Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
abun yayi masa dad'i sai
gashi da kamo d'ayan shima ya fara tsotso zumui zumui,gaba d'aya sun shagala sun manta a
ina ne suke Allah ya taimakesu wurin ba yawan mutane masu wulgawa, kukan da yaron ya
canyara NE shi ya dawo dasu daga duniyar saman da suka shiga, cikin jin nauyin abunda ya
faru tsakaninsu Amrah ta ture masa kai ya d'ago yana lasar baki saboda d'and'anon zakin
nonon da ya zuk'a, yana wata shuumar dariya yana kallonta da idanunshi da suka yi jajawur
saboda jaraba, ta kasa had'a ido dashi ta kawar da kanta tareda turawa yaron nonon ya fara
zuk'a sannan yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya.
Nazir ya ri'ko hannunta yace,, "Ki tausayawa kanki kada k'i bari shirmen dake kanki yayi tasiri
har ya hanaki abunda kike so, ni nasan kina bukatata a kusa dake saboda haka ki tausayawa
kanki kizo ki mori kurciyarki, kada ki bari rudin zuciya ya jaki kije kina cizon yatsa, don ba
alfakhari ba ki tara maza goma bazaki samu kamata ba, saboda haka kiyi shawara da zuciyarki
ki fiddowa kanki mafita."
Yana k'are maganar ya tada motar suka bar wajen, zuciyarshi cike take fam da soyayyarta uwa
uba da mahaukaciyar sha'awarta dake ranshi tun ranar da yasan wacece ita, don duk tsawon
watannin da aka yi bai rabeta ba zuciyarsh cike take da kewarta, yana dauriya ne kawai ba don
yana so ba.
Amrah dai k'anzil bata ce dashi ba sai shayar da yaronta take yi, amman fa zuciyarta ta lula
tuno ranar da ya rabata da budurcinta, sannu a hankali har zuwa lokacin da ya maidata mace
da kyau tareda mamayeta da soyayyarshi da yakeyi a lokacin kwanciyar auren nasu, sannan
yanzu wannan abun da ya faru yasa ta cikin wani rud'ani, har suka kai gidan bata daina nazarin
neman mafita ba. Yayi horn maigadi yazo ya bud'e masa ya shiga da motar d'an wadataccen
gidanshi, don baza'a kirashi da k'aramin gida ba, ya sami cikin wata rumfa yayi parking sannan
ya fito, yayinda ita kam ko motsi kasa yi tayi saboda zuciyarta da ke ta halbawa da sauri da
sauri, har sai da ya zagayo ya bud'e murfin ya zura hannu ya d'auko Umar dake ta barcinshi,
sannan ya d'orashi a kafad'a ya yi mata wani sihirtaccen kallo yace
"Welcome to your ne home my wify" Amrah tayi kamar bata ji shi ba ta yunk'ura cikin sanyin
jiki ta fito, ta kai kallonta ga gidan ya burgeta sosai amman ta waske ta tsaya jikin motar ta
rungume hannuwa tana kallon k'asa, Yayi 'yar dariya sannan ya rik'o hannunta ba shiri ta
rumtse ido saboda jin wani shock da ya ziyarci gangar jikinta, ba musu tabishi har zuwa 'yar
k'aramar k'ofar da zata sadasu da sashen Inna, gaban Amrah sai fad'uwa yakeyi gaba d'aya jin
kanta takeyi wata iri, saboda sabon yanayin da take jin kanta da gangar jikinta har ma da
zuciyarta da ruhi gaba d'aya.
Akafta
D/Auta ce
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Comment's d'inki yana sani farin ciki ba kad'an ba Alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke,
masoyana da masoya book d'ina na BAKAN Gizo dukanku ina maku son so fisabilillah*
*PAGE 34*
Da Sallama Nazir ya shiga d'akin Inna rungume da yaronshi, Inna ta amsa tareda k'ara fad'ad'a
fuskarta da fara'a saboda hango d'an jikallenta da tayi, Nazir kai tsaye wurinta ya nufa ya mik'a
mata yaron cike da tsantsar farin ciki Inna ta karbeshi tana jin k'aunarshi har cikin ranta.
Amrah kam sai da tayi jim na d'an lokaci sannan ta shigo d'akin da sallamarta, Inna da
Nazir d'in duka suka amsa mata sallamar kai tsaye wajen Innar ta nufa tana gayar da ita cike da
jin nauyinta, Inna ta amsa faran faram kamar ba wani abu a tsakaninsu sanna ta koma tana
gyarawa Umar zaman hularshi, don barcinshi yake yi sharkaf saboda yasha ya k'oshi, Inna ta
mik'e ta d'auko zane ta goye yaron ram abayanta, a cewarta yaro yafi jin dad'in bacci in aka
goyashi aiko ya lafe abinshi yana ta barcinshi har da su ajiyar zuciya.
