Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
zo gidan ba
zumuncinsu iya waya ne, amman yawan wayar da suke YI yasa soyayyarshi ta fara ratsa
zuciyar Amrah, saboda a kullum da shawarwarin da yake bata wad'anda take amfana dasu,
kuma suke k'ara sakata tsantseni da rayuwar duniya, saboda malam nura mutum ne mai kaifin
basira da daddad'an lafuzza masu k'ara cusawa mutum tsoron ALLAH a zuciya.
Aunty Asabe kam taji dad'in wannan zumunci nasu, saboda a tunaninta koda Allah yayi aurensu
matsalar Amrah zata kau har ta zama tarihi.
Mahaifiyarta kam ina wuta ta jefa Amrah ta huta saboda jin haushin sakewar da taga tana yiwa
malam nura, domin acewarta Amrah taci baya sosai matuk'ar ta lalace akan malamin islamiya.
A ranar da malam ya fara zuwa gidan har waje taje tayi masa wankin babban bargo, ran malam
a b'ace yabar gidan batareda ya sami damar ganawa da Amrah'r ba.
Tasha kuka sosai saboda cin zarafin da mahaifiyarta tayiwa malam, ta d'aga waya da niyarr ta
bashi hak'uri mamar ta k'wace wayar tana ta danna masa asharr.
Zama yak'i dad'i a tsakanin Amrah da mahaifiyarta, saboda a sace watarana take fita taje gidan
Aunty su sha firar su da malam hankali a kwance, sai dai idan ta dawo mamar tayita surfa mata
zagi ta uwa ta uba duk da batada masaniyar inda take zuwa.
A ranar da mamar ta gano kuwa tattaki tayi har gidan Asaben taci karo da Amrah da malam a
farfajiyar gidan Aunty suna fira, aiko tayi cikin Amrah da duka tareda jifarta da miyagun kalamai
marasa dad'in ji, ita ko Aunty tatas ta wanketa da soso da sabulu bayan tayi ta jera mata ALLAH
ya isa tafi dubu, akan wannan auren tsiya da take so ta had'a tunda ba itace ta haifi Amrah ba.
Duk da Auntyn taji ciyon abunda tayi mata Amma bata biye ta ba har taci fad'anta ta gaji ta bari,
sannan taja Amrah sukayi gida tareda k'wace mata waya ta b'oye.
Amrah ta shiga k'unci sosai saboda matsin lambar da mamar take yimata, gashi ta rasa wayar
da zata kira malam ko Aunty taji sanyi, ko k'awayenta suka zo kad'a su takeyi subar gidan bata
fita ko'ina daga gida sai gida.
Tana cikin wannan matsin lambar ne wani d'aya daga cikin k'annen baban su Amrah yazo da
sadaki tareda goro ya kawowa mamar, a cikin tuhuma take tambayar na miye ne?, a take ya
sanar da ita sun d'aura auren Amrah da malam nura.
Kwacagiya wannan aure fa akwai k'atuwar sark'ak'iya a cikinshi ku biyoni domin kuji wace
sark'ak'iya ce wannan
Akafta♀️
D/Auta ce⛹♀️
Anya mamar Arah
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 11*
**********************
A zabure zuwaira ta mik'e tsaye tareda yiwa goron da kud'in kallon k'yama tamkar wadda taga
wani k'aton kashi, bakinta yana rawa ta nuna shi da yatsa tace, "Yanzu don kun maidani ba a
bakin komi ba, shine kuka yiman rufa rufa kuka daurawa d'iyata aure ba tareda masaniyata ba,
ai ko wallahi kaf d'inku sai kunsan dani kuke zance idan har ba kuyi gaggawar raba wannan
tsinannen auren ba."
K'anin baban amrah yayi wani murmushi sannan ya fara taku zai bar cikin gidan yace, "Aure
kam ya riga da ya d'auru kuma ba wanda ya isa ya kunce shi, matakin da duk kikaga zaki iya
d'auka bisimillah muna jiraye dashi."
