Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
amma a cikin
zuciyarshi sai tunani yakeyi yana so ya tuno lokacin da hakan ta faru amma ya kasa, shiyasa
ya bar abun a ranshi domin shi a tsammaninshi ko ita amrah'r ce ta bada aka siyo cefanen
shiyasa takeso ta zolayeshi.
Yace da ita ta saka hannunta suci a tare da tak'i ya d'ebo ya kai mata a baki dole ta bud'e
bakinta ya saka mata lomar daga nan suka dinga ciyar da junansu, malam yana cin abincin sai
zuba santi yakeyi amrah tayi masa waigi da wani plate tana yi masa dariya.
Koda suka k'are cin abincin malam ya fara jagulata lungu da sak'o, har sai da ya tabbatar ya
kamata a hannu sannan yayi k'ok'arin jefa k'wallonshi a raga, aikuwa sai ga malam ya tafi luu
yana ta sharar bacci bindi mik'e yana sambatun,amrah kam shirun da taji ne yasa ta bud'e
idanuwa a hankali, domin taga wace wainar ce ta tsayar da malam daga wannan d'imaucewar
da yayi akan son biyan buk'atarshi, aikuwa caraf idanuwanta suka kai akan wutsiyar malam da
take tsaye tsam yana zuba sambatu irin na jiya, aikuwa a zabure ta mik'e zaune tana mamakin
faruwar wannan lamari, domin idan bata manta ba ko ajiya hakan ce ta faru dashi da yayi
k'udurin yi mata tsome, aranta tace, " anya dai ba aljanu suke damun malam ba? To kuma
idan har sune ya akayi yau ya sami lafiyar gwangwajewa da ita.?"
Shiyasa tayi saurin k'aryata hakan jiki a sanyaye ta saka gefen zanen gadon ta rufe masa
al'aurarshi, sannan ta sauko gadon ta mayar da kayanta da yayi cilli dasu d'aya d'aya a cikin
d'akin, sannan ta fara tattara kayan abincin taje takai kitchen, ta fara wanke wanke a
makwararar gidan tana k'arewa ta k'ara gyara gidan ko'ina tas ta feshe da turaren wuta, amma
har izuwa lokacin malam bai tashi daga baccin ba gashi yamma ta gabato, har sai da ta shiga
d'akin ta tarar dashi ya gyara kwanciyarshi kuma ya daina sambatun, sannan ta zauna a gefen
gadon ta cira hannu ta fara shafo fuskarshi tana hura masa iska a idanuwa.
Sannan malam yayi firgigit ya tashi zaune yana kallonta da wani tsadadden murmushi akan
fuskarshi, yace da ita, "Nagode sosai zaujatu Nura 'yar aljannah ina godiya da farincikin da
kike sakani nagode nagode amaryata nikam nafi kowa dace da mata a kaf fad'in duniyarnan
fatana kawai ALLAH ya barmu tare har aljannah."
Amrah taji dad'in wannan yabo da yayi mata tayi fari da ido tana murmushi sannan tace, "kayi
hak'uri na tada kai daga bacci sabida naga marece har yayi shiyasa gashi kuma kasha fad'a
mani ba kyau baccin marece."
Malam ya kai mata sumba yace, "Ai ni kin gama mani komai tunda kike bani abunda yake
sakani manta ina nake."
Amrah tayi saurin rufe fuskarta tana murmushi, a tare suka fito ta raka shi bayi ta taimaka masa
yayi wanka sannan ya shirya ya fita zuwa islamiya, domin yana so yaga abunda yake gudana
acen kasancewar shi malamin da ragamar makarantar take a hannunshi.
Koda dare yayi abincin da ta dafa da rana shi suka Ci har suka kyautar da saura ga wani
almajiri da yayi bara, sannan suka dinga firarsu ta ma'aurata mai cike da tsokanar juna a
tsakaninsu, inda labarin yasha bambam lokacin da malam nura ya nemi ya k'ara komawa a filin
daga, aikuwa 'yar gidan jiya ce ta k'ara kasancewa ya bige yana ta shan barcinshi mai cike da
sambatun kiran sunan amrah'r.
