Bakan Gizo Compelet Book

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 44

24K to 27K   out of 129.9K words

gidansu Amrah wurin Zuwaira.

Yanayin da Zuwaira taga Aunty ta shigo ne yasa ta adana makaman rashin mutuncinta, saboda
hankalinta ya tashi sosai taji tsoron ace mata Amrah ce ta mutu, don tun lokacin da aka ce
mata Amrah tazo bata nan, k'annen Amrah'r suke fad'a mata yanda ta rame ta lalace taji jikinta
yayi sanyi, kullum tana son tasa 'yarta a ido amman tuno yanda aka nuna mata fin k'arfi akanta
aka nuna mata bata isa da ita ba, shiyasa ta k'i zuwa kuma tak'i barin k'annenta su tafi.

Aunty hankali a tashe take sanar da Zuwaira Amrah tana asibiti jini ya tsinke mata ana neman
jinin da za'a saka mata da gaggawa, Zuwaira ta aza hannu aka tace

"Wayyo ALLAH Nazir ga ranarka tazo gashi kuma kayi muna nisa."

Aunty ta k'urawa Zuwaira ido saboda duk da tashin hankalin da take ciki, sunan Nazir da,
zuwaira ta fad'a yasa ta tuno da abunda yake faruwa da Amrah sannan tareda mafalikin da tayi
tana ta kiran sunan Nazir, a cikin rawar baki Auntyn tace "Wanene Nazir?" Zuwaira ta
fashe da wani irin kuka ta jawo hijabi cikin rud'u har ta kai bakin k'ofar fita Aunty cike da mamaki
tace da ita , "Ina zaki je kuma?" Hawaye suna zuba akan fuskar Zuwaira tace, "Zanje in
taho da Nazir don shine kad'ai wanda zai iya bata jini wanda zai yi daidai da nata, don in za'a

tara mutane ashirin dak'yar za'a sami mai daidai da jininta."

Aunty jikinta yana rawa tace, "Muje to ai daga cen sai mu wuce." suka fita hankali tashe
suka tari Napep kai tsaye tsohuwar unguwar da su Zuwaira suka taso suka nufa, basu zame
ko'ina ba sai k'ofar wani gida wanda tun kafin su k'arasa suka hango k'aton kwadon dake sagale
a kofar gidan, Zuwaira ta d'ora hannu aka tareda fashewa da wani sabon kuka tace
"Na shiga Uku ni Zuwaira ina suka shiga?"

Suna nan tsaye suna nazarin mafita Aunty tace, " Ko mu shiga wannan gidan muji inda suka
tafi" Zuwaira ta kalli gidan tayi mere tareda yamutsa fuska tace, "Munafukai ne a gidan
bana shiga kizo dai mu tafi muga yanda za'ayi asami jinin tunda basa nan."

Aunty ta kalleta ta kalli gidan zuciyarta ta bata ta shiga kawai akwai wani abu ak'asa, kai tsaye
ta tunkari gidan da zuciya d'aya don bata yarda da maganar Zuwaira ba, aiko da sallamarta ta
shiga gidan wata 'yar dattijuwa zaune akan kujera 'yar tsugunno gindin murhu tana suyar kosai,
sai da ta gyara itacen da suke ta hayaki sannan ta d'ago kanta ta kalli Aunty tareda amsa mata
sallamarta, Aunty ta k'araso tace

"Sannu Inna" dattijuwar tace "Yawwa 'yarnan k'osan kika zo siya na nawa za'a baki?"
Aunty tayi D'an murmushi sannan tace, "A'a inna tambaya nike yi gidansu Nazir nazo naga
kuma gidan dantse da kwad'o, shine nace b'ari na shigo nan na tambaya ko kinsan inda suka
je, saboda Nazir d'in nike nema afujajan don ALLAH kinsan inda zanje in same shi?"
'yar tsohuwa tayi sagale tana kallon Auntyn baki a sake tace, "Cabd'i jam ai tsawon shekara
d'aya gidan ba kowa a ciki, Nazir kam tun ranar da yazo da dillalai aka siye gidan ko labarinshi
bamu sake ji ba."

