Bakan Gizo Compelet Book

Author :  Hadiza D Auta Category :  Read Hausa Novels

Chapter   1 / 44

1 to 3K   out of 129.9K words

*BAKAN GIZO*



*NA HADIZA D/AUTA*



*Alhmdllh Allah ina godiya da ya bani ikon d'ora alkalamina akan sabon littafina mai suna
BAKAN GIZO, Allah ya kareni da sharrin dake cikin wannan littafi, alkhairan dake ciki kuma ya
sadani daku makaranta gaba d'aya*

*labari ne wanda ya k'unshi;*
Cin Amana
Tausayi
Yaudara
Daukar fansa
Tawakkali


*PAGE 1*


********************

Abokai ne su biyu d'aya a jikin mota tsaye yayinda d'aya yake tsaye suna magana, a bakin
k'ofar wani gida, wanda a duba d'aya zaka gano cewa sabon gida ne, saboda yasha kayan
k'arau tareda sabon fenti, gida ne naji da fad'i wanda gaba d'aya unguwar ba wani gida da ya
kamo k'afar shi, duk da unguwar ta kasance ta manyan masu, wadda sai kasha gishiri ne kake
gini a unguwar.

Salis ya kalli Nasir, a cikin fushi dake kwance a kan fuskarshi, wanda ya kasa b'oyuwa a fuskar
shi yace;

"Nasir shin nine dai nace zan auri Amrah ko? to yanzu nafasa, bazan aure ta ba, don haka ni ba
ruwana da duk abunda mutane zasu fad'a akan haka, aure dai ne ni wallahi na fasa bazanyi ba"

Nasir yabi salis da kallo, tamkar wani sakarai, saboda tsananin mamakin da ya bashi, ganin
rashin hankalin da yake k'ok'arin aikatawa, ace saura kwana biyu aurenshi ya dawo yanzu yace
ya fasa, shin me hakan yake nufi?, su zama k'ananan mutane ko yaya?, a cikin damuwa nasir
yace;
Wai salis kana cikin hankalinka kuwa?, amrah ce fa yarinyar da ka mato akan k'aunarta,

yarinyar da kace zaka iya salwantar duk abunda ka mallaka , domin ka sameta, shine yanzu
ana saura kwana biyu aurenka da ita kace ka fasa, kuma ka fad'a da bakinka ba wani laifi da
tayi maka ra'ayinka ne hakan, shin don Allah me ya shiga k'wak'walwarka ne salis?, wanda ya
birkice lissafinka kake son kayiwa kanka wannan d'anyen aiki?, kayi tunani fa, yanzu don Allah
idan yarinyar nan taji wannan zance, wane hali kakeso ta shiga?, ta sakankance akan kwana
biyu ya rage, yanzu kwatsam taji wannan mummunan sak'o?"

A zabure salis ya fara magana tamkar wani tab'ab'b'e yace;

"Nasir ni wad'annan lissafe lissafe naka baya gabana, aure ne na fasa bazan auri amrah ba,
koda daga ni sai ita muka rage a duniya, kaje na barmaka ita da duk wani abu da na kaimata,
sadaki na lefe na, duk na bar maka kaje a d'aura maka auren da ita, amman nidai wallahi da in
auri Amrah gwara ace in mutu yanzu, kaje kawai idan kana buk'atar auren kuyi, nidai kam
bazanyi auren ba na fasa"

Nasir zai fara magana, salis ya katse shi da sauri, ta hanyar cewa;

Bana buk'atar duk wata magana da zata fito a bakin ka, dangane da wannan magana, kaje
kawai Allah ya baku zaman lafiya.

Yana k'are maganar ya juya ya shige get d'in gidanshi da yasha fenti sai k'yallin sabunta yakeyi,
ta hanyar 'yar k'aramar k'ofar, yana shiga ya bugo k'ofar da k'arfi.

Nasir ya bishi da kallon mamaki, ya dad'e tsaye a wajen, yana ta tunanin anya salis ba jinnu
akansu?, jiki a sanyaye ya fad'a motar shi yaja, ya bar k'ofar gidan sai tunanin mafita yakeyi,
saboda shi har ga Allah baya jin son Amrah a ranshi, amma saboda ya tausayin halin da zata
shiga in taji dole ne ya amince ya aureta, don a cewar shi wannan tozarci ne babba salis yake
shirin yiwa Amrah.




