Bakan Gizo Compelet Book

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 44

33K to 36K   out of 129.9K words

"Yau ma tafiyar zakayi ba tareda ka jira k'anwarka ba?" ya waigo ranshi a
b'ace yace, "Haba Inna kinfa san Jamila bak'ar Nawa (ganda) ce da ita haka kawai tasa
mutum yayi latti a dake shi a banza." ya k'are maganar cikin had'e fuska, Mahaifiyarshi wadda
naji ya kira da suna Inna ta k'ura masa kallo cike da takaici tace,

"Ai in baka jirata anan ba sai kaje inda kaine zaka jira har ma a saka ka aikin da zai janyo
makka lattin."

Nazir ranshi a b'ace ya kalli kanwarshi da ba zata wuce shekara shidda ba, dake ta cin
d'imamen tuwonta yace, "WALLAHI kika yarda na isa gidansu Amrah baki shirya ba, ni ba
jiranki zanyi ba don ma ki sani." yana k'are fad'ar maganar ya tusa kanshi zai fita NE
Babanshi ya fito daga d'akinshi yace, "Saboda saurin kaje gidan Malam bukar yau har kud'in
taran ka manta kenan?" ya k'are maganar yana 'yar dariya sannan ya kalli Jamila dake ta guma
lomar tuwonta yace, "Ke kuma kiyi sauri ki k'arasa kar kuje kuyi latti." Jamila ta mik'e tsam
ta wanko hannunta tace, "Ni nama k'oshi ai" Innar tasu ta tsiyaya mata kunu a wata gora
ta mik'a mata Baban ya basu kud'in taransu, kasancewar Nazir ne ya fara karb'ar kud'in ana
bashi yace dasu "ya wuce" suka bishi da addu'ar "a dawo lafiya" Jamila kam sai da ta tsaya
saka sucks da sandal d'inta sannan ta rataya jakarta ta bishi da gudunta, koda ta fito har ya
shige gidansu Amrah, da sallamarshi a baki ya shiga gidan, inda ya taradda lokacin ma aka
k'are yiwa Amrah wanka, ta fito da gudu zuwa d'akin Mamarta tana yarfa hannu, Nazir ya
kalleta yana 'yar dariya yace, "Lalle ma to kiyi sauri dai kada muyi latti yarinya" sai ga
Zuwaira ta fito daga bayin tana ajiye bokiti tace, "A'a Nazir har an fito to bari inyi sauri in
k'arasa shiryata sai ku tafi" ya d'an sosa kanshi yace, "Ba damuwa Mama ina kwana?"
Tana amsa masa ta shige d'akinta da sauri tana shiryawa Amrah,Sai dai Zuwaira daga cen cikin
d'akin tace dashi "Don ALLAH Nazir zubar man da sharar nan kafin in k'arasa shiryata." Aiko
ya ajiye jakarshi ya sungumi sharar yaje zubarwa ne sai ga jamila ta fito daga gidansu, tana
hangoshi yana zubar da shara ta rufe bakinta tana dariya, yayi kamar bai ganta ba ya dawo ya
ajiye abun sharar yana kakkab'e jikinshi da wani k'aramin hankacif d'in dake hannunshi, ta shigo
gidan da sallamarta ta tsaya tsakar gidan tana jiran Amrah'r ta fito su wuce.

Sai ga Amrah ta fito d'akinsu da hijab a hannunta tana saka sandal d'inta da sauri sai rawar jiki
takeyi, Nazir ya kalleta yayi dariya yace, "Kiyi a hankali fa kar kije ki fad'i kawo hijabin in saka
maki." ta mik'a masa bayan ta k'are saka sandal d'in yana cikin saka mata tana 'yar dariya,
sannan Zuwaira ta fito da jakarta ta mik'a masa tareda kular abincin Amrah duka, idonta yakai
kan Jamila dake rakub'e jikin gini tana kallonsu, tana 'yar dariya tace. "A'a D'iyar Inna an fito?"

