Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
gashi naji d'azu kince bayan fitarta ne kika
dauko Suwaiba, to shine abun yake ta damuna nace Bari in tambayeki inji"
INNA ta yi shiru Sannann tace, "Nazirun bai fad'a maki ba ashe?"
Amrah tace, "ba muyi maganar dashi ba gaskiya har yanzu"
Inna ta sauke ajiyar zuciya tace, "waton ita Sadiya rudin zuciya da sharrin shedan ya jata da
kuma miyagun abokai da shawarwarin munafukai Yan zuga wad'anda basa son suga ana
zaman lafiya"
Amrah ta yi shiru tana kallon Inna cike da son karin bayani akan zancen nata, gano hakan yasa
innar tace,
"Tun ranar da kika bar gidannan Nazir ya sauya gaba d'aya don ba ita da take Matarshi ba har
Ni nan Naziru sai da ya sauya man akan rashinki da yayi, ita kuma ganin hakan yasa ta shiga
damuwa ta ki barwa zuciyarta ta fara fad'awa kawayenta halin da take ciki, inda wata ta bata
shawarar ta fara shan kwayoyin hana d'aukar ciki don muddin ta fara haifuwa bata janyo ra'ayin
Nazir gareta tun da kurciyarta ba to da ta jagwabe ta fara haifuwa shikenan ita tata ta k'are,
shine ta amince ta fara shan maganin hana daukai ciki, Sannan ganin yanda Nazir yake ta fad'i
tashi akan yaronshi yasa ta fara kishi tana jin haushi, tun bata kulawa har zugar kawaye tasa ta
fara zaluntarshi a b'oye ba Wanda ya sani amman a gabanmu ta dinga nuna masa so Kamar ta
hadiyeshi, ana cikin yanayin ne muka bar Katsina muka dawo nan to anan d'in ma tana had'uwa
da miyagun makotan da ta kulla kawance da su suka k'ara zugata suna nuna mata cewa na
takurata haka kawai in kwaso jiki in biyosu don kawai in zo in takura masu, suka nuna mata ta
bi duk hanyar da zata bi in bar garinnan in koma inda na fito ko da zata samu Nazir ya dinga
bata kulawa fiye da wadda yake nuna Mata, ta biyesu ta fara adawa da zamana har tana
k'ok'arin yi mani rashin kunya sai dai ban tab'a sanar da shi ba don bana son rigima ta bullu a
tsakaninsu, Sabida baya zama kullum idan ya fita tun safe sai k'arfe hudu zuwa biyar yake
dawowa watarana ma har shida ya ke kaiwa kasancewarshi ma'aikacin Banki.
Sai dai shima a dan zaman da yake yi a ranakun hutun mako ya fara korafin shige da ficen da
munafukan makotan suke yi wurin Sadiyar, nice nake hanashi idan ya yi kudurin korarsu sai dai
Ashe a b'oye yaje yayiwa mazajensu magana akan su daina shigo masa gida, amman duk da
hakan ita da taga Nazir ya fita sai ta wanke k'afa ta je wajensu suna k'ara hure mata kunne.
To sai dai shi mutum duk abunda yake yi yau da gobe matuk'ar bai daina ba watarana sai Rana
ta batar masa, don kuwa haka ta faru gareta wata rana ya dawo gida ya taradda ita tana yi man
rashin kunya akan taci zalin Umar na yi magana, Aiko ya fara dukanta da kyar na tabeta
hannunshi na hanashi saboda rantsewar da na yi akan kada ya sake dukanta, to tun daga ranar
rashin jituwa ya shiga tsakaninsu nima ta k'ara k'arfin kiyayyarta gareni don a ganinta Ni na
sakashi ya daketa, don a lokacin Abu kad'an zai sa ta kama Umar ta yi ta dukanshi har sai na
zo na karb'eshi a hannunta, idan na yi magana tace Ni banga barnar da yayi mata ba k'arshe
dai dashi zata fake ta yi ta yaba man bakankanun maganganu amman duk da hakan bana
sanar dashi, ana cikin hakan watarana Umar ya tafi d'akinta bansan me yayi mata ba sai ganin
na yi ta turoshi da k'arfi ya fad'i sai fad'a take yi tana zaginshi ta rufo k'ofar d'akinta da k'arfi, na
zo da sauri na d'aukeshi abun mamaki sai Naga yaro ya langabe mani a jiki yana wani mashalo
gwanin ban firgita, kafin kace me sai ga kumfa ya fara fita a bakin yaro aguje na tallaboshi na
fito na nufi gidan wata Yarinya da ke girmamani sosai a unguwar kasancewarta malamar Asibiti.
