Author : Hadiza D Auta Category : Read Hausa Novels
inzo inyi abunda bai dace ba, kiyi hak'uri da duk abunda zaki gani don ALLAH amman
kar ki mance sonki a raina bazai tab'a goguwa ba koda ko bama tare balle gaki a kusa dani ina
jin diminki kina jin nawa, kiyi hak'uri kinji Mmn Uwar farouk d'ina ?" ta d'aga kanta ta fara share
hawayenta ta d'auki spoon ta fara ciyar dashi yana karb'a yana lumshe ido, shima ya dinga bata
tana ci cikin k'arfin hali har suka cenye abincin plate d'in, ya k'aro masu suka ci sannan ya jata
suka yi d'aki tana turjiya tana komi sai da ya k'ara shiga gonarshi, sannan yayi wanka ya fito
zuwa d'akinshi yaci nasarar ba wasu mutane a tsakar gidan, a gurguje ya shirya cikin kayanshi
na angwanci sai baza k'amshi yakeyi ya nufi d'akinta, koda yaje ya taradda itama ta shirya cikin
jin dad'i ya taimaka mata, sannan ya ri'ko hannunta suka fito ta rakoshi har bakin k'ofar
sashensu tayi mashi addu'a ya fice ta dawo d'akinta, inda taga dangin su Sadiya sai lek'ensu
suke yi suna mamakin irin wannan k'auna tasu, Amrah dai ko kallonsu bata yi ba ta shige abinta
tana nazarin ta wace hanya zata karkato mijinta ta karb'e abunta ita kad'ai?, Tana nan zaune
sai ga Jamila da wasu matasan mata na 'yan uwansu suka shigo wurinta, ganin yanda suke ta
janta a jiki ne yasa ta ware suka ci gaba da firarsu suna dariya, Jamila tace da Amrah tazo su
tafi inda 'yan uwan Sadiya ta gayar dasu, Ba don taso ba ta mik'e suka rakata ta gayar dasu
d'aya bayan d'aya, aiko sai gashi sun aje tseguminsu sun karb'eta hannu bibbiyu har wata tana
tsokanarta da cewa ai itama Amarya ce don wannan kwalliya duk wanda bai sani ba zai d'auka
cewa Amaryar ce suka kawo, da d'an barkwancinsu suka fito zuciyar Amrah kamar ta fashe
saboda tuno ana cen ana d'aurawa Nazir aure da wata, idonta suka yi rau rau ta shige k'uryar
d'akinta tana ta kukanta, sai ga Jamila tazo tace da ita tazo tayi bak'uwa taje toilet ta wanko
fuskarta harda guzurin shafa powder ta fito.
Aikuwa cike da tsantsar farin ciki ta k'araso da gudunta baki har kunne tace
"Aunty Asabe ya akayi kika gane gidan?" Aunty ta bita da kallo saboda ganin yanda ta yi b'ul
b'ul abinta haskenta ya k'ara fitowa siririn hancinta ya k'ara tsawo gwanin burgewa, cikin
tsantsar farin ciki Aunty tace
"Lalle 'yata masha ALLAH Nazir ya iya kiyo wannan kyau haka masha ALLAH ina mai gidan
nawa ne?" Amrah ta kalli Jamila tace,
"Jamila ina yaronku ne? Aunty tana so ta ganshi"
Jamila ta mik'e tace da ita "bani minti biyu Aunty yanzu zaki ganshi tunda har yaronmu ne mu
kad'ai banda ita" Aunty tayi dariya tace,
"Kinsan 'yar tawa ba daikawaici ba" Jamila ta fice sauran matan ma duk suka fita suka barta
da Auntyn, Aunty sai kallon Amrah takeyi tana jinjina hukuncin ubangiji ranta tace
_" ashe dama daman Nazir ne mai saki natsuwa tun farko wauta ta jaki, ALLAH ya soki akwai
sonki a ranshi da ko kallonki bazai yi ba saboda irin butulcin da kuka yi masa..... "_
Shigowar Jamila ne ya katsewa Aunty tunanin zucinta cike da murna ta karb'i Umar tace, "A'a
masha ALLAHU kice dai yaron shima yasan gidan Babanshi yazo, ya baje abinshi masha Allah
ya cika bayanshi gwanin burgewa, Lalle Amrah ki godewa ALLAH da ya baki Miji mai sonki
tsakani da ALLAH" Amrah ta fara hawaye tace,
"Aunty fa yau ake d'aura masa aure da Amaryatai" cikin kuka ta k'are maganar, Aunty ta bita
da kallo cikin tsananin jn dad'i tace,
"Ina sane ai shine ma yaje har gida ya rok'eni inzo in lallasheki in baki hak'uri." Amrah tayi
saurin kallonta Aunty tace, "Tabbas shine ya ce inzo in zauna dake don ki kwantar da
hankalinki, don in banda shi da banzo gidannan ba saboda nayi alk'awalin bazan sake shiga
sabgarku ba tunda Aunty Zuwaira bata san mai sonta ba."
