Kashe Fitila Book Complete By Batul Mamman .pdf

Author :  Batul Mamman Category :  Read Hausa Novels

Chapter   30 / 42

87K to 90K   out of 124.7K words

tana bata labarin kayan dadin da take ci wanda yayi sanadiyar
chanjin da Maamun ta gani a jikinta.

"Ta kyauta min kuwa zan aika da tukwici" inji Maamu.

Wayar Rumana ce tayi kara ta duba ta ga sunan uncle. Kasa dauka tayi wai kunyar Maamu ai
kuwa ta rinka mata dariya wadda tasa ta fita ta tafi dakin Baaba Hure. Tana sa kafa suka hada
ido dashi gabanta ya fadi yana zaune shima shigarsa kenan bayan ya kira bata dauka ba.

Kamar ta juya sai kuma ta daure ta karasa ta fara gaishe da Baaba sannan ta gaishe shi kanta
a kasa. Wani irin dadi taji da ta ganshi kunya ta hanata nunawa. Shi kuwa kallonta yake duk ta
chanja ta kara kyau. Baaba ta dan zungure shi.

"Nace ba, ai kana da daki a gidan nan ko? To ku tafi can ku gaisa sosai ba a nan ba. Kai ka
kura mata ido ita tana satar kallonka kun manta ina dakin. Ni da dakina babu mai korata"

Rumana ta tashi zata gudu Baaba tace "baki isa ba yarinya wuce ki bishi kuyi gaisuwar yaushe
gamo kada kisa ya kasa komawa bakin aikinsa" ta kare da dariya.

Awaisu kansa kunya yaji ya tashi "daga zuwa gaisheki sai ki koreni ko Baaba"

Tace "a ranka kana shi min albarka ba...a tafi dai kafin nace tazo ta min tausa"

Yasan zata aikata hakan ya fita ta koro masa Rumana wadda kunya ta hanata tashi.

"Ina jiranki a daki ki kawo min abincin yunwa nake ji please" yace ya fara tafiya.

Sai lokacin ta gane ashe girkin da sukayi nasa ne Allah Yasa tayi kokarin ganin yayi dadi. Da
can tana zuwa kai masa abinci ko damunsa da hira dakin amma yanzu kunyar zuwa ma take yi.
Dakin su Mama taje duka ta gaishesu sannan ta dauki kwandon abincin ta wuce dakinsa.

Zuciyarta na dukan uku uku ta shiga da sallama. Wata katuwar katifa ce a dakin shimfide da
bedsheet mai quilt mai kyau. Wardrobe da dressing mirror. A kasan da karfet kalar labulen dakin
sai akwatin kayansa a gefe da abin sallah. A gefen katifar yake zaune ta durkusa daga bakin
kofa ta gaishe shi.
"Yau kuma tsorona kike yi? Gashi kuma kin shigo dakin nan kenan ke da fita sai da safe"

Idanu kamar su fado tace "kayi hakuri Uncle"

Murmushi yayi "to karaso mu gaisa wasa nake yi miki"

Baki ta dan turo "ai mun gaisa tun a dakin Baaba"

"Kina son kwana tare dani a dakin nan ne?"

"A'a don Allah"

Dariya ta bashi duk ta rude. Ba mamaki yasan dole iyaye zasu yi mata nasiha akan meye aure
shiyasa take tsoronsa. Ai kuwa bazai bari hakan yayi tasiri a ranta ba. Burinsa yanzu ta koyi
sonsa kafin komai.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta karasa inda yake. Hannun damansa ya mika mata ta
saka nata ciki sukayi musabiha sai dai bai barta ta tafi ba ya janyota ta zauna a kusa dashi.