Tofa d'and'ano daga littafin Bakan gizo....




Akafta

D/Auta

*BAKAN GIZO*


*NA HADIZA D/AUTA*



*PAGE 2*



**********************


Amrah a bayi tana wanka, sai tunanin ango angonta na jibi takeyi, a zuciyarta sai wassafa
yanda zasu shinfid'a rayuwar aurensu, mai cike da k'aunar juna takeyi.

K'arar kiran wayarta ne ya katse mata, daddad'an tunanin da takeyi, aguje ta saka zane da
kumfa a jikinta ta fito, saboda sautin kid'an da taji ya tabbatar mata da cewa habibinta ne ya
kira, saboda caller tone d'in da tasaka masa daban ne dana kowa.

Abokanta dake cike da d'akin, sai tsarguwa suke yimata,tana dariya ba tareda tace dasu komi
ba, jikinta yana b'ari ta fisge wayar dake hannun wata k'awarta, a cikin zumud'i ta kasa jiran taji
abunda zai fad'a, saboda shauk'in son da yake kwasarta, ta rigashi magana da cewa;

"Habibina! Yanzu nike son inkiraka, ka turo mun mota gasu zee nan sun zo, ni kawai suke jira
zamuje gidan lallen"

A d'aya gefe salis ya yamutsa fuskarshi, tamkar yaji sak'on mutuwarshi, a cikin bak'in cikin
sunan da ta kirashi dashi, wai habibi, yace da ita;

"Waye habibin naki?, ni bari kiji in fad'a maki, daman na kiraki ne in fad'a maki cewa, na fasa
aurenki, lefe da sadakin da na kawo maki, na barwa mijin da duk yazo da nufin zai aureki, na
bar masa kyauta halas malas, ina maki fatar alkhairi ke da shi Allah ya baku zaman lafiya,
amma kisani koda wasa kada kiyi tunanin zaki k'ara samuna a waya, kuma duk wanda ya
kuskura ya nemeni da maganarki, sai na wulak'anta mutum, don haka a kiyaye zuwa gidana ko
gidan iyayena"

Yana k'are maganar taji kit! ya kashe wayar, Amrah da tunda ta fara jin lafuzzan da ke fitowa a
bakin shi, jikinta ya d'auki rawa, k'afafunta suka kasa d'aukar gangar jikinta, ba shiri ta fad'i
zaune sharaf, fuskarta d'auke da wani tashin hankalin da ya ziyarci ta ba shiri, hawaye sai zuba

sukeyi wasu bayan wasu, tana jin k'arshen maganganunshi, masu kama da saukar aradu a
kanta, wani k'unci ya ziyarci zuciyarta, wanda yasa zuciyar ta kasa hak'uri har saida tayi
sanadin da bakinta ya bud'e ta kwarma wani irin gawurtaccen ihu, tareda buga wayar a k'asa
duk ta tarwatse.
Da sauri k'awayenta suka yo kanta, mutanen dake cike da gidansu wad'anda suka zo domin
bikin, daga garuruwa mabanbanta suka yo d'akin aguje hankali a tashe, suna tambayar me
akayiwa amrah?,.

Amrah dai sai fisge fisge takeyi, tana wani irin kuka na tashin hankali, sai sanbatun kiran ya
fasa aurena takeyi, zanen dake d'aure a jikinta sai yakice shi takeyi, ana maida mata saboda
tsananin furgicin da ta shiga, batama san a yanayin da take ba, kuka takeyi iya k'arfinta, tana
kururuwar fad'in ya fasa aurena.
mahaifiyarta dake rik'e da ita, saboda rud'ewar da tayi, ba shiri ta wankawa Amrah mari tareda
katsa mata tsawa tace;

"Amrah k'i dawo a hankalinki kiyi muna bayanin abunda yake faruwa, me akayi ne kika shiga
cikin wannan tashin hankali, don kawai kina son ki d'agawa mutane hankali, meke faruwa dake
ne waya fasa aurenkin da kike fad'a?"