Amrah kam izuwa lokacin abun ya fara bata tsoro saboda ganin wannan hali da mijinta yake
kasancewa, da tunani fal aranta tayi bacci har da mafalkai kala kala wad'anda ta kasa gano
kansu ballantana ma'anar su.
Koda safiya ta waye bayan sun karya tayiwa malam rakiya kamar jiya ya fita, sannan ta fara
'yan aikace aikacenta aiko sai ga malam ya dawo afujajan yana neman hak'k'inshi, ba musu ta
amince masa duk da a zuciyarta tana ta jin tsoron abunda zai faru, aikuwa abun mamaki sai
gashi yayi mata bazata domin kuwa har sai da tayi ta rok'arshi akan yayi hak'uri, saboda ya
gajiyar da ita sosai sannan ya k'yaleta yaje yayi wanka ya mayar da kayanshi, yayi mata
sallama daga kwancen ya fitawar shi.
Yazo k'ofar gidan kenan yana sauri yayi kicib'is da aunty asabe zata shigo gidan, ba shiri
gabanta ya fad'i taja baya ta bashi hanya ya fice tana mai jin nauyin wannan gaf da gaf d'in da
tayi da surukinta, amma abun mamaki ko waiwayo aunty baiyi ba ballantana ya tsaya su gaisa,
aunty ta bishi da kallo a cike da mamakin faruwar hakan domin tasan yanda malam yake
girmamata ba kad'an ba, tun kafin ya auri Amrah muddin ya ganta koda bata kula dashi ba sai
ya tsaya ya gaidata.
Akafta♀️
D/Auta ce
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*BAKON YANAYI book ne da ke tafe da zafin shi kada ku bari abaku labari salonshi daban
yake da saura 200 kacal zata sa ki kasance d'aya daga cikin member ta BAKON YANAYI
*
*KAR KU MANTA LITTAFAN HADIZA D/AUTA*
*Tartsatsi*
*Ruwa da kanra*
*Bakan Gizo*
Sai
*BAKON YANAYI mai take da nashi kalar salo kar ku bari a baku labari sayen nagari
maida kud'i gida*
*PAGE 13*
**********************
Aunty da k'aton mamakinta a zuciya ta shiga gidan tareda sallamarta abaki, Amrah tana jin
sallama tayi saurin tashi zaune ta kimtsa jikinta, sallamar da aunty ta k'ara yi ne yasa ta gano
muryarta aikuwa da sauri ta tako a hankali ta fito d'akin, saboda k'afafuwanta da suka yimata
sanyi saboda ba k'aramar jigatata malam yayi ba, tana k'yalla idanuwa ta hango aunty da sauri
taje ta rungumeta tana murna, auntyn ma taji dad'in ganinta musamman yanayin da taga
tafiyarta, sannan da abunda taji yana tashi a jikin amrah , zuciyarta ta tabbatar mata da lalle
Amrah ta sami lafiya, ta jawo hannunta suka shiga d'akin tana kai dubanta akan gadon ta k'ara
tabbatar da lalle komi yayi zam kasancewar d'aki guda ne k'ato ba falo, a cikin farinciki ta
zauna a kan d'aya daga cikin kujerun dake d'akin tana murmushi tace, "to ya gidan dafatar dai
komi yayi normal.?"
Amrah ta sunne kai tana murmushi aunty ta k'ara tabbatar da lalle zarginta ya zama gaskiya, a
cikin farin ciki suka fara fira a cikin dabara ta tambayeta ko akwai wani laifi da tayiwa malam
shiyasa ya fita yana fushi?, Amrah ta tabbatar mata da lafiya lau suka rabu aunty ta k'ara jin
dad'i a ranta, saboda ganin kwanciyar hankali a tattare da amrah amma zuciyarta bata daina
yimata mamakin akan abunda malam yayi mata ba, ta tsayu akan magana d'aya da cewa bai
kula da ita ba ne , saboda ko a jiya har gida yaje yana ta yimata godiya shiyasa tayi matuk'ar
mamakin abun.