A hankali ya soma magana "rannan naga text ance anyi missing dina amma nazo naga ba haka
ba. Maybe daya yarinyar ce ta turo ba naki bane don ke baki taba min text ba"

Da sauri ta dago ta kalle shi zuciyarta har tana bugawa da karfi "dayar kuma Uncle?" Ta fada a
raunane

Farinciki da mamaki ne suka dirar masa. Lallai Rumana ta fara sonsa ko da bata sani ba
sannan gashi har da alamun kishi yana gani. Hakan ya kara masa karfin gwiwar ya cigaba da
nuna mata soyayya saboda baya son ta tare komai yazo mata wani iri saboda rashin sakewa
dashi.
"Eh ke naga kamar baki damu dani ba"

Da shagwaba tace "nice na turo fa"

"Are you sure? Me kika rubuta a naki?"

Yadda ta haddace text dinnan ko cikin bacci ta tashi bazai mata wuya ba ta karanta masa yana
bin bakinta da kallo.

"To kinyi missing dina? " ya tambayeta idanunsa a kanta.

Kasa daga kai tayi sai kai da ta gyada a hankali.

"I miss you too Umm Ruman. Amma yanzu fara bani abinci"

Tana zubawa ta fada masa yau ita tayi girkin yace to bari yaci ya bata maki.

Cokalin farko da ya kai bakinsa zafin attaruhu ya kama masa harshe. Da kyar ya iya hadiyewa
saboda yadda take kallonsa tana jira yaci yace da dadi. Runtse ido yayi tuwon nan yana sauka
a cikinsa yaji ya mamaye ko'ina.

Kasa hakuri tayi tana murmushi tace "Uncle da dadi ko? Yanzu ina ta kara koyon girki a wurin
Anti"

Kallonta yayi yaga murna take tayi masa abinci yace "yayi dadi sosai yau har kyauta zanyi miki"

Murmushin da tayi na jindadi har sai da hakoranta suka bayyana. Tace "cinye na kara maka
kaga wannan malmalar karama ce"

A zuci yace tashin hankali. A daddafe ya kara loma hudu yaji bakinsa kamar ana hura wuta. Da
kyar yake iya magana saboda yaji yace mata bari ya nemi yaro cikin kannenta ya siyo masa
batir din rediyo. Dakin ta kalla babu wata rediyo a ciki. Shima ya rasa me zaice mata ne ya dan
fita don fankar kamar bata masa komai. Tashi yayi yace ta taya shi ci kafin ya dawo su cinye
tare.

Ko kofa bai rufe ba ta dauki nama ta saka a bakinta. Ihu kawai yaji tayi yayi saurin dawowa
harda rufe kofar don kada a ji daga ciki ta tara masa mutane.

Ido har ya fara ruwa ta rike baki "Uncle harshena"

Kamar yayi dariya yadda ta tashi tana dire kafafu "Me ya sami harshen?"

Hawaye yaga ya zubo sai ta bashi tausayi " ya fita daga bakina"

Rikota yayi "yana ciki ki nutsu bari na zuba miki juice"

Jug din ya dauko kafin ya zuba a cup ta kafa kai a haka amma ko kadan harshenta bai dena
radadi ba.

"Bai dena ba" tace tana wasu sababbin hawayen

"Bude bakin na gani" ya fada a hankali

Tana budewa ya soma kissing dinta sai da yaji a ransa duk nacin yajin nan dolensa ya ragu ko
bai tafi ba duka ya kyaleta.

Kokarin hada ido ya rinka yi da ita kunya tasa ta kasa daga kanta daga kirjinsa "yajin ya tafi ko

na kara miki maganin?"

Ji yayi ta sake rungume shi tana murmushi don bata san da wane idon zata kuma kallonsa ba
"Ya tafi"

"Ni nawa bai tafi ba yaya za'ayi kenan?"

Dagowa tayi kadan "in baka juice?"

"Saboda kirki yayi miki yawa? Wanda naci yama fi naki amma juice din bai korar miki ba sai ni
zaki bawa...kuma ma dai nasha ya isheni"

"Yaushe?"

