Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
ke faruwa.
"Kayi hakuri abokina, bani da masaniya akan hakan. Da tun farko bazan bijiro da maganar
hadasu ba"
Awaisu duk sai yaji babu dadi. Yanzu da Alh Mudi baizo nemawa dansa ba shikenan ya bata
zumuncin abokan.
Muryar Saminu ce ta katse masa tunani "Babu komai, ai kaga yadda Allah Yake nuna ikonSa.
Sai muje gidan ka fada masa ka bada auren Mardiya ga Fawaz a matsayin waliyinta tunda bani
da dan uwa namiji. Shi kuma Awaisu sai na nema masa auren Gimbi"
Sai a lokacin Harisu yayi murmushi hankalinsa ya kwanta ganin Saminu bai dauki abin da zafi
ba.
Washegari kuwa suka dunguma sai gidan Alh Mudi aka daidaita magana. Sallah karama da sati
biyu aka sha bikin Awaisu da Gimbi. Ganin cewa bai samu muhallin kirki ba Alh Mudi ya bashi
gida da sunan Gimbi a Abuja inda zasu fara zama kafin ya sami nasa. Ita kuma Mardiya suka
tare a Kaduna ina Fawaz yake aiki. *****
*Bayan shekara 12*
Cikin shekarun da suka gabata Awaisu ya sami budi sosai. Domin har gida ya gina kato a Abuja
yana shirin tarewa. Inda Allah Ya kara taimakonsa shine kasuwanci da yake yi. Duk da yana aiki
ga rashin lokaci haka ya sami yara biyu 'ya'yan kawunan sa da ya budewa shago suke sayarda
atamfa da shadda. Abu kamar wasa sai da ya hada shaguna hudu a jere a Wuse market. Ga
kwazonsa a wurin aiki yasa ya sami mukamin manaja a bankin.
Gidan Harisu kuwa yasha gyara sosai har mota ya saya masa sannan ya kara masa jari.
Zamansu gwanin sha'awa. Tsakaninsu da Gimbi babu wata matsala. Dayake itama aikin bankin
take yi bata da lokaci na zuwa Fika sosai. Yaransu hudu babban ciki Haris, sai Daula mai sunan
babar Gimbi, Amir mai sunan Alh Mudi da kuma auta Sa'ad suna kiransa Mu'allim. *****
A gajiye Awaisu ya shigo bayan isha yaran suna ta murnar dawowarsa daga Fika. Sai da ya
gama dasu ya wuce dakinsa. Sauri yake yi idanunsa su gane masa matar da yake jin bazai
taba iya hadata da kowa ba saboda irin son da yake yi mata ga kuma albishir a bakinsa.
Taci kwalliya tayi kyau sosai tazo ta tarbe shi tana murmushi
"Ashe ka shigo maimakon ka kira kafin ku karaso na hada maka ruwan wanka"
Ya shafi gefen fuskarta yana murmushi "kada ki damu, zo ki zauna kiji albishir din da nazo miki
dashi har biyu. Dayan ina hanya akayi min waya aka fada min"
Kaskon turaren wutan da yake gefen gado ta dauke sannan ta dawo ta zauna kusa dashi yana
rungume da ita yayi ajiyar zuciya.
"Gimbina Allah Ya yarda. Visa dinku ta fito"
Ta dago kai da sauri cikin farinciki "wace visa kuma?"
"Dama na boye miki ne sai komai ya tabbata. Na biya muku Hajji ke da Yaya Harisu, Baaba da
Maamu. Sai Yaya Zakiyya tunda su Anti Baraka da Ummu mazansu sun kaisu. Kinga za ta
tayaki kula dasu Baaba. Albishir na biyu kuma kuna dawowa nake so mu tare a Apo. To babban
abin jindadin shine dasu Maamu zamu tare"
Shiru yaji Gimbi taki dagowa bare tayi magana. Ko da ya dago kanta hawaye take yi sosai.
Wani sonta ne yake shigarsa domin yasan kukan farinciki take yi. Rungumeta yayi yana shafa
bayanta.
