Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 42

51K to 54K   out of 124.7K words

taje tana bankar tarkacensu na asibiti nasara ya hore musu
kunne anki haifa min jikoki."
Yana kanta a kasa ta soma shafa mata lallen a kafa idanunta fal hawaye taji Hajiyan ta cigaba
da fada
"Ke nifa da ace ba Mujahid bane kadai namiji babu abin da zai kawoni gidansa. Yo gidane

banda yahudanci da nasaranci babu abin da ake yi. Ni dai hadin zumunci baiyi min rana ba. Da
bare ya aura mai halin nan da tuni tasan inda dare yayi mata. Yanzu kuwa ko me nayi sai ace
babu kara babu zumunci. Ko ita uwar taki Yakaka ai tasan ina kokari"

Cikin siririyar murya tace "Hajiya kiyi hakuri"

Tsaki tayi tace ita dai a saka mata lalle kuma ta rinka yi daki daki kada wani wurin yafi wani
kamawa.

Mujahid da yake daga wajen dakin yana jinsu ya koma bangarensu zuciya babu dadi. Samun
mace irin Yana sai an tona. Matar da bata da burin da ya wuce ta kyautatawa mutane. Idan ya
nuna rashin jindadinsa game da yadda Hajiya take yi mata ranar kwana take yi tana fushi dashi.
A cewarta bazata taba jindadin rayuwa ba idan ta zama silar da mijinta yayi wasa da aljannarsa
dalilin kin kyautatawa mahaifiya.

Zaman jiranta yayi sai bayan awa biyu ta dawo. Tana shigowa dundu tayi masa a baya tana
fara'a kamar ba ita ba. Wanka suka yi sannan suka ci abincin da tayi musu kafin ta fita aiki.
Suna gamawa aka kira magariba ya fita sallah ita kuma bayan ta idar ta gaggauta dora tuwo
wanda ta gama kafin isha. Da ya dawo ne suna hira take bashi labarin Maamu da taji a wurin
Rumana

"Yaya ba don cin fuska ba nake baka labarin nan amma gaskiya wasu matan basu iya samun
wuri ba. Yanzu ita Allah Ya bata wadda zasuyi zaman fahimta ga zuria amma ta daukowa kanta
balai da hannunta"

Hannuwanta ya rike tare da kokarin hada ido da ita "Kanwata don Allah kada naji kin shiga
wannan case din. Nasan halinki na tarar aradu da ka. Amma har yau ban manta mutumin da
kika taimaki matarsa akaje alkali ya kashe auren saboda dukan da yake mata. Kinfi sati ba kya
fita daga gidan nan saboda fakonki da ya rinka yi. Ni kaina a tsorace na rinka fita kada a
sabauta ni" ya kare da dariya

Jinsa kawai take yi amma ko kadan bata tsammanin yadda labarin nan ya shigeta zata dauke
kai. Ita fa salihancinta daya ne a rayuwa gaban uwar miji. Daga nan kuwa bata ki a hau sama a
rikito ba indai zata kwatarwa mutun yanci.

Yadda ya kula tana juya kai yasan maganar bata shigarta. Girgiza kai yayi don yasan aiki ya
same shi.
*****

A gaggauce Awaisu yake ta shiri ya watso kaya daga wardrobe yana cusawa a karamin akwati.
Takun Gimbi yaji gabansa ya fadi sai dai ya dake ya cigaba da zubawa amma a hankali.
Kallonsa tayi tare da akwatin

"Indai kayan tafiyarka Lagos ne na hada maka tun jiya"

In'ina ya soma sannan da kyar ya iya saita kansa yace "nasan wancan kayan duka suits kika
zuba. Ni kuma yanzu Fika zan tafi na fasa zuwa Lagos din."