Aiko tana dubashi ta karb'eshi da sauri cikin firgici ta ce in biyota, Muka shiga motarta cikin
tsananin tashin hankali muka nufi Asibitin da take aiki, cikin gaggawa aka shiga dashi domin a
bincikeshi don izuwa lokacin har numfashinshi ya fara yin k'asa, Ina nan tsaye Ina ta sharar
kwalla Ina add'ua a raina Sabida gaba d'aya naji tsoro don jikina ya bani kamar yaron ba zai
tashi ba.
An d'auki lokaci mai tsawo sannan yarinyar ta fito tana share gumi fuskarta d'auke da tashin
hankali, ganin yanayin da ta ganni yasa ta fara lallashina akan inyi hak'uri an samu sa'ar shawo
Kan matsalarshi, sai dai cikin tsananin b'acin Rai tace dani
"Inna ya aka yi yaronnan yasha guba???"
Na zaro Ido cikin firgici nace ,. "Guba???"
Ta tabbatar man da lalle guba ce aka bashi yaci Allah ma ya tsare yana da sauran numfashi a
duniya da mai aukuwa ta auku, sai dai tace dole sai anyi masa aiki an cire gefen hanjinshi da
suka lalace.
Na fasa kuka Ina salati ta nuna mani in kwantar da hankalina sun yi masa wata allura kuma
zata kashe duk wata kwayar cutar da ke jikinshi, amman Dole ne sai anyi masa aikin don haka
a sanarwa da Mahaifinshi abunda yake faruwa duk da ba'a buk'atar a ja dogon lokaci.
Ina kuka na ce da ita na baro wayar gida shine ta ce in sanar da ita inda wayar take ita zata je
ta d'auko man sai a Kira Nazirun, na yi mata bayani ta je ta d'auko wayar don tun a cen ma ta
kirashi tana sanar dashi abunda yake faruwa, Aiko sai gashi kusan a tare ma suka iso Asibitin
don tana shigowa yana shigowa shima cikin tashin hankali yake tambayar meye mafari, Ina
kuka na sanar dashi abunda na sani kai tsaye ya saka hannu akan takardar zuciyarshi kamar
ta buga aka shiga da Umar d'akin da za'a yi masa aikin, sai ga Nazir ya kasa dauriya ya fashe
da kuka ya nufi motarshi ya fad'a aguje ya bar Asibitin.
Ashe wai fitowar da yayi dawowa gidan yayi ko da ya zo ya taradda d'akin Sadiyar har lokaciin
a dantse cikin hargowa ya fara Kiran sunanta sai gata ta bud'e tana mutsutsuke Ido alamun
daga bacci ma ta tashi, ba tare da binciken komi ba ya fara kai mata Mari cike da masifa ya yi
mata dukan kawo wuk'a, Sannan ya had'ata da saki har uku kuma ya kira yansanda suka tafi da
ita Ni duk ban ma san ya yi ba Ina cen Asibitin ina jiran tsammani har sai da ya dawo ne yake
sanar dani.
