Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
tsoron
kada ta daketa, Zuwaira cikin tsananin mamakin da Amrah ta bata tace,.
"Banga laifinki ba don kin watsa man k'asa a ido saboda Namiji ki zab'i ki tozartani a gaban idon
duniya, WALLAHI baki da laifi nice mai laifin tun farko da har na shiga cikin sabgarki, ki je ko
yau kike son ki koma gidan Nazir Hanya a bud'e take amman kisani duk abunda kika yi mani sai
anyi maki don kema ai kin haifa"
Zuwaira ta k'are maganar cikin kuka saboda takaicin da take ji a zuciyarta na abubuwa da
yawa, daman cen k'arfin hali ne kawai take yi amman tana bukatar kukan ko don taji sanyi a
zuciyarta.
A ranar haka suka kwana daga ita har Amrar zuciya ba dad'i don shi kanshi Abdallah tun da ya
fita da safe sai dare ya dawo ya lallaba ya shige d'akinsu ya kwanta, zuciyarshi cike da tsoron
haduwarshi da Zuwaira idan safiya ta waye.
Aiko sai gashi tunda sassafe Zuwaira tana baccin gajiya ko lafiya ma bata isheta ba kwana tayi
juyi saboda ciyon jiki gashi zuciya ba dad'i.
Sai ga Sallamar Mai gidan a k'ofar gida Abdallah ne ya fito yana amsa masa sallamar bayan
sun gaisa ne ya mika masa kud'i yace
"Ka kaiwa Mamarka kace da ita su tattara kayansu su bar gidannan na fasa bata hayar saboda
naji labarin abunda suka yi da wad'anda na baiwa hayar gidan, don haka bazan yarda su je su
kashe junansu a jaza man bala'i ba haka kawai, don haka yau yau d'innan ku tattara kayanku
ku bar gidan tun kafin in zo insa a fito maku da su in baku bi abunda na fad'a ba cikin ruwan
sanyi ba"
Yana kare maganar ya wuce fuuu ya bar Abdallah rik'e da kud'i a hannu, cikin b'acin rai ya
shigo d'akin Zuwairar ya ajiye mata kud'in a gefen gadonta yace
"Ga kudinki nan inji wanda ya baku haya yace ya fasa mu tattara kayanmu mu bar masa
gidanshi don bazai yarda ayi masa kisan kai a gida ba"
Zuwaira ta rik'o hannun Abdallah ta tashi zaune ta Kai kallonta ga kud'in ta yi shiru tana nazari
sannan tace
"Je ka harhad'a kayanka sannan kaje ka samo muna motar da zata kwasar muna kayanmu"
Abdallah ya fita cikin b'acin rai ta bishi da kallo sannan ta mike ta fara had'a kayanta masu
muhimmanci tana fito dasu tsakar gidan.
Amrah ta fito da nufin ta shiga kitchen ta dafa masu abun karin safe ne taga duk sun fiffito da
kayansu a tsakar gidan, cikin mamaki ta leka d'akinsu Abbati taga duk Abdallah ya fito da
kayansu waje, ta dawo da sauri zuwa k'ofar d'akin Zuwairar ta leka ta hangota sai had'a zufa
take tana nishi tana banbare katakon gadonta, cikin mamaki ta shigo daga ciki kad'an ta tsaya
don har lokacin tsoron abunda Zuwairar zata yi mata take ji, cikin rawar murya tace
"Mama lafiya naga anata had'a kaya?"
Zuwaira tana k'ok'arin dauke katakon ta jingine tace,. "Au wai kina nan baki tafin ba? Ai ni na
d'auka tun jiya kin tafin tunda har kin sami damar hakan to zaman me kike yi anan??"
