Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   32 / 42

93K to 96K   out of 124.7K words

So bani labarin yadda kike managing a irin
wannan lokacin"

Ya tabo abin da bata son tunawa ko kadan saboda yana cikin abubuwan da suka saka mata jin
haushinsa a lokacin. Ta kwashi kusan minti uku yana kallonta kafin ta fara fada masa yadda
suke kwana kuka ita da Maamu domin idan ta gaji da rarrashinta itama kukan take yi. Babu
zancen magani sai dai ta gasa mata kafar tunda Allah Yasa kowane daki na gidan akwai heater
ta bandaki.

Zuciyarsa ta karye sosai da tausayinsu. Da ace zai iya maida hannun agogo baya da ya mayar
ya gyara abubuwan da suka gabata. Godiyarsa daya ga Allah daga ita har Maamu duk suna
raye da baisan yadda zaiyi ba. A lokacin kuka take yi sosai da ta tuna yadda lokutan al'adarta
suka zama lokutan ciwo da kazanta a gareta.
"Uncle Awaisu yana so kiyi hakuri da dukkan abubuwan da suka wuce kinji. Sannan mijinki yayi
miki alkawarin sauke duk wani hakkinki harda kari. Nasan kinsan komai game da abin da Gimbi

tayi min amma duk da haka ba uzuri bane a ganina"

Hawayen da yake bin kumatunta yasa yatsansa yana gogewa a hankali. Akan abu da bai kai ya
kawo ba Gimbi ta tarwatsa musu farincikin rayuwa. Tsoron kada uwarmiji ta koreta ya kaita ga
aikata manya manyan laifuka da sunan soyayya.

Cigaba yayi ta matsa mata yana ja mata yatsun karfar daga ita har shi suna jin wani yanayi.
Suna haka Hafiza tayi sallama ta shigo da kayan Rumana a hannu. Wai itama 'yan mata harda
rufe ido ganin Awaisu yana yiwa Rumanan tausa a kafa. Itama kunyar ce ta kamata tana ta
kokarin dauke kafarta sai dai ya rike sosai gashi wani sabon ciwo da yafi na dazu take ji.
Dariya kunyar tasu ta bashi yace da Hafiza kayan waye ta kawo

"Maamu tace tayi wanka ka kaita asibiti ayi mata allura"

Rumana ta kwabe fuska "ni wallahi bana son allurar"

Hafiza dai ficewa tayi duk kunya ta isheta tana dariya. Ba jimawa ta dawo da ruwan zafi a bokiti
ta shigar dashi bandakin Baaba ta sake fita.

Awaisu ya tashi ya miko mata hannu "taso kiyi wanka"

"Ni bazani asibitin ba. Allurar kara rike min kafa take yi"

Yayi murmushi "naji amma dai ya kamata kiyi wanka kafin na fara toshe hanci matata bata
wanka"

Daga hijab din tayi batare da ta sani ba ta fara sansana jikinta. Shi kuwa sai dariya. Da
taimakonsa ta tashi ta shiga toilet din. Sai da ta rufe kofar yaji tace

"Uncle amma zaka fita kafin na gama ko"

"Sai kin kirani Son So" ya bata amsa yana daga kayan da Hafiza ta ajiye. Riga da wrapper skirt
ne na atamfa sai underwears da bodyspray. Wata leda ya gani ta pad ya tuna labarin da ta
bashi dazu. In sha Allah kwalaye zai rinka ajiye mata a gida don kada ta taba nema babu.

"Uncle pleaseeeee"

"Son So pleaseeee" ya kaikwayeta.

Gaskiya bata so ta fito yana nan da ta sani ta kwashe kayanta ta shiga dasu.

Kamar mai rada yaji tace "Son So"

Shiru yayi ta sake fada yana jindadi sai a na ukun yace mata ya tafi.

Ta dade tana gasa kafafunta sannan tayi wanka ta fito kai tsaye daure da tawul.