Amrah tana jin zafin saukar mari a kan fuskarta, ba shiri ta dawo a cikin hankalinta, hawaye na
tsiyaya a fuskarta bakinta yana rawa tace;

"Salis ne ya bugo man waya yake sanar dani wai ya fasa aurena, lefe da sadakin da ya kawo,
duk ya barwa wanda yazo da nufin aurena, yace kuma duk wanda ya nemeshi akan yaji ba'asin
maganar sai ya wulak'anta mutum"

Ga baki d'aya d'akin aka d'au salati, kowa da jimamin abunda yake fad'a, mahaifiyar Amrah ba
shiri takai zaune, sabida jikinta yayi mugun sanyi, a cikin muryar kuka tace da Amrah ;

"Me kikayi masa da zafi ne?, da har ya zab'i ya yimuna wannan tozarcin?"

Amrah tana kuka tace ;

"Wallahi mama banyi masa komi ba, yanzu haka jira nikeyi ya turo mota muje wajen lalle, don
jiya na fad'a masa yace bazai sami damar zuwa ya kaimu ba, don akwai wasu bak'in abokanshi
da zasu zo daga USA, zaije ya dauko su, a filin jirgi"

Aiko dai ko yanzu wata kabbarar mutanen dake d'akin sukeyi, kowa da abunda yake fad'a akan
salis, don mamakin wannan abu da yayi, saboda dukansu sunsan yanda Salis yake son Amrah,
don ko wannan gidan da suke zaune shine ya basu shi, suka dawo a ciki, b'arin dukiya yake
yimasu sosai da sosai.

Daga nan suka dinga baiwa amrar hak'uri, akan tayi imani da k'addara tasa a ranta hakan shine
alkhairi, suna cikin wannan maganar ne, wani k'anenta ya shigo yace;

"Amrah kizo ga Nasir nan yazo yana son ganinki"

Jikin Amrah har rawa yakeyi wajen saka zunbulelen hijabinta, har takai k'ofa zata fita, k'anwar
mahaifiyarta, ta kirata ta dawo, tace da ita ta saka koda doguwar riga ne kafin ta taje wurin mai
kiran nata, sannan hankalinta ya dawo mata ta tuna daga ita sai zane ne, da sauri ta jawo wata
doguwar rigar ta ja hijabi ta fita kamar zata tashi a sama saboda sauri.
Nasir tsaye a jingine da motar shi, fuskarshi ba walwala ko kad'an, ganin yanayin da Amrah ta
fito, ya tabbatar masa taji abunda yake faruwa, yaji kunyar kallonta, sannan ya tausaya mata
matuk'a, asanyaye Amrah ta gaidashi, tareda zubowar wasu sababbin hawaye, shima kanshi
yaji saukar hawayen akan fuskarshi, saboda tausayin halin da ta tsinci kanta a ciki na bazato
ba tsammani.

A cikin sanyin murya Nasir yace;

"Ki daina kuka, ni a shirye nike zan aureki idan kin amince, rana da lokacin da aka saka duk
abarsu yanda suke, idan kinyi shawara kinada number ta sai ki kirani ki sanar dani"

Amrah ta k'ura masa wani kallo, wanda ni kaina bansan taya zan fassara maku irin kallon ba,
saboda abun tana kallon shi kamar a mafalki, ko shirin film, ko novel.




Kuyi mata bayani a cikin inane ake wannan kwacagiya


Bazanyi posting buk d'in a ko'ina ba sai a group din D/Auta novel fan's mai bukatar group din
tayi man magana zan bata link.



Akafta‍♀️





D/Auta

*BAKAN GIZO*


*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*littafin bakan gizo littafi ne wanda zan dinga post a group d'aya wato D/Auta novel fan's duk
wadda take buk'atar book d'in zatayi magana sai asaka ta, ban hana a watsa shi a sauran
group ba, amman ni dai a group d'aya zan post*


*PAGE 3*


**********************

Nasir ya gyad'a kai alamar tabbatarwa, sannan ya k'ara da cewa;

"Ki shiga gida kiyi shawara, duk abunda kika yanke sai ki neme ni"