Lebenta ya rinka zanawa da karamin yatsansa "wanda nasha daga nan ya isa saura ayi min
maganin yajin nan ko ki fada min me kike nufi da haka..."
yayi mata wannan alamar da hannu
"Ko kuma na fadawa Yaya Harisu irin wannan yajin da kika tura min. Zabi daya" ya mata
murmushi ita kuwa ta hadiyi yawu da kyar. Babu na zabe duk cikinsu.
*KASHE FITILA*💡43

*Batul Mamman*💖



"Ke nake jira fa" taji ya fada yana murmushi. Dubawa tayi ta ga babu zabin da yayi mata. Idan
ya fadi yajin miyar nan yau mai rabata da Anti Ummukulsum sai Allah. Maganin yaji kuwa ko da
wasa bata hango kanta tana wannan abin ba...karshen rashin kunya ma kenan! Zabi na uku
kuma da wane bakin zata fada masa ma'anar abin da tayi da hannu. Wai waye ma ya aiketa
tayi ne?

Ya kula da yadda tayi zurfi a tunani a ransa yace yau fa an hada mata da aiki. Hannunta ya riko
"Kin bani zabi?"

Rufe ido tayi bakin nan an dan turo shi tana magana cikin sauri kuma can ciki a hankali yadda
ba'a ji sosai tace "Dakayibakajiyajinyatafiba"

"Me kika ce?" Don shi ko kalma daya bai tsinta ba.

Sake maimaitawa tayi a hankalin yace bari kawai ya tashi ya fitar da food flask din da aka zuba
miyar. Tayi saurin katse shi

"Uncle cewa nayi da kayi baka ji yajin ya tafi ba?"

Ya daga mata gira daya yana son yin dariya
"Da nayi me?"

"Abin mana" ta amsa tana kara turo baki.

"Wane abu nayi da bashi da suna Umm Ruman?" Ya gane me take nufi amma yana jindadin
tsokanarta.

Kamar zata yi masa kuka tace "Uncle ka fa gane me nake nufi...ni dai don Allah ka hakura da
wannan"

Shima irin muryarta yayi "ni dai don Allah bazan hakura ba"

Wani siririn hawaye ne ya gani ya fara bin kumatunta sa hannun ya goge shi "dadina da mutum
shagwaba. To kiyi kukan idan aka tambayeki a ciki sai kice kiss mijinki ya nema kika kasa.
Kuma kinsan ana ganin idonki za'a gane kinyi kuka ayi ta tambayarki sai kin fada. Gara ma ki
tashi ki tafi babu ruwana"
Dankwalinta ta kwance ta janyo kasansa ta goge fuskarta tana murmushi "kukan wasa ne fa irin
wanda mukeyi a makaranta idan bama son bulala"

Jinjina kai yayi "gaskiya ban yarda ba wannan wayo ne. Kin gama yiwa malamai fitinar 'yan
makaranta kuma nima kiyi min"

Dariya tayi "to ba kaine ba..."

Nishadin da yake ji a lokacin ya dade rabonsa da irinsa. Komai na Rumana yana burge shi
musamman shagwabarta da kuruciya. Addua yayi a ransa Allah Ya bashi ikon kula da komai
nata yadda bazata taba kaucewa hanyar da ta sabawa shari'a ba.

"To naji kinyi min wayo amma ba hakura zanyi ba. Kawai dai kinci bashin da zaki biya nan kusa.
Saura na biyu me wannan yake nufi?" Ya sake hada yatsunsa yadda tayi.
Murmushi yaga tanayi harda dan sosa keya. Wannan dabi'ar kuwa yana kyautata zaton a
wurinsa ma ta koya domin halinsa ne.

Ita dai yau ta shiga tsaka mai wuya daga wannan sai wannan. Dabara zata yi masa kawai don
shima ya hakura
"A film din 'yan Korea ne fa na gani ko ma'anarsa ban sani ba"

Dan fiddo idanu yayi "baki san ma'anarsa ba amma kika yi min. Shikenan kila ma zagina kika
yi. Zuwa zanyi na tambayi waye yake kunna miki gashi a kaina ya kare"

Gani tayi da gaske ya tashi tsaye bata san lokacin da tace
"I love you "

Wata irin juyowa yayi a hankali yana kallonta. Ita kuwa kamar ta nutse a kasa.

