Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
tako kafarki wurinta WALLAHI ko tunota kika sake yi ban yafewa
Yan uwantakar da ke tsakanina dake ba, tunda dai ke kin zama uwar naci akanta ita Kuma
kullum bata jin kunyar tozartaki da duk Wanda yarabeki,to kije ki bi Mijinki tsinuwarta ba inda
zata je balai har ta kamaki,don kowa yasan baki yi Mata abunda ALLAH zai yi tirr da ke ba
ballantana har tsinuwarta ta banza ta yi tasiri akanki"
Yana K'are fadar maganar ya kalli Nazir da ke fitowa gidan kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki
saboda tsantsar tausayin Amrah da ya kamashi,cikin jarumta yace dashi
"Ni Abbati na baka amanar Aunty Amrah ka zame mata Uwa da Uba har ma da mu danginta
duka, ALLAH ya kaiku gida Lafiya ka gaida Inna da fine boy dinmu"
Nazir cikin sanyin jiki ya mika masa hannu suka yi musabuha sannan ya karb'i numbarshi suka
yi sallama ya ja Motarshi suka tafi.
Abbati Kam sai da ya sake komawa gidan inda ya taradda Lantana sai miyagun maganganu
take cab'awa Zuwaira,amman ko ta kanta bai bi ba ya fara balbalawa Zuwaira ruwan fad'a
kamar ya daketa yace
"WALLAHI in baki nemi yafiyar Aunty Amrah ba kika mutu a wannan halin naki da kike ciki to da
wuya in kina shiga aljannah, kin cutar da rayuwar Yar da kika haifa da cikinki don kinga tana
tsoronki, to bari kiji ni Wallahi da nice ita da har abada ba zaki sake jin duriyata ba, na barki har
abada don ba halittata kika yi ba haifata kika yi kuma ban zalunceki ba kece kika zalunceni,
yanzu ko wannan abun da ya faru bai isheki ishara ba??? Kin sai da gida kin raba aure kuma
gashi Allah bai kasheshi ba sun sake mannewa har da karin tukuicin rabon da ya sake shiga a
tsakaninsu, don haka ki godewa ALLAH da har rabo bai kasheki ba aka sake baki wata damar
domin ki tuba ga ALLAH ki sami tsira, idan kin hankalta kin nemi yafiyar yarki mai tsananin
biyayya gareki tom! Idan kuma kince haka zaki ta biye wannan Munafukar matar Kuna rabawa
kanku abun fad'i a unguwa to ki ci gaba gata ga ki nan Ni kunga tafiyata"
Ya fice fuu ya bar gidan zuciyarshi sai tafarfasa take yi da takaicin halin Uwarsu, wadda arzik'i
bai yi da ita sai anbi ta hanyar tsiya.
Nazir kam kai tsaye gidan Baban Jamilu ya tafi ganin halin da suke ciki da shi da ita yasa ya yi
ta basu baki tare da nusar da su amfanin hak'uri, basu bar gidanga har sai da ya tabbatar ya
saka masu natsuwa a zuciya sannan suka nufi gidan Jamila, inda suka gaisa da su suka wuce
gidansu don a acen za su kwana tunda asuba su kama Hanya.
Nazir ya b'oye damuwarshi yayi ta kwantarwa da Amrah hankali da nuna mata misalai kala kala
na masu hakuri wad'anda suka ci ribar hakurinsu a gaba, da hilata da wayo da dabara ya
kwana yana morewa aurenshi inda yayi nasarar cusa farin ciki a zuciyarta ta saki ranta suka yi
ta shan soyayyarsu.
Asubar farin suka kama hanyar barin garin Katsina suka nufi hanyar zuwa Gombe, sun ci tafiya
mai suna tafiya sannan suka isa Gombe cikin dare gaba d'aya duk sun jigata iya jigata, Amrah
sai faman narkewa take yi saboda a rayuwarta kaf bata taba tafiya mai nisa irinta ba.
