Author : Batul Mamman Category : Read Hausa Novels
ka zata gaske ne naji zafi...to wasa nake yi kawai."
Dariya yayi wai kamar shi zata yiwa wayo. Tsoron da ya gani tattare da ita yasa ya kyaleta. So
yake ta soshi ba taji tsoransa ba. Motar ya tayar suka kama hanyar gida yana satar kallonta
tana sosa wurin. Da ta ga ya juyo sai ta dauke hannunta da sauri. Wani chemist ya tsaya ya
sayi magani suka wuce.
Cikin kannenta ya kira wani mai suna Jamal ya bashi ledoji biyar manya cike da naman kajin
nan yace ya kai ciki a raba musu. Shi kuma ya dauko leda uku a hannu ya zagayo bangarenta
ya dauki nata.
"Muje na kaiwa su Maamu nasu sai na shafa miki magani"
"A ina? Wanne?? Maganin meye???"
"Bana son musu ki wuce muje kawai" ya fada tare da yin gaba.
Jikinta a sanyaye tabi bayansa. Ta yaya zai shafa mata magani a cinya. Shi ko kunyarta ma
baya ji. Ita ce fa Rumana!
Dakin Maamu suka fara zuwa har tayi bacci. Ya bude fridge zai saka Rumana ta karbi ledar tace
bari ta cire albasa da kabejin da yake ciki kada ya bata naman idan ya kwana.
Kamar yadda Hajiya Umma yayar Mama ta fada mata komai tayiwa mahaifiyarsa zai kara mata
kima a idonsa haka ta kula da yadda yaji dadi sosai. Jiranta yayi ta cire sannan ta saka a fridge
din suka tafi wurin Baaba.
Ga dukkan alamu itama baccin take shirin yi. Fuskarta a sake da ta gansu dadi ya mamaye
mata zuciya.
"Awaisu kai da kake da tafiya a gabanka gobe shine baka yi shirin kwanciya ba?"
Leda daya ya ajiye mata yana murmushi "nama na tafi nema miki Baaba"
"A'a wannan kurar dai ta kusa da kai ka sayawa na sani." Ta bude ta dauki daya tana dariya
saboda Rumana tace ita ba kura bace.
"Yaya ya shigo ne?"
"Bai dade da tashi ba. Dama maganar tarewar Rumana ne. Kana ganin nan da sati hudu masu
zuwa yayi maka? kada ta rasa da yawa a karatunta. 'Yan uwanka suna son su kammala shirye
shirye don ko tsinke ba'a fara tanadar mata ba"
Zama yayi sosai Rumana zata fita yace ta zauna itama. Baaba Hure ya kalla sai kuma ya dukar
da kansa.
"Yanzu Baaba ni Yaya Harisu zai yiwa haka? Ko ban auri Rumana ba waye zaiyi mata kayan
daki idan ta tashi aure?"
Baaba ta dan murmusa "kai ne."
"To wallahi bana bukatar komai daga wurinsa. Ban isa na rama muku komai da kuka min ba
Baaba. Bani da wannan niyar ma. Amma burina bai wuce na ga na kyautata muku iya yadda
Allah Ya bani iko. Banda al'amura sun zo mana a haka Rumana a gida ya kamata ta zauna har
aurenta. To kuma yadda nasan da hakan ta faru bazanso kowa yace zai shigar min kan
maganar kayan daki da abubuwan da amarya take bukata ba yanzu ma bana so. Kawai ku
saka mana albarka shikenan"
Baaba ta share kwalla "Awaisu meye baka yi mana ba? Yayanka da mazan yan uwanka mata
babu wanda baka karawa jari ba. Yaransu duka babu wanda baici moriyar samunka ba. Duk
wata aike baya yankewa tsakaninmu da kai ko da baka zo garin nan ba. Me zamu ce maka mu
kuwa. Allah Ya kara yi muku albarka Ya rabaku da dukkan sharri"
Suka amsa da amin. Satar kallonsa Rumana tayi tana murmushi hannunta na daidai wurin
kunar ta ma manta ta dan sosa wurin.
""Ya soma kaikayi ne?"