Sai gashi cikin ikon ALLAH aka fito dashi anyi nasarar aikin satinmu biyu a Asibitin aka
sallamomu yaji sauk'i Masha Allah, a lokacin ne nace dashi ya sa a fito da ita ta koma gida
hakanan ai ta lallasu, to kinji mafarin fitar Sadiya"
Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya
Akafta
D/AUTA ce✍
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*Wattpad PrincessDija246's*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 61*
Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya tace,. "Gaskiya abun bai yi dad'i ba ALLAH ya kyauta ya
k'ara karemu da kariyarsa"
Inna da Suwaiba suka had'a baki wajen fad'in "Ameen"
Inna ta kara da cewa,. "Ke ma kanki sai kinyi hankali da wad'annan mutane don kuwa nasan da
sun kyalla Ido sun hangoki za su ce sai sun shiga jikinki, don ba abunda suke yawo dashi a
gidajennan sai gulmace gulmace da kananan maganganu don haka kisan yanda zaki zauna da
kowaccensu, don idan aka d'auke maki wannan yarinyar ma'aikaciyar Asibiti da wasu cen da
ban da basa shiga sabgarsu kusan dukansu haka suke da kananan maganganun"
Amrah cikin jimamin labarin Sadiya da Innah ta bata tace,. "Ni daman cen Inna kinsanni ba
ruwana da shirgin kawaye barkatai, yanzu hakan ma ni ko kawayena wad'anda muka shaku da
su sosai na dad'e basu ganni ba ban gansu ba balle wad'annan marasa aikin yi"
Cikin jin dad'i INNA tace,. "Ai baza'a ce mutum ba zai yi kawaye ba amman dai kasan su wa ye
suka dace kayi huld'a da su?, Don wasu rimi rimi za su nuna suna tare da kai amman idan aka
tona sune gaba gaba wajen zama ayi da Kai, su kwashi sirrinka su je su bazawa Mutane sai dai
ka ji ana kallonka a d'age ana kus kus ana yi maka kallon banza, wani fa don bala'i sai ya shiga
jikinka ya san sirrinka tas abu kad'an zai had'aku fad'a ya je ya dinga fallasa ka mafita d'aya ce
a wannan lokacin da muke cikinshi ka koyi b'oye sirrinka ta kowace hanya, don mutane yanzu
sun zama abunda suka zama fatanmu kawai ALLAH ya karemu da sharroransu"
Su Amrah suka ce "Ameen"
Suna ta tattauna zancen ne aka kira sallahr la'asar kowacensu ta mike suka nufi wajen
arwallah, Amrah Kam d'akinta ta nufa tayi sallah ko da ta k'are ma ta dad'e akan sallaya tana ta
adduoin tsari da sharrin mutum da na aljan, ta yiwa Mijinta da dan yaronta da ya tsallake rijiya
da baya don bancin da ALLAH ya tsare da yanzu ya zama tarihi.
Ta share yar guntuwar kwallarta sannan ta mike ta nade sallayar ta je ta sake yin wanka domin
tarbar Maigidanta, aikuwa sai gashi tana Cikin shirinne ta ji shigowar Motarshi, cikin sauri ta
feffesa turaren ta fito sai dai kuma ta ji nauyin yanda zata fita ta tarbeshi a gaban INNA, dole ta
ja ta tsaya k'ofar shiga falon tana dakon shigowarshi ai kuwa sai gashi ya shigo kai tsaye wurin
Inna ya nufa ya yi mata barka da gida sannan ya dauko Umar suka nufo d'akinta.
Tun kafin ya k'araso ya ji kamshin turarenta da sauri ya shigo falon suka yi arba da juna cike da
tsantsar farin ciki suka rungume juna kowanensu cikin shaukin murnar ganin dan'uwanshi,
Amrah ta karb'i jakar ta yi gaba ya biyota a baya yana faman murmushi har lokacin yana sabe
da Umar a kafadarshi har kuryar d'akinsu, ya ajiye Umar akan gadon ya k'araso wajenta ya
rungumota yace
"Sannu da gida Matata?"