Sannu a hankali yana ratsa unguwanni da tituna aiko sai gasu wata unguwa wadda a duba
d'aya zaka gano Quaters ne na ma'aikata, sannu a hankali har yayi parking a k'ofar wani Gida
da yasha fenti sabon dal, abun burgewa gidan tsaf tsaf gwanin sha'awa yana rik'e da Jakar
kayanta tana biye dashi har cikin gidan.
Shigarsu ke da wuya Inna ta fara fad'in "lale lale marhaban lale da zuwanku mutanen
Katsinawan Dikko"
Amrah ta fara sunne kai cike da jin nauyin Innar Sabida cikin da ke jikinta da ya fito kuru kuru
ana ganinshi, Inna ta yi saurin k'arasowa ta kamo hannunta Kai tsaye ta nufi d'akinta da ita tace
"Zo muje in kaiki d'akinki don daga ganinki wannan tafiyar ta gajiyar da ke sosai"
Amrah sai sunne Kai take yi tana biye da Inna har zuwa wani falonta madaidaici Wanda yaji
kayan karau na gyara muhalli da luntsuma luntsuman kujeru sai tashin k'amshi yake yi kamar
na wata sabuwar Amarya, bata tsaya da ita nan ba ta nufi kuryar d'akin da ita inda shima yasha
kayan furniture's na alfarma sai kamshin sabunta suke yi, ta zaunar da ita akan gadon tace
"Zauna Kan gadonki ki sa albarka kafin Mijinki ya zo ya ya bani kud'in siyen bakina"
Amrah ta rufe fuskarta Sabida kunyarta da take ji don gaba d'aya Inna ta murje ta zama wata
Yar gayu tsufanta ya b'oye saboda riritatan da Nazir yake yi, don ba yanda bata yi ba akan ya
barta cen katsinar ta samo mai tamata zama amman yak'i, sai gashi zuwa da ita yayi Rana
Saboda matsalolin da suka yi ta afkuwa itace ta yi ta d'ora Nazir a Hanya har komi ya zama
tarihi.
Nazir ya shigo da jakar Amrah rungume da Umar a jikinshi Inna ta rik'e baki tace
"Yanzu sai da ka ta da yaronnan yana baccinshi???"
Nazir ya ajiye jakar cikin farin ciki yace
"Gara ya tashi Inna shima ai sai a tarbemu da shi "
Inna ta fice tana cewa
"To ni bari inje in kawo maku abincin anan d'in don nasan gaba dayanku a gajiye kuke"
Nazir ya kalli Inna yace,. "Ina Suwaibar ko tayi baccin itama??"
Inna tace,. "Ai tana gama sallah ta Fara kwana kasanta da nauyin bacci musamman idan ta yini
tana aiki"
Nazir yayi dariya yace
"Bamotar ba to Ni dai tunda Matata ta dawo ALLAH ya fansheni daga yau na dena cin
jagwalgwalon abincinta"
Inna ta bud'e baki tana dariya tace,. "Yau din ma ka bar mata kayanta ai sai ta d'umama da
safe ta ci abunta in don Suwaiba"
Ta fice zuciyarta cike jin dad'in ganin Amrah da cikin dake jikinta sai jinjina girman tsalkin mulkin
Ubangiji take yi,Wanda shine ya ke baiwa Wanda ya so a lokacin da ya ga dama.
Nazir ya kalli Amrah da ke ta satar kallon Umar yayi dariya yace
"To kunyar ta me kuma gaki gashi nan kiyi ta kallonshi don daman donki na daukoshi don nasan
a k'agauce kike da ki ganshi"
Ya k'are maganar tare da Dora mata shi a saman cinya, Umar da har lokacin mayen baccin bai
sakeshi ba ya fashe da kuka yana kallon Babanshi, Amrah ta kalleshi zuciyarta fari sol saboda
ganin yanda yaronta ya koma tamkar dan indiyawa, gashi fari jajir da cikar bak'in gashi a
nannde matsa ALLAH kamar dan Buzaye, gashi katoton gaske daga ganinshi zaka gano anyi
barin gwangwanayen Madara a jikinshi.
