafinsa ya dauko ya rinka surkulle wanda Ovi da Rita duj yawan zuwansu kullum
tsoronsa suke yi.
Wata irin kibiya ya soka tun daga kai har tsakiyar wani mutum mutumi ya chake shi a jikin
bango.
*****

Cikin barci Dr. Yana taji jikinta yana zafi kamar an hura wuta. Lokacin shadayan dare. tayi aiki ta
gaji ga girkin da tayiwa Hajiya surukarta bayan ta dawo. Mujahid ta soma kira yana falo bai ji ba.
Ido a rufe har lokacin ta ga Gimbi ta biyota da wuka ta soma kuka tana rokonta tayi hakuri.
Shure shure take ta yi a kan gadon har ta fado ta bige da bedside drawer amma bata farka ba.
Karar faduwar abu Mujahid yaji ya shigo ya ganta a wannan yanayin.

Duk yadda zaiyi taki bude ido amma ga hawaye yana ta zubowa. Fita yayi a guje ya kira Hajiya
Allah Yasa idonta biyu.

Suna zuwa suka ji tana cewa "Gimbi! Gimbi!! Gimbi kada ki kasheni!!!!"

Hajiya ta daga kanta ta dora a cinyarta tana kuka don duk irin zamansu ba wai ta tsaneta bane
ko don zumunci. "Yana bude idonki waye Gimbi?"

Jikinta ne ya saki ta dena motsi sai ga jini ya biyo ta karkashinta yana zuba. Mujahid ya tashi
ya fita neman key din mota ita kuma Hajiya tana duba jinin ta dafe kirji.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Yana bari kika yi?"

Sai a lokacin Dr. Yana ta bude ido da kyar maganarta bata fita sosai saboda zafin ciwo "Hajiya
kiyi hakuri niyata sai ya cika wata uku zanyi muku kyakkyawan albishir ashe ba me zama bane"

Wani abu ne ya tsaya mata a makwogaro tana tuna yadda cikin mafarki Gimbi kw fada mata sai
ta rabata da abin da tafi so. Kuka sosai suke yi ita da Hajiya. Da taimakonta ta tashi ta dan
gyara jiki a daren suka tafi asibiti. Sunyi kusan awa biyu sannan aka shawo kan matsalar don

jini take zubarwa ba da wasa ba. Hajiya ce take yi mata komai cike da tausayawa tana jira ta
sami kwarin jiki ta fada mata wacece ko waye Gimbi.
*KASHE FITILA*💡44

*Batul Mamman*💖


_*Shafa'atu Aminu a madadin dukkanin members na BMN muna yi miki fatan alkhairi da
addu'ar Allah Ya karo Son So.*_


Hajiyar Mujahid yadda taga rana haka taga dare wannan asabar din. Tunani ne ya addabeta na
son sanin alakar Yana da Gimbi da kuma barin da tayi daidai lokacin da take ambaton wannan
sunan.

Mujahid din ma a asibitin ya kwana. Bayan sallar asuba da ya shiga dakin Hajiya ta kasa hakuri
ta tambayeshi wace ce Gimbi.

Dafe goshinsa da yake masa ciwo saboda rashin bacci da fargaba yayi "Hajiya ki bari ta tashi
zata yi miki bayani sosai. Ni kaina abin da na sani game da matar kadan ne"

Hajiya tace "Allah Ya kaimu ta tashin. Wallahi ko wace ce bata isa ta kashe min jika ta kwana
lafiya ba. Idan tana takama da hatsabibanci gidansa tazo. Ni har akwai wanda ya isa ya taba
jinina ina raye ban dau mataki ba"

Tsoro ne ya bayyana akan fuskar Mujahid "Hajiya tun yaushe kika rufe wannan shafin don Allah
akan barin nan kada ki koma abin da ya shude. Tsautsayi ne kawai da kaddara"

Tabe baki tayi "sai kuma kayi. Ka kira 'yan uwanka ka sanar dasu tunda gari ya waye su kawo
abinci kafin ta tashi".