Amrah ta marairece tace
"Kiyi hak'uri don Allah nasan na bata maki bazan sake ba Ina zamu je yanzu nima inje in hado
nawa kayan?? "
Zuwaira a gajarce tace da ita,. "Mai gida ya koremu gidanshi wani gidan hayar zamu je mu
nema"
Cikin jin dad'in faruwar hakan aranta tace,. "Bari nima inje in hado nawa kayan"
Ta fice cikin farin ciki a zuciyarta saboda daman ita zaman gidan kamar a kaya take jinta,
saboda tsoron lafazin matarnan da tace Idan aka nakasa mata idon 'ya sai ta kashesu, kuma
tabbas zata iya aiwatar da abunda ta fad'a saboda kwayar idanunta sun nuna hakan.
Zuwaira sai da ta had'a komi nata ta fito dashi tsakar gidan sannan ta yafo hijabinta ta fito ta
nufi gidan Lantana, abun mamaki Lantana ta matse fuska tamau kamar bata tab'a saninta ba,
cike da mamakinta ta zauna ta kalli Lantanar tace
"Huta da Shan mur unguwar ma zamu bari yanzu saboda maigida ya koremu yace mu bar
masa gidanshi yanzunnan"
Lantana ta dafe k'irji tace
"Ina zaku koma to yanzu??"
Zuwaira tace
"Wani gidan hayar zamu je mu kama ya zancen Alhajin ??"
Lantana cikin ganin samu ta ga rashi tace, "Banda ina jin tsoron ku sake jaza mani abunda
zanyi asarar kud'i ban ci ban sha ba ai da kun dawo gidannan mun zauna tare don dai Kinga
wancen d'akin ya isheki keda 'yarki Abdullahi kuma ko a soron gidan ai zai dinga kwanciyarshi"
Cikin jin dad'in taimakon da Lantana zata yi masu tace,. "Nagode k'awata ALLAH ya bar zaman
tare"
Lantana tayi mere tace,. "Ba fa a kyauta zan baku ba Zuwaira jinga za muyi daku sai mu
daidaita da ku ku biya"
Zuwaira ta maka mata Harara tace
"Yanzu ke saboda Allah bazaki ji kunyar karbar kud'ina ba???"
Lantana tayi shewa tace,. "Yo in kinji kunya sata kenan amman nikam Wallahi zuruf zan karbe
kud'ina in tura aljihu"
Zuwaira ta rik'e baki tace,. "Nawa zan biyaki a shekara??"
Lantana tayi wata yar dariya tace
"Ai tunda ku na gida ne ku bada d'ari da hamsin kawai"
Zuwaira ta maka mata Harara ta yi wani mere tana k'arewa gidan kallo tace,. "A irin wannan
tsukakken gidan kike ambatar wad'annan manyan kud'in??"
Lantana ta b'ata fuska tace,. "Idan kinsan cin fuska zaki yi man ki tashi kije ki sami wani don
Allah bana son renin hankali akan abunda ke ko rabin rabinshi baki mallaka ba"
Zuwaira ta karkace ta zura hannu a kwagirinta ta zaro kud'i ta lissafa ta mayar da sauran ta
mik'awa Lantana kud'in tace
"Ga abunda naji zan iya baki idan har kinji basu yi maki ba to ki bani kud'ina inje in nemi wani
gidan saboda gari da yawa....."
Lantana ta fara lissafa kud'in har ta k'are sannan ta ce
"Naga dubu Hamsin yaushe zaki cika sauran to?"
Cikin b'acin rai Zuwaira ta mik'e tsaye tace,. "Sisi ba zan k'ara maki ba idan ba zaki bar man a
haka ba ki bani kud'ina in tafi"
Lantana ta yi shiru Sannann tace
"Don dai kina ke ku kwaso kayan an ci sa'a ma d'akin a sharenshi yake"
Zuwaira ta juya zata fita Lantana ta bi bayanta da harara tace,. "Kinyi da mai ramawa in dai
nice"
Aiko aka saka baro tun kafin Abdallah ya dawo aka fara jido kayan ana jifgewa har aka k'are,
sannan Zuwaira taje ta zo da dillaliya ta siyi kayan d'akin Amrah suka daidaita ta bada fiye da
rabin kud'in aka fara jidar mata kayan zuwa gidanta, da nufin sauran kud'in sai daga baya zata
bayar sannan suka tattara suka nufi gidan Lantana.
