Bakan Gizo Compelet Book

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 44

21K to 24K   out of 129.9K words

tana tsakar gidan sai kuka take yi gwanin ban tausayi, Aunty ta ri'kota cikin tashin

hankalin da ya bayyana akan fuskarta tace, "Na shigesu Meke faruwa ne?ko wani abu yana
maki ciyo ne?" Amrah ta girgiza kai tareda k'ara sautin Kukanta, Aunty ta k'ara rud'ewa hankali
tashe tace, "Don ALLAH kiyiman bayani meke faruwa wai!" Amrah tayi mata nuni da inda
takardar take a yashe, a cikin kad'uwa Aunty ta nufi takardar zuciyarta sai bugawa take yi da
sauri da sauri, saboda zargin da take yi akan cewa takardar saki ce Nura ya bata, to akan wane
dalili?me yayi zafi, tunaninta ya katse ne lokacin da ta fara karanta abunda takardar ta k'unsa,
aiko da sauri ta dafe k'irji cikin wani sabon tashin hankali tace, "Me nike shirin gani ni Asabe,
wannan bala'i da me yayi kama?" jikinta har tsuma yake wajen kwad'awa Amrah mari a cikin
d'aga murya tace, "Miye had'inki da wanda ya rubuto takardar?me kika yi masa da zafi wanda
har ya zab'i ya saka maki da wannan masifa ta bak'in k'azafi."

Amrah ta dafe gefen da Autyn ta mareta tareda k'ara sautin kukanta tace, "Wallahi Aunty nima
bansan komai akan takardar ba."

Aunty ta maka mata wata k'atuwar harara sannan tace, "Kada ki renawa mutane wayo, taya
zaki ce baki sani ba ga sunanki a rubuce?" Amrah ta fara rantse rantse sai ga Malam ya fito
daga ban d'aki,saboda zawon da ya je ya tsiyaye na tashin hankali duk da dai kaso mafi rinjaye
yana tabbatar masa da ciki nasa ne, to anman in babu rami me ya kawo zancenshi?, dole ne
ayi bincike don wannan al'amari da d'aure kai yake.

Aunty tana ganinshi tace "yawwa Malam don ALLAH zo ka warware man wannan k'ulli, shin
ya aka yi wannan takarda ta shigo hannunku?" kai tsaye yayi mata bayanin komi ranshi a
jagule, Aunty ta kalli Amrah da zungureren cikinta sannan ga idanuwanta har sun kunbure
saboda kukan da tasha, kanta gaba d'aya ya k'ulle ta rasa me ma zata fad'a kai tsaye ta nufi
k'ofar gida, jiri yana kwasarta saboda tsananin firgici da ta shiga, jiki ba kuzari taje wurin mai
gidanta ba tareda bayanin komi ba ta mik'a masa takardar, ya saka hannu ya karb'a a cikin
mamakin takardar miye, shima a take ranshi ya bashi sakin Amrah Nura yayi, sai gashi yana
gama karantawa yayi saurin d'ago fuskarshi yace, "Wasik'ar waye?" A cikin zubowar wasu
hawaye Aunty tace, "Ta Amrah ce" da firgici akan fuskarshi yace, "Garin yaya hakan ta
faru to?" Aunty ta share hawayenta tace "Nima bansani ba,kuma itama wai bata san komi
ba yanzu haka ma tana cen tana kuka na tashin hankali, ina zamu kai wannan Masifa da
darennan?"

Mijinta yayi shiru sannan yace, " ina shi maigidan nata?" Aunty tace "Yana ciki" yace
"Kiyi man sallama dashi don wannan abu akwai d'aure kai sosai, amman kuma fa ruwa basu
tsami a banza kira shi dai muji ta bakinshi."