"Dama nasan zakiyi murna sosai Gimbina. Shiyasa ban fada miki batun tafiya Hajjin ba sai da
na gama. Tunda kinga ni naje har sauu biyu kuma last year munyi umara tare dake. Shiyasa
bazan bi ku ba. " ya cigaba da cewa
"Kuma fa yadda naso har da Baaba zamu tare. Sai dai lalurar idonta yasa Yaya yaki yarda.
Shine na hakura ba don naso ba. Burina ya cika zan dawo da Maamu kusa in kula da ita. Itama
taji dadin arzikin da Allah Ya bani. Ta dade tana jin nauyin su Baaba da Yaya Harisu. Duk da
naso hadawa da Baaba hakan bai samu ba. Amma zan dauko Rumana. Gimbina da ina da
yadda zanyi fa wallahi Yaya Harisu ya dena fita neman kudi. Komai ni zanyi masa"
Can kasan makoshi tace "uhmm hakane." Domin ji take yi ya cikata da surutu mara kan gado.
Mikewa yayi ya shiga bandaki domin yayi wanka ko zaiji saukin gajiya.
Yana shiga Gimbi ta fice ta tafi dakinta ta rufe kofar da mukulli. Gadonta ta hau ta saki kuka
cikin tashin hankali. Ko da wasa bata taba kaunar zama da uwarmiji ko dangin miji ba. Can
daga nesa dai yayi musu kyauta suna kauye ba sai sun rabesu ba.
"Tabdi, akwai matsala. Matar da ko Hausar kirki bata iya ba sai anyi magana tayi ta yankare
hakora tana murmushi. Shine don kana jin ka fara kudi zaka dauko min su ka kawosu ko neman
izini na bakayi ba. Da sake Awaisu....bana cikin matan da za'a hada da uwarmiji ace mu zauna
lafiya gida daya"
Dankwalinta tayi jifa dashi ta rasa me yake mata dadi. Ita fa shi kadai take so ba danginsa ba.
Duk halaccin da tayi masa ta aureshi talaka ko gidan zama bashi dashi. Shine yanzu arzikin
nasa kuma sai sun raba tare da wadda bata nan lokacin da suke nema. Ta hana kanta sukuni
tana fita aiki duk domin ta taimaka masa. Ba don kada ace tayi sharri ba ma sai tace gabadaya
gidan Harisu wari yake yi mata idan taje Fika. Shiyasa bata son zama idan taje.
[2/7, 10:42 PM] +234 814 971 0186: *KASHE FITILA*í ½í²¡7
*Batul Mamman*í ½í²–
Gani tayi kukan bazai kaita ko ina ba ta yanke shawarar washegari zata kira Mama ta fada
mata. Dole ma a dauki mataki don ba bauta tazo yiwa kowa ba.
Shirin bacci tayi sannan ta koma dakin nasa. Kwance ta same shi akan abin sallah da gani
sallah ya idar bacci ya dauke shi. Tausayinsa kuma taji, ya mayar da kansa tamkar agogo.
Bashi da hutu kwatakwata duk domin ya farantawa su Maamu. Tsaki taja a fili tana tunanin
yadda zata bullowa lamarin da ya tunkaro ta.
"Saboda zan kawo mahaifiyata gidana shine kike tsaki haka Gimbi?"
Muguwar faduwar gaba taji. Shi kuwa ya mike tsaye yana kallonta rai a bace. Bakinta yana dan
rawa tace "haba my dear, kada kayi min mummunar fahimta mana. Dazu da kanka ka gani ina
murna harda kukan..."
"Kukan bakinciki ba. Da farko har ga Allah nayi zaton dadi kika ji ganin yadda na damu da
yanayin da mahaifiyata take ciki. Bata da wurin da zata kira gidanta. Sai da nayi wanka na biyo
bayanki naji kina kuka sosai a dakinki."
Rasa bakin magana tayi shi kuwa ya cigaba da magana cikin kunar rai
"Duk duniya bayan Maamu babu wanda ya cancanci kyautatawa daga gareni kamar Yaya
Harisu. Ban taba boye miki asalina ba. Amma abin mamaki kina nuna bacin ranki akan
kyautatawar da zanyiwa wanda suka zama jigon rayuwata. Idan bazaki iya zama dasu ba sai na
auri wadda zata iya"
Tun da ya fara magana bata tanka shi ba sai yanzu da ya ambaci kishiya.