Ba su zauna ba har sai da suka gyara d'akin da zasu zauna a ciki, Abdallah Kam cewa yayi shi
kam bazai kwana a soron gidan ba sai dai in Gidan dangin Babanshi zai koma tare da Abbati,
Zuwaira tana kiranshi ya kinkimi jakarshi ya tafiyarshi ya barta da sharar k'wallah.
Kwanansu biyu a gidan Lantana Zuwaira ta gano cikin da Amrah take ta b'oye b'oye bata so ta
sani, saboda gaba d'aya gidan toilet guda ne ba damar ta b'oye tayi amai idan ya zo mata, dole
dai tsakar gidan zata fito tayi shi idan har ya turnukota dole sai ta yi.
Cikin fad'uwar gaba Zuwaira ta bita da kallon tuhuma sannan ta matso inda take ta tsaya tace
"Yanzu sakayyar da zaki yi man kenan AMRAH??"
Amrah ta fara ja da baya tana bata hak'uri amman duk hakan bai hana ta matso wurinta ta falla
mata wani shahararren mari ba, bakinta yana kumfa tace
"Yanzu don kina munafuka kinsan kina da ciki shine kika b'oye man?? To Wallahi bud'e
kunnuwanki kiji bazan tab'a yafe maki ba matuk'ar kika haife cikinnan don ya zama dole a zubar
da cikinnan ko kina so ko ba kya so, in banda tsabar jaraba ma me ya kaiki sakar masa jiki
daga zuwanki har ya dirko maki wani sabon cikin?? Bayan ko mirmijewa baki yi daga haifuwar
da kika yi ba? Lalle albasa bata yi halin ruwa ba don ni WALLAHI in shekara zanyi da Namiji
bazai d'aga man hankali ba balle har in bashi fuskar da zai dirka man ciki alhali Uwata tana
hakilon rabani da alakakai, to ai daga ke har shi din WALLAHI baku isa ba kunyi kad'an don
kuwa wannan k'addararren cikin sai na zubar dashi a gidannan"
Amrah ta share hawayenta cikin dakiya tace
"WALLAHI bazan tab'a bari a zubar man da ciki ba tunda dai ba shege bane"
Zuwaira ta zaro Ido waje ranta a matuk'ar bace tace
"Yau akan Namiji Ni kike d'agawa murya Amrah???"
Amrah ta janyo hijabinta ta saka zata fita Lantana da ke zaune tana kallonsu ta yi hanzarin
Shan gabanta tace
"Ina zaki je Mahaifiyarki tana yi maki magana?? WALLAHI kiji tsoron ALLAH tun kafin hakkinta
ya kama ki"
Amrah ta galla mata wata jar harara ta murgud'a mata baki tace
"Idan zaki cire son rai da kwadayin abun duniya to kema ki fito fili ki nuna mata abunda zata
aikata ba dai-dai bane, don nasarar da taci a farko ta rabani da yarona da Mijina yanzu kam
WALLAHI bazan tab'a lamuntar hakan ba, yanzu zan je in sanar wa da Yaya Nazir don yaja
hakkinshi matuk'ar aka zubar masa da ciki"
Tana k'are maganar ta zagaye Lantana zata fita ta sake riketa aiko ta fisge da k'arfin tsiya ta
fice, ta kalli Zuwaira cike mamakin Amrah tace
"Ki hanata ta fita fa kar ta je ta b'aro maki aiki"
Zuwaira ranta a b'ace fuskarta a d'aure tamau tace, "WALLAHI bazan hanata ba ki barta taje
duk inda zata je ai zata dawo ne ta sameni don wannan tsinannen cikin Naziru ko da Innarshi
yake kwana saboda tsabar rashin mutunci to bai isa ya hana Ni in zubar dashi ba"
Tana k'are maganar ta saka hijabinta ta fito gidan kai tsaye chemist ta nufa tace da mai tsaron
shagon ya bata maganin zubar da ciki, ya zaro Ido yace
"ciki!?"