Cikin jin dad'i ta d'aukeshi ta sakashi a jikinta tana lallashinshi aiko ya langabe abunshi a jikinta
kafin kace me har ya koma baccinshi, ta lallaba ta ajiyeshi inda yayi dai dai da fitowar Nazir da
yayo arwallah ya kalleta yace
"To maman biyu kema ki shiga ki yo arwallar ki zo mu Rama sallolinmu"
Ta mike tana waigen Umar ta shiga toilet d'in zuciyarta fes da d'inbin farin cikin da ya ratsa
ko'ina na jikinta.
Akafta
D/AUTA ce✍
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*Wattpad PrincessDija246's*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*60*
Bayan sun k'are sallolin ne Nazir yace da ita ta dauko kulolin ta zuba masu abincin, tayi kamar
yanda ya umurceta suka ciyar da junansu suna yar firarsu suna dariya har suk k'are cin abincin,
Amrah ta kalleshi da kyau tace
"Ina son in yi maka wata tambaya sai dai ban son kaga ban ji kashedin da ka yi mani ba"
Nazir ya kalleta ya yi Yar dariya yace,. "Nasan mi ke cikin zuciyarki ko baki fad'a ba don haka ki
adana tambayarki sai gobe wannan lokaciin bacci ne ko ke babu gajiyar tafiyar a jikinki?"
Amrah ta b'ata fuska tace,. "Wai me yasa kake kaucewa ne idan na yi maka maganar Sadiya?
Naga banji motsinta ba har yanzu shiyasa na so in tambayeka"
Ya b'ata fuska ranshi a b'ace yace,. "Bana son ko sunanta inji an fad'a shiyasa kika ga bana
son maganar tashi ki je ki yi wankan ki zo in maki tausa don nasan a gajiye kike ya fi maki da
wannan tonon zancen da kike"
Ya mike ya ya d'auki Umar ya je ya kaiwa Inna shi sannan ya dawo ya taradda ita a inda ya
barta ta yi tagumi tana nazarin maganar tashi, ya kalleta ya b'ata fuska yace
"Ki ma cire wannan tagumin ki tashi ki yi abunda ke gabanki in don macen da ta so ta sakamu
kuka"
Ya saka hannu ya d'agota ta mike cikin sanyin jiki ya taimaka mata ta cire kayanta suka nufi
toilet, tare suka yi wankansu wanda ya d'auki lokaci suna wasanninsu na masoya sannan suka
fito dukansu suka bi lafiyar shimfida makale da juna Amrah sai juye juye take yi saboda
tsananin gajiyar da ke jikinta, Nazir sai dariya yake yi mata yace
"Ashe shi Naziru Matarshi raguwa ce"
Ta b'ata fuska ta turo baki tace
"Wannan doguwar tafiya ai dole jiki yayi ciyo ni fa ban tab'a yin irinta ba kaf rayuwata"
Nazir ya lakuce mata hanci yace,. "Sai gashi yanzu kin biyo Mijinki Uwa Duniya"
Amrah ta harareshi ta rufe idonta ta yi shiru kamar mai bacci ya janyota jikinshi yace
"Ki jira ki yi excersice mana ko da zaki ji jikin ya warware makk"
Ta fara tureshi amman duk da hakan bai hanashi neman hakkinshi ba, sai da ya gano dai da
gaske bata so ne ya hak'ura ya koma yi mata aikin tausa har tayi bacci Sannan shi ma ya baje
suka yi ta baccinsu mai cike kwanciyar hankali da gajiya.
Asubar farin ya tashi ya tada ita ita ta yi toilet shi ya nufi masallacin da ke unguwar ta su ,
bayan sun k'are sallahr ne ya nufi d'akin Inna ya yi mata ina kwana don ka'ida ne kullum idan ya
dawo sai ya biya ya ga kwanansu sannan ya koma d'akinshi.
