Bakan Gizo Compelet Book

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   34 / 44

99K to 102K   out of 129.9K words

ta halako a banza watak'ila ma garin zubar da cikin ki je ki mutu
ko kuma a jaza maki wata matsalar mahaifarki ta lalace ki zo ki kasa samun wata haifuwar a
gaba, da ko shikenan ta kassara rayuwarki"_

Haka tayi ta tunanin zuci har suka isa Gusau inda kai tsaye ta shiga motar Kaura-Namoda,
zuciyarta cike da fargaba da tsoro har suka isa garin.

Mai Napep yana sauketa a k'ofar gidan Kakan nata taji gabanta ya kire ya fad'i saboda tsoron
abunda zata je ta ta taras, don labarin da Mamarta ta bata na masifaffiyar Matar Kakan nata
yasa ta jin tsoron shiga gidan, don ita bata yi wayon saninta ba don ba wani zuwa Zuwaira ta ke
yi garin ba balle har su ta zo dasu su san danginta sosai ba, cikin dar dar ta kutsa kanta cikin
gidan da guntuwar sallamarta, sai gashi ta ji an amsa a cikin wani d'aki dake fuskantar Wanda
ya shigo gidan, kai tsaye ta isa k'ofar d'akin ta sake yin wata sallamar, sai gashi ko tsohon ya
sake amsawa daga cikin d'akin ya bada umurnin ta shigo.

Ta cire talkamanta ta shige ciki bakinta d'auke da wata sabuwar sallamar ta Sami gefen shi ta
zauna ta tankwashe kafafuwa ta gaidashi sannan ta sunnen Kai tana wasa da wani dan Kare da
ta d'auka, Dittijon tsohon ya kalleta da kyau duk da shekaru sun ja amman kar yake saboda dan
jikin fillani da yake dashi, ya kura mata kallo yace
"Ina Uwarki? ko ke kad'ai kika zo ne??"

Amrah tayi saurin d'ago Kai ta kalleshi cike da mamakin saurin ganota da yayi, tayi dan
Murmushi tace

"Tana gida amman ya aka yi ka ganoni?"

Tsohon yayi Yar gajeruwar dariya yace, "ai ko cikin duhu mutum yasan ta inda zai zura abinci
cikin bakinshi, don haka kamar yanda hannu yake gano Baki a cikin duhu haka Ni ma nake
gane zuri'ata duk inda na ganta a fad'in duniya"

Amrah ta yi Yar dariya tace,. "Allah ya bamu ya taku muma idan mun kai shekarunku, ina matar
gidan ne naji gidan shiru??"

Dattijon ya yi Yar dariya shima yace,. "Tana ciki yanzu ta fita d'akin bari in kirata"

Amrah gabanta ya fad'i tace,. "A'a bari in je da kaina in gayar da ita itama"

Har ta tashi yace da ita,. "Dawo ki zauna fad'a man me ya kawo ki wurina?? don nasan banza
bazata sa zomo ya je kasuwa ba, don fuskarki ta nuna damuwar da zuciyarki ta kunshe da ita"

Amrah ta dawo cikin sanyin jiki tuno abunda ya kawota yasa hawaye suka zubo mata, ta saka
hannunta ta share Sannan ta ja majina tace

"Mama ce ta ke so ta zubar man da ciki bayan ta raba Ni da Mijina da Jaririn yarona"

Dattijon nan take b'acin Rai ya bayyana akan fuskarshi yace,

"Yi man bayani dalla dallah yanda zan gane ki saki jikinki da kyau kin zo inda za'a share maki
hawayenki in dai akan matsalar Zuwaira ne"

Amrah ta gyara zamanta ta fara bashi labarin duk abunda ya faru tun daga zancen aurenta da
Salis har zuwa yanzu da Zuwaira take son zubar da cikin Nazir tana kuka ta kare sanar dashi,
tsoho tun yana gincire har ya Kai ya zaune ba shiri cikin tsananin b'acin rai ya share hawayen
tausayin Amrah da su suka cika masa idanuwa, ranshi a b'ace ya mike ya fita minti sha biyar a
tsakani sai gashi ya dawo tare da wata Mata Sannan ya zauna, itama tana kallon Amrah cike da
tausayi ta zauna ta fara lallashinta, cikin matsananciyar damuwa ya sauke ajiyar zuciya yace,