Aunty tayi shiru na minti biyu sannan tace

"To yayi Inna nagode" har ta juya zata fara tafiya ne innar tace,

"Tsaya 'yarnan ga k'osan kisa man albarka"

Aunty ta juyo tace

"A'a nagode Inna ALLAH ya bada lada ya k'ara bud'a kasuwa"

Cikin jin dad'i inna tace "Ameen Amee 'yarnan ki sauka lafiya"

Aunty ta fito zuciyarta sai maida zancen 'yar tsohuwar take aranta, koda tazo Zuwaira ta fara
masifa akan taje tayi zamanta, Aunty cikin sanyin jiki tace

"Shekara d'aya gidansu Nazir a rufe ba kowa asali ma yanzu ba gidansu bane sun sayar da
shi."

Zuwaira ta zaro ido tareda yin fifita da hijabinta sannan ta fara rafka salati tana nanatawa, Aunty
tace "Yanzu miye mafita? saboda WALLAHI buk'ace ake da asaka mata jinin."

Zuwaira ta k'ara rud'ewa tace, "Eh muje asibitin ai baza'a rasa na siyarwa ba sai mu saya."

Aunty tayi shiru bata ce komi ba har suka je asibitin, koda suka je har Malam ya rigasu isa
tareda manyan dalibanshi su biyar da yazo da su da nufin agwada aga in jininsi zai yi,suna nan
tsaye cirko cirko sai ga likitan ya fito ya kalli su Malam yace, "Alhmdllh jinin Mijinta yayi
daidai an diba har an mak'ala mata."
A cikin rashin fahimtar zancenshi Aunty tace,

"An sami jinin kenan?"

Likitan yace "Eh an samu ku kwantar da hankalinku, saboda yana zuwa aka d'auki jinin ba
b'ata lokaci muka saka mata."

Malam cikin tantama yace, "Wanene ya bada jinin"

Likitan cikin kaguwa da tambaye tambayensu yace

"Mijinta mana ko baka Ji nace shi ya bada jinin ba?"

Dukansu suka zaro ido, Malam bakinshi yana rawa yace, "Nine fa Mijinta likita kuma ai ka
gwada nawa jinin kace ba zai ba." Likitan ya maka masa harara yace.

"To bayan tafiyarku kai da wannan matar da kuka kawota tare, sai ga wani yazo yace muna
shine mijinta a gwada jininshi aga in zaiyi, aka yi sa'a ana gwadawa yayi muka dibi gora d'aya a
jikinshi aka saka mata"

Malam cikin rud'ewa ya cakumo wuyan likitan yace, "Sai ka gaya man Jinin wa ka d'iba ka
sakawa matata?"


Tofa



Akafta�

D/Auta ce

*BAKAN GIZO*


*NA HADIZA D/AUTA*


https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*⭐⭐⭐TAURARI WRITERS ASSOCIATION⭐⭐⭐*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)

*ASHE ZUMA KAMA TAKE YI DA K'UDA BAKAN GIZO shine yake shanye ruwa*




*PAGE 18*

**********************

Aiko ganin hakan yasa D'aliban Malam suka yo kanshi suna bashi hak'uri tareda b'anb'are
hannunshi daga cakumar da yayiwa Likitan, a cikin fushi likitan yace

"WALLAHI da nasan abunda zakuyi man kenan da ban saka hannuna cikin lamarinku ba,
amman bakomai ko yanzu sai ku nemi wanda zai tsaya maku akan case d'inta."