Aunty ta koma gidan minti biyu a tsakani sai ga Nura ya fito, Mijin Auntyn ya fito daga motar ya
mik'a masa hannu suka gaisa, sannan yace dashi "Me ka sani dangane da wannan takarda?.
"

Yace sam shi baisan komi ba shi hasali ma shi zuciyarshi bata yarda da cewa hakan zai faru ba,
mijin Aunty yaji dad'in maganganun da yaji ga Nura, yayi ta kwantar masa da hankali tareda

k'ara nusar dashi akan ya zama ido sosai akan gidanshi ko don ya kare martabar iyalinshi.

A cen cikin gida kuwa Aunty ce take ta yiwa Amrah fad'a akan sai ta fad'a mata wanda yayo
takardar, amma ta kafe kai da fata akan ita batasan komi ba, dole aunty ta ajiye tambayoyinta ta
koma lallashin Amrah, Amrah da jajayen idanuwanta da suka kumbure saboda kuka, ta d'aga
kai ta kalli Aunty tace, "Don ALLAH Aunty ki tafi dani a gidanki WALLAHI tsoron gidannan nike
yi, saboda bansan wani kalar sharri za'a k'ara biyo man da shi ba."

Aunty tayi jimmm na minti biyu sannan ta ri'ko hannunta, ta taimaka mata ta mik'e tsaye suka
fito k'ofar gidan inda suka tarar da su NURA sai firarsu suke yi, Aunty ta kalli Nura tace,
"Amrah ta rok'i alfarmar mu tafi da ita idan ka amince sai in wuce da ita in yaso gobe sai kaje ka
d'aukota."
Yace,, "Ba damuwa"

Amrah ta shiga motar ta zauna sannan suka yi sallama da shi suka tafi, Amrah dai har suka je
gidan aunty bata sani ba, saboda zuzzurfan tunanin da ta fad'a sai dai jin tayi aunty tace, " ki
fito muje ko" sannan ta muskuta ta lallab'a ta fito jikinta gaba d'aya ba kuzari suka shiga cikin
gidan sai jiri ke kwasarta, saboda kanta da yake ta sara mata har wani dushi dushi take gani
dasu, tana zuwa d'akin Aunty tayi tsinke ta fad'a kan gado ta kwanta tareda k'udundunewa a
bargo saboda wani zazzab'i da take ji, aikuwa kafin minti biyar sai gata tana kyarmar rawar d'ari
saboda sanyin da take ji yana ratsa k'assan jikinta, hak'oranta sai had'uwa suke yi da juna suna
kuka kaf! kaf!, Aunty ta shigo d'akin ta isketa a wannan hali jikinta yana rawa ta d'auko mata
magunguna ta matsa mata dole sai da tasha sannan ta koma ta kwanta, yayin da wani Bacci
yayi awon gaba da ita mai cike da mafalkai barkatai.

Aunty ta kashe fitilar d'akin sannan ta ja mata k'ofar ta nufi d'akin maigidanta, domin tana son
su k'ara tattaunawa akan matsalar.
Amrah kam tsakar dare tana baccinta sharkaf sai gashi tayi zumbur ta mik'e zaune tareda dafe
kunnuwanta ta k'walla k'ara tana fad'in, _WALLAHI Nazir bazan baka d'ana ba haka kawai
da rana tsaka kazo kace sai na baka yarona wallahi bazan bayar ba._

Aunty da mijinta da gudu suka shigo d'akin suka yi cirko curko suna kallonta, suna k'are mata
kallo a cikin Mamaki Aunty ta zauna tareda dafota da hannunta biyu ta girgizata sannan ta fara
kiran sunanta tana tambayarta lafiya, sai a lokacin Amrah ta dawo a hayyacinta tana ganin
Auntyn tayi saurin fad'awa jikinta tana Kuka, Aunty ta rungumeta tsantsan tana bubbuga
bayanta tana lallashinta, bayan ta d'an lafa sannan Aunty tace da ita tayi addu'a ta koma ta
kwantawarta ba abunda zai samunta, Amrah tace sam ita ba zata iya bacci ba saboda tana jin
tsoron miyagun mafalkan da take yi, Aunty tace to taje ta d'oro arwallah sai tayi salloli kafin
asuba, aiko tsam ta mik'e taje tayi arwallar Aunty ta shimfid'a mata carpet, sai da ta tada sallahr
sannan ta fito d'akin zuciyarta sai tunani take yi akan wanene Nazir d'in da taji Amrah ta fad'a,
anya ko wai wannan abu babu k'amshin gaskiya a ciki?taci alwashin idan safiya ta waye zata
tambayeta wanene shi, don idan bata manta ba ko Zuwaira sai da taji sunan Naziri a bakinta