"Kiyi hak'uri Amrahtu insha ALLAHu daga yanzu wannan matsalar ta wuce Ni zan nemo Mijinki
da kaina in bashi hak'uri akan abunda aka yi masa ki koma gidan Mijinki ki zauna, ita kuma ki
barni da ita gobe tunda safe zan tafi har katsinar in nuna mata cewa ko gaba da gabanta"

Matar da ke rungume da Amrah tana share mata hawayen da take ta yi tace,. "A'a Maigida ka
rabu da Zuwaira ka dai sa a nemo maka Mijin Yarinyar ka mayar masa da Matarshi kawai"

Dattijon yayi shiru sannan yace

"Na gaji da matsalar Zuwaira Dije ya zama dole in nuna mata kuskuren da ta aikata, don rashin
Imani irin nata ace tayi yajin k'ujen raba Yarinya da Mijinta Kuma duk abun bai isa ba har sai da
ta rabata da yaronta da ta haifa ko wata biyu bai yi duniya ba?haba abun yayi yawa sannan
yanzu tace wai zata zubar da ciki sai kace wanda aka yo a titi ba cikin Sunnah ba? To WALLAHI
wannan karon sai na nunawa Zuwaira cewa ba itace ta haifi kanta ba Haifuwarta aka yi, ALLAH
ya jikanki Meramu da har bakayi tsawon ran ganin wannan rashin mutuncin na Zuwaira ba"

Matar da ya kira Dije ta mikar da Amrah da ke ta kuka suka fito d'akin zuwa cikin gidan, Kai
tsaye d'akinta ta kaita ta zaunar da ita akan gadon tace

"Zauna in kawo maki abinci kici sai kije kiyi wanka ki yi sallah"

Amrah ta kalleta har zata fita cikin shakakkiyar muryarta da tasha kuka tace

"Bari in fara yin sallahr don bana jin yunwa"

Matar ta mika mata buta cike da ruwa ta nuna mata bayi Sannan ta koma d'akin ta shinfida
mata tabarma da carpet a kai ta fito ta nufi d'akin dattijon tsohon.

Bata yi mamakin ganin halin da ta taraddashi ba domin kuwa kuka ta iske yana yi kashirbin na
tausayin jikanyarshi Amrah saboda halin da ta tsinci kanta a ciki kuma duk ta sanadiyyar bak'ar
Uwa da ALLAH ya bata.

Matar ta zauna cikin sanyin jiki tace

"Don ALLAH kayi hak'uri Malam wannan kukan ba shine mafita ba mafita kawai ka sa a nemo
Mijinta ka damka masa ita da hannunshi shikenan anyi maganin matsalar, don in kace ka biye
halin Zuwaira sai ta fama maka ciyonka ya tashi ta samu shiga Uku, don ALLAH na tuba ai ko ni
da ban haifeta ba ai nasan halinta ballantana kai da ka haifeta da cikinka"
Dattijon ya share hawayenshi yace

"Ni Dije ba komi Nike tunani ba irin halin da yarinyar nan ta shiga da kurciyarta, shin ita Zuwaira
ta manta cewa muma irin haka tayi muna lokacin aurenta? K'iri kiri ta ki Auren Sahabi ta fitittike
ta ce bata sonshi duk da yake d'anuwanta ta nuna tafi son bare a kanshi, Kuma a hakan muka
bata wanda take so d'in ba tare da da mun rabata da shi ba, aka zo ya rasu tun da kurciyarta
maimakon ta dawo gida ta nemi yafiyarmu amman bata yi ba, don tunda ta yi aure bata sake
tako ma gidannan ba sai da taji Mahaifiyarta ta kwanta ciyon ajali, sannan ta zo ta ganmu ta
koma tun daga lokacin bata dawo ba sai da sak'on mutuwar Meramu ya risketa sannan ta zo
tana yi muna kukan munafucci, don Mijinta kanshi yayi zuwa yafi uku kafin ya rasu amman ita
tunda ta zo gaisuwar Uwar bata dawo ba har sai da ta kwashe shekarru sannan ta zo kuma ta
nuna zata ci zarafinki na koreta, to tun daga lokacin Kuma yau za'ayi shekara uku rabonmu da
ita, mu bamu takurata ba amman wai ita ta saka yarta a gaba da masiba kala kala karamar
Yarinya irin wannan"

