MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 38.3K words

tunanin da shi take ?wana kuma da shi take ta shi rashin barcin nan shi ne mafarin birkita lissafin ta.

Hadiza kuwa na ta ganin yanzun zata soma tashenta na shiga bokaye, tunda A'isha ta haihu. Su kuwa su Hajiyarmu sun du?a addu'a fatansu Allah ya juyo da hankalin Wan nasu ga matarshi, domin gaban kowa ya nuna tsana A'isha, kuma koda wasa bai taSa batun komawarta gidanshi ba,hakan nan suma ba su ce mishi zasu maida ta ba, maimakon haka ma yanzun sun fi yi mata shirye-shiryen komawa makaranta don an dawo daga yajin aiki.

Sun yi shawarar haWa ta da Uwani don kula da yaron tare da nemo mata ?ar aiki ?arama. A'isha ta so zuwa gida, amma Abbanta ya ce a'a ta koma makarantar ta in ta kuma samun wani hutun ta zo tunda shi ya zo Ummanta kuwa suna waya koda yaushe,gurin Alhajinmu Uncle Win ta yaji batun komawarta makaranta,nan take ya yi kicin-kicin ya haWa rai amma bai ce ?ala ba, duk da mahaifin nashi ya lura da hakan bai nuna ya gane me Wan na shi ke nufi ba tunda dama ya dai sanar da shi ne amma ba wani gana neman izinin shi ba ne. Koda yaje gida ranar bashi da walwala gefen Hadiza yake ya shiga bai same ta ba sai Tabawa,nan take ya ?ara Waure fuska, ina Hadizan? Ta ce Um ta tafi gaisuwar mutuwa ne. Ya ce,a ina? Ta ce unguwarsu nan ma?otansu,tsaki yaja kafin ya fita ya tsani halin da wannan matan suke yi na fita babu izini, Allah ya sani shi ba zai yafe ma dukkan wadda ta fita babu izini ba, gefen Jummai ya nufa so yake ya watsa ruwa yaje gidan Nafisa,sa?o zai bata zuwa gurin mahaifiyarsu, ya sani in ta amince Alhajinmu ba zaya yi wuyar fahimta ba.

Lokacin da ya kira Nafisar ya sheda mata cewa zai zo don yana son ganinta sai ta ce itama tana son ganin shi dama Wakin Jummai ya soma shiga tana zaune ta zabga tagumi duk ta yamutse ta yi baki yace Jummai lafiya wai duk ?wana kin nan kin yi wani iri, ta ce (cikin rawar murya) ni wallahi duk duniyar nan ta isheni, ina ga dai an sa min hannu ne komai nayi sai ya lalact, cikin rashin fahimtar zancan ta ya ce me ki kayi ya lalace? Nan kuma sai ta dawo hankalinta ta gane da wa take magana, sai ta ce ni dai Alhaji to kalleni fa, Allah asiri ne to komai na duniya baya min daWi ya zauna gefenta,haba Jummai ina Tauhidinki ya je ne? Kullum kin fi son ki ji ki cikin jin daWi da walwala? Ki sani Ubangiji yana jaraba imanin bayinsa ta kowace hanya,shin ba?ya ganin kema imanin ki ake taSawa? Sai ta mi?e tsaye imani? Ni fa babu wani imani asiri ne. Tsaki yaja ya mi?e ya fita fasa yin wankan ya yi ya nufi motarshi,yana tu?i yana tunanin matsalar mata ita ce ajalinshi, ya fito ya shiga cikin gidan, ita ce ta fito ta buWe mishi ?ofar falo, ya shiga ciki yana cewa Sister na gaji da halin da gidana yake ciki na gaji da halin matana,mata uku amma ba wadda zan tunkara in ji sanyi? Mata fitina ne bala'i ne shin ku ma dama haka ku ke yiwa mazajanku? Dole ne ace mata kun fi yawa a wuta. Nafisa ta iso kusa da shi ta nuna mishi kujera zauna Bros kada ka faWi zauna mu tattauna insha Allah zaka samu sau?i.