tace "Eh ina kwana?" tace "Lafiya k'alau" ta k'arasa maganar da kallon Nazir tace, "Yau ma
dai kam Amrah bata da kud'in tara, GA dai abincinta nan sai ta ci in an tashi break " Nazir ya
ri'ko hannun Amrah yace, "Ba komi ai sai in bata nawa zo muje kar muyi latti, mun tafi sai
mun dawo" Zuwaira ta bisu tana yi masu ALLAH ya tsare hanya har k'ofar gida, sannan ta
juyo tana 'yar dariya tace, "Ai tunda kana bata ni nawa sun huta sai in k'ara a dashena da nike
zubawa d'an kullum."

Nazir kam goye yake da tashi jakar a baya sannan ya rik'o kular Amrah da hannu d'aya, ya rik'e
hannunta da d'ayan hannun suna tafiya Jamila tana biye dasu a baya, sai sunyi mata nisa ta
biyosu da gudu tana fad'in, "Dob ALLAH yaya Nazir ku jirani" Nazir ya juyo ya maka mata
wata k'atuwar harara yace, "Idan bazakiyi sauri ba WALLAHI bazamu jiraki ba, raguwa kawai
sai shegen son jikin tsiya, amman in wajen CIN abinci ne lomarki tafi ta kowa auki."

Amrah ta juyo tana yimata dariya haka suke tafiyar har su kai makarantar, kasancewar ba wata
tazara ce dasu sosai ba, don da sun fito kwararon gidansu Titi kawai zasu tsallewa sai
makarantar.

kasancewar Makarantar had'e take da Primary da secondary, shiyasa idan ya kai Amrah ajinsu
ya mik'a mata kularta sai shi ya wuce sashensu na 'yan secondary, da kuma an tada su Amrah
break indai ya manta bai bata kud'in tarar ba, to duk dabarar da zaiyi sai ya fito ya kai mata
kud'in koda ko ace da malami a ajinsu.
Shi kuma ba ya fitowa ma break saboda yasan baida kud'in da zai kashe, haka zaiyi ta zama a
class har sai an dawo aci gaba da karatu, sai dai wani zubin idan abokanshi sun ja shi dole ya
fito in har sunada kud'in su bashi ya siye abunda yake so.

Idan aka tashi kuwa don su Amrah ake riga tashi kasancewar akwai yara da yawa 'yan
unguwarsu, sai su had'u su tafi tare gida gaba d'aya, amman fa duk wadda tayi gangancin
tab'a Amrah da ya dawo makarantar sai ya biya gidansu ya tambayeta, dawa dawa suka
daketa ita ko tayita lissafo masa su ko d'aya bayan d'aya, duk sai ya rama mata dukanta koda
ko da Jamila a ciki, shiyasa da yawa ma basa tab'ata don sun san sauran, don da a daki Amrah
gara adaki Jamila sai goma yafi son haka da a tab'i lafiyar 'yar gaban goshinshi.

Shiyasa wani zubin Inna take yi masa fad'a kamar ta dake shi, duk ko da take mace mai sanyin
hali amman watarana Nazir sai ya janyo tayi ta fad'a kamar taci babu, Musamman idan yazo
dukan Jamila akan ta daki Amrah, har sai dattijuwar nan mai kosai taji ta zagayo tana bata
hak'uri, saboda katangarsu a had'e take indai ka d'aga murya dole ne a jiyo sautin juna.
Nazir kam ranar ma hakan ce takasance ya manta shaf bai bata kud'in ba sai da yaji an tada
su break, sannan yace da malaminsu dake ta rubutu a allo, yana son yaje ya kaiwa kanwarshi
kud'in taranta, Ba tareda ya waigo ba yace dashi minti biyu ya bashi idan ya wucesu jikinshi zai
gaya nasa, aiko da sauri ya fito yana ta rabon idon ta ina zai hangota, sai cen ya ganta rakub'e
jikin k'arfe k'ofar ajikinsu tana kuka, da sauri ya k'araso ya kira sunanta yace, "Wa ya dake

ki?" Amrah ta fara goge hawayenta da hijabinta tace, "Kowa da kud'inshi yana ta kashewa ni
kad'aice ba'a bani ba"