Dijen tayi ta bashi baki tana tausarshi har ta samu ya sauko Sannan ya d'auki wayarshi ya kira
Babban danshi Wanda suka fito ciki d'aya da Zuwaira yace ya zo yana nemansu duka ya tattaro
sauran Yan uwanshi.

Dije ta mike tace

"Bari in baiwa yarinyar nan Abinci in dawo"

Ta fita ta je ta Kai wa Amrah tuwon dawa da miyar danyen yaud'i taji manshanu, aiko Amrah
ganin mutuminta yasa ta washe baki ta saki jiki ta ci abunta har ta koshi sannan ta fito da
kwanon Dije tana tsarguwarta akan cewa

"Shikenan tunda kin iya cin tuwon gobe sai ki surfa muna dawar ki tuka muna tuwon"

Amrah tayi dariya tace

"Ai har da fura ma duk sai na yi maku kusha ke da Mijinki har sai kunnuwanku sunyi motsi
saboda zakin hannuna"

Suna cikin barkwancin ne suka jiyo Sallamar Yan uwan haifuwar Zuwaira maza da mata na

d'akinsu da na Dijen suna shigowa d'aya bayan d'aya.

Don wasu da yawa ma Amrah ta sansu lokacin aurenta na farko da suka zo, mazan dai ne ba
duka tasani ba sai dai kamar da suke yi da juna don kusan dukansu Kama da Baba Nuhu suke
yi shiyasa kamarsu ta zo d'aya da juna, don ko ita kanta Amrah kama da su take yi saboda
gaba d'aya kamar Zuwaira ce ta d'auke sai Karin farin da ta fita wanda sai yanzu ta gano ta
d'auko farin ne ga Baba Nuhu don har yanzu farin bafillace ne tas! Duk da tsufa ya fara dusashe
farin.

Amrah cike da jin dad'in ganin yanda suke ta faram faram da ita ne yasa ta saki jikinta da su
kamar daman cen ta saba dasu, bayan sun gaisa ne duka suka tattara zuwa d'akin Baba
Nuhun, kasancewar dare yayi yasa bai b'ata lokaci ba yace da Amrah ta fad'a masu abunda ta
sanar dashi, aiko fillah fillah tayi masu bayanin komi da ya faru har irin dawainiyar da Nazir yayi
dasu a baya, dukansu jikinsu yayi sanyi da jin labarin cikin b'acin rai Babban wansu duka ya yi
gyaran murya yace

"Baba Ni a ganina a nemo mijin yarinyar a mayar da ita gidan Mijinta, amman kafin Nan sai mun
tuntubi dangin Baban Yarinyar don muji ta bakinsu"

Gaba d'aya duka suka yi amanna da shawarar Yaya Harun babban wan nasu, sannan wani
dan matashi daga cikinsu yace, "To ita Aunty Zuwairar wani mataki zaa d'aukar mata?"

Baba Nuhu yace

"Ku barni da ita Ni zan yi maganin matsalarta don ko hakkin Yarinyar Nan kawai aka barta dashi
ya isheta darasi a rayuwa"

Haka dai kowa yayi ta tattauna abunda ya dace, har suka tsayu akan gobe mutum biyu zasu je
Katsinar a binciki abunda yake faruwa wajen dangin Babansu Amrah sannan dukansu suka yi
sallama da juna kowa ya nufi gidanshi.