Ko yau hakan ce takasance suna k'are gaisawa ne ya nufo d'akin Amrah, inda ya taradda ita
kwance akan sallayar ta dunk'ule cikin Hijab sai baccinta take yi, ya yi dan murmushi ya janyo
filo ya ajiye kasan sannan ya tallabota ya d'ora akan filon shima ya kwanta ya d'ora nashi kan
suna fuskantar juna ya fara fesa mata iska a ido, ta yi saurin bud'e idanuwanta suna kallon juna
Ido cikin Ido tace
"Barka da safiya Mijina"
Nazir cike da jin dad'in maganarta yace,. "Barka juna Matar Nazir da fatar kin tashi lafiya?"
Ta yi masa wani kallon kauna tace,. "K'alau Kai fa?"
Ya dan b'ata fuska yace,. "Ni dai kam ba lau ba tunda har banji d'imin Babyna ba"
Amrah ta zunburo Baki tace,. "Wai kai me yasa baka gajiya ne kullim dai abu d'aya?"
Ya saka hannu ya fara shafo fuskarta ya janyo siririn hancinta yace,. "Saboda yanzu ne nake
yin Angwancin don a cen baya ban karadda komi ba"
Amrah ta zaro Ido tace,. ,"Angwanci da wannan abun?"
Ta k'are maganar tare da d'ora hannunshi akan tulelen cikin nata, ya yi yar dariya yace,. "Ai ko
shi ni ban kawo ta yanda ma nayi shi ba saboda fargabar da take cikin zuciyata a lokacin"
Amrah ta kyalkyale da dariya tace
"Au! cikin mayen bacci ka yi shi kenan aikam dai naga alama"
Ya sake janyota yana Murmushi ya fara aika mata da sak'una kafin kace me sun fad'a dausayin
soyayya ta ma'auratan da suke tsananin son junansu.
Da k'arfe takwas dukansu sun shirya ya taka mata har d'akin Inna ta gaisheta sannan ta kalli
Suwaiba da ke ta faman gyaran d'akin Innar kasancewar taganta babba yasa cikin ladabi tace
"Ina kwana"
Suwaiba tana dariya tace, "lafiya lau Amaryar Naziru"
Nazir ya harareta yace,
"Uwargida kuma Amarya yau dai sai ki nemo masu cin abincinki don nikam girkin Matata zan ci
bazan sake cin jagwalgwalonki ba"
Inna tana dariya tace
"Banda cika baki dai Naziru ka mance irin santin abincinta da ka sha yi sai yanzu ka dawo kana
yi mata godiyar maye?"
Suwaiba tana dariya ta ce
"Kyaleshi Inna ina zaunena daga shi har Matar tashi sai sun nemeni"
Nazir ya nufi hanyar fita yace
"Ni dai bata abun karin namu ta shigo Muna da shi idan kin had'a amman ki sani daga shi
shikenan ba zamu sake ci ba"
Inna tace, "Au baka tuba ba kenan har yanzu?"
Nazir ya fita yana fad'in, " daga yau ne kawai ai Inna"
Dukansu suka saka dariya Amrah dai iyakacinta murmushi bayan fitarshi ne Inna ta kalli
Suwaiba tace,. "Suwaiba yau kinga Mamar Umar ko?"
Suwaiba ta kalli Amrah ta washe Baki tace,. "Naganta Inna Masha ALLAH da ita ALLAH dai ya
basu zaman lafiya? Lalle da gaske Umar ita ya dauko sak! da kama"
INNA ta kalli Amrah tace,. "Amrahtu wannan da kika gani diyata ce saboda yar kanena ce
Mijinta ya rasu bata tab'a haifuwa ba shiyasa na daukota saboda ta taimaka mani da renonshi
tun lokacin da Sadiya ta fita"
Amrah ta ji gabanta ya fad'i amman ta dake tace, "ALLAH sarki sannunmu ALLAH ya jikanshi
da Rahama"
Suwaiba da Inna Suka ce "Ameen"
Amrah ta kalli INNA fuskarta cike da son tambayarta gano hakan yasa Inna tace da ita , "Tashi
ki je ki sallami Mijinki kada yayi latti a wurin aikin nasu" ta Kalli Suwaibar tace, "D'auki abun
karin ki shigar masu da shi"
Amrah ta mike jiki ba kuzari zuciyarta cike da son jin me ya fitar da Sadiya?? Don tasan ko ma
minene ba k'aramiin Abu bane tunda har INNA ta amince Nazir ya rabu da ita, zuciyarta cike da
mamakin abun har ta isa falonta inda kai tsaye Suwaiba ta nufi tsakiyar falon ta ajiye ta fito,
Amrah kam d'akinta ta nufa sai dai bata iske Nazir ciki ba ta fito falon sai gashi ya shigo shima
da shirinshi na fita Office yasha suit ta kalleshi tace
"Ba dai fita zaka yi baka karya ba?"