Baaba tace meye yake kaikayi kuma. Cinyar Rumana ya nuna mata tare da bayanin me ya
sameta. Saman wardrobe dinta ta nuna masa.
"Ga zuma can dauko ka shafa mata kada ya tashi. Kasan ba'a raina kuna."
Rumana ta tashi har tana tuntube da kafar Awaisu.
"Bari na dauko naje daki na shafa"
Baaba ta wurga mata wata uwar harara "kin sami wuri kin zauna ko kuwa. Dauko kaji dan
albarka" ta yiwa Awaisu murmushi.
Dariya yayi yadda Rumana tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Shima kuma da ya
dauko sai ya kalli Baaba a dan kunyace ya mikawa Rumana kwalbar zumar. Duk abinsa da
kunya ya kwaye mata cinya a gaban kakarta.
Baaba ta kada kai "Ahaf, abin da yanzu aka fara auren. Meye a shafa zuma mu da za'a kawo
mana 'yan dugwi-dugwi mu goya. Indai don nice ku kara gaba don ba fita zanyi na bar muku
dakin ba."
Kafin ma ta kai karshen maganar Rumana ta fice da sauri Awaisu ya bi bayanta yana dariya. Ita
kuwa Baaba suna fita addua take Allah Ya kara hada kansu.
Da kyar ya kamota zata yi hanyar dakin mamanta.
"Wannan sauri kamar zaki tashi...ga wannan maganin shima na shafawa ne. Ki bara shafa
zumar yau gobe sai kiyi amfani dashi. Ga naki naman kici kafin ki kwanta. Lastly kuma kada ki
kashe wayarki zan kira"
Juyawa yayi ya tafi ya shige dakin Mama. Bata yi mamakin ganinta ba don taji sanda Baaba
Hurw ke fadawa Maamu wai yaran yanzu basa lissafi. Ji dai Awaisu da Ummukulsum wai sun
kai Rumana can gidan bayan a nan zaifi ganinta son ransa. Ko da suka fara zancen Mama fita
tayi don kunya suka sa taji. Nata naman ne a gabanta tana ci tace yanzu aka raba aka kawo
mata. Rumana duk kunya ta isheta ta shige uwar dakin ta dauko charger ta tafi nasu dakin
bayan tayi mata sai da safe.
Wayar kusan awa daya sukayi kafin sukwanta duk da shine yake kaso casa'in na maganar.
Tun da tayi asuba bata koma bacci ba ta zauna gari ya danyi haske tayi wanka ta shirya.
Takwas da mintuna kadan ya kirata yace ya shirya ta fito ya kaita gidan Anti Ummukulsum ya
wuce. Sai a lokacin yake danasanin kin tahowa da drebansa.
Harisu ya fito sunyi sallama yaje wurin Maamu suka taba hira tace yaushe zai dawo yace
Juma'a. Ai kuwa ta rinka dariya tana cewa ya hakura sai nan da wata biyu ita ta warke. Yadda
yayi mata da fuska ya kara bata dariya.
"Wasa nake maka angon Rumana"
Ya dan sosa keya "Maamu harda ke a tsokanar"
"Nice ma kan gaba." Ta gyara zama "Ka kula da amanar Rumana kaji ko. Kada naji ko na gani.
Idan wancan karon tsautsayi ya ritsa damu sake faruwarsa sunansa sakaci daga gareka. A
wannan lokacin kuma zan nuna maka fushina"
"In sha Allah bazan taba ganin fushin nan ba kuwa Maamu. Zan rike miki ita tsakani da Allah"
"Haka nake son ji. Allah Yayi albarka Ya tsare hanya Ya kaika lafiya. A kiyaye haram komai
kyau da dadinta halaka ce"
Yaji dadin adduar sosai yayi sallama da kowa ya fita sannan Rumana ta fito don kunyar biyo
bayansa take ji gaban mutane. Gaishe shi tayi sanna ta shiga ta zauna. Kallonta ya rinka yi tayi
kyau duk da hijab ne ma a jikinta.
Sun fara tafiya taji hannunsa akan cinyarta.