******

Karfe goma na safe ta wuce Maman Rumana ta shiga kitchen zata dora abincin rana saboda
yara da wuri duk me girki take gamawa. Tray din da ta hada na breakfast din Awaisu ta gani
nan inda ta barshi ba'a taba ba. Ranta kuwa yayi mugun baci ta rinka kwalawa Rumana kira. Jin
bata amsa ba yasa ta zuwa dakin 'yan matan. A kwance ta sameta ta rufa ido a rufe. Kanta tayi
ta daka mata duka a baya wanda yasa ta tashi a firgice. Mama ta harareta
"Tun daren jiya ban fada miki da safe kije ki dauki abincin Kawunku Awaisu ba? Mutum yazo kin
masa horon yunwa tunda bai sami abin arziki da zai iya ci da wuri ba sai bayan magariba.
Sannan da safen ma shadaya na neman yi ko karyawa baiyi ba"

Idanun Rumanan dama a kumbure suke sai kawai ta soma kuka "Mama bani da lafiya ne"

Bata gaskata ba tace "wa kika fadawa a gidan nan?"

Tana share ido tace "kafata ce kuma su Hafiza duka basa dakin shiyasa ban fada ba"

Jiki a sanyaye Maman ta zauna tana shafa mata baya "sannu bari na dora ruwa sai a gasa
kafar kiyi wanka. Allah Ya sauwake."

Tana fita ta kira Sajid shima kanin Rumana ne na wurin Anti Amarya ta bashi tray din tace ya
kaiwa Awaisu ya fada masa bata da lafiya shiyasa baa kawo da wuri ba.

Karo na biyar kenan da yake kiran wayarta bata dauka ya fara tunanin ko abin da yayi mata jiya
ne yasa take gudunsa. Murmushi yayi yana tunanin idan ta tare akwai rigima kenan.

Sallamar Sajid ce ta katse masa tunanin yana zaune sanye da dogon wando brown da farar
shirt. Ko yanayin aiki ne da baya samun isasshen hutu yasa bashi da wani jiki wannan sai
Harisu.

Gaishe shi Sajid yayi kafin ya tambayeshi ina Rumana ya fada masa bata da lafiya. Hankalinsa
ne ya tashi ya matso kusa dashi "me ya sameta? Tana ina?"

Sajid ya dan kada kai "ina jin ciwon kafar nan ne ya tashi. Uncle idan tana yi fa bata iya tafiya
ranar ko bandaki zata sai an riketa"

Awaisu ya yiwa Sajid kallon rashin fahimta. Wane irin ciwo ne wannan yace a ransa. Tare suka
fito sai dai kafin ya shiga kofar da zata sada shi da ainihin gidan ya dan tsaya. Kansa ya dan
shafa ya fara tunani. Yana mamakin kansa da yadda yake jin nauyin iyayen Rumana yanzu. A
da can Mamanta abokiyar shawararsa sannan bashi da na biyun Harisu. Amma yanzu darajar
aure baya iya sakin jikinsa akan abu indai ya shafeta musamman da yake a cikin gidansu ne.
Ya zama dole ginin da ya soma ya banzatar ya cigaba da yinsa saboda babu yadda za'ayi idan
ta tare duk lokacin da zasu zo garin ya tare musu a gida shi ba yaro ba yana rabe-rabe idan zai
ga matarsa.

Idan ya shiga tabbas akwai yiwuwar haduwa da Mama sannan idan bai je ba sai su iya tunanin
bai damu da ita ba. Uwa uba yadda ya matsu ya sanyata a idonsa bazai barshi ba. Shiga cikin
gidan kawai yayi ya gaisa da sauran matan gidan da ya gani suna fitowa daga kofar dakinsu
Rumana.
Har yaje bakin kofar sai kuwa ya jiyo muryar su Baaba da mama. Maamu wadda bai san itama
tana ciki ba yaji tana cewa dasu Baaba

"Yarinyar nan duk wata haka muke fargaba idan ta kusa a gidan Kawunta. Saboda ciwo dama
indai a gida ta fara ranar bata zuwa makaranta. Da yake babu wanda ya damu da lamarinmu

lokacin haka zata ci ciwonta na kwana biyu sannan ta ware. Idan munyi sa'a kuma kwana daya
take ta tashi "

Mama yaji tace "sai dawowarta muka san tana yi amma idan anyi mata allura tana dan samun
sauki"

"Mata sai hakuri wai kafin ayi maganar ciki da haihuwa ma fa kenan. An fadawa mijinta?" Cewar
Baaba.