tana fad'ar cewa, _kada dai ace hak'k'inshi ne yake bibiyarsu_ Shin shi Nazir d'in
wanene? Miye alak'arsu dashi ne? Da har hak'k'inshi zai bisu? Shin to ta yaya ma wai to?haka
Aunty ta kwana tana tunanin sunan Nazir da taji Amrah ta ambata tana ta Alla Alla akan safiya
ta waye suyi maganar don saboda a gano ta inda kan zaren yake.
Amrah kam bayan tayi ta jera sallolinta ne tareda addu'o'inta, wata azababbar yunwa ta
ziyarceta dole ta had'a tea mai shegen kauri ta shanye da guntun biredin da tagani a d'akin
sannan hankalinta ya dawo jikinta, ana yin sallar asuba ta samu ta gabatar da ita, ta d'an
kishingida a gefen gadon sai bacci.
Koda safiya ta waye har k'arfe takwas Amrah tana ta baccinta, Aunty mayarta biyu tana dubawa
bata tashi ba sai a ta uku ce da ta shigo taji motsinta toilet, ta sami gefen gadon ta zauna tana
jiran fitowarta, aiko sai gata ta fito da alama wanka ma tayi tana ganin Auntyn ta k'araso da
sauri tace, "Aunty ina kwana?" tace "Lafiya lau." Sannan ta bita da kallo mai cike da
tausayin yanda ta k'ara zabgewa har k'ashin wuyanta ana gani, Amrah da duk da bata da wani
jiki amman wuyanta a cike yake,saboda tsanannen jiki ne da ita kibarta tayi dai dai da jikinta,
Aunty tace da ita idan ta k'are ta fito falo ta yi breakfast, taje ta fiddo mata wata doguwar riga
bubu a cikin kayanta ta bata ta saka, sannan ta fice zuciyarta cike da sak'e sak'e.

Amrah ta bita da kallo sannan ta d'an shafa mai sama sama ta zura rigar ta fito, kai tsaye falon
ta nufa ta zauna inda Aunty ke zaune tana kallon tashar Arewa 24 itama tazo ta zauna Aunty
tace, "Yawwa kin fito?" tace. "Eh" Aunty ta mik'e tsaye taje ta kawo mata abun karin sannan
ta zauna, Amrah ta sauko jiki ba kuzari ta fara karyawa kamar bata so, cusawa kawai take yi
amman ba don zuciyarta tana so ba sai don kawai abin cikinta dake ta damunta da motsi, da
alama neman abinci yake yi, bayan ta k'are ne ta kalli Aunty tace, "Auncle fa ko har ya fita?"
Aunty tace "Eh ya fita saboda akwai shari'ar da za'a yi yanzu da k'arfe tara."

Tace "OK " sannan taja bakinta ta tsuke saboda daman maganar ta k'arfin hali ce take yi,
Aunty ta kalleta ta gyara zama sannan ta kira sunanta a hankali, Amrah tayi saurin d'ago kanta
ta kalleta hawaye suka gangaro mata tareda wata fad'uwar gaba da ta diro mata ba shiri, a
hankali tace, "N'aam Aunty"
Aunty ta sake kiran sunanta tace, "Wanene Nazir da naji kina ta fad'a jiya akan bazaki bashi
yaronki ba?"