Daga nan suka ci gaba da firarsu a nan ne Amrah take tambayar aunty ko tana da labarin
mamarta?, a cikin damuwa aunty ta fara bata hak'uri saboda tuno zuwan da zuwaira tayi har
gidanta, taci mata mutunci ta uwa ta uba bayan had'a tan da iyayensu da tayi acen garinsu,
Amrah ganin yana yin aunty yasa ta fara kuka saboda jikinta ya bata akwai abunda mamar ta
k'ara yiwa aunty wanda ya b'ata mata rai bayan aurensu, a cikin dauriya Aunty ta saki jiki tayi
ta yiwa amrah bayanan yanda zatayi ta k'ara cafko zuciyar malam, tareda dubaru irin na kamo
kan miji a rik'e jabau har asa shi ya manta sunanshi, daga nan tayi mata sallama ta tafi suka
rabu a cikin kewar juna.
Sannan taje ta k'arasa 'yan ayukanta tayi wanka ta d'ora sanwar rana, zuwan jamila k'anwar
malam yasa ta saki jiki ta cire damuwar dake damunta dangane da matsalar mamarta, suka yi
ta firarsu har malam ya dawo ta tafi gida da kular abincinsu.
Koda safiya ta k'ara wayewa malam ya fita ya k'ara dawowa ya k'ule da amrah a d'aki yana
kwasar gara, bayan ya gama yaje yayi wanka yayi amrah sallama ya fito yana saka talkaminshi
zai fita, sai ga jamila ta shigo gidan da kuzarinta domin tasan malam baya gidan a lokacin,
kawai sai fashi tayi kicib'is dashi a gidan, ba shiri ta zaro idanuwa tana nunashi tace, "ba
yanzu na baro ka makaranta ba yaushe ka shigo gidan ban ganka a gabana ba.?"
Malam ya shak'o wuyanta ya matse ga gini da jajayen idanuwanshi yace da ita, "Kika kuskura
kika fad'awa wani wannan maganar wallahi a ranar zaki bar duniya."
Yana k'are maganar ya wurgata kanta ya bugu da gini ya fice abinshi, to tun daga ranar malam
bai k'ara dawowa a gidan da wannan lokacin ba.
A haka dai zaman nasu yaci gaba da kasancewa har tsawon sati biyu, wanda a 'yan kwanakin
amrah take jin wani canjin yanayin da bata saba dashi ba a jikinta,saboda a kullum da zazzab'i
take kwana sai safiya tayi ta tashi garau, shiyasa bata maida abun wani abu ba duk da malam
yayi ta zancen suje asibiti tana dojewa, don batason ace za'a yimata allura saboda a rayuwarta
sam ta tsani ace za'a yimata allura, tafison tayi ta shan magani har ALLAH ya kawo mata
sauk'i, don ko a gida ba k'aramar tarzoma akeyi da ita ba idan batada lafiya aka zo za'a yimata
allura.
Wasa wasa har tsawon wata d'aya tana fama da ciyon kai da dare kuma ta kwana da zazzab'i,
shiyasa malam ma ya daina matsa mata sabida ganin yanda take fama da kanta,a wani dare
da ta kwana tana wani zazzab'i mai zafi tana ta kelaya amai, tun da sassafe Nura yaje ya
fad'owa aunty suka kwasheta sai asibiti saboda ta jigata sosai aman yaci k'arfinta, koda suka je
a binciken farko aka gano tana d'auke da juna biyu na wata d'aya, daga malam har aunty babu
wanda baiyi murna da wannan samuwar cikin ba, saboda a ganinsu shine k'arshen duk wata
matsala, aka baiwa Amrah gado tareda manna mata k'arin ruwa bayan anyi mata allurai tana ta
kuwwa.
Koda auntyn taga bacci ya d'auki amrah tace da malam zataje gidansu Amrah ta sanar da
mahaifiyarta abunda yake faruwa domin abata hak'k'inta, duk da malam yaji tsoron abinda zaije
ya dawo amma yayi mata adawo lafiya, aunty ta fita ta tari napep sai gidansu Amrah zuciyarta
sai fargabar yanda zasu kwashe da zuwaira takeyi.