Ta k'ara daure fuska tamau tace
"Ciki ko"
Yayi Yar dariya yace
"Bamu da irin maganin anan shagon sai dai ki matsa gaba ko zaki samu"
Zuwaira ta soka hannu a kwagiri ta kirgo dubu goma ta fito da su ta ajiye masa saman katako a
gabanshi tace
"Ko da yafi haka d'in ka d'auki sauran kud'in na baka" ..
Yaron ganin kud'in yaji yana ra'ayin bata maganin sai dai yana jin tsoron wani Abu ya biyo baya
ya jawowa kanshi jidali, cikin dakiya ya shiga kuryar shagon ya d'auko wani kwayar magani
d'aya ya saka a leda ya Mik'a mata yace
"Gashi zan baki amman kisani duk abunda ya biyo baya babu ruwana"
Zuwaira ta karb'a cikin jin dad'i tace
"Bale ma ba abunda zai biyo baya sai alkhairi"
Ta soke maganin kwagirin zata tafi yace da ita,. "To ai ban fad'a maki yanda zakiyi amfani da
maganin ba"
Ta dawo tace..
"Ina saurarenka"
Yaron yace
"Matsashi zata yi a cen cikin jikinta da zarar ya narke zai yi gaggawar fito da koma miye a cikin
mara Koda ko ya Kai d'a biyar ba d'aya ko biyu ba fit! za su fito duka a lokaci d'aya"
Cikin tsananin jin dad'i tayi masa godiya ta koma gida zuciyarta cike da jin dad'in nasarar da tayi
ta samun maganin.
Akafta
D/Auta ce✍
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Jinjinar ban girma gareku masoyana kusani a duk inda kike HADIZA D/AUTA tana alfakhari da
ku tsakanina da ku son so fisabilillah*
*PAGE 53*
AMRAH kam tana fita kai tsaye Napep ta tara ta sanar dashi sunan unguwarsu Nazir, suna tafe
tana kuka har k'ofar gidan sai dai gabanta ya kire ya fad'i saboda hango k'ofar gate d'in gidan
da tayi da k'aton kwado, cikin fargabar abunda take tunani ta fito ta nufi k'ofar gidan ta k'ara
tabbatar da abunda take zargi waton basu nan masu gidan, ta koma Napep d'in cikin tsananin
takaici tace da shi su tafi unguwarsu Jamila Kanwar Nazir domin taji ina zata samu Nazir d'in,
gashi ita ko wayarta ma tana hannunshi tun a kotu da ya shaka mata abunda ya somar da ita,
ya d'auketa ya saka aljihu tun lokacin bata sake ganinta ba kuma shima a lokacin tsoron
Zuwaira ta kirata ta hure mata kunne yasa bai bata ba ya kaita ya b'oye.
Kai tsaye suka nufi unguwarsu Jamila itama abun takaici bata sameta a gidan ba, sai wata
tsohuwa da ta iske da yarinyar Jamilar tana yi mata wasa, cike da takaicin rashin isketa tace da
tsohuwar don Allah ta bata takarda da biro zata bar mata sak'o, tsohuwar ta kalli Amrah tace
"Nikam Yarinya ina naga wata takarda bale biro? Da dai zaki bar sak'on a baki da na fad'a mata
idan sun dawo don sun tafi gaisuwa dangin Maigidan a wani k'auye"
Amrah ta fito tace da Mai Napep d'in ya ara mata biro ko pencil in yana dashi, ya lalaba
aljihunshi ya fiddo wani pencil ya bata yace
"Ga dai wannan shima a hannun wani kanena na karb'eshi"
Amrah ta karba cike da jin dad'i ta nufi wani kwali ta yago ta tsugunna ta yi rubutu a jiki ta bashi
pencil d'in ta koma cikin gidan ta mik'awa tsohuwar tace
"Idan ta zo ki bata kice inji Amrah na zo bata nan"
Tsohuwar ta karb'a ta mik'awa yarinyar tace "je ki kaiwa Mamarki a d'aki"
Amrah ta yi godiya ta fice ta sake shiga Napep d'in tace su tafi gidan Aunty Asabe, aiko tana
sanar dashi sunan unguwar ya cilla Napep dinshi kan titi suka nufi unguwar, cike da jin dad'i ta
fito ta nufi cikin Gate d'in saboda hango gidan da tayi a bud'e.