Amrah ta zaro ido a waje tace, "Nazir kuma?" Aunty ta had'e fuska sannan tace, "Eh shifa
sannan ko Aunty Zuwaira ma naji ta fadeshi lokacin da kika fito gidan ALHAJI mai akwai, tana
fad'ar kada ace Hak'k'inshi ne yake bibiyarku, ko dai da gaske shine Uban cikinki?don gaskiya
na fara zargin kamar akwai lauje cikin nad'i a cikin lamarinki, saboda jiya banyi baccin kirki ba
ina ta sak'awa da kwancewa akan wannan hargitsi da ya ratso cikin rayuwarki."

Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya sannan tace, "Aunty tun ina budurwa na kame kaina ga
kowane namiji, ballantana yanzu da nayi aure nikam me zai jani da har zanje in zubar da

mutuncina a waje, WALLAHI ni ba wani d'a namiji da ya tab'a sanina 'ya mace a duniya sai
Malam, don ko Salis da muka yi soyayya sosai dashi WALLAHI ban tab'a bashi damar da zai
kai jikina ba balle wani cen don ALLAH Aunty ki yarda dani WALLAHI ni bansan komai ba akan
wannan bak'in k'azafi da ake so ajefe ni dashi." ta fashe da kuka gwanin ban tausayi Aunty tayi
shiru tana kallonta sai cen ta nisa tace, "To Nazir d'in fa miye had'inki dashi?."

Amrah zata yi magana kenan Text ya shigo wayarta, ta kai kallonta ga wayar dake gefenta
ajiye ba shiri ta zaro ido da sauri ta d'auko ta k'ara duba text d'in, ba shiri tace, " na shiga Uku
Aunty nikam meke shirin faruwa da rayuwata ne?" Ta fashe da wani kuka mai tsanani Aunty ta
d'auko wayar ta duba itama sai gashi ta zaro ido saboda ganin abunda aka rubuta,
_A ranar da kika haifu a ranar zan zo karb'ar yarona_

Aunty tayi saurin dealing d'in numbar aiko har ta tsinke ba'a d'auka ba, bata hak'ura ba ta sake
kira aikuwa sai gashi an d'aga, kafin ma Aunty tayi magana sai ya rigata da cewa, "Ki
shiryawa zuwana a duk ranar da kika haifu don bana buk'atar shayarwarki ga yarona." kit ya
kashe wayar a cikin tashin hankali Auntyn ta sake kiranshi sai gashi taji wayar a switch up, ba
shiri ta aza hannu aka tace

"Wannan wane irin kalar bala'i ne yake so ya ruguzo muna ni Asabe?"

Itama sai ga hawaye shaaaa a cikin kuka kalli Amrah tace, "Ki fad'a mani gaskiya Amrah
bana son shiga cikin lamarin da ba gaskiya."

Amrah zata yi magana sai ga Muryar Malam Nura yana sallama a waje, da sauri Aunty taja
hijabinta ta fita yanayin da taganshi yasa gabanta ya fad'i, da sauri tace "Kayi hak'uri malam
Nura Insha Allahu za'a yi bincike komai zai zo da sauk'i."

Malam Nura ba tareda yace da ita k'anzil ba ya mik'a mata wata envelope babba ta zura hannu
ta karb'a a cikin mamaki ta bud'a envelope d'in domin taga abunda ke ciki, ta zaro photunan da
tagani da yawansu zai kai guda goma, dubawar farko da zata yi idanuwanta suka yi tozali da
Amrah zigidir rungume da wani wanda fuskarshi bata fito ba amman shi da guntun wandonshi,
Aunty bata k'ara tsayawa duba sauran ba jikinta yana rawa ta koma cikin gidan gadangada tayi
kan Amrah da duka tana kuka ta watsa mata photunan duka a jiki.

K'irnjin Amrah ya buda dam! dam! Don ita dukan ma bata jinshi saboda bak'in cikin da ke cikin
zuciyarta yafi dukan zafi, tabi photunan da kallo d'aya bayan d'aya da suka tarwatse a tsakiyar
falon, ta zura hannu ta d'auki wani dake saman cinyarta tana kai idanuwanta ba shiri ta tashi
tsaye, saboda abunda ta gani wanda yake so ya saka zuciyarta barazanar tarwatsewa,
photonta ne tareda wani hannuwanshi rik'e da breast d'inta duka biyu.