Aiko yana k'are maganar a zuciye zuwaira tayi cikin Amrah dake tsaye tana saurarensu da
duka, a cikin zafin nama k'anin baban ya dawo ya fisge amrah daga wannan dukan
mahaukaciya da zuwaira take yimata, yace da ita taje ta sako hijabinta aiko jikinta yana rawa ta
fad'a daki ta sako hijab ta fito, yace da ita,
"Zo muje gidana ki zauna kafin gobe mijinki yazo ya tafi dake, don bazan barki anan gidan ba
haka kawai ta kassaraki a banza."
Ya saka Amrah a gaba suka fita saboda mamaki zuwaira sakato tayi tana kallon wannan almara
da take faruwa, ta maida kallonta akan goron da kud'in da ya ajiye mata atake wani b'acin rai
ya mamaye dukkan zuciyarta, ba shiri ta jawo hijabi ta saka a guje ta biyosu wanda fitowarta
yayi daidai da tashin mashin d'inshi goye da amrah dake ta sharara kuka, zuwaira itama bata yi
kasa a gwiwa ba ta bisu da gudu tana kiran atare atare, da taga ba wanda ya kulata ta fad'i a
tsakiyar titin tana wani bajimin kuka, mutane suka taru akanta ana tambayarta lafiya? me ya
faru?.
Saboda tsabar bak'in ciki kasa magana tayi sai gurzar kukanta da takeyi bilhak'k'i tamkar wadda
akace za'a zarewa rai a lokacin, da taga mutane sai tururuwar zuwa kallonta sukeyi, saboda
d'an k'aramin go slow d'in da ta had'a a cikin k'ank'anin lokaci, wanda har mutane sun fara zage
zagen tare masu hanya da aka yi, jiki ba kuzari ta yunk'ura ta shige gida tareda jawo wayarta
jikinta yana bari ta dannawa Aunty Asabe kira.
Bugu d'aya biyu har ta tsinke batareda Auntyn ta d'aga wayar ba, itama kam bata daina kira ba
har sai da taci nasarar da aka d'auki wayar, jikinta yana rawa saboda masifa ta fara magana,
"ALLAH ya isa tsakanina dake asabe wallahi nayi danasanin zuwanki a garinnan, domin idan
ba ke ba babu wadda zata yiman irin wannan tozarcin kuma ace in k'yaleta, amman ko ke kisani
daga yau na datse duk wata alak'ar da kika sani a tsakanina dake, Amrah ce kije na bar maku
ita duniya da lahira keda dangin ubanta, ko mutuwa nayi akayi mata gaisuwata ta karb'a wallahi
ban yafe nonona da tasha ba."
Aunty Asabe bata katse ta ba har ta k'are banbamin masifarta, sannan ta sauke k'atuwar ajiyar
zuciya tace da ita, "Aunty zuwaira ina guje maki ranar danasani saboda nidai aure na had'a
ba zaman banza ba, saboda haka duk wani tsine tsinenki ko d'aya bazai kama Amrah ba
ballanta ni da baki haifa ba."
Zuwaira ta k'ara kufula jikinta yana mazari kamar zata kai duka a cikin wayar tace, "Asabe
ALLAH ya tsine maki albarka dai gwargwado, CIN amanar da kuka yimani kuma wallahi kuje
na barku da ALLAH."
Kif!!!! ta kashe wayar sai huci takeyi tamkar wata kasa, k'anen amrah mai bi mata ya shigo a
cikin tashin hankali saboda labari yaje kunnensa, anga mamar a kan titi tana ta risgar kuka
shine ya dawo gida a firgice domin yaji meke faruwa, ganin yanayin da ya isketa a ciki ne
hankalinshi ya k'ara tashi, a cikin fargaba yace, "Wai mama mike faruwa ne.?"
Mamar kam wasu sababbin hawaye suka zubo mata ta kalleshi da rinannun idanuwanta da
suka yi ja tace, "dangin babanku sun d'aura wa amrah aure da matsiyacin malamin cen da na
tsana batareda sanina ba."