Amrah ta marairece fuska tana kallonta hawaye suna sauka Aunty ta kalleta ido cikin ido tace,,
"Shawara d'aya ce zan baki duk runtsi kada ki bari a raba ki da Mijinki, don yanzu haka Aunty
Zuwaira ta siyar da gidan da kuke zaune akan ta biya Nazir kud'in da aka nemi ta bashi don ya
sauwak'e maki, a sanadiyyar haka ma yanzu haka Abbati yana gidan Dangin Babanku saboda
yazo har gida ya sanar dani komi, har kud'in da ya d'auke ya b'oye don kar ta biya ta rabaki da
Nazir din, da yaji zata kai abun wurin bokaye ne ya maida mata da kud'inta a d'akinta sai dai
yayi masu mugun b'oyon da bazata san inda suke ba, akan hakane ta koreshi gidan tace
matuk'ar bai kawo kud'in ba kada ya dawo, to yanzu ni dai shawarata guda biyu ce gareki ta
farko ki natsu ki kula da Mijinki da Mahaifiyarshi da 'yan uwanshi har da kishiyar taki, na biyu ki
jajirce ki tub'ure akan bazaki rabu da Mijinki ba matuk'ar Zuwaira tazo da zancen rabuwarku,
don WALLAHI kika kuskura kika biyeta kece a wahala ba kowa ba, haka duk da ban tara sani
ga Ubangiji ba amman ki karad'e duniya kaf bazaki samu mai sonki irin Nazir ba don haka
shawara ta ragewa mai shiga rijiya, kimsan dai wahalar da kika sha a baya yanzu kuma ALLAH
ya musanya maki da alkhairi duk da butulcin da kuka yi masa a baya, don yanzu kam na
tabbata kika kuskura kika saki Nazir bazai bibiyeki ba don ko cen da don baya da wata mata ne,
amman yanzu ke sheda ce da Amaryarshi sharr a gida don haka kiyiwa kanki kiyamullaili ki
natsu gidan Mijinki ki kula da tarbiyyar yaronki."
Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya tace, "Yanzu Aunty ke bazaki nusar da ita ba ta
mayarwa da mai kud'i kud'inshi abar zancen ba?" Asabe ta dafe k'irji tace,
"Ni a suwa? Tufani ki saya WALLAHI alk'awali nayi bazan koma shiga sabgarta ba, kedai da
ake abun kanki ki kwaci wuyan hannunki daga raba ki da Mijinki da take so tayi, don ke za'a kai
a baro a barki da wahala don na tabbata yanzu kina son Nazir, muddin kuma kika bari kuka
rabu WALLAHI sai kin fishi shan wahala wannan karon"
Amrah ta share hawayenta tace, "Kinsan halin Mama sarai Aunty bana son mu maimaita
abunda akayi lkcn aurena da Malam Nura, kina kallon irin cin zarafin da tayi mani akan auren"
Aunty ta maka mata harara tace
"To ki zauna ki zura ido ta kassa maki rayuwa kiyi zamanki wata rana ita da kanta zata gano
gaskiya ta dawo hanya"
Haka dai Aunty tayi ta yiwa Amrah famfo har zuwa marece, inda ta ce taje ta k'ara yin wani
sabon wanka saboda tarbon Amarya, Aiko taje ta kara canzo wata shigar wadda tafi duk
wadda tayi tasha dauri sai k'amshi ke tashi jikinta sai kace itace Amaryar.