Akafta







D/Auta ce

*BAKAN GIZO*


*NA HADIZA D/AUTA*


https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp

*⭐⭐⭐TAURARI WRITERS ASSOCIATION⭐⭐⭐*

(We entertain and educate according to our religion and ethnics)


*PAGE 17*

**********************

Ba shiri ta fasa wata k'atuwar k'ara tace,

"ALLAH ka d'auki raina in huta da wad'annan musibu da suka dabaibaye rayuwa, ko'ina na
dafa ba sauk'i sai tarin k'alubale mai hana kwakwalwa da ruhi zama lafiya."

Aunty Asabe ta je ta shigo da Malam Nura da yake tsaye inda ta barshi har lokacin, saboda
gaba d'aya jikinshi ya mutu murus ya kasa motsa ko d'an yatsanshi, musamman da yaji
kalaman da Amrah take furzowa,daga inda yake yana jin sautinta zuciyarshi ta tabbatar masa
da akwai wani k'ulli a cikin rayuwar Amrah, wadda itace yanzu ta bibiye aurensu domin cikar
bak'in nufin da tun farko ake ta so a cika akanta.

Idonshi akan Amrah har ya zauna zuciyarsh cike da tausayinta, saboda izuwa yanzu ya
tabbatarwa zuciyarshi Amrah bata da masaniya akan lamarin, saboda kalaman da yaji suna fita
abakinta.

Aunty ta zauna tareda yin tagumi daga ita har Malam kallon Amrah sukeyi gwanin ban tausayi,

hankali a tashe suka yo kanta saboda dukan cikin da ta fara yi a haukace, tana sanbatun bata
son cikin gara ma ta mutu kowa ma ya huta, daga Auntyn har malam hankalinsu ya k'ara tashi
sosai saboda yanda suka ga ta rikice masu, Aunty ta rik'ota tareda mik'ar da ita tsaye da nufin
ta hau kan kujera, aiko sai ga wani jini sun gani da yake biyar k'afafunta, Aunty ta fasa k'ara
tace

"Wayyo ALLAH ka kawo muna agaji."

Malam a rud'e ya rungumota jikinshi ya rasa ma me ya dace yayi, Aunty dake rik'e da hannunta
tace dashi, "Je yi sauri kazo muna da abun hawa mu kaita asibiti."

Aiko a d'ari ya fice har hularshi ta fad'i amman ko waiwayowa baiyi ba, Amrah ko sai murd'e
murd'e take yi saboda azababben ciyon da mararta yake yi, Aunty sai faman sannu take mata,
minti biyar a tsakani sai ga Malam ya dawo da Napep d'in, cikin azama Aunty ta d'auko hijabi ta
sakawa Amrah itama ta saka nata suka rik'ata suka fito da ita, har sai da suka shiga napep d'in
Aunty ta tuno bata d'auko kud'i ba, dole ta fito ta koma cikin gidan ta d'auko sannan suka tafi.

Koda suka je asibitin basu sha wata wahalar jira ba saboda jinin da ke ta zuba jikinta ya tsorata
mutane da yawa, direct aka wuce da ita emergency tareda yimata taimakon gaggawa, sannan
wani likita ya fito da sauri ya cewa su Aunty, ana buk'atar jini gora biyu da za'a saka mata da
gaggawa saboda ceto ranta da abunda ke cikinta, hankalinsu ya k'ara tashi daga Malam har
Aunty suka ce agwada jininsu aga in zai yi, aiko koda aka gwada gaba d'aya ba wanda yayi
daidai da nata, kasancewar ita amrah jininta Group O nagetive ne ba kowane jini ne ke yi mata
ba, hankali a tashe Malam da Aunty suka rok'i alfarmar zasu je su samo mutane a gwada aga in
za'a dace, Malam ya nufi makaranta Aunty tayi

8 / 44