Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 42

60K to 63K   out of 124.7K words

daya yasa ta gane ba karamin
ciwo tayi ba. Kanta tayi da gudu har tana takawa Hindu matar Bomai hannu ta fada jikin Maamu
tana kuka.

"Maamu me ya sameki haka? Ina can ni ban sani ba"

Tsigar jikin Maamu har tashi tayi jin rungumar da Gimbi tayi mata. Tsana da kyankyaminta take
yi sosai saboda tasan ita ce silar wargajewar farincikinsu.

Ba Awaisu da yake da tabbacin ya sanar da ita rashin lafiyar Maamu har tace karya ne ta kara
da yiwa su Baaba sharri kowa na dakin da yasan me yake faruwa mamaki ne ya kamashi na
wannan karfin hali irin na Gimbi.

Da fuska cike da hawaye ta dubi Awaisu ta soma korafin me yasa bai fada mata ba shine ya
taho shi kadai don ya sa tayi bakin jini. Wannan abu da take yi duk tuggun Ovi ne da tace mata
a haka zata wanke kanta. Ita kuma sukuwa bata san bakin jini Ovi take son kara mata ba yadda
asirinta zaiyi saurin tonuwa ta bar gidan Awaisu.
Baaba ce tayiwa Rumana alama da hannu akan su fita ita da yaran. Sauran bakin ma duka
suka fice don abin ya zama matsalar family.

Jikin Awaisu har wani tsuma yake yi saboda bacin rai wai shi Gimbi zata yiwa wannan rainin
hankalin a bainar jama'a. Yunkurin karasawa gabanta yayi mata magana yayi Harisu ya girgiza
masa kai. Cikin bacin rai ya kaiwa bango naushi zuciyarsa na kuna. Da wace irin mace yake
zaune tsahon shekaru sai yanzu halayenta ke bayyana kansu gare shi.
Maamu tana kallonsa ga tausayi ya bata taji kwalla ta cika mata ido. Sanin cewa Gimbi bata jin
yarensu kuma ita idan ta fada mata da hausa sakon bazai isa yadda take so ba yasa ta yafito
Baaba da hannu. Magana tayi mata kasa-kasa yadda sauran bazasu ji ba. Baaba ko dogon
nazari batayi ba akan maganar duk da tayi matukar mamaki ta dago ita da Maamu duk suna
murmushi

"Awaisu jeka wurin Rumananka ka rarrasheta naga ta fita kamar zatayi kuka. Kaima a yadda
ranka ya baci dinnan ganinta nasan zai sanyaya maka rai."

Anti Baraka da kanenta duka suka bi Baaba da ido cikin rashin fahimtar inda zancen ya dosa.
Shi kuwa Awaisu kamar jira yake yi ya fice daga dakin don yasan idan zai cigaba da zama yana
kallon Gimbi tana wannan karyar kulawar zai iya kai mata hannu a yadda zuciya ke dibarsa.

Fitarsa tayi daidai da zare dukkan wani farinciki da yayi saura a zuciyar Gimbi sai nauyin da taji
kirjinta yayi mata. Tsabar takaici ma kasa magana tayi ta rinka kallonsu daya bayan daya. Wai
yaje wurin Rumanansa??? Kai kila kunnena baiji daidai ba ta fada a fili ba tare da ta sani ba.

Shi kuwa sai da ya kusa isa inda suke tare da su Daula sannan ya tsaya cak yana tunanin me
Baaba tace. Rumanansa? Me take nufi da hakan? Daga ido yayi suka hada ido da Rumanan da
yake tunani ta dan yi masa murmushin karfin hali a zatonta ko yaji haushin yadda ta nuna
tsoron matarsa ne don tasan yana sonta sosai. Shi kuwa wannan murmushin jinsa yayi tamkar
an *kunna fitila* a cikin zuciyarsa har abin ya bashi tsoro. Rumana ce fa 'yarsa.

A cikin sakin kuma cikin yarensu Anti Ummukulsum ta tambayi Baaba me take nufi da Rumanan
Awaisu. Nan tayi bata bayanin sunyi ne kawai don bata ran matarsa. Maamu ta kafe Harisu da
ido tace
"ni ba da wasa nake yi ba dana ka taimakeni ka kara yi min wannan alfarmar"

Baaba tayi saurin kallonta "Da gaske kike yi Awaisu kike son hadawa da Rumana?"