Abba duk da yaji ba dad'i amman sai ya wayance yace, "Kiyi hak'uri mama tabbas basu
kyauta ba yanzu ina ita Amrah.?"
Mamar tayi wani mere murya aciki ciki tace,
"Sun tafi da ita babban gida tunda a ganinsu sun fini iko da ita."
Abba yayi shiru na d'an lokaci sannan yace, "mama fa wannan aure ba haramun bane, kawai
dai hukuncin da suka yanke ba tareda saninki bane basu kyauta ba, duk da shima d'in idan aka
yi duba da k'arfin da suke dashi a kan hakan ba laifi bane a musulunce, saboda haka kiyi hak'uri
ki yafe masu."
Zuwaira tayo cikinsa kamar wata zakanya zata dakeshi, ba shiri ya ja baya yana ta kallon yanda
take ciccika, a wurin zuwaira kuwa Abba ya k'ara tono fushinta ta fara amayar da zantuka
bakinta yana kunfa tace, "Ai dama ni nasan ba goyon bayana zaka yi ba, sabida daman cen
ina sane dakai ai kafi son su dani, to kaima ka tattara yanaka yanaka ka koma wurinsu tunda
har sun fini iko da ku."
Abba salun alun ya fita ya barta tana ta zazzaga ruwan bala'i, tareda tsinewa auren akan kada
yayi albarka.
***
Amrah kuwa tana gidan k'anin babanta musa sai cisgar kuka takeyi ana lallashinta, ganin tak'i
daina kukan ne iyayen suka had'a baki akan cewa da malam nura yazo gobe ya tafi da
matarshi, sannan aka tada gwaggonninta biyu da suje gidan mamarta su kwaso mata kayan
d'akinta aje ajero mata gidan malam nura.
Koda aka je tufafinta ma zuwaira hanawa tayi tareda sauke masu da kwandon masifa kala kala,
da yake suma a jiraye suke da ita haka suka had'u aka yita jifar juna da miyagun kalamai, aka
rabu baram baram suka dawo hannu rabbana ba ko tsinken da suka samu suka d'auko, dole
aka baiwa malam nura hak'uri gameda tarewarta akan ya basu sati d'aya, kafinnan sun
gangand'a sun saya mata kayan d'aki, shi ma suka ce ya nema mata kayan da zata saka kafin
lokacin, aiko a cikin rufin asiri aka tarkato mai taro mai sisi aka sai mata duk wani abunda zata
buk'ata a gidan aure, shima malam nura ya had'o mata kala goma daidai karfinshi suka tattarata
da kayanta suka mik'a ta gidan Nura, bayan an kaiwa zuwaira ita saboda amrah ta rok'eta
gafara, amman saboda miyagun lafuzzan da tayi ta jefawa auren dole ba shiri aka dunk'ulo
amrah tana kuka aka kaita d'akin mijinta, tareda yimata addu'ar neman zaman lafiya da jan
kunne kalakala akan tayi hak'uri da duk abunda ta gani ta baiwa mara d'a kunya.
Bayan kowa ya watse ne malam ya shigo tareda guzurin ledar shi da ya siyowa amaryarshi
kazar ci muyi, aiko bayan sunyi sallah tareda dogayen addu'o'i ga zaman lafiyarsu, suka ci suka
k'oshi malam yazo ya fara share fage wasa ta mik'a yana gaf da fara neman hanyar b'ullewa ya
fad'i sharaf akan gadon yana wani bacci mai nauyin gaske, abun mamaki kuwa sai ga malam
wutsiya a mik'e sai sambatu yakeyi yana kiran sunan amrah tamkar wanda yake kwanciyar aure
da ita.
A cikin mamaki amrah ta k'ura masa kallo ganin yanda yake bacci sharkaf amma bakinshi ya
haukace da sambatun dad'i, bata kawo komi a ranta ba ita a lokacin har dariya ma ya bata
ganin yanda ya rud'e yana kiran sunanta, a cikin ranta tace,
"Watak'ila jiganiyar biki ce tasa ya tara bacci har yaci k'arfinshi haka."