#######
[12/21, 22:31] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 10*



Ya zauna ta Waga waya ta kira mai yi mata hidima, ta sanar da ita cewa ta kawo abin sha mai san yi tana da bako,ta haWo da zoSo ta ce to sai da ya cika kofi da zoSon ya shanye tas,ya dubi Nafisa da gidan Hajiyarmu nasha zoSon nan da na ce Beby ta yi shi. Nafisa ta ce wannan ma ita ce ta yi shi shekaran jiya da tazo. Ya Sata rai shi ne ki ka ba ni? Nafisa ta dubeshi,Bros ka ce kana son ganina dama nima Ina son mu tattauna wata matsala, ya ce ina jin ki, ta ce ko dai ina jin ka fara sanar da ni taka matsalar Bros.

Ya gyara zama Nafisa wallahi na gaji da abin da matan nan suke min musamman A'isha. ta gyara zama me A'isha ta ke maka haka da zafi? Ya yi shiru yana son lakubo laifin da take mishi, amma ya kasa. Ya lumshe idanu, Sister na kasa tuna laifin da take min amma nafi jin haushinta. Nafisa kinga dai ke ?anwata ce kuma ?arama daga cikin ?annena, ina miki rantsuwa da Allah ba zan tuna Waya daga cikin laifukan da A'isha take min ba, amma ina tsakanin jin haushin ta." Nafisa ta ce "Brother nima dalilin da yasa ni ke son ganinka kenan, to wannan abin ba sihiri ba ne kuwa? Ya girgiza kai tare cewa, a'a Nafisa kada ki zama cikin marasa yarda da ?addara komai ace sihiri Nafisa ta ce amma kasan gaskiya ne sihiri ko? Ya ce na sani amma wannan mu bar shi a ?addara, yanzun a taki shawarar mece ce mafita? Nafisa ta ce Yauwa nawa ganin dama lamuranmu ga Allah suke,to mu sake mi?a wuya gareshi, sannan mu samu malamai na ?warai su taya mu da addu'a, Brother ka rage bacci ya ce haka ne,kin san ni ne? Ta girgiza kai, ya ce a ?asan zuciyata ina jin zafin abinda nake yi wa yarinyar, amma tsananin haushinta ya sha ?arfina, sannan ?arin damuwata wai yanzun shirin komawa makaranta su Hajiyarmu suke mata ga yaro bai yi ?wari ba,dama sa?on da zan miki ga Hajiyarmu ki ce mata ban amince ba, sai yarona ya yi ?wari."

Nafisa ta yi ?ar dariya, "Bros ba zan iya yiwa Hajiyarmu batun A'isha ba,don zata ce bakinmu Waya da kai, kuma kaima a shawarce kada kayi mata magana, don kaima jiranka take yi ta warware ka, zuba musu idanu kafin lokacin da zamu samu warware matsalar ka." Ya ce shi kenan, bari in tafi ta ce dama kenan matsalar A'isha ce damuwarka?" Ya ce kusan haka ne, sauran ma da tasu matsalar amma bata shan kaina Kamar ta A'isha.

Ta fito da kasko yau ?wana biyu bata kara hantar a rushi ba,kai anya ma maganin yana yi kuwa? To ta gane tunda A'ishan ta haihu sai Sarin kuWi kawai yake yi sannan in kana son gura ta yi tsawo to sai dai in labarin Abulkhairi zakayi mishi,bari taje ta aiki su Suby su Wibo mata rushin wuta gurin matar maigadin ma?otansu,yau zata zafafa mishi zuciya, rufe ta samu ?ofar ta soma mitar cewa ?an iskan yara yanzun haka sun bar gidan zan zo in san yanda zan yi da ku baza ku ?ara min hawan jini ba,bayan wanda nike da shi Allah ma ya sani. Tana tura ?ofar me zata gani? Suwaiba da Safiyya tare da wasu ?awayansu guda biyu tsirara haihuwar uwarsu suna aikata masha'a da junansu, sannan tsakar Wakin ga ?walabe nan na pakalin, totolyn da kuma wata ?waya wai roci. Jummai bata san lokacin da ta saki kaskon hannutaba tare da faWin na shiga uku me zan gani? Wannan iftila'in da ya faWa mata ta gani da idanunta shi ne sanadin fashewar kaskon ta gami da zubewar gantar ta har ta manta da batun kasko,da me ya fito da ita daga Waki ma,wata sabuwar damuwa ta shiga gami da tashin hankali mai tsanani,komai yana da sanadi wannan shi ne sanadin da Alhaji Saddi? yana zaune cikin Office Win shi yaji shi tamkar yana jin ?ishi, sai da ya shanye goran swan water babba guda Waya mai sanyi ya jingina yana mamakin kanshi, domin ya sani sai ya tashi daga Office bai shanye goran ba,jin zuciyarshi ya yi tamkar an wanke wani nishaWi gami da annashuwa, ya rasa jin shi yake tamkar sabo yau akayi sht,nan take ya mi?e ya nufi fita daga Office Win cikin zuciyarshi yana son ya ji shin shi ne kuwa? Sai yake ganin tamkar wani zai kalleshi ya kira shi da wani suna ba nashi ba.