"Ba don na huce takaici ko bacin ran da matarsa ta saka min ba kawai na kula kamar shima
yana son hakan"

A raunane take maganar ta rike Baaba Hure "kiyi hakuri idan na bata miki rai, ban ko yi tunani
ba"

Baaba tace "da gaske kina son wannan hadin?"

Su Harisu duk suka zaro ido jin wannan maganar ta iyayensu. Maamu na cewa eh Baaba tace

"In sha Allahu anyi an gama alfarmar Manzon Allah SAW"

Dakin tsit yayi su Harisu an ma rasa me cewa komai. Gimbi tana tsaye suna yare bata fahimci
komai ba sai dai zuciyarta ta bata akwai abin da suke kullawa jin an ambaci sunan Rumana da
na mijinta. Wani zafi ta fara ji a jikinta tun daga tsakiyar kai har tafin kafa.
*KASHE FITILA*💡35

*Batul Mamman*💖


Babu wanda ya kula ta sai ma Harisu da ya fita don ya rasa abin cewa. Awaisu ya hango ya
kusa karasawa inda su Rumana suke yayi saurin binsa ya tare shi. Rasa abin fada yayi don jin
wannan hadi da bai taba tsammani yayi ba daga sama. Sai kuma ya daidaita kansa yace ya
kamata yaran suci abinci a mayar dasu gida saboda sun sha hanya, gashi suna isowa an sake
tahowa dasu asibiti.

Awaisu yayi na'am da shawarar "ni zan zauna a nan waje har su gama don raina bazai jurewa
karairayin Gimbi ba"

Kafadarsa Harisu ya dafa "kayi hakuri Awaisu ni bana son wata rigima ta tashi a asibitin nan ba
mutumcinmu bane. Duk abin da zamuyi ka bari a koma gida"

Daga nan Rumana ya kira ya umarceta da zubawa su Amir abinci. A dan tsorace ta shiga dakin
kai a kasa taki bari su hada ido da Gimbi wadda take sankame a gefe guda zuciyarta tana ruri
kamar ana hura mata wutar bacin rai.

Ganin Rumanan sai ta dan saita kanta ta rungumota. Tamkar mazari jikin Rumana ya hau bari
saboda tsabar tsoro.

"Oyoyo Rumana kin tafi kin barni da kewa ganin Maamu yasa ban kula babbar 'yar Mummy ba."

Yawu ma kafewa Rumana yayi ta kasa daga harshe tayi magana sai murmushin yake. Gimbi na
kula da yadda ta tsure a ranta taji dadi yarinyar nan bata isa ta kawo mata raini ba don ta riga ta
dasa mata dafi a zuciya. Hannunta ta kama tayi hanyar fita daga dakin da ita tana dariya

"Shine kika biyewa Abbanku baku fada min Maamu babu lafiya ba ko? Muje waje dai musa
labule akwai labari"

Rumana ido yayi kwal-kwal da hawaye ta juyo neman agaji wurin iyayenta tana so wani cikinsu
ya hana Gimbi fita da ita daga dakin. Anti Suwaiba ce tayi yunkurin tashi ta hana Baaba ta

girgiza kai. Bayan fitarsu ganin cewa akwai su Haris a dakin ta sake magana da yarensu

"Ku kyaleta hakan da tayi ya tabbatar min tayi zargin wani abu game da maganganun da
mukayi dazu. Ga dukkan alamu tsorata ta zata yi."

"Kuma shine zaki hana a tsayar da ita? Kada ta cutar da Rumana" cewar Maamu tana sako
kafarta kasa daga kan gadon.

Baaba ko a jikinta harda dariya tace "nafi so ta cigaba da tunanin tayi nasara wannan ne zaifi
kona mata rai idan taji an shafa fatiha"

Abinci ta zubawa yaran da kanta tace su ci a kama hanyar komawa Fika su huta. Su Maamu
duka hankalinsu a tashe tace kada su damu da kanta zata fita ta dawo da ita. Tafi so dai ta bata
damar da zata ji kamar babu wanda ya isa sai ita kadai.