Koda safiya ta waye malam sai jerawa Amrah albarka yakeyi yana godiya, mamaki ya kama
amrah saboda ita dai tasan ba wani abu da ya shiga tsakaninsu, a ranta ta sak'a kodai mafalkin
da yayi ne da ita yake ganin kamar da gaske ne?.
Bayan sun karya ne yace zaije makaranta a cikin farinciki ta raka shi har k'ofar gida, yace da
ita zai aiko da cefane don bazai dawo ba sai k'arfe biyu, sannan ya fara tsokanarta suna yiwa
juna barkwanci sukayi sallama ya fita ta dawo gida, bayan kamar minti talatin da fitar shi sai
gashi ya dawo hannunshi da cefane, da murnarta ta tareshi shima a cike da begenta ya shigo
gidan ba tareda b'ata lokaci ba, ya mamayeta da soyayyarshi mai zafi suka fad'a d'aki ba shiri
daman ita d'okance take da ganin wannan rana, a d'imauce ta saki akala malam ya dinga
sarrafata ta yanda yakeso, amrah tun tana farinciki har ta koma jin zafi ta fara neman ceto a
hannun malam, saboda ya saki jiki ya gwangwaje angoncinshi dakyau sannan ya tsallaketa ya
barta tana ta kuka, bayan yaje ya watso ruwa ne yazo yana yimata sallama akan zai koma,
yace da ita tayi sauri ta tashi ta kimtsa jikinta ga ruwan zafi cen ya aza mata ta gaggasa ko'ina
,sannan yace da ita akwai cefanen da ya bada asiyo a kawo mata yana nan zuwa, a cikin jin jiki
tace dashi, "Wanda ka shigo dashi yanzunnan fa.?"
Yayi murmushi yace da ita, "Eh wancen na fara badawa a siyo da naga zanzo gidan, to
shine naje na siyo wannan kawai don bana son ayi delay d'in kawo wancen ki dad'e baki d'ora
sanwar ba."
Daga nan kwance Amrah tayi masa a dawo lafiya, ya fice yana wani munafukin murmushin, da
shikad'ai yasan ma'anar shi tareda yin wata k'ofa mai sauti.
Babbar buta cike da ruwan zafijama'a wasar fa yanzu ta fara anya anya dai nayi shiru
nidai kada aji mutuwar sarki a bakina ku ci gaba da biyoni domin jin yanda wannan cab'a zata ci
gaba da kasancewa
Akafta
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Ashe zuma kama takeyi k'uda BAKAN GIZO shine yake shanye ruwa*
*BAKON YANAYI shine sabon book dina da ke tafe ba da jimawa ba LITTAFI ne mai k'unshe da
hargitsi rungutsumi tareda nishadantarwa sannan ga fadakarwa kada ku bari a baku labari
BAKON YANAYI takunshi daban yake dana saura *
*PAGE 12*
**********************
Tana nan a kwance tana jinyar jikinta saboda ba k'aramin jin jiki tayi ba, asanadiyyar wannan
sukuwar dokin da malam yayi akanta tamkar da k'eta a cikin lamarin nashi, aikuwa sai zancen
zuci takeyi saboda a ganinta malam huce haushin tuzurantakarsa ne yakeyi akanta, amman
duk da haka ta jinjinawa k'ok'arinsa sosai saboda ya tabbatar mata da cewa, tabbas shi
cikakken namiji ne wanda a ko'ina za'a nunashi a fad'in duniyar nan, shiyasa a lokaci d'aya ta
k'ara jin k'aunarshi ta mamaye lungu da sak'o na zuciyarta.
Tana nan a kwance tana ta wannan tunanin zucin sai ga wani yaro ya shigo gidan, rik'e da
cefane a hannunshi sai rafka sallama yakeyi Amrah tana jin wannan sallama wadda tak'i
k'arewa, a daddafe ta yunk'ura ta tashi zaune ba shiri ta cije baki tareda runtse idanuwa, a
dalilin wani irin zugi da ya ziyarci k'asanta ta saka hannu ta dafe gado, sannan ta lallab'awa a
hankali ta mik'e tsaye ta fara taku bakinta a cije tamkar wata mai koyon tafiya, dak'yar ta samu
ta bud'e murya ta amsa sallamar saboda yawan nanata sallamar da yaron yakeyi.