Aiko da sauri ya bar wurin ranshi a b'ace Aunty tabi shi cikin tsananin rud'u tana bashi hak'uri,
tafiya yake yi amman bata daina biyar shi tana magiya da bashi hak'uri ba, har sai da ya tsaya
tareda waigowa lokaci d'aya saboda raunin da zuciyarshi tayi da magiyar da yaga Auntyn tana
yi masa, saboda maganganun da take fad'a wad'anda suka karya masa zuciya, inda take kuka
tana cewa,

"Don girman ALLAH kada ka zare hannunka akan matsalarta kayi hak'uri kayi don ALLAH
WALLAHI yarinyar tana cikin gararin rayuwa mai cike da tarin k'alubale wanda ita kanta da za'a
barta ta mutu d'in da tafi kowa farin ciki da hakan, amman kuma mutuwarta ba shine maslahar
kalubalen dake tattare da rayuwarta ba, kayi don ALLAH ka ceto rayuwar marainiya ALLAH zai
baka lada, saboda ko mijinta da kaga yayi ma hakan baya cikin hayyacinshi shiyasa, ka auna

akanka ace hakan ta faru dakai ka kawo matarka asibiti kaje nemo wanda zai bada jini a saka
mata koda ka dawo ace maka mijinta yazo an d'ibi nashi wani hali zaka tsintsi kanka?, saboda
haka ina nemarwa Malam yafiya a wurinka saboda ya shiga rud'u ne bada gangan yayi ba."

Jikin likitan yayi sanyi zuciyarshi ta sauko daga dokin fushin da ya hau, cikin tausayawa Patient
d'in yace, "OK badamuwa komi ya wuce yanzu mun samu an tsayar da jinin haka ma
abunda ke cikin yana lafiya, kada ku damu wannan jinin da ake saka mata kuwa ya wadatar, sai
dai zamu rubuta mata wasu magunguna da zata CI gaba da sha kafin lokacin haihuwarta,
wad'anda zasu k'ara mata jinin da zai wadaci jikinta"

Cikin jin dad'i Aunty tace, "Mun gode likita ALLAH ya biyaka da gidan Aljannah."

Cikin jin dad'in adduarta yace "Ameen"

Har ya fara tafiya Aunty tace, "Zamu iya shiga mu ganta?"

Ya juyo yace, "Zaku shiga ga amman don ALLAH kada ku dameta da hayaniya."

Aunty tace. "Mungode sosai"

Sannan ta dawo inda su Malam suke zaune suna jiran suji yanda suka yi, kowanensu ido zuru
zuru, Musamman Malam da a lokaci d'aya shima duk ya zabge saboda tashin hankali, koda
tazo tayi masu bayani d'ii suka bi bayanta zuwa d'akin da ake kwantar da masu lalurar ciki,
Zuwaira kam biye kawai take dasu zuciyarta cike da tsanar Malam,saboda kallon kaskancin da
take masa wai ace shine mijin kyakkyawar 'yarta Amrah, ji take kamar ta shak'oshi tayi ta jibga,
gefe d'aya kuma na zuciyarta tana ta sak'e sak'e akan cewar da aka YI mijinta ya bada jini,
saboda atake yanke zuciyarta ta tabbatar mata da kowaye da wannan d'anyen aikin.

Koda suka shiga sun tarar da ita kwance sambal da tsinin cikinta, sai sharar bacci take yi
sharkaf tana maida numfashi da sauri da sauri, saboda jinin da ake zuk'a mata yana bata
reaction sosai.
Zuwaira tazo gefen kanta ta shafo fuskarta hawaye suna kwaranya a idonta, saboda tsananin
tausayin 'yarta da rabon tasa ta a ido tun kafin aurenta, wanda yake cikin wata na takwas dai
dai da watannin cikinta, amman tabi duk ta rame ta fita hayyacinta kamar wadda TAYI shekara
tana jinya.
Malam kan tsaye kawai yake amman gaba d'aya zuciyarshi cike take da tunani kala kala,
musamman abu biyu photunan da yagani sannan da zancen da likita yayi a yanzu, wai mijinta
ya bada jini shin to wanene mijin bayan shi?, kodai cikin tsoffin mazanta ne da ta aura? in ko
haka ne tabbas WALLAHI bazai tab'a zura ido aci masa dunduniya ba, dole ne ta zab'a ko shi
ko kuma su don bazai tab'a zama da ita ba alhali tana kula mazan da ta aura baisani ba, yasa
aranshi da taji sauk'i za'ayi wadda za'ayi don baza'a maida shi lusari ba.