Ya k'araso wurinta ya rungumota da jakarshi a rataye ya sakar mata kiss a goshi yace,. "Na
makara fa ko so kike yi a bulaleni?"
Amrah ta zare jikinta ta rikoshi har wajen kayan ta zaunar da shi akan d'aya daga cikin
luntsumammin kujerun da aka k'awata falon da su, ta karb'i jakar ta ajiye ba tare da ta ce da shi
kanzil ba ta fara had'a masa abun breakfast d'in ta mika masa, ya karb'a a gurguje ya kammala
ya sabi jakarshi ya fito yana gaba tana bayanshi har d'akin Inna yayi mata sallama suk fito ta
rakoshi har gindin motarshi, tana yi masa ALLAH ya kiyaye har ya fice da tana d'aga masa
hannu, Sannan ta koma d'akinta ta fara karyawar itama amman fa zuciyarta cike fam da tunanin
mafarin fitar Sadiyar, ta yanke shawarar zata tambayi Inna don ita bazata ki fad'a mata ba
kamar yanda shi yake ta shashantar da zancen.
Tana nan zaune tana zancen zucinta sai ga Suwaiba sabe da Umar yasha wankanshi tana
hangoshi sai k'amshi yake yi ta washe fuskarta da Murmushin jin dad'in ganinshi don daman
cen kawaici ne kawai ta yi lokacin da taje d'akin Inna bata ganshi ba, Suwaiba ta k'araso wurinta
ta ajiyeshi gabanta tace da ita
"Ga yarona nan na kawo maki ya tayaki fira"
Amrah tana Murmushi ta rik'o hannunshi tace,. "Nagode dafatar dai ya iya bada labarai ?"
Suwaibar ta kwashi kayan break d'in ta nufi hanyar fita tana dariya tace,. "Kala kala kuwa duk
wanda kike so"
Sannan ta fice AMRAH ta janyoshi ta zaunar dashi akan cinyarta tana k'are masa kallo
zuciyarta cike da tsantsar farin ciki saboda ganinshi Masha ALLAH dashi gwanin burgewa, ta
shafo sumar kanshi da take kwance luf luf da yayi gado irinta fulanin usuli, shi ko sai kallonta
kawai yake yi tayi dariya ta lakuce masa hanci tace
"Ka sanni ne? Miye sunanka"
Shi dai kallonta kawai yake yi da ma yaga ta matsa masa da kallo ne ya sauka jikinta ya dafa
kujera ya mike ya yi ta biyar jikin kujerun ya nufi wajen remote d'in da hango ya dauka, sannan
ya yi zaune yana ta wasa da shi yana ta gwarancinshi shi kad'ai cike da jin dad'i Amrah ta mike
ta daga saman carpet d'in da take ta zauna kan kujerar tana ta kallonshi tana jinta cikin farin
ciki.
K'arfe goma dam Nazir ya aiko da cefane Kai tsaye Suwaiba ta kawo mata suka had'u kitchen
suka fara girkin Abincin, suna yi suna yar firarsu ta rashin sabo da juna har suka k'are ne
AMRAH ta je ta yi wanka tayi sallah Sannan ta nufi d'akin Inna da zummar ta yi mata tambayar
da ke ta yi mata kaikayi a zuciya.
Aiko bayan sun gaisa ne ta kalli Inna cikin d'ar! d'ar! Tace,
"Wai ni ko Inna tunda na zo banga Sadiya ba sai