Akafta





D/Auta ce✍

*BAKAN GIZO*

*NA HADIZA D/AUTA*
*Wattpad Princess Dija 246's*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*Jinjina a gareki malatyn Wattpad Ameera Madobi uom Aslam barkarki da k'ok'ari ta
wajena ALLAH ya bar zumunci*



*PAGE 54*


Tunda sassafe yayan Zuwaira wanda suke Kira da suna Yaya Harun ya iso gidan tare da wani
k'aninshi dan d'akin Inna Dije mai suna Mustapha, suka yi sallama da su Baba Nuhu dangane
da tafiyar da za su yi ya basu sak'on su je gidan Zuwaira su ce ta zo yana nemanta, Amrah
kam zuciyarta sai bugawa take yi saboda tsoron abunda zai je ya dawo, don tasan Mahaifiyarta
sarai da abunda zata iya yi mata idan har ta damk'eta matuk'ar ta gano itace ta kawo k'ararta,
sai dai Kuma Dije ta yi ta tausarta tana nuna mata ba wani laifi da tayi hakan da tayi shine dai
dai don matuk'ar ba'a yiwa abun tufkar hanci ba ba'a san iya inda abun zai tsaya ba, ta lurar da
ita ta kwantar da hankalinta ba abunda Zuwaira ta isa ta yi mata in dai tana gaban Baba Nuhu,
amman duk da hakan zuciyarta ta ki natsuwa da hakan.

****

Tun k'arfe takwas suka bar garin kasancewar daga KAURA ba wani nisan zango bane zuwa
Katsina, shiyasa koda k'arfe goma tayi masu suna cikin garin kai tsaye gidansu dangin Babansu
Amrah suka nufa, Wanda ya kasance big house na familynsu duka sai 'yan d'aid'aikun da suke
zama a wasu wuraren daban.
Anyi masu tarba mai kyau sosai cikin mutuntawa da karrama juna kamar daman cen su
'yan'uwan juna ne, bayan komi ya lafa ne suka fara aiwatar da abunda ya kawosu, inda Kai
tsaye yaya Harun ya fara tambayar ba'asin abunda ya ke faruwa,cikin natsuwa babban wan
Babansu Amrah ya fayyace masu komi da suka sani ya faru tun daga lokacin da Baban Jamilu

Abokin Nazir ya zo akan zancen aurenshi da Amrah har zuwa wannan lokacin da ake ciki da
Zuwaira ta kai kud'i aka raba auren, da matakin da suka d'auka saboda jin haushin Sakin da
Amrah ta nema a gaban kowa a kotu duk ta ji gaskiya a bakin mutane dan'uwansu Baba
Mamman, wanda a sanadiyyar jin haushin hakan ne suka ce sun zare hannunsu akan zancen
Auren Amrah da Nazir tunda har ta goyi bayan Zuwaira aka raba aurenta da shi.

Yaya Harun ya sauke ajiyar zuciya Mai k'arfi ya fara basu hak'uri akan duk b'ata masun da aka
yi, sunji dad'in halin dattakonsu Yaya Harun suka nuna ba komi komi ya wuce, cikin jin dad'i
Baba Harun yace

"Idan har ba zaku ga munyi maku shishigi ba to muna bukatar a mayar da Amrah d'akin Mijinta,
saboda har yanzu tana cikin idda tinda Koda ya saketa da cikinshi a jikinta, idan ba damuwa
muna son ku rakamu mu had'u da ku muje gidansu yaron mu basu hakuri Kuma mu rok'eshi
akan yayi hak'uri ya maida Matarshi d'akinta"
Dukansu suka yi amanna da hakan kuma suka ji dad'in wannan shawara da ya kawo masu, a
tare suka mik'e suka nufi Unguwarsu Nazir sai dai ko da suka je sun taradda gidan nashi a
dantse da kwad'o wanda alamu duk sun nuna basa garin saboda k'ura da suka hango a
harabar gidan sosai da suka leka, cike da takaicin rashin samunshi da basu yi ba Wan Baban
Amrah ya ce da su su zo su tafi gidansu Baban Jamilu wanda shine a yanzu yake kallo a
matsayin Uba suka d'unguma dukansu suka nufi gidan nashi.

Sai dai shima ko da suka je d'in sun taradda baya nan yana Kasuwa sai dai sun karb'i
numbarshi sun kirashi yace da su su jirashi gashi nan zuwa, ya bada umurni aka bud'e masu
sittroom d'inshi suka zazzauna zaman jiran zuwan nashi.