Cikin farin ciki ta shiga gidan aiko sai gashi ta hango Aunty cikin kuka ta nufeta ta fad'a jikinta,
cike da fad'uwa gaba ta d'agota tace
"Lafiya Amrah? Me ya faru kuma?"
Amrah ta yi jarumtar share hawayenta tace
"Tare muke da Napep Aunty in kina da kud'in bani in kai masa ko sisi babu a hannuna"
Aunty tace da ita "to zauna bari in d'auko maki kud'in"
Amrah ta kasa zama tace, "Bari in Kai masa kud'in dai kafin in zauna don kar yaga an
tsaidashi, saboda munsha yawo dashi sosai"
Aunty ta shiga ta d'auko kud'in ta mika mata ta fita da sauri ta kai masa yabata canji ta dawo ta
mik'awa Auntyn sannan ta zauna tana wasa da yan yatsunta hawaye suna zubo mata a fuska
tana sharewa tana shan majina, Aunty ta kalleta tace
"Kinsani a gaba kina Kuka Amrah meke faruwa ne??"
Amrah ta share hawayenta cikin muryar kuka tace,. "Ciki ne da Ni Aunty kuma Mama tace sai
an zubar"
Aunty ta zaro Ido tare da dafe k'irji tace,. "Ciki ?? Ikon Allah kice dai ke zuri'ar Nazir a jikinki
take? to ke meye na tada hankalinki?? Ki ma kwantar da hankalinki don ma wannan abun da
zata yi ba mai yiyuwa bane, don kuwa ya zama dole ki sanar da Nazir kina da cikin ko don ya
kare cikinshi ya hana Aunty Zuwaira cika wannan bakin nufin nata, don haka ki kirashi a waya
yanzunnan ki sanar dashi kawai yafi"
Amrah ta fashe da kuka tace
"Bani da waya a hannuna yanzu Aunty amman yanzu haka daga gidanshi na fito ba kowa a
gidan, naje gidan Kanwarshi Jamila itama ta fita na bar mata sak'o dai a bata ta sanar dashi ina
da ciki"
Aunty tace ,. "Masha ALLAHU kinyi abunda ya dace amman ya zama wajibi ki je da kafafunki a
Zamfara ki fadowa Baba Nuhu halin da ake ciki, don shi kad'ai ne zai hana Zuwaira aiwatar da
wannan danyen aikin"
AMRAH ta zaro Ido tace,. "Aunty baki ganin kamar Mama zata ga laifina idan na had'ata da
Mahaifinta??"
Aunty ta b'ata fuska tace,. "Koda zata ga laifinki to gara ta gani da dai ace ki zura ido ta zubar
maki da ciki akan wani dalilinta na banza, yanzu ki tashi ba sai anjima ba zan baki kud'in mota
ki je ki fado masa da kanki don bama zan je ba don kada taga Ni na zuga ki, ta zo ta sake ci
man zarafi don wannan karon ba zan kyaleta ba gaskiya"
Aunty cikin takaicin Yar uwar tata ta shiga d'aki ta d'aukowa AMRAH kud'in ta mika mata tace
"karb'i ki tafi amman bari in zubo maki abinci ki ci kafin ki tafi"
Amrah ta karb'a jiki a sanyaye tace,. "Aunty ki bar Abincin kawai Ni zan tafi don kada dare Yayi
mani a hanya sai dai ina ganin Ni bazan gane gidan ba sosai"
Aunty ta yi mata bayani dalla dalla har ta gane sannan ta rakota har bakin titi ta hau Napep
suka nufi Tasha inda kai tsaye ta shiga motar Zamfara, sai tunani take yi a ranta
_"Anya Mama bazata ga na munafunceta ba?"_
Wata Zuciyar tace
_"Gara hakan da ki je ta Kai ki