Amrah a cikin tuk'owar wani kuka ta juya, zata shiga gida, ta k'ara juyowa a cikin tantamar
abunda yake shirin faruwa, Nasir yana nan a tsaye inda ta barshi, duk'e da kansa a cikin
damuwar da shi kad'ai yasan me yakeji, ya d'ago kansa yakai kallonshi gareta, ganin har yanzu
kamar bata gasgata abunda yace ba, yayi murmushin k'arfin hali yace da ita;
"Ni nasir na amince zan auri Amrah, budurwar abokina salis da ya fasa aure"

A guje Amrah ta fad'a gida, tana wani kuka a cikin d'imaucewa, saboda yanzu ta k'ara yarda da
gaske salis ya gujeta, ba shiri ta zube tsakar gida tana gunjin kuka, sai kace wata 'yar k'aramar
yarinya, gaba d'aya akayo kanta da tambaya, amma ita kam bilhak'k'i da gaskiya kukanta
takeyi.
A cikin damuwa kowa yayi zugum ana sauraren kukan da take ta rerawa, masu k'aramar zuciya
ma, suka fara tayata kukan, masu dauriyar ne suka nace sai bata hak'uri sukeyi, akan tayi imani
da duk abunda ya sameta, ta rungumi k'addarar ta.

Bayan tayi kukan ta rage rad'ad'in abunda ke damunta ne ta fara yi masu bayanin kamar haka;

"Nasir ne abokin salis yazo, wai idan na amince shi zai aure ni, a rana da lokacin da duk aka
saka na aure nida salis, a shirye yake da a d'aura muna aure ni da shi a ranar"

Gaba d'aya gidan aka d'auki sowar farin ciki, saboda kowa yaji dad'in wannan rufin asiri da Salis
zai yiwa Amrah, mahaifiyar amrah tana zubar da hawaye tace;

"Ni mahaifiyar ki, NA amince da ki aure Nasir, kuma na bada goyon bayana d'ari bisa d'ari,
saboda haka ki kwantar da hankalin ki, wani hanin ga Allah baiwa ne, Allah ya yiwa wannan
yaro albarka, yanda ya rufa muna asiri shima Allah ya rufa masa"

Ga baki d'aya wurin aka amsa kiran; "Ameen".

K'anwar mahaifiyar ta wato aunty Asabe tazo ta tada ita, daga zaman dirshan d'in da tayi, ta
kaita har d'akinta tace da ita;

"Kiyi hak'uri amrah, a rayuwa ba duk abunda kake so ne, yake zama alkhairi a gareka ba, wani
sa'in abunda baka so shine alkhairin ka, saboda haka ki rungumi wannan aure da zuciya d'aya,
ki koyawa kanki son wannan yaron, a hankali zakiji dad'in zaman auren ki, salis kuwa kiyi
k'ok'arin fidda shi a ranki, kibar shi da Allah zai yimaki sakayya akanshi, yanzu ki tashi kuje
wajen lallen keda k'awayen ki, kici gaba da duk shirye shiryen ki kinji?"

Amrah ta d'aga kanta tareda runtse ido, wasu hawaye suka gangaro mata akan fuska, tasa
hannu ta dafe bakinta, dak'yar ta saita kanta ta fara magana, tace da aunty;

"Ni Aunty mamakin da nike tayi shine, shin me nayiwa salis a tsakanin jiya da yau ne?, da ya
sauya masa ra'ayi akaina?, saboda nasan salis yana sona, ba ni ba ma, duk wani wanda yake a
tare dani ya sani, ina da tabbacin indai har salis yana a cikin hayyacinsa, to inada tabbacin
bazai tab'a fasa aurena ba, sai dai in har wani abu ne ya hau kanshi, wanda yayi silar saka shi
aikata wannan aringizon tozarci a wurina, amman insha Allahu, zanyi k'ok'arin cire damuwar shi
a raina"

Aunty Asabe taji dad'in abunda tace, a cikin daddad'an kalamai, tayi ta kwantar mata da
hankali, har ta samu natsuwa tazo wa Amrah, sannan tace da ita, ta d'auko wayarta ta cire sim
ta saka a wata wayar, ta kira salis ta fad'a masa ta amince, Amrah tayi k'ok'arin shanye kukan
dake son tuk'ak'ota, tace;
"Aunty bazan iya kiran shi ba, wallahi nauyi nikeji "

Aunty Asabe tace ;

"To ki tura masa sak'o yama fi sauk'i"

Amrah jiki a sanyaye ta zare Sim's d'inta a jikin wayarta da ta kwankwatse, ta saka a wata

tsohuwar wayarta, da itama salis ne ya saya mata ita, kafin wannan da ta fashe, jiki a sanyaye
ta tura masa text d'in ta amince da aurensa.