"Kayi kadan kace zaka auro wata ka ajiye a gidan nan. Ko ka manta cewa nawa ne. Suna na ne
a jikin takardun gidan"
"Dadin abin nima ina da nawa. "
Ta turo baki cike da tsiwa. Tsiwar da a da take bashi sha'awa idan tayi
"Haka nan zaka kare rayuwarka kana yiwa wani kato bauta. Sai shegen aure da tara iyali. Kai
kuma an barka da siyan shinkafa da ragon suna"
Shiru yayi har sai da ta gama maganarta tukunna sannan ya tako gabanta fuskarsa babu annuri
ko kadan. Ja ta rinka yi da baya yana binta
"Yaya Harisun ne kato Gimbi?" Ya fada a hankali amma kana jin muryarsa har wani rawa take yi
saboda bacin rai.
Duk da a tsorace take amma ta kule da yadda yake zare mata ido akan 'yan uwansa.
"Karya nayi ba katon bane? Ko baiyi biyunka ba"
Bata karasa magana ba taji ya gwabje mata baki. Nan take jini ya soma zuba saboda fashewar
lebenta na kasa.
Cikin kuka tace "Awaisu ni ka fasawa baki?"
"Idan baki fita daga dakin nan ba sai nayi miki abin da yafi wannan."
Murya ta soma dagawa tana kuka "babu inda zani, gidana ne ba naka na. Idan kaji haushi ka
fita ka koma naka"
Fitar yayi zuciyarsa tana tafasa. Wai akan iyayensa da bashi da tamkarsu shine Gimbi take yi
masa abin da bai taba tunanin zata aikata ba. Lallai ba'a shaidar mutum. Yasan halinta na
kyankyami da ji da kai. Shiyasa yake mamakin irin son da take masa farkon haduwarsu. Falo
yaje ya samu yaransa uku sunyi bacci sai Haris da yake karasa homework. Tashinsu yayi daga
su sai kayan baccin jikinsu suka fice. Motarsa ya bude suka shiga suna tambayarsa inda zasu
je. Bai basu amsa ba ya rinka dannawa mai gadi horn. Yana budewa ya fita a guje.
Karar horn din ce ta fito da Gimbi. Tsoronta kada da gaske ya fita daga gidan. Sai dai abin
mamaki ba shi babu yaran.
Nan fa hankalinta ya kara tashi. Mai aikinsu Laminde ta shure da kafa tana bacci itama a falon
ta tambayeta ina su Daula
"Hajiya gasu nan suna hamok. Jiransu nake yi su karasa aje a kwanta."
Ta galla mata harara "ina kika gansu. Aikin banza babu abin da kika iya sai bacci"
Waje ta fita inda mai gadi ya tabbatar mata da yaran Alhajin ya fita. Haka ta rinka kiran wayarsa
yaki dauka. Karshe ma kashewa yayi yana kallon yaransa suna bacci a makeken gadon
dakinsa. Gidansa na Apo ya tafi dasu.
******
Da sassafe yaji ana buga gate ya leka ta taga. Maigadinsa ya gani yana ta washe baki ya
budewa Gimbi gate ta shigo. Ko rufe kofar motarta batayi ba ta fito ta shiga gidan cikin sauri.
A falo ya sameta yace kada ta tasar masa yara.
"Wane irin wulakanci ne zaka daukar min yara cikin dare"
"A iya sanina lokacin da muka tare a gidan nan ke kadai kika shigo sai akwatunan kayanki. To
mene ne na bacin rai don na kwashe yaran da jinin Maamu yake yawo a jikinsu"
"Wai duk saboda maganar jiya da bata taka kara ta karya ba kake min wannan cin kashin harda
fasa min baki"
Ya tabe baki "ina jin baki san girman uwa bane"
Neman sulhu take yi domin tun aurensu basu taba samun sabani irin haka ba. Kwantar da
murya tayi ta soma magana
"Duk laifinka ne, ta yaya zaka shirya kawo Maamu batare da neman izinina ba? Nima fa ina da
hakki akan ka. Kuma abu irin wannan sai ka fara shawara dani kaji nawa view din"
"Neman izininki? Wai dama haka kike ne ko kuwa sabon salo ne kika fito dashi kawai don baki
son dangina. Ba fa tun yau na san kina nuna musu kyama ba. Sharewa kawai nake yi saboda
babu wanda ya taba korafi cikinsu."