Wani dan wuri da babu kowa Gimbi ta kai Rumana ta sakar mata hannu tare da hade fuska
sosai
"Rumana kin fadawa su Abban Haris wani abu ne?"

Hadiyar yawu tayi da kyar "Mummy wane abu?"

"Au har kin manta na fada miki ni ba Mummynki bace? Da kika dawo gidan ubanki baki hadu da
taki uwar ba?"

Bata ce komai ba hakan ya kara tunzura Gimbi amma dole ta daure tana wurin da dolenta tayi a
hankali saboda 'yan uwan Awaisu ne ko ta ina. Zaro idanu tayi tana mata kallon banza

"Akwai wani abu tsakaninki da Abban Haris? Naji ana ce miki Rumanansa"

Wannan karon ma kasa magana tayi sai ma tsoro da taji ya mamayeta tunda bata nan lokacin
da Baaba ta fadi hakan.

Ta gama kidemewa karshe kamar daga sama taji muryar Awaisu ya kirata cikin sanyin muryar
da ko kadan batayi kama da muryar da uba zai kira 'yarsa ba. Ita kanta Rumana ba don rashin
sabo ba da ta dago cewa Uncle Awaisu fa wani salon shagwaba yayi mata.

"Umm Ruman kije ki gani idan sun gama cin abinci ku fito mu tafi dare yana yi kuma nima
yunwar nake ji baki bani abinci ba"

Tirkashi, zuciyar Gimbi ta kumbura suntum da bacin rai mara misaltuwa. Kallon Rumana tayi
wadda ta kara shiga cikin duhu saboda rashin fahimtar meyasa yayi magana irin haka. Ita ina
ruwanta da cin abincinsa? Ko da can ma ai ba ita take bashi ba. Yadda ya tsareta da kallo yasa
ta cewa "bari na duba idan akwai saura sai na zuba maka"

Kamar zata bi iska don sauri haka ta bar wurin. Bayanta yabi da kallo kuma yasan tabbas Gimbi
shi take kallo yayi dan murmushi yayi gaba yana jin yadda take kiransa hankali a tashe.

Sai da ya koma wurin Harisu yake fada masa me yaji Gimbi na tambayar Rumana. Dama tare
suka hango fitowarsu Awaisu yayi saurin tahowa don yasan bazaa kulla alkhairi ba.

Ita kuwa Gimbi da zaa aunata a lokacin tabbas jininta ya hau. Ta rasa gane meye yake faruwa.
Tunda tazo fa ko kalma daya bata shiga tsakaninta da Awaisu ba. Abubuwa ke neman rikecewa
ta zaro wayarta daga jaka ta kira Ovi. Kuka ne ya taho mata ta danne don kada wani ya fito ya
ganta ta zayyana mata halin da take ciki.
"Ovi please kije wurin Boka ki sanar dashi. Idan abubuwa suka cigaba a haka ina kyautata
zaton komai zai lalace zuwa matakin da bazaa iya gyarawa ba."

Ovi ta gimtse dariyarta tace "ki turo kudi yanzun nan zan tafi wurinsa. Ina muka ga ta zama ana
neman bata shirin da aka jima ana yi. Dayan maganin nan dai da ya baki kiyi kokari ko ta wane
hali ki shafawa maman tasa. Boka yace da kanta zata ce ya biyoki ku tafi kuma bata son kara
ganinsa. Kinga daga nan kin huta"
Gimbi ta sauke ajiyar zuciya sai dai tana kokontan yadda zata iya shafawa Maamu magani
babu wanda ya kula. Ta kula wani kallon tsana suke yi mata shiyasa take tunanin ko Rumana
tazo ta fada musu irin zaman da sukayi. Sai kuma ta ga babu dalilin damuwa saboda idan boka
yayi mata aiki a kansu babu wani wanda ya isa ya daga mata yatsa. A take ta turawa Ovi dubu
hamsin sai dai tana jin faduwar gaba game da maganar Baaba Hure akan kiran Rumana ta
Awaisu.