Ganinsa tayi a zaune yana juya bra dinta a hannu yana dagowa suka hada ido yace "wannan
ma acuci ce ko size din kenan idan na koma zan hada lefe. Nasan yanzu ance mata komai kari
kuke yi"

Mantawa tayi da ciwon kafar ta nufeshi gadan-gadan ta mika hannu zata karba saboda kunyar
da taji da sauri shi kuma ya daga hannun sama yana kare mata kallo. Kula tayi da abin da yake
yi ta kwasa a guje ta koma bandakin tana cewa
"Yau naga boni"

"Za dai ki ganshi yarinya har me akayi kike gudu tun yanzu"

Yadda ya saba jin farinciki idan tana wasu abubuwan haka yaji yanzu musamman idan ya tuna
dan jikinta da ya gani. Tashi yayi don kada ta kasa fitowa ya dan jingina da kofar ta waje

"Fito ki shirya kinji zan jiraki a dakin Maamu"

Sai da ta dan kara lokaci ta leko don ta tabbatar ya tafi. A gaggauce ta shirya saboda kada ya
dawo ta koma gadon ta kwanta tana zumbura baki yau gabadaya Uncle ya gama da ita.
*****

Hawayen da Dr. Yana take yi sune suka tabbatarwa da Hajiya cewa ta farka. Matsowa tayi kusa
da ita ta dafa kanta.

"Sannun kinji Yana. Allah zai baki wani. Mutanen Maiduguri na hanya kada su iso kina wannan
kukan ki karyawa kanwata zuciya"

Yana ta daga hannunta mara kwari ta share ido. Mafarkin da tayi da Gimbi tar take tuna shi
kamar yanzu yake faruwa.

Mujahid na shigowa ta sake saka wani sabon kukan mai cin rai. Hajiya fita tayi ta barsu yana ta
rarrashinta. Bayan kusan rabin awa Hajiya ta koma dauko purse dinta da ta saka goro a ciki taji
suna magana. Kara kunne tayi sosai yadda zata ji da kyau.

"Shiyasa nace ki dena shiga sabgar mutane a asibitin nan"

"Yanzu sai na ga abu da idanu na na dauke kai don bai shafeni ko wani nawa ba?" Ta fada tana
kuka

Rarrashinta ya koma yi "ba haka nake nufi ba amma kuma ba kowa ne zaki shiga lamarinsa ba
haka kawai ya rabu dake. Wannan Gombo din din take ko Gimbo da bakinki kika ce an fada
miki tana asiri. Infact da idonki kika ganta..."

"Da ban taimaka ba Allah kadai Yasan me tayi niyar yiwa tsohuwar nan. Ban taba nadamar
taimakawa mutane ba domin kawar da kai da mukeyi idan abu bai shafemu ba shine babban
rashin hadin kan da mukeyi a matsayin musulmi. Ya Mujahid idan har Allah Ya bani iko to duk
inda naga rashin gaskiya zanyi kokarin taimakawa."
Girgiza kai yayi "ban hanaki ba Yana amma ba kowane abu bane zaki shiga. Wanda yafi karfinki
sai ki nemi mutanen da ya dace. Yanzu dubi yadda matar nan tayi mana sanadin zubewar cikin
nan. Wallahi bazan yafe mata ba "

Yana ta dafa hannunsa "kayi hakuri in sha Allah zamu sami wani amma nima wallahi wannan
matar sai na nuna mata kurenta"

Hajiya ce ta bude kofar dakin ta shigo tana kallonsu zuciyarta a hasale.
"Cikinku waye zaiyi min bayanin Gombo dinnan yadda zan fahimta"

Mujahid ya matso kusa da ita ta daga masa hannu.
"Wallahi kada ma ka soma cewa nayi hakuri don bazanyi ba. Yana ke nake saurare don wannan
mijin naki babu abin da zai iya"

Ba don taso ba Yana ta bata labarin da ta samu a wurin Rumana da wanda idonta ya gani.
Hajiya ta dan cije lebenta na kasa

"Sai tasan ta taba gudan jinin Hajiya Fanta. Hatsabibanci gidansa tazo da kafarta"

Yana da Mujahid duka a tsorace suka fara rokonta tayi hakuri kada tayi abinda tayi niyya. Bata
sauraresu ba ta dauki jakarta ta fita.