Inna ta mik'e ta je ta kawo masu abinci da ruwa sannan ta fice tana ta 'yan k'ananun
ayukanta, Nazir ya kalli Amrah da ke rakub'e tamkar wata mai jin tsoronsu, yayi d'an guntun
murmushi ya Mik'e tsaye ya cire babbar rigarshi da fula ya ajiye sannan yace, "Ki taso muci
abinci" Amrah tayi kamar bata jishi ba ta k'ara gyara zamanta, Nazir ya zuba abincin a plate
d'aya ya saka spoons ya zo wurinta ya ajiye sannan yace da ita,
"Bismillah Maman Umar farouk" kanta a sunne tace, "Na k'oshi" ya d'ago kanshi ya
kalleta yace "Me kika ci?" tak'i bari su had'a ido tace "Bana jin yunwa ne kawai" kafin yayi
magana sai ga Inna ta shigo tana fad'in, "Kici ki k'oshi don maijego bata zama da yunwa, ko
don yaronta ai taci abinci don ya sami ruwan nono sosai" Amrah cike da jin nauyin Inna ta
d'auki spoon ta fara ci a hankali, Nazir ma ganin Inna yasa yana ta cin abincinshi ba tareda ya
sake bi takanta ba, Inna gano kamar tana jin nauyinta yasa ta yi k'uryar d'aki ta bar masu
falon, zuciyarta cike da tausayin Nazirunta saboda tunanin Zuwaira bazata barsu suyi zaman
aurensu ba, duk da ko ita kanta da zai sahale mata d'in da tafi son hakan tunda bata sonshi,
kuma muddin idan suka ci gaba da zama a hakan shine a wahale, ga kuma Auren da zaiyi tana
jin tsoron itama tazo ta gano Amrah bata girmamashi itama ta bi sawunta su maida mata da
yaro Mijin tace, motsin da yaron yakeyi abayanta yasa ta lallab'a ta saukar dashi a hankali ta
kwantar dashi akan gadonta, tana k'are masa kallo zuciyarta cike da tsantsan k'aunarshi, wani
gefen kuma tausayinshi take ji saboda tabbacin da take dashi na Zuwaira zata bi duk hanyar da
zata bi ta raba auren Iyayenshi.
Amrah da Nazir kam sai aikawa juna sak'onni sukeyi ta ido, saboda idan ya kalleta ta maka
masa harara yayi 'yar dariya, haka suka ci gaba da cin abincin har Amrah ta ajiye spoon d'in
tace ta k'oshi, Nazir bai kulata ba yaci gaba da cin abincinshi har da su k'ari, Inna ta fito tayi
waje tana ci gaba da hidimar had'a mata kunun ganyen da take yi mata, wanda tun kafin su zo
ta fara hidimarshi, aiko sai gata ta damo kunun da zafinshi cike da wani k'aramin bokiti ta ajiye
mata tana 'yar dariya tace, "Ga kunu nan kiyi k'ok'ari ki shanyeshi kafin Dare."
Gaban Amrah yayi saurin fad'uwa saboda daren da taji ta ambata, saboda ta tuno da Zuwaira
da 'yan k'annenta aranta tace,
_" waton dai ana nufin anan zan ta ci gaba da zama kenan har sai an kawo kud'in?"_
Zuciyarta ta karye sai ga Kuka shaaa akan fuskarta, Inna ta bita da kallo cike da mamakinta
tace,, "Bakya son kunun ne ko kuwa?" Amrah ta goge hawayenta ta janyo bokitin kunun
gabanta ta fara zubawa tace, "Zan sha Inna"
Inna ta zauna tana nazarin yanayinta, Nazir kam Mik'ewa yayi ya yi sashenshi inda d'akinshi
yake, zuciyarshi cike da tsantsar farin cikin zuwan Amrah gidanshi, duk da wani sashe na
zuciyarshi yana kokwanton zaman nata ya d'ore.