Duk da ta razana ta daure tace "bangane ba"

"Ashe tun daren jiya Yaya Harisu ke kirana Maamu tana kwance a asibiti. Bansan yadda akayi
wayar ta koma silent ba sai da safe naga text dinsa"

Gimbi ta hade girar sama da ta kasa. Dama ita tayi silencing wayar da ta ga Harisu yana kira
"yanzu don sun rainaka shine tun tafiyarsu baa nemeka ba sai yau zasu ce Maamu babu lafiya.
Anya ba wani abu suke kullawa ba? Kayi tafiyarka Lagos din kawai Abban Haris ina zaton
maganar da Amir ya fada min bayan dawowarsu daga Fika kwanakin baya gaskiya ne"
"Me ya fada miki?" Ya tambaya yana kokarin zuge karamin akwatin.

Shiru Gimbi tayi taki magana. Awaisu ya sake tambayarta sai kawai ta fashe masa da kuka.
Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba domin kuka take mai cin rai. Duk yadda zatayi kada ya tafi
sai tayi domin gudun bacin aikin boka. Zama yayi yana ta rarrashinta har zuwa lokacin da idea
tazo mata sannan ta fara magana murya a dashe.
"Kasan tun bayan dawowar Maamu garin nan ka rage zuwa Fika."

Kansa ya gyada yana cigaba da kallonta.

"Dasu Amir suka dawo shine yace min wai yaji Kawu Harisu da Baaba suna cewa yanzu ka
rage basu kudi tunda Maamu tana nan. Wai zasu san yadda zasuyi ta koma Fika dole ka rinka
zuwa"

Jin haka ya mike da sauri rai a bace "bari naje na sami Amir din naji gaskiyar zancen nan"

Kafin ya kai kofa Gimbi ta riko shi tana wasu hawayen "kada ka tambaye shi saboda ranar da
ya fada min baka ga irin dukan da nayi masa ba nace bana son gulma. Nace masa kuma yayi
min alkawarin bazai sake zancen ba"

Hannunwanta ya zame daga jikinsa ya sake nufar kofa "ai ba wani zai fadawa ba sai ni."

Har ta fara tsorata tace "amma Abban Haris baka ganin bata tarbiya ne hakan. Ni nace yayi
alkawarin barin zancen kai kuma zaka sa ya fada. Kaga zai tashi da rashin sanin girman
alkawari"

Har zuciyarsa yasan ko kadan bai gamsu ba amma kuma zuciyarsa tana ingiza shi akan ya

hakura. Wani irin bacin rai ya rinka ji ya juya a fusace ya dauko jakar da ta zuba masa kayan
zuwa Lagos ya fita. Wani asirtaccen murmushi tayi a fuskarta kuwa tsantsar damuwa ce kawai
take nunawa. Har waje ta biyo shi tana bashi hakuri akan kada ya dauki zafi da su Harisu 'yan
uwansa ne. Shi dai bai tanka mata ba ya shige bayan mota dreba ya ja.
Dakinsa ta koma ta daka tsalle tana murna. Su Harisu basu isa su dagula mata lissafi ba. Tasan
duk ranar da hankalin Awaisu ya dawo jikinsa akwai rikici tsakanisu. To amma ko kadan bazata
lamunce uwar miji ta rinka juya mata miji ta zama borar karfi da yaji ba. Aure tayi don taji dadi
bata fatan irin zaman da wasu suke yi iyayen miji su mayar dasu tsumman goge goge. Mace ta
kasa sakewa a gidanta saboda suruka me kenan akayi. Gara da tayiwa tufkar hanci taci karenta
babu babbaka.

Awaisu kuwa tunda suka fita zuciyarsa take masa wasu sake saken banza. Har ayyana masa
takeyi Harisu ya killace Maamu ne kawai don yaci kudinsa. Abin haushin shine duk nemansa
saboda su da iyalinsa ne. Me ya ragesu dashi da zasuyi masa haka? Numbar Maamu yayi
niyyar kira sai wata zuciyar ta hana shi. Tsaki kawai yaja ya lumshe idanunsa har suka isa
bankinsu. Aiki zai dan rage kafin lokacin tafiyarsu airport yayi.
*****

Kwanaki biyu a tsakani Harisu ya cika fam da bacin rai. Ya sake kiran Awaisu wai shi yake
fadawa ayyuka sunyi masa yawa yanzu ma yana Lagos. Harda cewa ya duba accout dinsa yayi
masa transfer na dubu dari biyu su kara a kudin asibiti. Da wannan takaicin ya tafi asibiti yana
zuwa Baaba take tambayarsa yaya sukayi da kaninsa ya daure fuska kuwa. Ganin haka Maamu
ta soma hawaye. Bacin ranta ba na komai bane sai yadda danta ya juya mata baya. Harisu ya
kula da haka ya dawo kusa da ita ya zauna yana murmushi.