Koda dare yayi misalin k'arfe takwas dam aka fara gud'a tareda shewar ga Amarya nan tazo
gaban Amrah ya k'ire ya fad'i dam! Dam! Dararam!!!!
Tofa kuyo agaji da k'aton Dutse a danne zuciyar Uwargidan Nazirun Inna.
Akafta
D/Auta ce
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Happy Birthday to u Mardiyya D'ahiru wishing u the best life in your world and more money to
your account *
*KUYI hkr dani plss wayata ce ta zama 'yar k'waya♀️*
*PAGE 39*
Ta mik'e kamar wata zararra tana rabon idanuwa Aunty tayi saurin rik'ota tace, "Sai fa kin
natsu kin zama jarumar gaske ne zaki iya cenye wannan jarabawa, koda wasa kada ki bari
zuciyarki ta saki aikata abunda mutane zasu je dake a baki, kiyi k'ok'arin danne duk wani
abunda kike Ji aranki ko don ki jawa kanki girma wajen dangin Nazir da ita kanta Amaryar, ki
zauna dakyau kiyita fad'in *Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun* a baki insha Allah zaki ji zuciyarki tayi
sanyi k'alau, sannan ki had'a da *hasbunallahu wa ni'imal wakil* itama tana sanya aminci da
natsuwa a cikin zuciya" Sannan Amrah ta zauna ta fara fad'ar kalmomin a bakinta tana yi tana
nanatawa aranta har taji zuciyarta ta sami natsuwa fiye da tunaninta, sai gashi ta kalli Aunty tayi
'yar dariyar yak'e tace,
"Nagode Aunty ALLAH ya bar man ke kuma kema ya baki yara ko don su yi alfakhari da
samun Uwa tagari irinki"
Aunty taji dad'in adduarta daga nan tayi ta janta da fira har ta rage damuwar da take ji.
Firarsu ta katse ne saboda jin sautin gud'ar mutane da hayaniyarsu sun nufo d'akinta, Duk da
gabanta sai dakan lugude yakeyi amman tayi jarumtar danne komi har ma ta gayyato natsuwa
ta saka a zuciyarta, wata gwaggonsu Nazir ce ta fara shigowa da sallamarta rik'e da Amarya,
Aunty ta Amsa tareda taronsu da fara'arta har suka zo suka zazzauna, nan take mutane suka
cika falon taf kowa da son ganin k'wak'waf a ranshi, Gwaggon ta kalli Amrah ta fara magana
kamar haka,
"Amrah ga kanwarki nan tazo ta gaisheki, ke kuma Amarya ga Auntynki nan sai ku gaisa"
Amrah da ke dariyar yak'e tace "Sannu da zuwa Amarya ina yimaki barka da zuwa ALLAH ya
had'a kawunanmu"
Duka falon akace "Ameen" masu amsawa har zuci sunayi masu mere ma suna harararta suma
ba'a barsu a baya ba, Sadiya Amarya kam k'ara sunne kai tayi cikin gyalenta tace,
"Aunty barka da dare" Amrah tana 'yar dariya tareda jin sabuwar fad'uwar gaba tace,
"Yawwa Sadiya" sannan ta mik'e ta d'auko rafar 'yan d'ari bibbiyu sababbi kal ta nufi inda
Sadiya take zaune da 'yar guntuwar fara'arta, ta duk'a gabanta ta d'ora mata kud'in a cinya
sannan ta yaye lullubin tace,
"Na riga Ango sayen bakin Amarya don haka dole ne in rigashi ganin fuskarta"
Gaba d'aya falon aka saka dariya wasu da yawa Amrah ta burgesu, yayin da wasu suke
d'aukar hakan da tayi a matsayin wani sabon salon makirci irin nata.