*********
Zuwaira kam ganin Abbati yak'i dawowa da wuri yasa ta sab'a hijabinta ta yi wajen bid'ar
dillalin da kanta, ALLAH yasa ta taki sa'a ta iskeshi gida suka rankayo gidan tare, koda suka
zo sun taradda wani wanda Abbati ya kira gaba d'aya suka shiga gidan, duba nan lek'a nan
ko'ina sai da suka tantance sannan wanda ta kira ya fara yiwa gidan kud'i da miliyan biyu da
d'ari takwas, ta nuna rashin amincewarta d'ayan kuma yayi masa kud'i da miliyan Uku saboda
shi kanshi yasan gidan ko miliyan biyar aka sayeshi ya sayu, amman saboda ganin ita ke son
sayarwar shiyasa, Zuwaira kam duk da taji dad'in cinikin nashi amman ta nuna rashin
amincewarta da hakan, tace da su su dai k'ara in har suna so ta sayar masu, dole haka suka
rabu akan zasu je suyi shawara har d'ayan ya tafi wanda ta kira, sai ga wanda Abbati ya tafo
dashi ya dawo yace ya k'ara mata dubu d'ari akai ta nuna masa idan dai ba miliyan uku da dubu
d'ari biyu ba bazata sayar ba, ganin ko a haka ya sayeshi zai ci riba sosai yasa ya amince da
hakan, saboda yana jin tsoron abokin cinikinshi ya dawo ya saye gidan, amman ya rok'i
alfarmar ta bashi nan da sati d'aya zai zo ya biya kud'in, Zuwaira ta dafe k'irji tace
"Ai WALLAHI idan bazaka biya nan da kwana Uku ba to da naga mai saye zan siyar ni ba
ruwana,don ni in ta nice ma yanzu abani kud'in inje inyi abunda ke gabana, saboda ai kai
kanka kasan haka kawai bazan d'aga gidan da muke zaune ba ince zan siyar, tunda dai ba
bakin Uwa ce dani ba, ka dubi girman gidannan kai kasan idan ba dole WALLAHI nida shi mutu
ka raba, to amman dole ka dole ka bani kud'in kawai in kana son mu shirya ni da kai"
Mutumin ya nuna mata shima idan son samu ne ya biya yanzu a wuce wurin, to amma had'a
kan kud'in yake so yayi shiyasa, yayi ta rok'onta da ta bashi kwana bakawi d'in kamar yanda ya
nemi alfarma tun farko, Zuwaira tace da shi to kawai anman aranta taci alwashin da ta sami mai
kud'i hannu karb'a zata yi ta fita iskanshi.
Bayan fitarsu ne Abbati ya kalli Zuwaira yace, "Mama idan kika siyar da gidan to mu kuma ina
zamu koma? Tunda ai ko ainahin gidanmu kin sayar dashi shima"
Zuwaira ta maka masa wata k'atuwar harara tace, "Ina ruwanka da inda zamu zauna tunda
babu ko kwandalarka a ciki, amman tunda har so kake ka sani to bari in sanar dakai gidan haya
zamu Je mu kama mu zauna, sauran kud'in da zasu rage in fama sana'a mu sami abin rufawa
KAI asiri, kagin ALLAH ya fitowa da Amrah wani mijin aure"
Abbati yayi saurin kallonta yace, "WALLAHI ina jiye maki raba aurennan Mama, don ko har
abada Aunty bazata sami wanda zai sota irin son da Yaya Nazir yayi mata ba, yanzu KO don
albarkacin yaronnan da aka haifa bazaki bari ta zauna ba? Duk fa wanda zai aureta yanzu da
sunan bazawara zai aureta ba budurwa ba, sannan yanzu abun duba koda ya saketa ai dole ta
jira har sai ta yaye yaron sannan tayi wani auren, don ba mai aurenta da d'an wani ya ajiye
cikin gidanshi, to ko in hakane me zai hana ki barta cen har ta yaye yaronta sannan ta dawo,
tunda dai mu nan idan ma ta dawo ajiyarta za muyi ba auren zata yi ba yanzu."
Zuwaira ta kalleshi shekeke saboda tama rasa abunda zata fad'a taji sanyi aranta, saboda
Abbati ya kunnota da kyau da kyau ta had'e fuska sosai sannan tace, "Abbati!!" ta kirashi da
wata kakkausar murya tace,
"WALLAHI na koma jin sunan Matsiyacin yaronnan abakinka sai na ci ubanka munafukin
ALLAH, waton dai atak'aice na ganoka bak'in ciki ne kake yiwa 'yar uwarka, saboda baka son
taje inda zata huta taji dad'i muma muji, to ahir d'inka in kasan bakinka bazai fad'i alkhairi
akanta ba to kada ka sake shiga wannan magana, idan kuma gigi ya jaka ka fad'i wata
mummunar kalma akan haka to WALLAHI ban yafe maka ba, idan ba don kana wawa ba ai ci
gabanta namu ne duka, yanzu wannan gidan da muke zaune Ubanka ne ya bar muna shi cikin
gado muka gada koko arzik'inta ne muke ci?da ana nuna maka hanya kana kaucewa, to ka
kiyayeni bana son gutsuri tsoman munafuccinka."
Abbati ya shigewarsh d'aki abunshi ya k'yaleta tana ta zuba ruwan bala'i, har da su cewa ai ta
gano ba mai sonta tunda yanzu gashi k'iri k'iri Asabe ta had'a kanta da Mijinta anci Amanarta,
sannan su gasu dangin Baban nasu Amrah kowa ya zare jikinshi akan maganar bakinta yana
kunfa tace,
"Ai WALLAHI duk nasan zaman da nike yi da kowa, kuma duk bala'in mutum sai ya barni tunda
na zo duniya da bisimillahta abaki na shigo."