"Maamu ki dena saka damuwa a ranki. Kina warkewa da kaina zanje Abuja na sami Awaisu.
Yanzu kinga likitoci sunce baa son komai ya bata miki rai. "

Baaba ta kara da cewa kada ta damu tare zasu je sai wannan Gimbin ta gane bata da wayo. Ita
dai jinsu kawai take yi tana yake don nuna musu bata damu ba.

Suna haka Dr. Yana ta leko dakin da fara'arta suka gaisa ta tambayi jikin Maamu. Bayan ta
dubata ta ne ta dan kalli Harisu wanda a cewarta bata ga mutum mai karamcinsa ba.

"Uhmmm dama nace an kirawo mata Awaisun da take kira kuwa? "

Baaba Hure tace "amma wannan yarinya da fitina kike. Yanzun nan mun samu hankalinta ya
dan kwanta zaki zo ki tada zance."

Langabe kai Dr. Yana tayi tana kallon Maamu "ni wallahi tausayi take bani. Idan yaki zuwa ne
wani ya bishi mana a fada masa bata da lafiya yazo kada Allah Ya raba ganawar"

Harisu ya dafe kai yana kallon yadda yanayin Maamu ya sauya tana neman kara rikicewa.
Tsawa ya dakawa Dr. Yana yace ta biyo shi waje. A zuciyarta tayi dan murmushi bukatarta ta
biya. Sumsum tabi bayansa suka koma can reception suka tsaya daga gefe.

Hannuwansa biyu ya hada a gabanta yana roko "don Allah likita ki tsaya a iya duba jikinta ki
dena tado mana zantukan da zasu hanata warkewa da wuri. Idan da kinsan irin wahalar da
tasha za ki tausaya mata ne"

Dr. Yana ta dago kanta ta gyara fuskarta alamun ba da wasa tazo ba.
"Tunanin hakan ne yasa nake ganin ya kamata duk yadda zakuyi ku taimaketa kuyi. Bazan
boye maka ba gaskiyar magana wannan baiwar Allah da wuya ta tashi. Ka dubi yadda jikinta
gabadaya ya bushe ga cututtuka sun hadu da tsohon kashi. Idan kuka tsaya dogon tunani rai
yayi halinsa baku hadata da Awaisun nan ba ku kanku bazaku ji dadi ba"
So take ta sanar dashi tasan komai amma tana gudun yadda zai dauki abun. Tana kallo ya
zurfafa a tunani tace "ko kasan ganinsa yana daga cikin abubuwan da zasuyi saurin kwantar
mata da hankali ta sami sauki da wuri? Kuyi tunani akan shawarata. Indai yana da rai duk
yadda zakuyi ku kawo mata shi ku kawo shi ko yaya ta saka shi a ido"
Tana kaiwa nan tayi gaba. Rumana dake tsaye a bayansu dauke da kwanakan abinci ta goge
kwallarta. Ita da kannenta ne Abba ya kawo su. Ji tayi ta sake tsanar Uncle Awaisu sosai. A iya
sani da fahimtarta kawai yayi kudi ne yake wulakanta mahaifiyarsa da danginsa.

Karasowa sukayi suka gaishe da Harisu sannan suka wuce. Maamu tana nan jiya iyau sai
damuwa da ta karu. A cikin halin ciwo take sanar da Baaba Hure tana zargin akwai hannun
Gimbi a wannan halayyar ta Awaisu. Abubuwa da dama da suka wakana a Abuja ta bata labari
wanda itama Baaban ya kara tabbatar mata da zarginta na asiri ake yi masa. Hakuri ta kara
bawa maamu da alkawarin Harisu zaije da zarar Awaisu ya dawo daga Lagos din da yace ya
tafi. Da yake su kadai ne a dakin Maamu tana hawaye ta soma yiwa Baaba magana

"Baaba kada kiga ina nuna damuwa kamar babu kara. Idan kika zauna a gidan nan yanzu ko
yini daya ne zaki gane danki baya cikin hayyacinsa. Ina tsoron in mutu duk wani sauran
zumunci namu ya yanke. Abubuwan da kuka yi mana bani da bakin saka muku ko godiya. Nayi
tunanin Awaisu zai fitar dani kunya ya kyautata muku da zuciya daya. Sai gashi ni da na haife
shi ma...." kuka ne ya kwace mata sosai sai tari ya sarke ta.