Amrah da Sadiya kam yin tozali da fuskokin juna ya saka su fad'uwar gaba ba kad'an ba,
Musamman Sadiya da har sai da 'yan hanjin cikinta suka kad'a saboda ganin zallar kyau da
Amrah ta mallaka, aranta tace
_"Ashe ba banza ba Hubbyna yake ta faman kiran sunanta akai akai hmmmm!"_
Tayi ajiyar zuciya a wahale saboda wani kishin Amrah da taji ya tokare mata a mak'oshi, daga
nan aka fara yi masu 'yan nasihohin hak'uri da juna tareda addu'o'in zaman lafiya sannan suka
tashi suka nufi d'akin Sadiya.
Suna fita Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya ta kalli Aunty tayi dariyar yak'e tace
" Kinga Amarya masha ALLAH itama da kyaunta Aunty"
Aunty tayi murmushi sannan tace, "amman ai duk kyaunta batayi kyaun 'yata Amrah ba"
Amrah ta rufe idonta zuciyarta cike da jin dad'i tace, "Ni ko sai naga ma kamar ta fini kyau
Aunty, sannan naga da alamu zata yi sanyin hali" Aunty tayi 'yar dariya tace
"Wannan kuma Nazir ne zai banbance gaskiyar abunda na fad'a maki, amman ina son kar ki
yarda ki bada fuskar da reni zai shiga tsakaninku, ki tsaya matdayinki ba'a shedar halin mutum
a ido har sai an zauna dashi, sai kin iya taku sosai WALLAHI saboda zama da kishiya ba
k'aramin aiki bane musamman irinki da kuke zaune a gida d'aya dole ne ki kawar da kanki akan
duk wani abu da zaki gani, kiyi k'ok'arin kawar da kanki a komi ma nasu da zasu yi kada ki
zamo mai yawan saka masu ido saboda gudun ki hanawa kanki zaman lafiya ki tadawa kanki
hankali a banza, kiyi jarumtar samarwa kanki da mijinki kwanciyar hankali kada kiyi sakacin da
kishi zai hanaki ki farantawa mijinki rai, ki zama jajirtacciya wajen baiwa Mijinki kulawa yanda
ya dace domin ki k'ara dasa sonki a kowane lungu da sak'o na zuciyarshi."
Amrah ta sauke k'atuwar ajiyar zuciya tareda gamsuwa da zancen Aunty har cikin ranta,
Aunty taci gaba da lurar da ita hanyoyin da suka dace tabi sannan ta bata wata 'yar kwalba
tace, "kinga wannan ki rik'eshi dakyau kiyi amfani dashi kafin lokacin da zai dawo gareki
INSHA ALLAHU da kanki zaki neme ni har ma kiyi man gdy, sannan ki yawaita shan fruit sosai
saboda suna saukar da Ni'ima a jikin mace fiye da duk wani shaye shayen kayan mata da zata
yi, kinga had'in SAHARA ko ita kad'ai kika rik'e sha WALLAHI kin kulle....... " zancenta ya
katse ne saboda kiran da ya shigo wayarta ta kalli Amrah tace, "Ga Megidana ya zo ni zan
wuce ALLAH ya baku hak'uri, kar dai ki manta da duk abunda kika ji na fad'a maki ki ceci kanki
da kanki, don rayuwarki ce idan tayi dad'i sai kinfi kowa morewa"
Amrah ta rakota tana ta yi mata godiya tare suka je sashen Inna Aunty tayi masu sallama
sannan suka fito har harabar gidan ta rakata sannan suka rabu, Aunty ta wuce Amrah ta dawo
da sauri saboda kukan Umar da ta jiyo, aiko juyowar da zatayi suka yi kicib'is da Jamila rik'e
dashi tana lallashi, ta karb'eshi tayi d'akinta zuciyarta har lokacin cike take da rud'u ba k'adan
ba.