A hankali yace "Me kika ce"

"Uncle I love you yake nufi ba zagi bane" idanunta kamar su yo waje don ta tsorata.

Bata san yadda kalmomi ukun nan suka tsaya masa a rai ba tamkar wanda bai taba jinsu ba.

"Naji ma'anarsu amma da gaske kina yi min son so?"

Wannan karon ita ce ta tashi tana neman hanyar guduwa bazata iya jurewa wannan kallon da
Uncle Awaisu yake mata ba.

Hannunsa ya ware "Give me a hug kafin ki fita please."

Tsayawa tayi kanta a kasa tana wasa da hannuwanta.

"Kinga komai na tambaya bakya yi ga yaji kin hadani dashi"

"To ai kunya nake ji"

"Bari nayi miki yadda kika koya min"

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadda tayi masa wancan lokacin da zai tafi. Da yake ya fita
girma da tsaho sai ya rufeta gabadaya ya mata rada mata a kunne
"Ke special SS dina ce Umm Ruman. Allah Yayi miki albarka"

Amin tace a zuciyarta. A zahiri kuwa tace "Uncle idan na fadi ma'anar SS din zaka taimakeni
don Allah"

"Toooohhh wane irin taimako kuma. Ko me kike so fada kawai zakiyi"

Kwanukan abincin ta nuna masa.
"Idan na fita dashi fada za'ayi min kila harda duka ma"

"Maganin wannan kawai ki kwana a nan shikenan"

Dariyar da taga yana yi ce tasa ta gane tsokanarta yake yi. Ta tabbatar idan Mama ta ga
wannan miyar ko bata ji a jikinta ba kunnenta zai bada labari don bayan fada idan ta kama shi
ta murde bata da hanyar tsira.

"Don Allah kace ya zama assignment irin yadda na baka"

Yayi murmushi "Ya zama Umm Ruman, me SS yake nufi?"

Sai da tayi kamar mai tunani kada yace tayi saurin canka sannan tace "Son So"

Ya girgiza kai "sai hakuri ni Sabuwar Sarauniya nake nufi. Jeki kawai idan kinga zaayi miki
fadan ki gudu nan" kan katifar ya koma ya dan kashigida. Hankalin Rumana a take ya tashi.
Dama shi take tunanin zai rufa mata asiri gashi ta kula kamar bai damu ba.

Awaisu yana kallonta yana dariya.
"Jeki mana idan an gama ki dawo ina son magana dake"

Mamaki take yi amma kuma tasan dama can idan sunyi laifi baya cikin wanda zaka zo wurinsu
ya hana a hukuntaka. Sai dai yayi rarrashi idan anyi hukuncin. Duk wanda ya hana a hukunta to
fa sai dai idan ya tabbatar mutum bashi da laifi. Kanta ta dan rangwada gefe muryarta tana dan
rawa "na tafi Uncle"
Yana danna waya yana dariya ciki-ciki yace "sai kin dawo SS dina"

Ta durkusa zata dauki tray din "yau tun safe kunnena na dama ke dan zafi gashi Mama ita
kunne take murdewa. Uncle kana da panadol idan ta murde zazzabi ya kamani sai ka bani"

Wannan karon da kyar ya iya danne dariyarsa "idan kinje ki bata kunnen hagun tunda shi kalau
yake maybe bazaiyi zafin da zaki yi zazzabi ba"

Anya kuwa Uncle yana ma sonta ko da ba son so ba ta fada a ranta. Har wani dadi yake ji ga
Anti Ummukulsum itama duk wasanta da yara ta iya duka.

Hadiyar yawu tayi da kyar ta tuna rankwashin da Antin ta yiwa Iman jiya saboda ta fasa mata
plate. Harda sakin ajiyar zuciya ta sake cewa "bye bye Uncle"

"See you SS" yace daga inda yake.