"Kin hanani jinya bayan ni na jawo ciwon. How do you feel yau?"
Kunyarsa ta yau har tafi jiya saboda hasken gari yana ganinta sosai. Da kyar ta amsa masa.
Bakin ATM machine ya tsaya ya ciro kudi suka tafi gidan Anti Ummukulsum.
Da sauri sauri suka gaisa don yace baya son tafiyar dare. Dubu dari ya bata yace tayi masa
magana idan bai isa ba. Rumana ya nema har ta tafi wurin Iman aka kira masa ita.
Su biyu ne a falon da suka zauna jiya. Idonsa a kanta yace "kin tuna me ya faru a falon nan
jiya?"
Wayyo tace a fili tana rufe ido. Haka zata zauna dashi yana sata jin kunya haka. Yaushe zata
manta ita kuwa.
Tashi yayi tsaye "ban manta assignment din da kika bani ba. Ki shirya ina dawowa zaki cika
alkawarinki kema"
"Bafa alkawari nayi ba Uncle"
"Har kin karaya kenan. To ki kwana da saninki ina dawowa zaki biya da abin da na fada miki
jiya" ya dan daga kai ita kuwa sai ta juya gefe.
"Zan tafi Umm Ruman babu ko sallamar miji da zan samu? "
"Uncle Allah Ya kiyaye hanya Ya kaika lafiya"
"Amin amma sauran wannan"
Hannuwansa taga ya ware alamun tazo ya rungumeta. Sakin baki tayi tana mamaki. Ko da
wasa bazata iya ba.
Hannunsa ya kuma nuna mata da kansa yana jiranta.
"Zaki sa nayi dare fa. Ni fa babu inda zani sai kinyi min irin sallamar da nake so"
Tsaye take tana ta shawarar me zatayi. Uncle Awaisu ya sakata a tsaka babu mafita. Tana dago
kanta suka sake hada ido ya kyabe mata fuska shi ya gaji. A hankali ta rinka takowa gabansa.
Har ta kusa karasawa cikin hannuwansa yana murmushi sai kawai yaga ta zagaye ta bayansa
ta rungume shi a hakan ta hanyar zuro hannuwanta ta karkashin nasa ta kwantar da kanta a
bayansa. Motsin kirki Awaisu ya kasa saboda yadda yaji. Yatsunsa ya zura cikin nata masu
dauke da jan lalle mai kyau yana ta murmushi ya kasa ce mata komai. Rumana ta gama masa
komai ta shige ko'ina a cikin zuciyarsa. Tsoron abinda zai iya biyo idan ya kalleta yasa bai juyo
ba sai hannunta da ya dan matse sannan yace
"Kamar kullum ki kular min da kanki. Ina yi miki son so Umm Ruman. Wannan new way of
saying I love you ne"
Daga bayan nasa tayi wani kyakkyawan murmushi cike da kunya ta sake shi. Wai Uncle Awaisu
yana sonta. Shima bai juya ba ya yi gaba yana kara jin sonta ya wuce.
******
Bayan tafiyarsa Anti Ummukulsum ta kirata daki. Plate ta miko mata ta kalli abin ciki ta kasa
tantance ko menene.
"Daga yau kada na sake ganin kina cin komai sai abin da na baki kina jina. Wannan kasusuwan
nake son rufewa kafin ki tare. Kuma kina bukatar kayan gina jiki don haka kada na kuskura
wallahi na kamaki da kayan kwalamar da kuke ci da Iman."
Rumana tayi murmushi "To Aunty meye wannan din?"
"Zogale ne na dafa na soya soya da albasa mai yawa da tumatir da kwai. Kici kisha wancan
youghurt din" ta amsa mata.
Rumana ta ja plate tana kwasar dadi. Daga ranar Anti Ummukulsum ta dauki damarar gyaran
'yarta. Kullum sai tayi mata farfesun kaji, kifi, kayan ciki ko nama. Ganye kuwa wasu ko sunansu
bata sani ba haka take yi mata miyar tuwo ko farar shinkafa. Ga maltina sai tasha gwangwani
hudu a rana. cikin dan kankanin lokaci ta soma canjawa ita kanta tana ji a jikinta. ******
Washegarin komawar Awaisu yaje gidansu Gimbi ya sanar da iyayenta zai kawo su Daula na
dan lokaci. Mama tace dama taso tayi masa magana tun ranar da yazo ma. Sun sanar dashi
lokacin da ya tashi komawa Fika ya fada musu tare zasu je. Gidan nasa kuma a lokacin suka bi
bayansa zasu taho da yaran su ga Gimbi.