"Kaga ni ba rigima nazo muyi ba. Maganar fahimta nazo da ita. Idan kana so ka ginawa Maamu
sabon gida a Fika is up to you. Amma batun mu zauna tare is out of the question. Zama da
suruka baya taba haifar da alkhairi"
Duk yadda yake son ta a daidai wannan lokacin yayi nadamar aurenta. Rasa bakin magana
yayi yace mata kawai ta fita idan ta gama. Ganin wankin hula zai kaita dare ta ja motarta ta tafi
gidansu. Tana kuka ta zayyanawa Mama abin da ya hadasu. Mama ta dubeta sosai ta girgiza
kai.
"Idan kika kure Awaisu ya sakoki zaki gane kudi da gata aikin banza ne idan aka rabaka da
iyalinka. Ke da ya kamata ki nuna masa kinfi kowa farinciki shine zaki bata masa rai akan
mahaifiyarsa. To yayi miki adalci ma da bai hadoki da takarda ba. Shashashar kawai. Idan ma
zugaki akeyi ki sani aljannarki tana karkashin kafar mijinki. Shi kuma tasa tana tare da
mahaifiyarsa. Kada ki zama mace mai kashewa mijinta fitilar rayuwarsa Gimbi. Uwa haske ce,
uwa rahamace. Da kika shiga matsala ai gaki a gabana."
"Mama yanzu goyon bayansa kike yi"
"Ki kiyayeni Gimbi. Kuma ki wuce yadda kika bata mishi rai ki bashi hakuri ku sasanta. Idan
Alhaji yaji maganar nan ki kuka da kanki. Kinsan halinsa sarai. Bar ganin yana sonki hakan
bazai hana ya saba miki ba"
Dukar da kai tayi ta gama jin fadan Mama ta tashi ta koma sabon gidan.
Amir ne ya fada mata baban nasu yana daki ta shiga da sallama. Kafin ya amsa ta durkusa
gwiwoyi a kasa a gabansa tana kuka. Kamar ya basar sai dai Gimbi matsayinta daban a
zuciyarsa.
Tasowa yayi yazo gabanta. Cikin kuka da nuna nadama ta rinka bashi hakuri da nuna masa ta
gane kuskurenta. Kukan da tayi tana ajiyar zuciya yasa dolensa ya hakura tare da yi mata
nasiha. Cikin dan kankanin lokaci ta shawo kansa suka daidaita.
*****
Zaune suke cikin daki su biyu ta dubi kanwar Mama wadda take binta bayan ta bata labari.
"Anti Bebi wannan ita ce matsalar da ta tunkaro ni. Kuma Mama ta bashi goyon baya"
"Ki bar komai a hannuna 'yata. Indai ina raye babu wanda ya isa ya takura miki. Tun da dadewa
nace kizo muje a mallaka miki shi a tafin hannuki kika ki yarda ke dadi miji. Yau ga irin abin da
nake ta hango miki ya faru. Ke ko babu boka babu malam yayi kadan kinji ko. Shi din me?
Mijina na uku ma duk taurin kansa sai da ya koma albashinsa ma a hannuna yake balle wani
Awaisu."
Kalmar karshe ta sosawa Gimbi rai sai dai biyan bukata yafi dogon buri
[2/7, 10:42 PM] +234 814 971 0186: *KASHE FITILA*í ½í²¡8
*Batul Mamman*í ½í²–
A kwanakin da suka biyo baya Gimbi ladabi take yiwa Awaisu sosai. Tsakanisu tamkar wani abu
bai faru ba. Tarewarsu a sabon gidan da ake jiran sai bayan babbar sallah idan sun dawo daga
hajji kuwa tuni ta rushe. Kusan duk abin da suke bukata daga tsohon gidan sun gama
kwashewa.