Kuyi manage plsss♀️♀️
Akafta
D/Auta ce✍
*BAKAN GIZO*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITERS ASSOCIATION*
*PAGE 40*
Misalin k'arfe tara da rabi Nazir ya shigo gidan, sai da yaje wurin Inna yayi mata sai da safe ya
bata abunda ya siyo masu sannan ya nufo d'akin Uwargidanshi Amrah, inda ya taradda ita a
k'uryar d'akinta kwance sai juye juye take yi akan gado, cike da fargaba ya k'araso cikin d'akin
da sallamarshi, tana jin muryarshi tayi saurin tashi taje ta rungumeshi tare da aza masa wani
sabon kuka, hankalinshi ya k'ara tashi sosai ya ajiye ledodin da ya shigo da su sannan ya
zaunar da ita a bakin gadon yana ta lallashinta har tayi shiru, ya fara kwantar mata da hankali
da kalamai masu dadi har ya samu ya ciyo kanta, sannan ya dauko ledodin da suke nata ya
ajiye mata ya kalleta da kyau yace,
" tashi ki dauko plate ki juye kici ki koshi kinji?". Amrah ta bata fuska tare da kawar da kanta a
gefe tayi jarumtar fadin ,
" In sai tashi muje in raka ka bacci nike ji" Nazir cikin damuwa ya kalli Idanuwanta da suka
yi jawur saboda kukan da tasha, haka kawai yake ji a ranshi baya son barinta cikin wannan
halin, shiyasa ya mike yaje ya dauko plate da kanshi ya zuba kazar da tsiren da ya siyo masu,
cikin dabara ya dinga bata a baki tana ci yana yi mata fira mai dadi har ta kusan tashi da naman
duka, sannan ya dauko fresh yoghurt mai sanyi ya mika mata ba musu ta karba ta sha fiye da
rabi sannan ta rufe gorar ta ajiye, cike da jin dadi ya mikar da ita tsaye yace
"Zo muje in taimaka maki kiyi wanka don nasan ba kiyi ba ko?"
Ta daga masa kai kamar wata karamar yarinya, aiko da kanshi ya taimaka mata ta tube suka yi
toilet , sun d'auki tsawon minti talatin a ciki suna yan wasanninsu na ma'aurata, don shi kanshi
a nan yayi wankanshi sannan suka fito dukansu suka kimtsa, ya dauki ledodin da zai kaiwa
Amaryarshi ta biyoshi a baya zuciyarta cike da takaicin kwanan da zaiyi a d'akin Sadiya, har sun
kai bakin kofar da zata sada mutum da gefen sadiya ta tsaya saboda matsanancin bugun da
zuciyarta take yimata, har ya shige kofar ya dawo yace
"Zo muje mana ya kika tsaya kuma?"
Ta rungume hannuwa a kirji ta girgiza kai tace
"Ka je kawai Allah ya tada mu lafiya kasha angwancinka cikin aminci ina yi maku fatar alkhairi
kai da Amaryark......".
Muryarta ta karye saboda kukan da yazo mata ba shiri da sauri ta juya ta shige d'akinta ta
dantse, tare da jingina bayanta a jikin kofar tana wani kuka mai cike da tsantsar kishin Mijinta,
Nazir ya biyota da sauri ganin ta rufe kofar shima ya jingina a jikin kofar ya dafe kanshi dake
tsananin Sara masa saboda jin kukanta da yake yi har tsakiyar zuciyarshi.
Sadiya kam da ta cika ta bak'e saboda rashin zuwan da bai yi ba kuma bayan taji saukar
motarshi lokacin