Gidan Nafisa ya nufa bai shiga ciki ba a harabar ya tsaya ya kirata da waya,ta kalli mijinta ta ce "Dear,Bros ne wai ba zai shigo ba sauri yake yi." Alhaji Bello ya ce to ki je mana zan fito mu gaisa nima,tana isa gurin shi da fara'arta me zai hana ka shigo Bros sai kurum taji ya ce kalleni Sister ni ne kuwa? Ta zaro idanu ban gane ba kamar ya ya kaine? Ya ce ji na nike tamkar ba ni ba, ta ce kuma? Gaskiya ka tsaya da addu'a tsayin daka ya ce ina yi daidai gwargwadon hali, Alhaji Bello ya iso gurin yana cewa Alhajin Allah haWuwa ta yi wuya, Alhaji Saddi? ya ce a'a dama kana ciki ne? Ya ce dawowata kenan garin, Alhaji Saddi? ya bashi hannu suka gaisa, ya yi yayi su shiga ciki amma ya ce sauri yake yi.

Cikin ?wanakin Alhaji Saddi? yana jin canje-canje tare da shi, sai dai rashin lafiyar Hajiya Jummai ya hana shi nutsuwa sosai, zuwa aka yi aka sameta tana ?wance cikin matsanancin hali a ?ofar Wakin su Suwaiba, waWanda su lokacin tuni sun bar gidan. Bayan gwaje-gwaje Likitan ya tabbatar wa maigidan nata da wata ?anwarta cewa jininta ya yi matu?ar hawa fiye da da, sannan wasu alamomi sun sa mun yi mata gwajin suga, mun kuma gano tana dashi,ga kuma ciwon ta na tun farko waton zuciya,don haka tana cikin haWari,in dai zata dinga sa damuwa cikin zuciyarta. Alhaji Saddi? ya tausaya mata tare da buWe bakin aljihunshi don ganin ta samu lafiya, dangi suna ta zuwa dubara yawancin su sukan ce sai dai suje don mijinta amma ba wai don halinta ita kanta ba domin ba tsarin ta ba ne zuwa duba mara lafiya ko gaisuwa,ko barka, duk yanda ku ke in ba irin ?awayansu ba.

A'isha tare da Hajiyarmu suka zo, sun same ta zaune ta jingina da filo fatan acca take ci watan tuni ta soma amfani da abincin masu shuga, cikin zuciyarta tamkar ta sha?e A'ishan dan takaici,nan ta ture ?wanon gabanta gefe tsani wannan tsinanniyar yarinyar,da ?yar ta amsa gaisuwar su, maigidanne ya shigo yau ?wana uku A'isha bata sa shi a idanunta ba,tun ranar da ya zo ya sake yi mata kashedi game da yaron shi kuma ya yi mata rantsuwa da Allah cewa in har ya samu labarin cewa ta tafi makaranta ta banzatar mishi da yaro zata sha mamakin hukuncin da zai yanke mata.