Gimbi ta gyara dakin da Maamu zata zauna tamkar wata amarya. Dayake komai sabo ne idan
ka shiga kamar kada ka fita. Dakin Daula da taci burin gyaransa ma saboda tilon 'yarta sai da ta
matsawa Awaisu aka karo wani gadon a matsayin na Rumana. Karshe ta yiwa Maamu da
Rumana dinki kala biyar biyar ta kawowa Awaisu.
Shayi yake sha yana duba wasu takardu ta kawo ledoji manya biyu ta ajiye tare da durkusawa a
gabansa.
"My dear ga tawa 'yar gudunmawar"
Daya daga cikin ledojin ya bude. Kaya ya gani a dinke duka super holland har biyar. Ya kalleta
da alamar tambaya. Rausayar da kai tayi tana kifta idanu alamun zata yi kuka.
"Nasan babu wani abu da zanyi ya wanke wautar da nayi maka kwanakin baya. Amma don
Allah ina mai sake neman afuwarka. Na tsorata ne da jin labaran zama da surukai har naso
bata aurena akan labaran wasu da nake ji"
Tayar da ita yayi sannan ya matsa yadda zata iya zama kusa dashi. Ya kama hannunta ya rike.
"Bazanyi miki alkawarin cewa kullum cikin zaman lafiya zamu kasance ba idan Maamu tazo.
Amma ina so ki sani ba wai don ita ta haifeni ba, Maamuna bata da rigima ko kadan. Mace ce
wadda yanayin kaddarar rayuwa ta sanya mata mugun hakuri da kawaici. Ina jin ba domin
Baaba ba da a sangarce ma zan tashi saboda tsabar hakuri irin nata. Tabbas banji dadin abin
da kika yi ba amma na hakura. Da kinsan yadda nake mafarkin zama inuwa daya da ita nasan
baza kiyi waccan maganar ba tun farko"
Sake bashi hakuri tayi tana kuka da alkawarin gyara kuskurenta ta hanyar bin Maamu sau da
kafa.
*****
"Anti Bebi lokacin tafiyarmu sai kara matsowa yake fa. Ni wallahi bana son yin tafiyar da
mutanen nan. Dukkaninsu babu wata alamar wayewa. Muje airport su janyo a rinka kallona"
Dariya sosai Anti Bebi tayi sannan ta soma magana da shakakkiyar muryarta wadda tsabar
gayu da make murya wurin janyo hankalin maza ta koma haka
"Ki samu ya barki muje wurin da nake fada miki. Kuma kiyi a hankali kada uwarki taji labari.
Kinsan dai ba shiri muke da ita ba"
Gimbi ta tsuke baki jin an zagar mata uwa. Ita kanta bata fiye shiga sabgar Antin tasu ba sai da
wannan abin ya faru. Yadda Anti Bebi da Mama basa kama a fuska haka suka bambanta a hali.
Yanzu haka aurenta na shida kenan. Abin mamaki masu kudi take aure suyi ta mata bauta. Sai
ta tara abin da ta tara ta nemi sanadin da zasu saketa. Mama ta gaji da fada da nasihar ta
tsame hannunta daga lamuran kanwar ta ta.
"Shi kuma mijin naki ki barni da shege, idan Wangesi na tsangaya ya fara aiki akansa ina fada
miki sai juya alkalami yafi miki wahala akan yadda zaki rinka juya shi son ranki. Shi din banza..."
Mikewa Gimbi tayi tana rataya jaka rai a bace. Anti Bebi tace
"Me aka yi kuma zaki tafi muna magana"
"Haba Anti, zamana a nan kin zagar min uwa kin koma kan mijina. Ina sonsu bazan jure
zaginsu da kike yi ba"
Dukan cinya tayi irin na matan da suka ga jiya suka ga yau.
"Karyar banza, Amina dai zan yarda kina sonta tunda ita ta haifeki. Amma indai Awaisu ne
karya kike yi Gimbi. Duk matar da take son mutum take kin iyayensa ko 'ya'yansa na wani auren
kallon munafuka nake yi mata. So da ya amsa sunansa shine ki rungumi duk abin da mijinki ya
nuna yana so ki taya shi ririta shi"
Ganin Antin