Hajiya Fanta mutuniyar Damboa ce a jihar Borno. Tun tana karama take fama da lalurar aljanu
wanda da kyar aka rabata dasu. Su suka saka mata fitina, rashin hakuri da zafin nama wurin
aiwatar da kowane irin aiki. Bayan tashon lokaci da aka diba ana nema mata magani an samu
sun fita sai wata guda daya da ta nace wai bada magani take so Fanta tayi. A hankali ta zama
wata karamar yar bori inda daga kallo daya zata iya fadin ciwon dake jikin mutum kuma ta fadi
magunguna na gargajiya da zaayi amfani dasu a dace. Har tayi aure ta gama haihuwarta kowa
yasanta da sana'arta. Wani babban malami ne su Mujahid da yan uwansa mata suka nema da
kyar ya samu Fanta ta amince ta dena bada magani domin lokuta da dama abin yafi kama da
wani nau'i na sihiri. Magani da wasu lakani babu wanda bata bayarwa. An rabata da aljanar da
kyar amma kafin ta tafi ta nanata cewa duk sanda take neman taimakonta sunanta kawai zata
kira tayi alkawarin share mata hawaye. Malamin nan ya nuna mata hanya ce kawai take nema
ta dawo saboda haka duk runtsi duk wuya ta kai kukanta ga Allah shi kadai. Labarin Gimbi da

abin da tayiwa jikanta da ko numfashi bai fara ba tayi sanadin zubar dashi ya tuna mata da
cewa shekarun baya karyar mutum ya kara da ita. Aljanun ma bata shakkarsu balle wata Gimbi.
*****

Baaba da kanta taje ta koro Rumana tace suje asibiti. Ba yanzu ake ji ba sai dare yayi ne abin
ke tsananta ta kwana tana kuka mai jinyarta ko rintsawa bazai sami yi ba.

Mayafi ta yafa fuskarta duk tayi fayau dama haka take yi tana dafa bango ta fito ta shiga motar.
Baya ya bude mata yace ta kwanta sosai tace gaba zata zauna amma ya kunna mata AC zafi
take ji.

Kujerar gaban ya kwantar mata yadda zata fi jindadin zaman ya kaita wani health centre dake
kusa dasu. Sunyi sa'a da likita ya rubuta mata allura irin wadda ake yi mata tun dawowarta fika.
Jikinta a sanyaye suka bi bayan nurse din da zatayi mata. Allurar ba karamin zafi gareta ba har
wani dan tsayawa akeyi ruwanta ya shiga a hankali.
Nurse din tana tsartar da ruwan allurar daga sirinji tana dan kada shi Rumana ta zuba mata ido
wanda yake cike da kwalla . Awaisu ya kalleta duk ta bashi tausayi yace "kina so na rikeki?"

"A'a ka fita" sai ga hawayen ya sauko.
Nurse din tayi dariya "bazanyi miki da zafi ba. Hannuna kamar auduga yake wurin allura"

Tashi yayi zai fitan don yasan kila kunya take ji ayi mata a gabansa. Allurar ta sake kallo yana
daf da fita yaji ta cakumo shi a gigici.

"Don Allah Uncle ka rikeni wallahi da zafi allurar"

Murmushi yayi "Suna na Uncle?"

Ta girgiza kai da sauri "Son So"

Nurse din ya kalla shima ba karamin tsanar allura yayi ba don ko ciwo yake aka rubuta allura
baya zuwa idan ba yaji jiki ba.

"Yanzu dole sai anyi mata?"