Suna ta sallama ba'a amsa ba yana daga bayan Alh Mudi yace su shiga kawai yaran suna
islamiyya ne. Mama kai tsaye dakin Gimbi ta wuce. Waya take yi ma bata ji shigowarta ba tana
ta fada sai sakin kudi take yiwa su Ovi a kaiwa boka amma babu wani chanji. Ganin Mama yasa
ta tashi da sauri ta katse wayar.
"Mama yaushe kika shigo?"
"Fito falo babanki yana jira"
Gabanta ne ya fadi. Rabonta da shi tun lokacin da Awaisu ya saketa taje gida. Dankwalinta ta
janyo ta daura ta fito. Ganin Awaisu a wurin yasa tayi wani dan murmushi, wato ta nan ya bullo
kuma.
"Alhaji sannu da zuwa, Abban Haris yaushe ka shigo?" Ta fada fuska a sake.
Alh Mudi ne ya soma magana "kinga bana son gulma ki zauna kawai muyi abin da ya kawo mu.
Duk abubuwan da kikayi Gimbiya mun sami labari. Wallahi kin bamu kunya amma ki sani ba
kowa kika cuta ba sai kanki."
Kuka ta soma yi "Alhaji sharri yan uwansa suka kulla min don kawai basa sona. Zancen da
nake muku fa 'yar yarinyar nan da na rike suka aura masa"
Mama tace "Allah Yayi musu albarka da wannan hadin. Gimbi kada ki manta Bebi kanwata ce
saboda haka idan ma kina shirin wani rainin hankalin ne ki nemi wanda zakiyiwa ba mu ba.
Awaisu da danginsa bazasu miki sharri ba domin idanuna sun gani tun kafin ma Maamu ta dade
a gidan nan kika ce min ba haka ba."
Alh Mudi ya karba "Jiya muka dawo daga wurin Inna (babarsu Mama da Anti Bebi). Rokon su
Amina gafara take akan yadda ta juya musu baya komai sai Bebi. Tayi rantsuwa bata san
lokacin da take wasu abubuwan ba musamman danne musu hakki da Baba ya rasu da ta hada
kadarorinsa da dama ta bawa Bebi a boye. Abin da ya rage aka raba daidai kuma da ita. Ke
bari na takaice miki a yanzu Bebi da mahaukaciya fa bambancinsu bashi da yawa. Idan bazaki
tub.... "
Murmushi yaga Gimbi tana yi wanda ya bayyana tsantsar farincikinta jin ance Anti Bebi ta zama
kamar mahaukaciya. Abin ya konawa Mama rai ta kai mata duka. Haka suka zauna suna ta
nasiha da fada yana bi ta bayan kunne. Da suka tafi ta tashi harda kade riga tabi bayan Awaisu.
"To me zuciyar yara a karo na karshe ina fada maka ka barni na fita daga gidannan kafin ka ga
ba daidai ba"
Yana zare necktie dinsa yace "na nawa kuma. Kada ki damu kwana nawa ne zaki kara gaba"
Tsoro ne ya kamata don har mamaki takeyi wani azababben so da take masa yanzu. Duk
wannan ruguntsimin da suke fama dashi son Awaisu karuwa yake a ranta kamar ana hura wuta
'yan kwanakin nan. Da farko neman mafita take ko dai zamansu ya gyaru ko kuma ya saketa.
Yanzu kuwa ido rufe gyaran take nema. Haka ta fita ba don taso ba. Har juma'a ta zagayo suna
faman rigima tana son fita ga yaranta an kwashe sun koma gidan iyayenta. Wannan abu ma
yayi mata ciwo. A cikin kwanakin bashi da nutsuwa sai idan yana waya da mutanen Fika
musamman amarya Rumana. Daga banki sai gida yake zuwa. Bincike yake yi akan wadanda
Gimbi ke muamalar zuwa wurin yan tsibbu tare dasu.