Wannan cikin fa da amrah tayi shine silar bankade duk wani sirri dake lullub'e shin to
tayaya????ku biyoni domin kuji komi⛹♀️⛹♀️⛹♀️⛹♀️
Akafta♀️
D/Auta ce
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
https://www.facebook.com/106584514455096?referrer=whatsapp
*⭐⭐⭐TAURARI WRITERS ASSOCIATION⭐⭐⭐*
(We entertain and educate according to our religion and
ethnics)
*PAGE 14*
**********************
Da fara'arta ta rafka sallama Zuwaira dake tsakar gida tana tsintar shinkafa, tana d'ago fuskarta
suka yi ido biyu da Aunty Asabe ta had'e fuskarta tamau, sannan ta mayar da kanta taci gaba
da aikin da take yi, Aunty tayi kamar bata ji zafi ba ta jawo kujerar robar dake ajiye tsakar gidan
ta zauna, sannan tace da ita, "Aunty wajenki nazo."
Zuwaira TAYI banza da ita tareda tashi tsam ta kwashe robar shinkafar da tiren da take tsintar
tayi kitchen ta ajiye, sannan ta dawo ta cire d'ankwalin da ke kanta tasha d'amara, fuskar a
murtuk'e tace da Asabe, "Sawunki a likkafa ki tashi ki fita gidanna tun kafin in nad'a maki
shegen duka wallahi, in yaso sai akaini gidan yari a rufe ace d'an mabud'in ya b'ace."
Aunty ta Mik'e tsaye tareda gyara tsayuwarta ta fara murmushi mai cike takaici tace, "Ni ba
wannan ne ya kawoni gidanki ba, daman nazo ne na sanar dake Amrah ta sami juna biyu yanzu
haka tana asibiti an kwantar da ita."
Zuwaira duk da jikinta yayi sanyi jin Amrah ta sami lafiya wai har da ciki, amman bata fasa
aibata Amrah da malam Nura ba har da tayin cikin dake kwance cikin mararta, wajen fad'in,
"To ni miye nawa a ciki da zaki zo ki sanar dani, ai na riga da na bar maku ita ko mutuwa tayi
bana k'aunar ganin gawarta balle don tana asibiti ki kwaso k'afafuwa kizo ki fad'a man"
Aunty ranta a b'ace tace, "Hak'k'inki ne shiyasa har nazo na sanar dake, wai don kisan rabo
idan ya rantse sai ya fito to wajibi ne ya fiton ko ta hanyar halas d'in ko kuma ta hanyar da ba'a
so, saboda haka rabo ajali ne ki godewa ALLAH da bai kashe ki ba kuma anyi sa'a ya fito ta
hanyar halass, ni kinga tafiyata idan kinga da hali kizo kiga 'YARKI."
Aunty ta fara tafiya zata fita Zuwaira tayi saurin jawo hijabinta bakinta yana kumfa saboda bala'i
tace, "Da Amrah'r da Matsiyacin malamin da yayi cikin, da cikin kanshi sannan dake duka
ALLAH ya tsine maku gaba d'ayanku, Wallahi na k'ara ganin k'afarki a cikin gidannan sai na
yaga maki rigar mutunci, bak'ar munafuka ai wallahi duk bak'in kullin da kuka k'ulla sai kun
warware shi da hannunku, don kuwa indai ni na haifi Amrah bazata tab'a jin dad'in wannan
tsiyataccen auren ba don kuwa har abada ba zai tab'a yin albarka ba, ta dinga had'uwa da
musibu kenan matuk'ar ba kashe wannan bak'in k'addararren auren tayi ba."