Wani dadi ya kama Rumana tace "ina fa ba dole bane. Lokacin da ba'ayi min kwana daya nake
warkewa"

Ya kama hannunta har lokacin nurse din yake kallo "to kinji ki bata magani kawai mu tafi"

Rumana sai gyada kai take yi har wani kuzari yana kara shigarta "bari na jira a mota ko Uncle
idan ta baka sai mu tafi. Ni kaga bani da lafiya bazanyi ta tsayawa ba"

Shi kuwa yace ta tafi nurse din ta kwashe da dariyar yadda suke yi duk su biyun sannan tace
idan har Rumana tana son lafiya ta bari ayi mata allurar saboda kada nan gaba kafarta ta sami
matsala. Awaisu na jin haka ya janyota yace ta tsaya zai riketa.
Haba tuni hankalinta ya tashi ta soma kuka. Rungumeta yayi a hankali ya daga hijab dinta ya
kuma janye rigarta kadan. Nurse din na dukawa da allurar zata dan janye zanin kasa ya runtse
nasa idon kamar shi za'ayiwa. Kankame shi da Rumana ta sake sosai tana kuka a hankali ya
gane an tsira allurar shima ya kuma riketa sosai yana cewa tayi hakuri.
Nurse ta gama ta dago kai tana kallonsu. Shi da Rumana sai ka rasa wa akayiwa allurar idan ka
kalli fuskokinsu. Kasa hakuri tayi ta tambayeshi yaya suke da Rumana.

Bai saketa ba har lokacin tana kuka yace "matata ce Son So dina"

"Kun burgeni wallahi. Rumana zaki zama kawata daga yau ko?"

Zumbura baki tayi "bayan allurarki da zafi sosai"

"Tuba nake amarya bari na danna miki wurin kada ya tashi"

Kafin ta kai hannu Awaisu yasa hannunsa a wurin yana dannawa a hankali yana hura daidai
kunnenta. Daga shi har Rumana babu mai magana Nurse din ta rike baki kafin ta fita ta rufe
kofar tana cewa wannan sai ku makanta mutane ai. Kira taji daga bayanta

"Sister A'i maman hudu dagq ina haka?"

Daga hannu tayi ta rage murya sosai "hmmm soyayya na gani zata tayar min da tsohon tsumi"

Tafawa sukayi suna dariya ganin Awaisu ya fito rike da Rumana tana dingisa kafa.
*KASHE FITILA*💡45

*Batul Mamman*💖



Karkashin wata katuwar bishiyar umbrella fruit dake gaban gidan nasu Awaisu yayi parking din
motarsa. Da yake babba ce sai ta yiwa wurin inuwa sosai don suna yawan zaman hira a wurin.
Kuma yayi sa'a babu hayaniya sosai saboda yawancin mutane sun tafi cin kasuwar dake kusa
dasu mai ci duk asabar. Kallon Rumana yayi tayi bacci sai layin hawaye da yake kwance a
kyakkyawar fuskarta. Tunawa yayi da irin kukan da ta rinka yi masa a hanya wai ya bari anyi
mata allura. Bata san ko a jikinsa akayi iyakar abinda zaiyi kenan ba saboda yadda shima yaki
jinin allurar. Tana kukan yana rarrashi yaji shiru ashe bacci ne ya dauketa.

Yanzu da suka dawo yayi parking kallonta kawai yake yi yana kara jin sonta har cikin ransa.
Bayan kamar minti goma aka soma kiran sallar azahar. Tunani yake me ya kamata yayi. Da
gani tana jindadin baccin musamman da akace jiya kwana tayi tana fama da ciwo. Fita yayi ya
zagaya bayan motar tasa hadaddiyar jeep navy blue ya dauko abin sallah. Tagar bangaren da
take ya sauke kadan ya zira abin sallar ta ciki sannan ya mayar ya rufe. Sai yayi mata kamar
labule babu yadda za'ayi rana ta dameta ko wani ya ganta idan ba gaban motar ya zagayo ba
wanda kuma babu hanya don ta kusa taba bango. Sai da ya daidaita mata AC din ya kuma
kwantar mata da kujera sannan ya fito yayi sa'ar ganin Sajid zai shiga gida. Kiransa yayi yace
ya zauna a bayan motar ya jira shi ya dawo.

"Idan na dawo na samu ka tashi yayarka ni da kai ne. Kaga bata da lafiya ka barta tayi bacci"

Sajid ya dago kai a dan rikice jin yace zai gamu dashi "Uncle idan ta farka da kanta fa"

Hannu Awaisu ya dora a lebensa "shhhh da wannan surutun zaka tasar min ita."