Aiko minti Sha biyar a tsakani sai gashi ya iso gidan da fara'arshi ya tarbesu duk da bai wayi su
Yaya Harun d'in ba, amman haka suka gaggaisa cikin sakin fuska da mutunta juna sannan Wan
Baban Amrah ya fara yi masa bayanin abunda ya kawosu wajenshi.

Cikin tsantsar farin ciki yace,. "Alhmdllh naji dad'in jin wannan maganar Kuma nayi farin ciki sai
dai Kuma Nazir baya garinnan yanzu haka an turashi Aiki a garin Gombe, kusan satinsu Uku
acen tare da Matarshi da Mahaifiyarshi da d'anshi yaron wajen ita Amrah'r"

Cikin jin dad'in tayashi murnar samun aikin da yayi ne suka yi ta yi masa fatan alkhairi, sannan
Baban Jamilu yace

"Amman dai duk da hakan ba wata matsala ba ce bari in kirashi yanzu in sanar dashi abunda
yake faruwa, don na tabbata idan har ya ji to ba k'aramin farin ciki zai yi ba kar ki Sha mamaki
idan aka ce gobe gobennan zaku ganshi a garinnan ya zo don ba k'aramin so yake yiwa
Yarinyar ba"
Aiko kira d'aya biyu har ta tsintse amman ba'a sameshi ba cike da takaicin rashin samunsan da

bai yi ba yace dasu,

"Kada ku damu ko bayan kun tafi ne zan yi ta gwada kirannashi insha ALLAHu zan sanar dashi
komi kuma Ina da tabbacin zai zo d'in kamar yanda na fad'a"

Wan Baban Amrah yace,. "Yawwa mun gode da k'ok'arinka idan har ya zo Amrah'r tana
Zamfara gidan Mahaifin Mamarta don wad'annan ma daga cen suke asali ma sune ma suka zo
muna zancen"

Baban Jamilu ya ce "Allah ya biyasu ya saka masu da Alkhairi kuma ya sa mu dace gaba
dayanmu Kuma ya tabbatar muna da alkhairi dukanmu"

Dukansu suka ce "Ameen" Sannan Yaya Harun ya karb'i numbar Baban Jamilu akan zai kirashi
ya ji duk abunda aka Kai karshe idan har an Sami wayar Nazir d'in, sannan shima ya karb'i
numbar Nazir suka yi sallama da juna suka fito gidan suka yi sallama da juna suka rabu cikin
mutunci da mutunta junansu.
Yaya Harun da k'anenshi Mustapha suka nufi Unguwarsu Zuwaira, sai dai gidanta na da suka
nufa suka tambayi inda ta koma aka nuna masu gidan Lantana.

Suna zuwa k'ofar gidan su ka aika wani yaro cikin gidan akan ya kira masu Zuwairar, sai gata ta
fito da jajayen idonta na kukan rashin ganin Amrah da bata yi ba tun jiya ta sha yawon nemanta
gida gida, cikin tashin hankali ta ke har lokacin shiyasa da ta ji ana nemanta ta fito da sauri, don
tsammaninta ko zancen Amrahr ne aka zo yi mata, a rude ta fito gidan tana wara idonta aiko
sai gashi ta yi Ido biyu da 'yan'uwan nata, tayi saurin dafe k'irji saboda bugawar da zuciyarta ta
yi ba shiri, bakinta Yana rawa ta k'araso wajensu fuskarta cike da kuka tace,

"Yaya Harun Mustapha kuma kunji b'atan Amrah ko?"

Ta k'are maganar cikin wani sabon kuka, dukansu suka basar da zance nata kamar ma basu ji
me ta fad'a ba saboda haushinta da suke ji, Yaya Harun ya yi mata wani kallon reni yace

"Baba ke nemanki idan kinsan zaki b'ata Muna lokaci mu yi gaba ki biyomu daga baya"
.
Cikin sabon fad'uwar gaba ta zaro Ido tace

"Lafiya???"

Harun ya shige Motarshi yace,. "Idan kin tafi zaki ji daga bakinshi zaki zo mu tafi ko mu wuce?"

Zuwaira cikin kid'imewa ta juya tace

"Bari inyi sallama

34 / 44