Sannan Auntyn tace da ita, ta tashi suje wajan lallen, Amrah bata so zuwa ba sabida ita komi
ya fita a kanta yanzu, amma a haka ta daure ta shirya ita da zugar k'awayenta, suka tafi gidan
lallen, amma ta zama so silent, don idan son samu ne, tafi son a barta ita kad'ai tayi jinyar
zuciyarta, amman saboda ta ragewa kanta damuwa ta biye k'awayen, sai firar k'arfin hali akeyi
da ita, sunyi ta bata shawara a kan ta so nasir kawai tayi auren ta, Allah zai saka mata a wajen
salis.

**

Biki ya kankama sai hada hada akeyi, duk wani tsari da aka shirya na bikin salis da Amrah ba'a
fasa shi ba, duk da zuciyoyin ango da amaryar ba dad'i amma a haka suka b'oye damuwar su
akayi hidimar bikin aka k'are lafiya.

An d'aura aure, ankai amarya Amrah d'akinta,a gidan Nasir angonta, tareda rakiyar k'awayenta,
'yan uwa, da abokan arzik'i, sai fatan zaman lafiya ake yi masu.

Bayan kowa ya watse ne, ango ya shigo tareda abokin shi k'waya d'aya da ya rako shi, wanda
yayi masu nasiha sosai akan suyi hak'uri da junan su, su baiwa masu cece kuce, da 'yan gutsiri
tsoma kunya, saboda abokan Nasir da Salis da yawa basu goyi bayan auren ba, a cewarsu
Nasir yaci amanar Salis tunda har ya aure masa budurwa, wasu ma cewa sukeyi saboda ya
gano akwai b'oyayyiyar soyayya a tsakanin su ne, yasa salis ya fasa auren amrah, to yanzu
koma minene sai dai fatar Allah ya basu zaman lafiya.

Nasir tun da yaje raka abokinshi, amrah bata koma jin d'uriyar sa ba, sai dai taji k'arar rufe k'ofar
d'akin shi, tayi ta zuba idanuwa taga ya dawo d'akinta, amma shiru shiru bata ganshi ya dawo
ba, ta kalli ledodin daya shigo dasu, wani kuka yazo mata ba shiri, ga wani tsoro da takeji ita
kad'ai bata jin motsin komi sai na k'arar Ac'n dake manne a d'akin, a tsorace taje tayi arwallah ta
fito ta rama sallolinta, da bata samu tayi ba saboda kacaniyar bikin, bayan ta k'are sallah'r anan
ta b'ingire wani bacci mai k'arfi ya fisgeta, tareda wani mafalki mai firgitarwa da tayi.

A zabure ta falka tana ta waige waigen, ta ina zata ga wannan mutumin da ta gani a cikin
mafalkin, da yake ta yimata bak'in albishir akan cewa;

"Amrah aurenki zai mutu, aurenki zai mutu!, zai mutu! zai mutu!, nan da sati biyu"




‍♀️‍♀️‍♀️

Akafta




D/Auta ce

*BAKAN GIZO*


*NA HADIZA D/AUTA*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Jinjinar ban girma a gareki sis Billyn Abdul ki dad'e kiyi lastingmutunniyata.*


*PAGE 4.*


**********************

Ta waiga ko'ina bata ga kowa ba, zuciyarta ta tabbatar mata da cewa mafalki ne tayi, da sauri ta
dunk'ule a wuri d'aya tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, da taga kukan bazai fisheta ba
dole tayi shiru ta koma tasbihi a cikin zuciyarta, tareda i tuno irin soyayyar da Salis yake yimata
wadda baya shayin nunawa a gaban kowa.
A haka dai ta cenye rabin daren da tunanin tsohon masoyinta Salis, a lokacin ne wata
azababbar yunwa ta ziyarci cikinta, ta k'yalla ido ta hango

1 / 44