"Ai kuwa a tura yazo maza-maza ya kaita asibiti idan tayi wanka. Sannu kinji Rumanan Maamu"
Maamu ta fada tana tashi ita da Baaba.

Awaisu na jinsu ya dan ja baya don bazai shiga Mama tana ciki ba. Da suka fito gaishe su yayi
ya tambayi mai jikin a ransa yana cewa mai yasa ta zauna a dakin da bazai sake ba. Baaba
tace ya shiga tana ciki yayi saurin sake yin baya yana cewa zai dawo ya dubata. Murmushi tayi
tace masa yaje dakinta ya jirata tana zuwa zasuyi magana ita kuma ta koma dakin.
"Rumana zaki iya tashi?"

Mama tace "tun dazu nima nace ta tashi ta kasa kafar taki daukarta"

Baaba ta fita ta kira Anti Amarya da kanta tace ta kama Rumana ta mayar da ita dakin ita
Baaban saboda a nan hayaniya bazata bari ta huta ba. Suna fita ta mayar da hankalinta ga
Mama wadda ta kasa fahimtar dalilin Baaba.

"Awaisu na gani a kofar dakin amma nauyi ya hana shi shigowa" tayi murmushi ganin Mama ta
dan sunkuyar da kai itama sannan ta cigaba da magana

"Dama ina so nayi miki godiya da baki tayarwa mijinki hankali akan auren nan ba. Nasan dole
zaki ji babu dadi kiga an hadata da mutum kamar Awaisu mai shekaru kusan arba'in. Amma
kamar yadda na riga nasan kin sani kowane bawa yana da kaddarar da Allah Ya rubuta masa"

Mama tace haka ne. Baaba ta cigaba da cewa "addua'armu bata wuce Allah Ya basu zaman
lafiya da juna. Mu namu auren ma ko shekarunta bamu kai ba. Nasan wacece Rumana a
tarbiya shiyasa banji komai ba na bada goyon baya ga bukatar Maamu. Abu na gaba da nake
son jan hankalinki shine ko da nan gaba Awaisu ya nemi karin aure saboda yayi alkawarin
rabuwa da Gimbi don Allah kada ki tada hankali ganin tana da kuruciya. Bai zo min da zancen
ba amma kinsan yau da gobe sai Allah. Ko ba komai ina ganin tayi kankanta da daukar
dawainiyar miji da yaransa wanda suka tashi kamar kannenta ita kadai."

Mama da taji yar kwalla ta tarar mata saboda tausayin Rumana tace "Baaba kada ki damu in
sha Allahu tsakanina da ita sai karfafa gwiwa da fatan alkhairi. Kuma ni a nawa ganin gara yayi
aure idan yana da ra'ayi saboda nasan a yanzu kam wani lokacin sai yaji kamar ya zaneta" tayi

dariya.

Baaba ma dariyar tayi "Yo wannan shirmen nata ai shi ne zai kara sawa ya sota. Ku yaran
yanzu baku san komai game da soyayya ba. Misali yanzu da bance ta tafi dakina ba haka zaki
barta a nan shi da yazo saboda ita haka zai juya gobe ya tafi. Dan irin wannan lokutan kamata
yayi a barsu tare tunda matarsa ce. A haka zasu saba tunda ba wani lokaci sosai tarewa zatayi.
Idan akayi tariya tana tsoronsa ko ta kasa masa kallon miji kinga babu kanta."