Tana nan tsaye suka fito tare da su Anti Baraka yau Anti Ummukulsum ce zata kwana. Babu
wanda ya kulata taji jikinta ya danyi sanyi. Dakin ta koma tayiwa Maamu sallama harda
alkawarin gobe da wuri zata zo don ita zata kwana da ita ma ta fita.

Motar Awaisu ta nufa domin tana son magana dashi akan abubuwan da ta gani daga zuwanta.
Sai da Baaba Hure ta tabbatar nan ta taho har tana cewa su Haris su tafi motar da suka zo da
ita kawai Baaba tace

"Rumana kin gaji ne haka kike tafiya da kyar? Awaisu bude mata gaba ta zauna kannenta sai
su zauna a baya ku fara yin gaba"

Murmushi yayi ya bude kofar yana satar kallon yadda Gimbi ta kame kam a wurin tana kallon
ikon Allah. Rumana itama tsayuwa tayi zata waiga ta ga yaya Gimbi tayi don tayi tunanin tare
zasu tafi da Awaisu taji yace

"Shiga mana ko sai na dauke ki ne?"

Kunya taji tayi saurin shigewa yana yi mata dariya. Baaba Hure a zuci tace karen bana maganin
zomon bana Awaisu kayi min daidai. Taji dadi da ta lura da yadda kalar fuskar Gimbi ta canja
gabadaya.

Harisu dama ya riga ya tayar da tasa motar su Anti Suwaiba sun shiga. Baaba Hure suke jira ta
tsaya ta karewa Gimbi kallo

"Kun zo mota a cike zaki koma ke kadai. Ko na dawo taku motar ne na tayaki hira?"

Duk yadda taso daurewa bata san sanda ta watsawa Baaba harara ba sannan tayi gaba kamar
zata tayar da kura. Baaba tana dariya ta karasa motar Harisu suka tafi. Shima Awaisu jan tasa
yayi yaransa suna ta yi masa hira yana amsawa cikin nishadi. Rumana kuwa shiru tayi jikinta ya
kara mutuwa. Me zaisa ace ta shiga motarsa ga matarsa a wurin da ta gama bata tsoro dazu.
Gimbi na shiga mota sai hawaye ya balle mata. Tsawa ta dakawa dreban akan ya fita daga
motar. Jiki na rawa ya fita tana kuka ta kira uwargijiyarta Ovi ta fada mata sabon lamarin da
yake faruwa.

"Ovi cikin kankanin lokaci daga zuwana mutanen nan zasu kasheni da bacin rai. Ki fadawa
Boka ko wane irin shiri suke yi ya wargaza zan bashi ko me ya bukata"

Kwantar mata da hankali Ovi tayi da kyakkyawan alkawarin cewa daga gobe idan taso duka
gidan sai ta juyasu suga tsiya. Tayi wani mugun murmushin auno yadda zata fanshe bacin ran
da Awaisu ya saka mata.
*****

Har gari ya waye bata ga Awaisu ba domin jiya sun rigasu isa Fika. Da suka iso kuma bata ma
ga motarsa ba. Daki aka bata ta shiga tana tabe baki. Ta tsani zuwa garin nan domin a takure
take jin kanta. Su Haris sun bi 'yan uwansu maza yaran Harisu a dakinsu suka kwana. Daula
uwar iyayi ma wurin Rumana ta zabi kwana suka bar Gimbi ita kadai. Da aka bata abincin dare
cewa tayi bata ci saboda tunani yayi mata yawa.

Shiyasa da safe Anti Amarya taki aika mata da breakfast. Shiru Gimbi na jiran abinci don ba
karamar yunwa take ji ba taji shiru sai hayaniyar yara. Nata 'ya'yan da take ji kamar 'ya'yan gwal
babu wanda ya leko dakin. Takaici ya sake kamata.

Sai wurin karfe goma Awaisu ya shigo gaishe da Baaba kafin ya wuce asibiti. Bayan sun gaisa
yana cin abinci tasa aka kira mata Harisu.