Bayan ya rage tsawo ya gaida gyatumarshi ta tambayi mai jiki ya ce da sau?i, A'isha tamkar ko yaushe cikin girmamawa ta gaishe shi tasha mamakin yanda ya amsa cikin sakin fuska, idanunshi suna kallonta sannan ya iso kusa da ita yana cewa, kawo Alhajin nawa,wato Abulkhairi ta kunto shi daga bayanta ta mi?a mishi,yau idanunshi sun fi son kallon Beby fiye da yaron shi, itama ta lura da hakan ko in ce kusan duk ?an Wakin sun kula da hakan ne ma yasa Hajiyarmu mi?ewa tare da cewa juma Allah ya ?ara sau?i, sannan ko tana bu?atar wani abu ne ta faWa a kawo mata? Jummai wadda ta zurfafa tunani gurin tuno kaskon ta wanda sai yanzun ta tuno da shi a'a kawai ta ce ma Hajiyarmu ba tare da taji me tace ba, Hajiyarmu ta nufi fita tana cewa A'isha goyo shi mu je.

Ta dubi Uncle Win nata zamu tafi ya yi Wan murmushi, Beby ki zauna mana in kaiki,ta tsura mishi idanu,yaushe rabon da ta ji wannan sunan daga bakin shi? Yaushe rabon ta da ganin murmushin shi tare da muryarshi nan mai daWin sauraro, ta sauke ajiyar zuciya, kayi ha?uri direba ya kawo mu ya ce to juyo in sa miki shi,ta juya mishi baya yana sa mata yaron ta goya shi da ?yau ya ce kin yi ?yau da goyon, murmushi kurum ta yi bata ce ?ala ba ta dubi Hajiya Jummai mun tafi Allah ya ?ara sau?i,bata amsa ba sai hannu ta Waga mata. Shi kuma ya bi ta a baya sun fito daga Wakin ya ce Beby ta Wan tsaya amma bata juya ba, yaushe za ki koma makaranta? Ta dube shi sannan ta dubi ?asa,jibi ya zuba mata idanu. Ta yaushe zaki koma Wakinki? Ta ce sai dai ka tambayi Hajiyarmu, ta ci gaba da tafiya, daga nan ya tsaya yana kallonta, har ta Sace ya yi ajiyar zuciya tare da juyawa.

Kuka rurus ya samu Jummai tana yi, ya iso gurinta a tsorace lafiya kuwa Jummai? Ta soma tari cikin kukan faWin "shi kenan ni yanzun ba ni da amfani tunda cututtuka sun min katutu shi ne kana ganin A'isha ka bita." ?anwarta taja tsaki, gaskiya Jummai in ba zaki ?wantar da hankalinki ba zan tafi ba zai bita ba ba matarshi bace? Alhaji Saddi? ya ce haba Jummai,haba Jummai!! Wai shin ?aramar yarinya zaki koma ne? Kin san fa halin da ki ke ciki, A'isha ba?uwa ce a gare ki? Don Allah kiyi ?o?ari ki zama mai natsuwa don ki samu lafiya. Indo ?anwarta ta ce ina zata ?wantar da ranta ba saka damuwar ce tasa ta cikin wannan halin ba? Ita dai jin su take yi ba zasu gane halin da ta ke ciki ba ne. Alhajin fita ya yi cikin damuwa.

Yinin ranar A'isha ce a cikin zuciyarshi har zuwa dare. Ya fito wanka ?ananan kaya ya saka jeans blue da shirt fara turarenshi na ko yaushe ya saka, Hadiza ta shigo sanye da riga da sket na lallausan leshi mai ruwan madara. Ta dube shi Darling ka gan ka kuwa? Sai ka ce saurayi Wan shekara ashirin? Ya dubeta kada ki maida ni baya mana. Ta ce Allah kuwa, ya ?washi wayoyinshi da makullin motarshi ta kalli agogo ina zaka yanzun tara ta kusa? Kuma ga abincin ka fa,ya ce zan ci gidan Hajiyarmu yau tuwo nake son ci kin san basa rasa tuwo,ko dan saboda Alhajinmu, ta Sata rai shi kam bai kula ba ya fito abin shi ta biyo shi an kusan fara news fa, ya ce ai zan kalla a can ta tsaya tamkar hawaye ya zubo mata don takaici tasan gurin A'isha zai je ba wai don mahaifanshi ba, ta yi tsaki ta juya ciki.