Tana dariya tace
"Kai ake wa sannu Mijina kai da ke dawainiya da mu ka je ka samo ka kawo muna mu ci ALLAH
dai ya k'ara dafa maka akan al' amurranka na yau da kullum, kuma ya kara budi na alkhairi ya
tsare muna kai da dukkan wani sharri ko mi kankantarshi"
Cike tsananin jin dad'i ya ke ta fad'in "Ameen Ameen"
Ta taimaka masa ya je yayi wanka Sannan ya saka kaya zuwa doguwar jallabiyya ya nufi
masallaci kasancewar kiran sallar magrib da aka kira a lokacin, itama ta je ta yo arwallar ta fara
gabatar da tata.
Bayan ya dawo ne suka nufi diny ta zuba masu abinci cike da jin dad'i yake kallonta har ta k'are
ta zauna tace da shi
"Bismillah Mijina"
Ya kalleta yana murmushin jin dad'i yace,. "Na gode Matata Allah ya yi maki albarka"
Bakinta a washe tace
"Ameen"
Sannan suka fara cin abincin suna yar firarsu suna dariya cike da jin dad'i da annushuwa har
suka kammala ta kwashe kwanukan ta fito da su a kitchen ta ajiye, ko da ta dawo ta ganshi a
wajen kayan kallo yana had'awa ta Sami d'aya daga cikin kujerun ta zauna tana kallonshi har ya
k'are ya dawo ya zauna kusa da ita yana latsa remote yana saita tashoshin ta kalleshi da
shaukin sonshi ta langabe a jikinshi ta rik'o hannunshi tace
"Na gode da soyayyarka gareni Yaya Nazir ALLAH ya kara karemu da sharrin mutum da Aljan"
Nazir ya ajiye remote d'in ya kara matseta a jikinshi yana shafar gashin kanta yace,
"Ah yau dai Nazirun Inna ya zama dan gatan maman Umar, to ki adana kalamanki baki ga komi
ba indai akan soyayyarki ce"
Amrah ta mike daga jikinshi ta rik'o hannunshi tace
"Yawwa yaya Nazir in tambayeka?"
Ya k'ara damke hannunta cikin nashi yace,. "Tambayarni yanzu a shirye nike da in amsa maki
tambayoyin ko da ko sun kai d'ari ba cas'in da tara"
Daga shi har ita suka tuntsure da dariya sannan Amrah ta nutsa tunani na dan lokaci ta b'ata
fuska tace, " mi yasa lokacin da na baiwa Jamila sak'o akan ta sanar da kai ina da ciki baka
waiwayeni ba? ka kyaleni har tsawon lokaci ina ta dakon zuwanka gareni gashi a lokacin ana
ta kiran wayarka kullum ba'a samu ba"
Nazir ya sauke ajiyar zuciya ya sake matse hannunta har ta yi Yar k'ara sannan yace,
"Tabbas Jamila ta sanar da ni daga ni har Inna munyi farin ciki da jin hakan sai dai kuma mun ji
tsoron tunkararki ne Saboda halin Mama, shiyasa Inna tace da Ni in d'aga k'afa har ALLAH
yasa idan ta fahimci cikin ta sauko da kanta ta amince da aurenmu in ba haka ba ko tsugunne
bata k'are ba, don bazata tab'a zubar da makaman yakinta matukar dai ba ita ce ta sauko don
kanta ba, to a lokacinne nake yawan kashe wayata don bana son zuciya ta debeni inki bin
umurnin Inna duk da a takure nake kullum addu'ata shine ALLAH ya kawo sanadin alkhairin da
zai mallaka man ke ta ruwan sanyi ba tare da fargaba ko tsoron faruwar wani Abu ba, sai ko
gashi cikin ikon ALLAH Baba Musa waton Baban Jamilu ya kirani yana sanar dani abunda ke
faruwa, sai dai na nuna masa cewa ga abunda ya yi mani shamaki akan kusanto kaina gareki,
na hadashi da Inna suka yi magana ta fahimta suka yanke shawarar a dan d'aga k'afa kafin
muga nasarar da za'a ci ta bangaren ita Mamar, ana cikin hakan ne zaman Sadiya ya k'are a
gidannan ganin hakan yasa Inna ta bani Umurnin in je in dawo dake, cike da jin dad'i na nufi
Zamfara sai gashi cikin nasara na had'u da dattijan kirki mutanen arzik'i masu sanin yakamata
suka bani ke cikin ruwan sanyi ba tare da nasha wahala ba, to kinji dalilin da yasa baki ganni
tun a lokacin da Jamila ta sanar da ni ba"
Amrah ta share hawayenta saboda tuno Zuwaira da tayi cikin sanyin jiki tace,
"Mu godewa Allah tunda har yasa muna da sauran wani zaman"
Nazir ya rungomta jikinshi yana lallashinta yace,. "Insha ALLAHu kuma ba za mu sake rabuwa
ba sai mutuwa ce kad'ai ta isa ko ita don tana dole fatanmu kawai ALLAH ya ara muna lokaci ya
bamu Rai da lafiya mu mori aurenmu idan lokacinmu yayi yasa mu cika da imani"
Amrah tana kuka tace,. "Ameen"
***
Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwar aurensu cikin aminci da kaunar juna, kowane Yana
kaffa kaffa da bacin ran dan uwanshi haka ma ta bangaren Inna suna iya kokarinsu wajen
kyautata mata.