Mama dai kunya taji sosai amma tasan halin Baaba. Ko a gaban waye duk mai girki cikinsu idan
Harisu ya dawo ta rinka cewa bata son gulma a tashi a bi miji. Tun suna jin kunya har ya zama
indai ya dawo ko tana wurin sai su tashi.
******

Awaisu yana zaune jiran Baaba amma hankalinsa gabadaya yana wurin Rumana da tunanin
wane irin ciwo ne yake damunta haka.

Muryar Rumana yaji tana cewa bazata iya cigaba da tafiya ba Anti Amarya na cewa tayi hakuri
saura kadan. Tasowa yayi ya fito Antin na ganinsa tayi murmushi "wato Baaba turo maka
matarka tayi kayi jinya. To ni nayi nan ku karasa"

Hannun Rumana ta mika masa ya riketa ita kuwa ta juya tana tsokanarsa. Ko gama tafiya
batayi ba Awaisu ya dauki Rumana tana ta mutsu-mutsu ya shige dakin da ita. Kan gado ya
kwantar da ita fuskarta da sauran hawayen da take ta yi saboda ciwo.

Tausayinta yakeji sosai ya zauna a gefen gadon ya rike hannunta na dama.
"Me ya sami Son So dina?"

Ga ciwo kafafunta kamar ana sarawa ga kunyar an kawota dakin wurinsa ta rufe ido kawai.
Matsawa ya sake yi kusa da ita kamar zai rungumeta kamshin turarensa ya mamaye wurin shi
kadai take shaka.
"Naji Maamu tace duk wata kike yi. Period pain ne yake kama miki kafa?"

Wata irin kunya taji duk da ciwon da take ji ta soma sunne kai. Shi kuwa murmushi yayi yana
tsareta da ido gashi yayi kusa da ita sosai
"Ashe dai ba kwaila na aura ba. Nana da shekara zaki shaifa mana babyn So"

Kunya ta kamata amma dayake ba wuya tayi dariya saboda kalmar kwaila da yace sai gashi
tana yi a hankali amma taki kallonsa. Yaji dadi ganin ta dan sake dama tsokanarta yakeyi don ta
saki ranta ta dena hawayen.
"Kada ki damu kin kusa denawa in sha Allah."

Dan ware ido tayi "da gaske Uncle?"

Shan kunu yayi "nima sunana Son So kema kuma sunanki kenan"

A hankali ta dago ta kalle shi amma bata yarda sun hada ido ba. Wani iri take ji a ranta game da
Uncle Awaisu musamman idan yana mata irin wannan abin kamar yaro daidai da ita.

"Mace da namiji duk suna daya?"

"Mata da miji dai zaki ce"

Fuskarta ya gani ta chanja alamun tana jin jiki ya gyara zamansa sannan ya dago kafafunta ya
dora a cinyarsa. Janyewa take son yi ya rikesu
"Ki bari idan ba kina so muyi rigima ba. Matsa miki zanyi ko zaki ji saukin ciwon."

Dogon wandon bacci ne a jikinta rigar kuwa baya iya gani saboda hijab da tasa wanda ya sauko
har kusan cinyarta. Tausa ya soma yi mata a hankali yana matsa kafafun tana lumshe idanu.

"Tun yaushe kika fara ciwon nan?"

Bude ido tayi jin tambayar tasa sai kuma ta sake rufewa. Kamar bata son magana saboda
kunyar magana irin wannan dashi tace da ta koma Abuja.

"Kenan duk zamanku a can kina wannan ciwon kafar kowane wata?"

Kanta ta daga tace eh. Yanayinsa gabadaya ya sauya zuwa takaicin irin zaman da yayi dasu a
gidansa. Gimbi ya tuna a matsayin wadda ta zame masa shamaki ga sauke hakkokin da suke
kansa yaji ya kara tsanar wannan mummunar dabi'a da ta fadawa a dalilin son zuciya.

Muryarsa a hankali cikin nutsuwa take fita yace "Son

31 / 42