Rumana tana daga waje duk ta gama jin abinda suke fada domin ta wuce sauran yan uwanta.
Dama da kuka ta karaso na maganganun babanta da Dr. Barrister. Zantukan Maamu sun kara
karya mata zuciya. Tana jin ta soma tari ta tura kofar ta shiga. Baaba ta gani rike da Maamu
jikinta babu kwari tana ta tari. Dago kan da Maamu tayi daga cinyar Baaba sai jini suka gani
yana fita ta bakinta. A razane suke duka su biyun Rumana ta soma kuka don tsoro ta kasa
komai.

Baaba Hure itama a tsoracen take tace "ki ruga ki kirawo min babanku da likita"

Ta juya a guje zata fita taji muryar Maamu tana cewa "ki fadawa Awaisu na yafe masa"

Bata jira jin karshen maganar ba ta fita. A hanya suka hadu da Harisu tana kuka ta fada masa
Maamu na aman jini. Nan suka tafi shi da Abba kiran likita.

Dr. Yana tare da wasu likitoci biyu suka taho dakin cikin sauri. Suna isowa suka sallamesu daga
dakin suka rufo kofar. Jikin kowa a sanyaye suka tsaya jiran tsammani.
*KASHE FITILA*💡32

*Batul Mamman*💖


Bayan kamanin rabin awa aka bude kofar dakin. Tura Maamu suka ga anayi akan gado tana
kwance ko kwakkwaran motsi bata yi. Kuka ne ya barke daga bakin matan da ke wurin domin
duka matan Harisu da su Aunty Suwaiba sun iso. Baaba Hure ce tayi karfin halin hanasu a
lokacin Harisu ya bi bayan likitocin. Dr. Yana tasan yana binsu shiyasa bayan sun daidaita
Maamu a I.C.U ta fito ta same shi. Yanayin barkwancin nan duka babu afuskarta sai tausayi. Ita
ta soma magana da ta karaso inda yake tsaye hankalinsa a tashe

"Mun samu jikin nata ya dan daidaita. Ta kusa samun heart attack ne dazu"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Dr yanzu menene abin yi?"

"Addu'a ita ce za'a cigaba da yi. Sannan gaskiya ku dena taruwa da yawa a dakin tana bukatar
hutu. Wannan dakin bama bukatar kowa sai mutum daya itama kuma ba ciki zata zauna ba."

Godiya yayi mata ya juya ya tafi da niyyar hada kansu su tafi gida ta kuma tsayar dashi

"Awaisun nan da take kira har a cikin wannan tsananin ciwon addua take yi masa. Don Allah a
karo na karshe kada kace na shiga abin da babu ruwana ku taimaka ku kawo shi. cuta ba
mutuwa bace amma tana jin jiki."

Jiki a sabule ya koma kofar dakin nan suka tsare shi da tambayoyi. Ya gama yi musu bayanin
me likita tace yayyen Maamu maza suka zo da matansu har da su Tikeke da Bomai kanin
baban Awaisu. Harisu yaso sakaya lalurar Maamu amma Baaba Hure tayi musu bayani
dalla-dalla.
Nan wurin ya kaure da salati sai da security yazo yace duk su koma waje. A nan ma manyan
suka hado aka yanke shawarar su wuce Fika ayi maganar a gida.

Mazansu da matansu manyan haka suka hadu a falon Harisu ana fadar abubuwan da suka

faru. Baaba tasa aka kirawo Rumana domin shaida. Ita kuwa bata boye komai ba dangane da
yadda suka tsinci kansu a gidan Awaisu. Bomai da ake ganin yafi kowa shiririta ne ya soma
magana bayan an sallami Rumana.