To fa kunji sai ku rage zagin Zuwai don da shirinta tazo zaman duniyar
Manage plss♀️
D/Auta ce
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 35*
Zuwaira kam ranar bata yi kwanan kirki ba saboda masifar da take ta yi ita kad'ai, Abbati da
kanenshi ma sai da suka gaji da sauraronta suka yi bacci, sai Alla Alla take akan safiya ta waye
ta koma wurin dillalin da ta nemo in yana da kud'in shi ya bata ta sayar masa ta je ta karb'o
'yarta da d'an jikanta da tayi marmarinshi da kewar jin muryarshi koda ta kukanshi ce ko.
**
Gefensu Amrah da Nazir kuwa Inna tace dashi yaje ya siyo masu kayan da zasu saka koda na
kwana Uku ne, Nazir yaso ya tafi gidan Zuwaira ya d'auko masu kayan Inna ta hana tace yaje
dai ya siyo masu wasu saboda gudun tashin hankali, aiko yaje ya lafto masu kayan sakawa
musamman Amrah da nata gaba d'aya ready mate ne sai wasu da ya bada a d'inka mata
saboda shigar bikinshi da Sadiya idan har zamanta ya d'ore har lokacin, da wasu abubuwan da
zasu buk'ata ita da d'anta cike da jin dad'i Inna tayi ta sanya masa albarka, Amrah kam
iyakacinta ido ba baki saboda gaba d'aya daga shi har Innar sun dabaibayeta da karamcinsu,
wanda har yasata rasa ta wane gefe zata ajiyesu, shin matsayin abokan adawarsu ita da
Mamarta koko matsayin mutanen da suke da wani girma a idonta?.
Da dare ma Nazir ya dad'e d'akin Inna sunata fira yana gyarawa Umar kayanshi cikin wani
k'aton riyo, Amrah dai kallone nata don ko godiya ma bakinta nauyi yayi mata tayi tagumi tana
faman Nazari, har sai da ta fara jin bacci ne Inna tace dashi ya d'auki danshi suje sashensu
su kwanta, Wani fad'uwar gaba ya dirarwa Amrah sai ga hawaye wasu na korar wasu ta kalli
Inna tace, "Don ALLAH Inna ki barni nan in kwana dakinki har zuwa lokacin da zan bar gidan"
Inna tayi 'yar dariya tace, "Ina kika tab'a ganin haka Amrahtu? Ace mace da Mijinta ta kwana
wani d'akin? Kiyi hak'uri kinji kije kiyi kwanciyarki da safe sai ki zo nan d'in kiyi zamanki, in ma
zaki kawo man Megidana ne ya tayani kwanan ki kawoshi sai kije kiyi kwanciyarki acen"
Amrah kam sai kuka takeyi yana rok'on Inna don ALLAH ta barta nan ita bazata je wurinshi ba,
dole ba don taso ba tace da ita ta shiga d'akin to ta kwanta ita da yaronta.
Nazir dake rungume da farouk d'in yana 'yar dariyar yak'e don yaso ace Inna ta tilastata sai ta
bishi, amman ai duk da hakan ai ana tare kuma kwana k'alilan ne suka rage a kawo masa
amaryarshi, don yasan abunda take wa gudu duk bai wuce kada ya sami damar rab'ar jikinta
ba, ganin ta nufi k'uryar d'akin Inna yabi bayanta yana 'yar dariyar mugunta da nufinshi na
ajiye mata yaron, Inna ma biyarsu tayi da kallo zuciyarta cike da tausayinsu dukansu, saboda a
d'an zaman da tayi da su a gabanta ta gano ita kanta Amrah ba wai son Nazir ne bata yi ba,
kawai dai akwai k'ullin dake ranta wanda yak'i bari ta gano tana sonshi, shiyasa ta yanke
hukunci ta bishi cen koda ALLAH zaisa kafin Zuwaira ta kawo kud'in ya shawo kan Matarshi su
daidaita.
Nazir kam yana shiga ya ajiyeshi a gefen gadon sannan ya duk'o daidai sautin fuskarta yace,
"Yanzu shikenan haka zakiyi ta cutar da kanki ki cutar dani? K'iri k'iri kina buk'atar mijinki kina
nok'ewa?hmmmm!! To yayi ba komi amman kisani kina gaf da yiwa kanki sakiyar da babu ruwa
domin kuwa Amaryata tana nan zuwa nan da Kwana hud'u masu takwas masu zuwa, ruwanki
ne ki tallafi mijinki ya dawo hannunki ko kuma ki sakarwa wata idan tazo ta ririta maki shi tamkar
k'wai, saboda gaskiya zan gaya maki WALLAHI Sadiya tana sona