A cikin dubara ta saita tafiyar taje ta karb'o cefanen tazo ajiyewa ne idonta yakai inda ta bar
d'ayan cefanen da malam yazo dashi tayi murmushi, saboda tuno lokacin da dukansu suka fita
a hayyacinsu suna neman hanyar da zasu gamsar da junansu.
A cike da nishadi a zuciyarta taje ta d'ebo ruwan zafin da har sun fara tafasa taje tayi wanka
bayan ta gasa jikinta sosai sannan taji k'arfin jikinta, a gurguje ta fara d'ora sanwa kala biyu
saboda cefanen da aka kawo mabanbanta, d'aya tayi shinkafa da miya da salad yayinda d'ayan
cefanen tayi tuwo da miyar taushe,tareda taimakon k'anwar malam da tazo wurinta mai suna
jamila, bayan sun k'are taje ta feso wankanta ta cab'a kwalliyarta gwanin burgewa, k'anwar
malam sai satar kallonta takeyi saboda ganin tsananin kyawon da tayi.
Amra kyakkyawa ce son kowa k'in wanda bai samu ba, suna nan suna fira da jamila bayan
sunci abincinsu sun k'oshi, sai ga malam ya shigo da sallamar shi fuskarshi cike da annuri
saboda ganin kwalliyar da amaryarsa tayi masa, bayan sun gaisa da jamila ne ta fara shire
shiren barin gidan amrah tace da ita ta wuce da abincin da za'a kaiwa mahaifiyar malam,aiko ta
d'auki kular tayi masu sallama ta fice, malam ya kai dubanshi ga amrah da take ta jin kunyar
had'a idanuwanta dashi, don ko sannu da zuwan da tayi masa bata bari idanuwansu suka
had'u ba, saboda tsananin kunyarshi da take ji musamman idan ta tuno abunda ya faru a
tsakaninsu dazu.
Malam dai sai kallonta yakeyi tana jera masa abinci a gabansa yana jin dad'in sa'ar da yayi na
aure kyakkyawar mace irinta, uwa uba ga hankali da sanin yakamata tareda sanyin zuciyar da
take dashi, amrah ta k'are jera masa kulolin abincin tareda janyo plate ta zuzzuba masa abincin
duka kala biyu d'in, sannan tace dashi, "bisimillah."
Malam kam da idanuwanshi suna kan Amrah'r bai masan me takeyi ba, saboda ya riga ya
shagaltu da ganin amaryarshi kyakkyawa maganar da tayi ce ta dawo dashi daga santin ta da
yakeyi a zuciya, anan take k'amshin abincin ya daki hancinshi ba shiri ya kai kallonshi akan
abincin da ta zuzzuba masa, da sauri ya zaro idanuwa a waje yace,
"Lalle ni Nura d'an gata ne abinci har kala biyu duk ni kad'ai?, cab lalle kafin nan da wata d'aya
ma ni na fara ajiye tumbi, amman ke kam kodai yaron da na aiko ne bai kawo cefanen da wuri
bane shiyasa kika aika aka siyo wani.?"
Amrah da sauri ta d'ago fuskarta tayi mashi kallon ido cikin ido, zuciyarta a cike da mamakin
wannan magana ta malam nura ta ma kasa magana saboda jin wannan maganar da tafito a
bakinshi, a cikin d'inbin mamaki tace dashi, kana nufin bakasan lokacin da ka shigo gidan ka
kawo shi ba.?"
Ta k'are maganar a cikin dariya saboda tuno a yanayin da ya shigo tamkar wanda aka koro da
d'inbin shaawarshi a cikin k'wayar idanuwanshi, malam yayi murmushi yace, "Eh nine ko" ba
tareda ya k'ara tofa wata magana ba sannan ya fara cin abincin a hankali,