"Lallai biri yayi kama da mutum. Idan kun tuna zuwanmu gidan nan abubuwa marasa dadi sun
faru. Kuma daga bayanin wannan yarinya Rammana duk mai hankali yasan cewa akwai wata a
kasa"

Wanda Maamu take bi ya amshe "abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu kiyaye gaba. Dama
Maamu ga zurfin ciki tazo ta hadu da bacin rai dole ya taba zuciya. Ni dai idan da mai zuwa ya
kamataa gobe muje mu taho da Awaisu ko yana so ko baya so"

Kowa yayi na'am da wannan shawarar inda aka yanke cewa zasu tafi su uku harda Harisu da
Bomai.

Can asibitin kuwa Aunty Baraka ce ta zauna ko da zaa bukaci wani makusancin Maamu.

*****
Da yake jirgin safe Awaisu ya biyu kafin azahar ya iso gida. Yana zuwa ya tarar Gimbi bata nan
ga yara sun tafi makaranta. Rita ce ta fito da gudu tana yi masa maraba kamar zata rungume
shi. Abin ya bashi tsoro ma yayi saurin matsawa baya sai tayi murmushi ta wayance da karbar
jaka.
"Sir how was your trip?"

Fine yace kawai yayi gaba. Saurin shan gabansa tayi ta matso daf dashi tana karairaya "ga
abincin na gama hada maka"

A gajiye yake baya son yin magana shiyasa ya wuceta kawai yana mamakin wannan abu da
take yi kamar zata shige jikinsa.

Ita kuwa dariya tayi tana tunanin lokacin da nasu aikin zai fara aiki ta shigo gidan ayi waje da
Gimbi. Dakinta ta koma ba jimawa taji ana buga kofa da karfi. Ita da Awaisu kusan karo suka yi
suna sauri zuwa bakin kofar don jin ko lafiya.

Bashi hanya Rita tayi yana budewa suka hada ido da wata mace da jikinta duk ya motse ga
fuskarta kamar ayi amai saboda lalacewar fata. Tana tsaye tana ta susa tana bige bige a jikinta.
Maigadi yana bayanta yana son tabata ya fitar da ita amma kyankyami ya hana.

Ganin Awaisu yasa ta dan sakin rai "Awaisu fadawa wannan yaron gidan naka cewa nice Anti
Bebi"

Sake kallonta yayi cikin rashin gaskata me take fada. Wannan matar da ko almajira bata kai

matsayin a kirata dashi ba itace Anti Bebi. Yana cikin wannan tunanin yaga ta rike wuya tana ta
kakari. Da kyar ta saki wuyan tana haki

"Shegu yanzu kuma wuyana akace ku shake. Duk abinku ni Bebi nace dubu sai ceto"

Maigadi ne ya kuma yunkurin miko hannu sai suka ji horn a waje. Da sauri ya tafi ya fita duba
waye ya bar Awaisu da Anti Bebi da Rita.

Anti Bebi ta dan nutsu ta soma magana "Awaisu ta inda aka hau ta nan ake sauka. Ka fadawa
Gimbiya naji labarin komai daga wurin aljanun da tasa suke bibiyata kuma wallahi dani take
zancen domib bata ci riba ba. Yadda tasa nake dandanar balai a rayuwata itama ta shirye
gamuwa da nata. Nayi alkawarin ko zanyi yawo tsirara ne sai naga bayan Gimbiya"
Su Harisu ne suka shigo ta karamin gate din mai tafiyar kafa. Karshen maganar Anti Bebi kawai
suka ji suka kalli juna.

"Nasan bata nan shiyasa na shigo amma idan na kuma shigowa sai nayi ajalinta" yawu ta tofa a
kasa ta juya ta fita suna mata kallon mahaukaciya.

Sai a lokacin hankalin Awaisu ya kai kan bakin nasa. Da faraarsa ya taho yana musu sannu da
zuwa. Bomai ya kalli Rita da kayan jikinta

"Yanzu Awaisu meye

18 / 42