Kukan Zuwaira gaba d'aya ya karad'e d'akin har sai da wasu nurse's suka shigo suka kora
mutanen dake d'akin, sannan ta fito tana ta sharb'ar kuka Aunty tana lalashinta.

Kwanan Amrah uku asibitin ta d'an ji sauk'i amman kallo d'aya idan anyi mata za'a gano
tsantsar tashin hankalin da take ciki, saboda tsawon wad'annan kwanakin gaba d'aya tayi su ne
a cikin kuka da tunani, wanda har aka k'ara auna jininta aka ga ya hau sosai, duk da fad'an da
aka yi mata da jan kunne amman hakan bai hanata sake dilmiya a tunanin ba, don ita lafiya da
rayuwar gaba d'aya sun fita kanta, Zuwaira ce ke kwana da ita amman Aunty kullum tare dasu
take yini sai da dare maigidanta yazo ya d'auketa, dangin Babanta ma a kullum suna kan
hanyar zuwa dubata, sati d'aya da tayi asibiti aka sallameta amman da sharad'in a daina d'aga
mata hankali, saboda takatsantsan da lafiyarta da lafiyar abunda ke cikinta.

Ana sallamota kai tsaye Zuwaira ta wuce da ita gida lokacin Aunty da Malam basu riga suka
tafi asibitin ba, saboda da safe ne aka yi sallamar amman abun mamaki koda taje tambayar bill
d'insu aka ce da Zuwaira Mijinta ya biya kud'in, ba tareda dogon bincike ba suka tattaro
kayansu suka yo gida.
Ita kanta Amrah bata da wani zab'i da ya wuce zuwa gidannasu, saboda yanda zuciyarta take a
hirgitse sannan yanayin kallon da taga MALAM yana mata, zuciyarta ta tabbatar mata da cewa
zarginta ya shiga zuciyarsh ya zauna, shiyasa bata ji ko d'ar ba da tafiyarta gidansu asali ma
taimakonta aka yi, don ita gaba d'aya komai ma ya fita zuciyarta in son samu ne ta sami kad'aici
tayi jinyar zuciyarta, shigarsu gidan keda wuya sai ga Aunty ta diro da kulolin abincinta, don taje
asibitin aka ce mata an sallamosu kuma tana da tabbacin Zuwaira bazata kai Amrah gidan
Malam ba, saboda kallon tsanar da tagani da idonta Zuwaira tana yiwa Malam, Zuwaira ta
tarbeta ba yabo ba fallasa saboda fad'i tashin da Auntyn tayi dasu Asibitin yasa ta rage jin zafin
Auntyn, akan abunda ya faru baya, Aunty tace da Zuwaira, "Ashe an sallamota daga asibitin
cen na fito ai ake sanar dani anbata sallama."

Zuwaira tace "Eh yanzu muka shigo gidan muma" Aunty tayi murmushi tareda fad'ar
"Alhmdllh." sannan ta ajiye kulolin tace, "Ina Amrah'r?" Zuwaira ta nuna tsohon d'akinta tace
"tana ciki" Aunty ta nufi d'akin da sallamarta d'akin fess kamar lokacin da Amrah tana gidan,
saboda Zuwaira tana kula dashi sosai don wani zubin ma a d'akin take kwana, shiyasa d'akin
yake tsab tsab dashi ba abunda ya sauya.

Sallamar Aunty da Amrah tajiyo ne yasa tayi saurin share hawayenta, tayi k'ok'arin saita
natsuwarta saboda fad'an da Autyn ke yimata akan yawan tunanin da take yi, saboda kariyar
lafiyarta don an tabbatar masu da jininta ya hau sosai.