Ya dafe goshinshi yace, "Kash kiyi hak'uri kingansu nan mantawa nayi ban baki ba, karb'i kije
ki sayi duk abunda kike so kar ki baiwa kowa kinji?" ta d'aga kanta cikin murna ta karb'e kud'in
ta ruga da gudu wurin masu sai da kayan k'walam, ya bita da kallo zuciyarshi cike da tausayinta
sannan ya koma class, shigarshi ajin keda wuya Malamin ya katsa masa tsawa akan ya fita
waje ya durk'usa, ranshi ya b'aci sosai yak'i bashi hak'uri ya dawo k'ofar ajin ya duk'a, saboda
Nazir ba dai Zuciya ba ko kad'an baya da hak'uri matuk'ar ba akan Amrah bane, haka yayita
zama wurin har malamin ya gama karatun, ya fito da bulalarshi ta dorina yayita jibgarshi har sai
da yayi masa bulala goma sannan yace dashi ya tashi ya biyoshi Office, Nazir kan duk da yaji
zafin bulolin amman saboda kafaffiyar zuciya yak'i yin kuka, ya biyoshi Office d'in ya duk'a yana
jin rad'ad'in bulolin a jikinshi, Malamin ya ajiye littafan dake hannunshi saman benci, sannan ya
zauna yana kallonshi ido cikin ido yace dashi, "Nazir me yasa kake son wasa da karatu ne
duk da k'ok'arin da kake dashi?, na fahimceka a duk lokacin da nike yi maku karatu sai kayi
dabarar fita ka dad'e baka dawo ba, shin karatun ne nawa baka buk'ata ko kuwa dai a'a da
gangan kakeyi karatunne gaba d'aya baka buk'ata ?" Nazir ya duk'e ba tareda yace dashi
k'anzil ba saboda zuciyarshi ta kawo wuya, duk maganar da zai fad'a a lokacin ba mai dad'i
bace, har sai da Malamin ya k'ara cewa, "Kana da zuciya sosai na fahimta, amman kuma
sam baka gudun b'acin ranta, shin dolene sai kai za'a baiwa kud'in tarar k'anwarka?me yasa ita
baza'a bata abunta a hannunta ba sai kai dole?, da za'a ce a kullum sai ka shigo aji sannan ka
fita zuwa kai mata kud'i" sai a lokacin Nazir yayi jarumtar magana yace

"Mantawa nayi" Malamin yayi saurin fad'in, "To daga yau na tuna maka wajibi ne ka bata
kud'inta tun kafin ka shigo class, don matuk'ar ka sake na ji kace fita zakayi sai jikinka ya gaya
maka tashi kaje amman ka sani wannan shine last warning da zanyi maka"

Nazir ya mik'e ya fito yana gunguni aranshi yana fad'in, _"WALLAHI sai dai akasheni bazan
fasa fitowa na bata kud'in ba matuk'ar dai na manta ban bata ba, haka kawai sai in barta tayita
kuka abanza wallahi bazai yiyu ba sai dai ku tanadi wuk'ar yanka ni. "_

Haka ya dinga zancen zucinshi har zuwa class d'insu, inda suma abokanshi suka yo masa caaa
akai suna fad'a masa gaskiyar abunda yakeyi ya daina, dukansu ba wanda ya kula don idan ya
biyesu damben tsiya ne zai rabashi dasu, ya janyo littafinshi ya CI gaba da cofe rubutun dake
allon, Wani abokinshi mai suna Jamilu da tunda aka fara dukanshi ranshi ya b'aci yaji ba dad'i,
yayi tagumi yana kallonshi kasancewar kujerarsu d'aya da Nazir, haka ma unguwarsu d'aya
dashi sai dai akwai gidaje a tsakaninsu sosai, cikin sanyin Murya yace dashi