Abin da Gimbi bata sani ba shine kwanaki uku da suka wuce Anti Bebi da kyar da sidin goshi
Wangesi ya yarda ya ganta. A nan ne take fada masa cewa tana zargin Gimbi domin aljanu har
magana suke mata a kunne suce Gimbi tafi karfinta gashi sun jawo ana ganin kamar bata da
hankali. Bayan dogon bincikensa na tsafi ya gano gaskiya ta fada. Fushi yayi mai tsanani har
yaushe Gimbi ta isa tayi masa wasa da hankali. A dalilin haka yayi alkawarin ko me Anti Bebi
take so ayi mata zaiyi. Shine ta rokeshi ya cusawa Gimbiya soyayya da kishin Awaisu na fitar
hankali. Irin son da ko macen kuda bataso ta rabe shi. Ita kuma zata je ta tona mata asiri ya
saketa. Tasan wannan son shine zai zamewa Gimbi masifa a duniya. Ko babu asiri mahaukacin
son da take masa ne yasa bata son kowa ya rabesu musamman uwarmiji kada asa shi ya
saketa.
*****
Dan sakin fuska yau ta shiga dakinsa tana tsaye daga gefen mudubi shi kuma yana ta aiki
"kasan dai ina da hakki a kanka ko Abban Haris. Yaushe rabonka da zuwa inda nake?"
Tafi ya rinka yi har ya isa gabanta "amma dai baki da kunya Gimbi. Wai hakkinki. To na karfine
sai ki kwata ko kisa bokanki ya baki tunda dashi kika dogara."
Ranta a dagule ta soma fada "nifa bazaka dokeni ka hanani kuka ba. Ka rufe ni a gida babu fita
sannan ka tauye min hakki. Ga waccan shshh....."
Babu yadda za'ayi ta karasa zagin don wani mugun kallo yake watsa mata.
"Kina iya fita gobe duk inda zaki kada ki wuce karfe hudu ki dawo gida." Taji yace
Anya kunnenta ya jiye mata daidai kuwa? Bata son jan zancen kada yace ya fasa tace to kawai
ta fita. A baya ya bita yana jikin kofa yaji tana waya tana cewa zata zo gobe. Dariya yayi ya
koma daki. Ya rasa yadda zaiyi ya dauki wayarta saboda balain yadda take kaffa kaffa da ita ko
bandaki ta shiga idan ya duba dakin baya gani.
Ba dai haka yaso ba amma dole ya kira Rumana ya bata hakuri na rashin zuwansa a satin.
Dama ita da take jin kunyarsa sai ta nuna bata damu ba har yana ta mita wai taki fara yi masa
son so har yanzu yana so ta fara shiri tarbarsa sati mai zuwa.
Washegari kafin tara na safe Gimbi ta fita don ko ganinta baiyi ba. Yana fitowa daga daki da
yaga bata nan ya koma yayi alwala tare da nafila raka'a biyu don neman kariya. Dakin Gimbi ya
fara shiga ya fiddo kayanta daga wardrobe ya bincikesu. A ciki ya tsinci layu da guraye sunfi
goma. Karkashin gado, kasan kafet har su toilet babu inda bai duba ba. Abubuwa ya rinka gani
harda wasu irin ruwa masu kala a robobi. Jikinsa sosai yayi sanyi karshenta babu wanda baa
zuba masa ba.
Yana gamawa da dakinta nasa ya koma shi kam har cikin pillow da kasan katifa akwai ajiyar
layu. Haka ya wuni yana wannan aikin harda su kitchen, dakin Maamu da duka dakunan baki
da na yaransa. Bayan ya gama hadasu ya fita duk inda babu interlock a gidan yace maigadi ya
tayashi tonawa. Yawanci duk wuraren shuka ne amma sunyi sa'a babu komai a wurin.
Ciki ya koma duk yayi gumi ya watsa ruwa ya gyara dakinsa