Tafiya ta rinka yi kamar wadda kwai ya fashe mata. Ko dai kawai tayi tuntuben karya ne
kwanukan su zube. Amma kuma masu kyau ne kila ma na baban su Iman Antin ta zuba abincin
a ciki. Tana wannan tunanin har Awaisu ya kusa zuwa inda take bata kula ba. Tray din ya karba
ya dawo da fuskarta daidai tata.
"Kin canka daidai Son So din Uncle Awaisu. Yanzu me kike so ayi da miyar nan kada a taba min
mata"

Murmushinta kamar gonar auduga tace "zuciyata kamar ta fito don tsoro daurewa kawai nayi"

Hancinta ya ja "matsoraciya...jeki ki samo leda sai a juye miyar a ciki. Idan zan fita zan yar don
bana fatan kowa yaci kada a kare a gadon asibiti"

"Yau ma tsautsayi ne amma next time me dadi zanyi"

"Ni kam tsoron girkinki ya shigeni Son So"

Dariya ya bata yadda yayi da fuska. Fita tayi ta tafi kitchen ta sami bakar leda har uku ta diba
zata fita Mama ta shigo duba nama da take tafasawa.

"Ina zaki da ledoji haka kike sauri"

Da sauri tace "Uncle ne yace na kai masa"

Sanin halinta na rikicewa idan bata da gaskiya yasa Mama tunanin akwai abin da tayi.

"Zo nan Rumana" ta dan kaurara murya

Haba tuni ta karasa rikicewa "Mama don Allah kiyi hakuri tsautsayi ne."

"Me kika yi?"

Har ta soma kwalla ta fadawa Mama yajin miyar. Jira take taji ta kama mata kunne sai ji tayi
Maman ta sassauta murya alamar tausayawa.

"Jeki ki dauko min miyar"

Awaisu na jiranta yaga ta shigo a firgice. Flask din miyar ta dauka zata fita yace ina zata kai ta
fada masa zata kaiwa Mama ne. Tasowa yayi don yasan halin Mamanta
"Muje na bata hakuri don Allah kada ta taba min mata"

"A'a Uncle idan dare yayi ma sai tayi fadan gara ma ayi yanzu kawai"

Tausayi ta bashi sosai amma kuma duk da yana aurenta yana ganin bai dace ya shiga komai
tsakaninta da iyayenta ba kafin ta tare. Hannunta ya riko ya dan matsa "bana son kuka idan
anyi miki fada gyara ne kinji ko"

"Uhumm" ta iya cewa jiki ba kwari ta fita.

Tana kaiwa Mama ta bude ta dandana da cokali "wai Rumana kamar wadda aka aika kama
maye"

Har ta soma dariya ta gimtse ganin kallon da Mama tayi mata. Kabewa ta ga Mama ta dauko a
store dama raba musu akayi har su Anti Ummukulsum din. Ta bawa Rumana ta fere ita kuma ta
fita ta nemi yaro ya siyo mata alayyahu. Ga yamma bai samo da wuri ba.

Rumana tana kallo Mama ta hada markade na tumatir zalla da albasa nan da nan ta hada
ruwan miya bayan ta dafa kabewar. Basu fita ba sai da ta gama nunawa Rumana yadda zata
hada miyar taushen wadda ta kusa gama dahuwa da mai yajin sai ga dandanon yayi daidai
saboda tasu ta gidan yawa ce kuma bata saka attaruhu ba ko kadan.
Rumana ta kalla Mama taji ta kara sonta.

"Idan girki ya baci dabara akeyi a gyara ba zubarwa ba. Maza basa son almubazzaranci duk da
basu da dabarar kitchen irin tamu. Idan kinyi magriba ki zuba masa wannan miyar ki kai. In
koma bazai ci tuwon ba sai kizo a dafa masa wani abincin"

"Mama bazaki fadawa Anti ba ko?"

Murmushi tayi mata "babu mai ji in sha Allah. Amma idan kika kara nida ke ne. Ki kiyaye cin
abubuwa musamman tsami lokacin girki. Idan baki kware ba kina bukatar dandanawa. Kuma
dole harshenki zai iya jin dandanon da ya bambanta da na ainihin abinci saboda tsami ko zaki"
*****

Sallah taje tayi Mama tasa ta

30 / 42