Hajiyarmu tana kula da A'isha, tun da taga fara'ar maigidanta ta fara sukuni, yanzun ma su suna falo ne suna kallon labarai amma ita ta shiga Waki ta ?wanta alhalin ba wanda ya kai ta son labarai. Ita kam A'isha so take ta keSe kanta ta yi tunanin shin Uncle ya yafe mata ne? Ko ko don yaga Hajiyarmu ne? Kai a'a ba don haka ba ne tunda ko a cikin gidan ya kan yi mata wula?ancin da ya so, tana ganin Allah ne ya amshi addu'arta ya juyo mata da tunaninshi gareta. A fili ta ce Allah yasa haka ne, lokacin da take wannan tunanin shi kuma ya iso falon har yasa Baraka ta kawo mishi tuwo, bayan sun gaisa da iyayan nashi ya kasa cin tuwon na kirki domin waWanda ya zo domin su bai gansu ba, daga bisani ya mi?e yana kallon gefen da Alhajinmu yake yana cewa bari naga Abulkhairi ba su ce mishi ?ala ba ya nufi ciki,?amshin turaranshi shi ne yasa ta buWe idanunta da ke lumshe fuskarta kurum yake kallo ga nashi zaton bacci take yi ganin ta buWe ido sai ya yi murmushi, Beby dama idanunki biyu? Ta tashi zaune fuskarta babu yabo babu fallasa, ta gaishe shi. Ya amsa sannan ya isa gurin Wan shi yasa hannu ya Wauke shi yana kallon fuskarshi kafin daga bisani ya sumbaci gashin yaron tare da manna shi a ?irjinsa yakan ji wani irin daWi duk lokacin da ya rungumi Wansa,yana addu'a ga duk wanda bai samu Wa ba, Allah ya bashi A'isha tana kallonshi zuciyarta na yaba ?yawun shigar shi, da ?yan haibar shi banda ta san shi da in aka ce tayi mishi shekaru zata ce ashirin da biyar, ya dawo da dubanshi gare ta, sai ta Wauke kanta yayin da suka haWa idanu, ya matso daf da ita Beby wai me yasa naga kin kasa sakewa da ni ne? Ta ce ba komai, shi da kanshi ya sani abubuwan da ya yi mata can baya bai ?yauta ba Sai dai shi ba zai ce ga dalilin da yasa yake yi mata hakan ba, ya ce Beby Wazun na ce yaushe zaki dawo ba ki ce min komai ba, ta ce Uncle ka manta ne? Na ce sai dai ka tambayi su Hajiyarmu, ya ce kin dai san in dan ta su ne zaki yi ta zama ne ba zasu dawo min da ke ba, ta yi guntun murmushi a ranta ta ce kuji Uncle da wani zan ce mutumin da ke guduna. A fili kuwa sai ta ce, sun ga baka bu?aci hakan ba ne shi yasa ya ce Beby kenan cikin ruwan sanyi ki ke dafa mutum ni dai ki dawo gida kawai,ta tashi zaune Uncle jibi ne fa zan koma makaranta to menene ma zai sa in dawo tunda ba zama zan yi ba, ya yi shiru can ya ce ni fa don dai kawai su Hajiyarmu ne amma Allah da ba zaki koma yanzun ba sai yarona ya yi wayo bana son aje baa luran min dashi. Shiru ta yi mishi ya ce to in zaki shiga aji dawa zaki dinga barin shi? Ta dube shi da Uwani zamu tafi har ma da wata yarinya saboda aikin gida, ya Wan taSa baki da bana gari ma da sai dai in dawo in samu kin tafi abinki, ta ce Uncle naga kamar kafi bu?atar hakan ne shi yasa tunda tuni ka fitar da kanka daga cikin lamarina, ta sunkuyar da kai, wallahi a shekarar da ta wuce in wani ya ce min zan tsinci zuciyata cikin garari ba zan amince ba, domin na san uban goyona mai amana ne da halin dattako kuma zaya jure duk wasu laifuka da ?uruciya zata aikata matsawar ba alfasha ba ce, sai gashi yana zarginta da alfasha

8 / 13