Nutsuwa sukayi a gabanta tace tana fatan sun amince da maganar da akayi jiya na auren
Rumana. Awaisu ya dago kai da sauri

"Aure kuma Baaba karatunta fa? Saura watanni ta gama secondary. Daga dawowarta ko wata
biyar bata yi ba ta sami miji ne?"

Sai a lokacin ta tuna baya dakin suka yi magana a asibiti.

"Aure ne zaa hadaku Awaisu ina fata bazaka watsa mana kasa a ido ba"

Harisu yayi saurin kallo shi kuma ya kawar da nasa kan saboda har yanzu bai san yadda zai
kwatanta yaya ransa ya karbi wannan hadi ba.

Baaba Hure ta lura dasu tayi murmushi

"wannan hadi wanda bamu taba kawowa ko da wasa zamuyi shi ba ina so ku dauke shi a
matsayin rubutaccen al'amari. Bansan me Maamu ta gani ba amma ni dai tunda ta fada
zuciyata ta aminta ta kuma sami nutsuwa sosai akan hakan. Ina so a matsayinku na 'yan uwa
kuyi shawara da juna. Idan har wannan hadin zai taba muku zumunci kafin mu tafi asibiti yau ku
yanke shawara ku fada min."

Babu wanda yayi magana a cikinsu Baaba Hure ta tashi ta fita. Sai suka koma yiwa juna kallon
kallo. Awaisu kunyar Harisu yaji ta rufe shi. Shi da kansa yana mamaki tun zuwansa Fika yake
yiwa Rumana kallo na daban. Yarinyar da aka haifa a gabansa har ya saka mata suna. Wannan
abu da kunya sai dai ya rasa gane dalilin da yasa shima zuciyarsa take kwadaita masa da ya
amince.

Harisu ya gyara zama yana kallonsa "nasan yadda nayi mamakin wannan magana kaima kayi.
Ina so nace ban yarda ba domin Rumana 'yarka ce amma bazan taba yiwa iyayenmu musu.
Abu daya zan tambayeka dan uwana....ka amince da auren nan da zuciya daya?"

Ya Ilahi sosai Awaisu yaji kunya musamman ganin yanayin Harisu ba yadda ya saba ba. Yasan
ko shine zaiji kwatankwacin haka ko ma fi. Bai taba tunanin faruwar haka ba amma shima tasa
zuciyar ingiza shi take yi akan kada ya cuci kansa.

Kansa ya sunkuyar "Yaya Harisu... " sai kuma yayi shiru saboda nauyin amsar da zai bayar.

Tashi Harisu yayi batare da ya saurari amsar tasa ba ya fita. Bai dade ba suka dawo da Baaba
a gabanta yace ya amince. Awaisu ya kasa kallonsu duka su biyun saboda tsananin nauyi da
yaji. Harisu yasan cewa duka su biyun abin yazo musu a bazata kuma baya ganin laifin kanin
nasa sai dai har ga Allah yana tausayin Rumana.
Nasiha sosai Baaba tayi musu akan zumunci da fatan wannan hadi ya zame musu alkhairi mai
dorewa.

Awaisu ne ya fara fita Baaba ta cigaba da yiwa Harisu nasiha don tasan sai a hankali zai nutsu

da maganar. Ba kuma don baya son Awaisu ba sai dai ko waye yaji zaiyi mamaki duba da
alakar dake tsakaninsu.

Ranar Gimbi kirikiri taki zuwa asibiti wai bata da lafiya saboda Ovi bata kira ba. Abinci kuwa sai
da rana ta take Anti Amarya ta aika mata. Ba don gudun batawa Harisu rai ba ma ai so tayi ta
gasa ta yadda ta yiwa Maamu.

Da Maamu taji sun amince duka su biyun tayi ta saka musu albarka shi da Harisu. Sai kuma ta
bawa Awaisu shawarar ya koma bakin aikinsa tunda suna sa ran nan kwana biyu a sallameta.

Dr. Yana taji dadin yadda Maamu take samu sauki sosai idan ta gama round har hira take zuwa
suyi.

Washegari Gimbi ta sami kuzarin zuwa asibitin saboda Ovi ta kirata ta fada mata Boka ya
kwana aiki akan Awaisu da duk wani

21 / 42