Watan haifuwar Amrah yana kamawa ta haifo santalelen danta mai kama da Umar sak!, Farin
ciki ga Nazir kamar ya take kan jariri Inna kanta ba k'aramin dad'i ta ji ba don wannan haifuwar
da Amrah ta yi ya kara sakata kaunar Amrah Uwa Uba yanda take mutuntata kamar ita ce ta
Haifa ba Nazir d'in ba, hakan yasa ta ji shaawar ganin ta shirya da Zuwaira ko don hankalinta
ya k'ara kwantawa.
Yan Katsina da Zamfara su ma sunyo tattaki har garin Gombe domin tayasu murnar wannan
Haifuwar, cikinsu kuwa har da su Aunty Asabe da itama a lokacin take d'auke da cikinta amman
duk da hakan sai da ta zo don tsananin dad'in da ta ji, Fatima ma da wasu dangin Zuwaira
suma ba'a barsu a baya ba anyi taron suna lafiya aka sakawa yaron sunan Baban Nazir ana
kiranshi da sunan Abie.
Anyi taron suna Lafiya an watse lafiya Nazir ya yi masu goma sha tara ta arzik'i sai murna suke
yi suna yi masa godiya, lokacin da zasu ta fi ne Aunty ta janyo Amrah gefe ta sanar da ita itama
fa tana d'auke da ciki, cike tsantsar farin ciki Amrah ta yi tsalle ta ce
"Alhmdllh Aunty mun godewa ALLAH daman shi ko mi da lokacinshi WALLAHI na yi murna
sosai ALLAH ya wanye Ido lafiya Aunty"
Aunty ta ja mata kunne tace, "to ki dai natsu ki k'ara kula da Mijinki kin dai ga nasara a hankali
sai zuwa take yi cikin rayuwarki, Sannan ki yi ta yiwa ALLAH godiya da ya baki Miji irin Nazir,
abu d'aya ya rage maki yanzu shine ki shawo kan Mahaifiyarki ta fahimci gaskiya don yanzu
haka zancen da Nike maki naji ance tayi aure"
Amrah ta yi narau narau da Ido zata yi kuka Aunty tace
"Kada kiyi kuka ki dai ci gaba da yi mata addu'ar kawai ai ALLAH ma ji rokon bawanshi ne da
sannu komi zai wuce har ma ki ga ya zama tarihi"
Amrah ta share hawayenta Fatima ta k'araso tace da Aunty ta zo ita kad'ai ake jira motar da
zata kaisu ta zo, kasancewar mota biyu Nazir ya dauko masu yan Katsina dangin Baban Amrah
daban ta 'yan Zamfara dangin Zuwaira daban, wad'anda suka zo da motarsu kuma su tafi
abunsu amman duk da hakan bai fasa yi masu alkhairi ba.
Aunty ta yi sallama da Amrah ta fice don tuni an saka masu kayansu a motar, Fatima