"Yanzu shikenan Nazir haka ka zab'arwa kanka?, baka da aiki sai na bautawa Zuwaira da
'yarta? WALLAHI kayiwa kanka karatun tanutsu shikenan kai ka zama bawansu, har kud'in
taranma don mugunta bazasu bata ba kaine zaka dinga bata wanda ake baka daga gida?"
cikin fushi Nazir ya d'ago daga rubutun da yake yi yace, "Shin wai kai Jamilu meye naka a
ciki ne?, ina ga kud'ina ne ko kuma duk abunda nikeyi ba damuwar kowa bace, idan ba zaku iya

zura ido kuyi kallo ba to don Allah ku daina tankani aduk abunda kuka ga nayiwa Zuwaira ko
'yarta, ni naji na gani ku bari dani don ALLAH ba ruwan kowa, ya kukeso inyi da rayuwata ne?
yanzu fa koda na fita na tarar da ita tanata kuka fa, to don kawai in farantawa wani zan barta
tayi kuka akan abunda banfi karfinshi ba?to WALLAHI bazai yiyu ba kaji na fad'a maka, da
Amrah tayi kuka gara duk mutanen garinnan gaba d'aya suyi tayi WALLAHI." yana k'are fad'ar
maganar ya fisgi littafinshi yaje wata kujera ya zauna yana ci gaba da rubutushi, Zuciyarshi sai
zafi take masa saboda ganin yafi kowa sanin abunda ya dace.





Tofakuci gaba da biyoni sannu a hankali har muje inda muke son kaiwa�




Akafta




D/Auta ce

*BAKAN GIZO*

*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*I love you all my fan's*



*PAGE 23*



Koda aka tashi School Sai da Nazir ya biya ta gidansu Amrah, Zuwaira ta bashi kayan miya

yayo mata markad'e sannan yayi gida, inda shigarshi gidansu keda wuya yaci karo da Inna a
bakin k'ofar d'akinta tana sanya hijab, aiko tana jin sallamarshi cike da jin dad'in ganinshi tace

" Yawwa daman yaron da zai siyoman man k'uli nike nema, tun d'azu na k'are abincin ina
jiranka ka dawo ka siyo a soya muci abinci" Nazir ya b'ata fuska yace, "Haba Inna daga
dawowata kofa SALLAH banyi ba gashi itama Mamar Amrah yanzu na dawo kai mata
markad'e" Inna tayi sakato tana kallonshi rik'e da kud'i a hannu tace, "Eh lalle tunda Mamar
Amrah ta fini ai dole ita kaje nata aiken ni kuma nawa da zai amfane mu duka ka nuna baka son
zuwa, to WALLAHI idan baka siyo shi ba yau bazaka ci abincin gidannan ba." ya karb'i kud'in
fuska a had'e ya bud'a d'akinshi ya ajiye jakarshi tareda cire kayanshi ya sauya wasu, sannan
ya fito fuu ya fice gidan Inna tana nan inda take har lokacin cike da jimamin wannan hali na
Nazir, ace shi indai ba abunda ya shafi gidansu Amrah bane ko ma menene sai rayuka sun b'aci
kafin yayi abu a gidansu, ko da ko abunnan wanda zai amfaneshi ne ko, 'yan mintuna a tsakani
sai gashi ya dawo ya ajiye mata man ya d'auki buta yayi arwallah ya nufi k'aramin masallacin
dake unguwar tasu.