Aunty ta zauna idanunta akan Amrah atake ta gano kukan da tayi cikin damuwa ta kira sunanta,
Amrah ta d'ago fuskarta ta kalleta nan take wasu sababbin hawaye suka gangaro mata, Aunty
ranta ya k'ara jagulewa tayi saurin rik'o hannunta tareda share mata hawayen, a cikin wata
murya mai cike da tausayi tace, "Ki natsu ki ajiye komi ki fuskanceni muyi magana ta fahimta,
ada naso mu ajiye maganar har sai kin sauka amman ganin yanda kika d'aga hankalinki yasa

dole ne aci maganin matsalar, saboda tsoron abunda zai je ya dawo dangane da matsalolin da
suke ta kunno kai, yanzu ina son ki sanar dani wanene Nazir? Miye alak'arki dashi?sannan
wace dangantaka ce tsakaninku dashi a baya? Saboda ta wannan hanyar ce kawai zamu
kamo kan matsalar" Amrah ta share hawayenta sannan tace, "Nazir mak'ocinmu ne acen
unguwar da muka taso, akwai shak'uwa sosai tsakanina dashi, sai daga baya ne da idan yaga
ina kula samari muka yi ta samun matsaloli dashi, saboda baya son ya ga ina fira da wani ko
wani ya ganni yace yana sona idan muna tare dashi kasancewarshi abokina na kud da kud."
Aunty tayi shiru na d'an lokaci sannan tace, "Saurayinki NE kenan shima?" Amrah tayi
saurin girgiza KAI sannan tace "A'a gaskiya ba wata alak'ar soyayya da ta had'a ni dashi, sai
dai shak'uwar da kika ji na fad'a kawai itace tsakaninmu" Aunty cikin mamaki tace da ita
"kina nufin kice bai tab'a cewa yana sonki ba." ta d'aga kai tareda fad'in "Eh gaskiya sai dai
yana tsananin kishina, don yasha fad'a da samari masu zuwa fira wurina,saboda ko Salis sunyi
ta gwabzawa dashi kafin mu baro unguwar." cikin tsananin firgici Aunty tace, "Ko shakka
babu lalle nazir shine BAKAN GIZOnki wanda yake ta shanye maki ruwa ba wani aljani da yake
tare dake sai shi."

Sai ga Zuwaira ta fad'o d'akin kamar anjefota saboda daman cen kunnuwanta kaf ta baje su ne
wajen sauraren firar tasu jikinta yana rawa tace,

"Yanzu kina nufin duk wannan bala'in da muka shiga Nazir ne sanadi?."

Aunty ta girgiza kai tareda cewa, "ban fa tabbatar ba amman zuciyata shi take zargi, zargi
kuma ba gaskiya bane, abu d'aya ya dace muyi yanzu shine mu binciko duk inda Nazir d'in
yake, saboda akwai abunda muka b'oye maki bamu sanar dake ba, wanda ya zama dole sai
mun nemo Nazir koda ALLAH zai sa hakan ya zamo SILAR samun maslahar matsalolin"
Zuwaira takai zaune ba shiri tareda cewa "Meke faruwa sabo kuma bayan abunda na riga
nasani abaya?"

Amrah ta fashe da kuka Aunty ta kalleta cikin tausayi tareda sauke ajiyar zuciya tace,
"Wannan cikin dake jikin Amrah wani yayi ik'irarin cewa ba cikin Malam Nura bane nasa ne?"

A zabure Zuwairar ta Mik'e tareda dafe k'irji tace, "Kan Uba wato NI Nazir zai ciwa Amana,
waton duk gargad'iin da nayi masa akan Amrah baiji ba har saida ya k'unsa muna bak'in ciki
akan wani banzan tunaninshi na k'arya?wallahi sai yasan dani yake zance matuk'ar bai fita
sha'anin 'yata ba." A cikin Mamaki Aunty tabi Zuwaira da kallo hanci da baki, saboda kalamanta sun tabbatar mata
da lalle zarginta yazama gaskiya cewa Nazir ne BAKAN GIZOn Amrah, sannan kalaman
zuwaira sun tabbatar da cewa akwai wata ak'asa tsakaninsu da Nazir, wanda Zuwairar ce kad'ai
zata iya warware masu komi.
Shiyasa ta kalli Zuwairar tace, "Aunty ki fad'a mani gaskiyar abunda ke tsakaninku da Nazir."

Zuwaira ta zauna tareda fashewa da kuka, tana fad'in

"Nazir haka zaka yimuna? ina soyayayr da kace kana yiwa Amrah?haka ake so WALLAHI
ALLAH ya isa tsakaninmu

9 / 44