"Ita kadai ce taka Uncle mu kuma fa?" Sajid ya fada fuskarsa na nuna rashin jindadi.

Murmushi Awaisu yayi yasan halin Sajid da tambaya idan ya biye masa zai iya makara sallah.
Robar ribena daya ya dauko cikin wanda ya siyowa Rumana ya bashi ya fita daga motar yana
nanata masa ya kula da mukullin da ya bari a jiki saboda AC da bai kashe ba.

Har ya dawo daga masallacin bata farka ba sai ma gyara kwanciya da ta kara yi. Gaba ya koma
ya zauna ya cewa Sajid ya fita ya tafi gida. Yaro yayi kwal da idanu zaiyi kuka.

"Don Allah nima ka barni in sha AC bazanyi surutu ba"

Girgiza kai Awaisu yayi yana dariya ya daukowa kansa karfen kafa. Yadda yake da surutu
yasan ko hannun Rumana ya taba sai ya kai rahoto cikin gidan. Wayarsa ya dauko kawai yana
karanta labarai ba jimawa shima Sajid din ya bingere a bayan motar yana bacci. Sai bayan fiye
da rabin awa ya farka ya fita wai zaiyi fitsari. Buga kofar da yayi da karfi ne ya tashi Rumana ta
farka ta mike hannu tana mika ta kusa hadawa da fuskar Awaisu.
*****

Sajid na shiga tsakar gida ya hau bada labarin Uncle Awaisu yasa shi gadin Rumana yanzu ma
tana motarsa tana bacci. Mama kunya ta rufeta ita kuwa Anti Amarya kan Sajid din ta make
tana cewa bata son gulma.

"Uban surutu idan na kuma ji kana fadin abun da ba'a tambayeka ba sai na dirje maka baki"

Dakinsu ya tafi yana hawaye rai a bace an doke.
*****

Da sauri Rumana ta tashi tana waige gabadaya kanta ya juye ta kasa gane ina take. Awaisu
kuwa hannun da ta miko gaban fuskarsa da tana mika ya damke.

"Kwashe min fuska zakiyi Son So?"

Rufe ido tayi a kunyace tana cigaba da waige ta gano ina suke "yi hakuri kaina ne ya juye"

"Har kinsa na fara jin tausayin kaina" yayi maganar yana son hada ido da ita. Kallonsa tayi ta
tambayeshi meyasa yake tausayin kan nasa suka hada ido bata ankara ba. Sassauta murya
yayi yana mata murmushi "saboda haka zaki rinka bugeni akan gado idan kina bacci"

Zaro idanu tayi "La ilaha illallahu...."

"Muhammadur rasulullah SAW" ya karashe mata.

"Ni dai babu ruwana wallahi" ta turo baki a rude

"Ni kuma da nawa saboda haka kema da naki. Wai me kike zaton ina nufi har kin wani tsorata?"

Baki na rawa tace babu komai. Dariya yayi yana cewa tayi ta gama tsoron da firgicewar zata
dena ne.

Wata irin yunwa taji ta kamata don tun jiya rabonta da abinci. Cikin ta dafe ta kama kofar zata
bude taji ta a rufe .

"Uncle don Allah zan shiga gida yunwa nake ji"

Wani irin kallon yayi mata ta kuma gane dalilinsa taki yin abin da yake so saboda kunya ta sake
cewa tana jin yunwa.

"Babu inda zaki idan baki gyara sunan da kika kirani ba"

A hankali tace "ssssooonnn" don shi dai banda harafin *s* bai iya gane komai ba sai sautin da
bakinta ya fitar. Matso da kunnensa yayi daidai bakinta kamshin turarensa ya kara shiga
hancinta.

"Banji me kika ce ba fa"

Dagewa tayi ta saita bakinta a kunnensa da karfi tace " *SON SO* "

Da sauri ya daga ya hau dukan kunnen don ji yake kamar ya zama kurma. Rumana ta rinka
kyalkyala dariya allurar da aka mata tasa ta manta da ciwon kafa saboda

32 / 42