Bayan INNA ta soya man ta zuzzubawa kowa sannan ta zauna suna cin abincin ita da Jamila,
sai ga Amrah ta shigo gidan ganinta yasa Inna ta k'aro abincin suka zauna duka su uku suna
cin abincin a kwano d'aya, suna tsaka da cin abincin ne Inna ta Mik'e domin kawo masu ruwan
sha, abu ga k'urciya Amrah ta d'ebo loma jamila zata kai bakinta Jamila ta k'wace da k'arfi tace
bazata ci shi ba, sai gashi aka yi dace wajen kwacewar akaifar Jamila ta yanki Amrah kad'an a
hannu, aiko tana k'yalla ido taga wurin yad'an fasa kad'an har sawun jini ya fito, aiko ta k'walla
k'ara tana kallon hannun, wadda yayi dai dai da shigowar Nazir gidan da 'yar guntuwar
sallamarshi.

Inna tace "Haba Jamila me kika yi mata daga tashina yanzunnan?" Nazir ko yana zuwa bai
yi wani jinkiri ba ya fallawa Jamila Mari, da sauri Inna ta k'araso wurinsu tace, "Kai kuma me
tayi maka daga shigowarka?nifa bana son cin zalin" Nazir yana rik'e da hannun Amrah inda
take nuna masa yace da Inna,
"Ji fa don ALLAH Inna yanda ta ji mata ciyo a hannu" ya kalli Jamila yace, "WALLAHI kika
sake ji mata sai na rama mata kema kiji inda dad'i, bak'ar muguwa kawai haka kawai baki da
aiki a kullum sai zaluntar yarinya." yana k'are fad'ar maganar ya janwo hannun Amrah suka fita
k'ofar gida suka zauna a kan dakalin k'ofar gidansu yana lallashinta, sannan yaja hannunta
suka tafi wani shagon dake unguwar tasu, ya fiddo kud'in da Jamilu abokinshi ya bashi yayi
break baiyi ba, ya siyo mata minti da biscuit suka dawo yace ta shiga gidansu, sannan shi ya
koma gida inda ya tarar da Inna zaune tana lallashin Jamila, don bashida kunya ya nufi madafi
ya d'auko kwanon abincinshi, zai shige d'akinshi ne Inna ta kira sunanshi fuskarta a had'e
alamun ba wasa, jin yanayin sautin muryarta yasa yayi saurin juyowa, don duk abunshi baya
son ganin damuwa akan fuskarta, shiyasa ya dawo ya janyo kujerar tsugunno ya zauna sannan
ya ajiye kwanon agabanshi ya ce "don ALLAH Inna kiyi hak'uri WALLAHI kema kinsan
Jamila bata jin magana, haka kawai tayita dukan 'yar mutane ko bata yi mata komi ba"

Inna tayi masa wani kallo sannan tace, "To me yasa bazaka dinga yin adalci a tsakaninsu ba,
ai watarana agaban idona Amrah take tsokalar Jamilar, sai dai inji kace tayi hak'uri don nikam
ban tab'a ganin ka doketa kan tayiwa Jamila wani abu ba." yayi 'yar dariyar rashin gaskiya
yace, "Ni dai Inna don ALLAH yanzu kiyi hak'uri, nayi laifi ki yafemani ai kin yafe man ko
Jamila." Jamila dake kan cinyar Inna tana sharar hawaye ta yi saurin girgiza kai alamun bata
yafe ba, gaba d'aya suka saka dariya sannan ya d'auko spoon ya fara cin abincin, Inna tana ta
nusar dashi abunda yake bai dace ba, yayita bata hak'uri abu ga d'a da uwa atake suka shirya
suka koma firar duniya, har ya k'are cin abincin yasha ruwa yace da Inna shi zai fita ya d'an
lek'a gidansu Jamilu suje Kasuwa wurin Babanshi, in akwai wani aikin da zasuyi su sami d'an
na kashewa a kasuwar, tayi masa addu'ar Nasara da fatan adawo lafiya ya shafi kan Jamila
yace, "D'iyar Inna na tafi in kin yafe man in siyo maki agwalima." tana 'yar dariyar jin dad'i
tace, "Na yafe Yaya Amman don ALLAH kada ka siyowa Amrah ."

12 / 44