Aunty jikinta ya d'auki rawa da sassarfa ta fito gidan saboda Jim miyagun alkaba'in da Zuwaira
take ta jifar 'yarta dasu, taji tsoron lafuzzan da take furzarwa a bakinta wai kuma ga tilon 'yarta
mace da ALLAH ya bata, zufa sai karye mata take yi a jiki saboda tsananin tashin hankalin da
ta shiga, tayi da tasanin zuwa wurin Zuwaira don a ganinta duk itace ta jawo komi,tunda tun
farko sai da taja kunnensu akan bata ba Amrah, amman idan tayi duba da hak'k'in da take dashi
ga 'yarta sai taga ba wani abu bane don taje ta sanar da ita halin da 'yarta take ciki, koda mai
Napep ya ajiyeta bakin asibitin kai tsaye d'akin da aka kwantar da ita ta shiga, koda taje ta
tararda ita ta falka tana shan lemun fatar da Malam ya siyo mata, saboda bakinta da baya
yimata dad'i gaba d'aya ta rasa appetite, Aunty ta k'araso jikin gadon idonta akan Amrah tace,
"Masha ALLAH ashe ta tashi."
Malam yayi saurin tashi daga kan kujerar da yake zaune a cikin girmamawa ya ce "Eh Aunty
yanzu ta tashi."
Aunty tace dashi, "Ka kira Jamila tazo ta zauna da ita kafin inje gida in yi abinci in dawo."
Malam Nura yace "to yayi Aunty bari in kirata tazo sai kin dawo ALLAH ya tsare hanya."
Aunty taje kusa da Amrah ta ri'ko hannunta tace, "Ya jikin me kike so inje in dafo maki?."
Amrah ta yamutsa fuska a cikin rashin jin son cin komi tace, "Alale"
Aunty tace, "To yayi jirani zan kawo maki bada jimawa ba, ALLAH ya baki lafiya."
Ta k'are maganar tareda shafa kanta sannan ta yi sallama da Nura ta fice, zuciyarta cike da
tausayin Amrah saboda rashin dace da Mahaifiya da bata yi ba.
Malam ya jawo kujerar kusa da gadon ya zauna idonshi akanta yace "sannu" ta d'aga masa
kai saboda yawun da ya cika mata baki, ya yago tissue ya mik'a mata ta zubar da yawun ya
amsa yaje ya zuba a dustbin ya dawo, ta langab'e masa tace, "Da zan sami Abu mai bauri in
sha don bana son tara yawunnan da nike."
Malam ya yi saurin cewa, "Kamar me fa?" ta b'ata fuska sannan tace "ko d'anyen dabino
haka"
Yace, "OK jirani minti biyu inje in ga me zan samo maki" ta lumshe ido ta bishi da kallo har ya
fice sannan ta mayar da dubanta ga matan da ke cikin d'akin, masu jinya da majinyatan ta natsu
sosai cikin tunanin Mahaifiyarta Zuwaira da taji tana da cikin me tace, saboda ta mance shaf
bata tambayi Aunty yanda suka yi ba har ta tafi gida, don lokacin da ta farfad'o ne Malam yake
sanar da ita inda Auntyn taje.
Minti biyar a tsakani sai ga Malam ya dawo hannunshi rik'e da ledodi masu kunshe da kankana
da lemu ayaba gwaba gwanda da abarba,, sai lemuka na gora kala kala ya sami gefen gadon
ya ajiye ledodin sannan ya rik'o hannunta a cikin tausayawa yace, "ya jikin?" ta k'ura masa
kallo zuciyarta cinkushe da damuwa bata ce komi ba, ya tsargu da kallon yaga tana yi masa
shiyasa ya duk'a ya d'auko ayaba d'aya ya b'are ya mik'a mata, ta saka hannu ta karb'a duk da
zuciyarta bata son cin komi, ta kai bakinta ta d'an gutsura aikuwa sai gashi taji dad'inta a baki,
nan take ta canye ayabar ya k'ara b'allo mata wata ta cenye kasancewar cikinta ba komi duk ta
amaye, sai da taci uku sannan ya d'auko plate ya zuzzuba mata sauran kayan yanka yanka ya
d'ora mata akan cinya, sannan yace shi zai je ya dawo tayi masa murmushi