MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   4 / 13

9K to 12K   out of 38.3K words

me ganin laifin za ya maganta min? Nafisa ta ce shi kenan mu dai mun ga laifin shi gidaje nawa gareshi cikin Katsina da kewayenta? Ya maidata wani mana za'a tsaya Sarnar dukiya,kin san Allah, Alhajinmu da Hajiyarmu sun ji haushi, harkokin shi ma fa ya?i ya maida hankali sai ka ce yau ya soma gini. A'isha ta ce Allah ya ?yauta kuyi ha?uri kada suyi fushi da shi,tamkar Nafisa ta shiga ta waya ta doddoke A'isha don haushi, ta kula A'isha ba zata taSa ganin laifinshi ba, don haka sai ta canza zancan da cewa,ki je asibiti mana? A'isha ta ce nima tunani na kenan, sai kuma naga ni ba ciwo cikin ke min ba, kuma ba wani guri ne ke min ciwo ba a jikina, sai naje na cewa Likita ina jin motsi? Nafisa ta ce kin ji irin haukan naki ba? Ki je ki yiwa Likita bayani,in yaso ayi miki (Scanning) a ga me ke damunki,in bai ga komai ba a koma Islamic." A'isha ta ce, shi kenan zan je, ki gaida min su Hajiyarmu."

Lamo ta ?wanta tana tunanin me ya shiga kan Uncle ne? Don kawai yana yiwa Jummai gini sai ya share ta? Zata ce kada ya yiwa Jummai gini ne? Ba tare da ta gansu ba? Ha?i?a ranta fa ya Saci sai dai bata son ta nuna ma ?ar uwarshi ne. Ta kira wayarshi abin al'ajabi ya ?i Wauka, har sau uku, sai ta tura mishi da text cewa,in ta mishi laifi ne don Allah ya yafe mata, rashin sa ya saka ta cikin damuwa,don Allah yaushe zai zo? Sa?on na isa sai kiranshi har tana murna ga zatonta sulhu zaya nema, sai kurum ya ce "ke kin fa matsa min da yawa......




######
[12/19, 22:33] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 5*



Ban cika son mace mai jarabar tsiya ba, duka-duka yaushe ne ban zo ba na shekara ne? Kin dameni don Allah daina kirana in na matsu zan neme ki da kaina." Kan A'isha ya yi matu?ar Waurewa,bakinta yana rawa ta ce, "Yi ha?uri Uncle nima ba wai na ce kazo ba ne,na zaci na maka laifi ne shi yasa." Tsaki ya ja kafin ya kashe wayar, wannan lamarin ya firgita A'isha sosai, baiwar Allah ranar sai dai bacci Sarawo, amma bata runtsa ba. Ma?otanta su kansu cikin ?wanaki sun fuskanci tana da damuwa koda suka tambaye ta sai ta ce musu bata jin daWi ne. Anty Maimuna ma ta matsa mata dason sanin damuwarta, amma A'isha sarkin zurfin ciki ta yi ?ememe ta ce zuwan jarabawa ne. Yanzun suna karatu ba dare ba rana,Anty Maimuna ta ce to Allah ya taimaka.

Cikin haka ne A'isha ta samu ziyartar asibiti inda ta samu ganin Likitan mata. Bayan ta gama mishi bayani ya tambaye ta ko tana da ciki ne? Ta shaida mishi ita kam bata da komai,don haka ya bukaci ta ?wanta kan gadonsu na likitoci don yi mata (Scanning). Bayan ya gama bai ce mata komai ba, sai da ya fitar da sakamako ya dube ta, "kina da miji?" A'isha ta ce "Eh." Ya mi?a mata sakamakon, tana buWewa idanunta na sauka kan (EDD) ta maimaita kalmar a fili (EDD) kuma? Ta dubi Likitan ta ce,kana nufin ciki ne da Ni? Ya ce wata ba?wai ta zaro idanu tare da Wora hannunta kan mararta, sannan ta ce Likita ka kuwa duba sosai? Ya yi Wan murmushi,a katin ki naga cewa ke Walibarmu ce amma kin kasa gane kina Wauke da ciki,kina nufin ko kaWan ba wata alama da ki ka gane kina Wauke da ciki?" A'isha ta girgiza kai tare da cewa, "Ina al'ada duk wata sannan wata bakwai Win da ka ke magana nayi Sari lokacin wata uku."

Ya zuba mata ido, "Ya ya abin ya faru wancan lokacin? Ta bashi labarin a ta?aice, ya ce to wankin cikin da baayi miki ba shi ne dalilin da ba a wanke Wan ba, Allah ya sa zaya taka doron ?asa, sai dai zaya iya kasancewa watannin cikin ya koma baya. Yanzun dai cikinki wata bakwai da sati Waya.

Jugum A'isha ta yi tana tunanin wannan lamarin na Ubangiji,lallai wannan shine mafi girman abinda ya fi bata mamaki,iyaka tsawon rayuwarta, sannan ta yi murna mara adadi kuma ta san wannan labarin in ta bawa Uncle shi zai kawo karshen rashin jituwarsu, ko ta ce fushin da yake yi da ita, wanda bata san silarshi ba. Ta jawo wayarta ta shiga neman shi da glo Win shi har sau biyu tana rurinta tana katsewa bai Waga ba hakan (MTN) Win shi jikin ta ya yi sanyi, amma duk da haka ta daure ta kira (Seltel) Win shi daf da zata katse ya Waga, gabanta na faWuwa ta yi sallama,rai Sace ya amsa sallamar, kafin ta yi magana ya ce wai lafiya ne? Ta ce a'a dama ina son muyi magana ne. Ya katse ta da cewa,bani da lokaci, sannan ya yi tsaki ya kuma kashe wayar. A'isha ta zabga uban tagumi nan take kanta ya shiga sarawa,kuka mai ?arfi ne ya ?wace mata,ta yi shi har ta gaji babu mai lallashi. A'isha ta zama tamkar wata zararriya wa zata tunkara da matsalarta? Zuciyarta ta ce mata Ubangijinki, ranar kuwa ?wana ta yi kan sallaya tana kaiwa Allah kukanta, zuwa safe ta ji Wan dama kuma ta yanke hukuncin har ma cikinta batun cikin jikinta dama Ubangiji shi ne ya Soye kayanshi, ko Nafisa ba zata faWa mawa ba, haka ta ci gaba da rayuwarta cikin makaranta.

Jummai kuwa ta samu yanda take so,da tace kaza za ya yi mata, gini kuwa an gama an kuma dan?ara kaya na iyayan kuWi sannan ta shirya walimarta ta gani ta faWa suka shige ita da Suby da Sofy Sai gefen maigidan. Hakan ya yi matu?ar tunzura Hadiza nan ta tada bala'in cewa ba zata yarda ba, rigimar ta kai su ga manya inda Alhajinmu ya ce tunda ya yi wa Jummai dole ne sauran matan ya yi musu, dole yasa aka bige gefen Hadiza da nashi da na Jummai na da aka hau yiwa Hadiza nata amma A'isha dama ko ?asa da sama za su haWe ba za ai mata wani gyara ba. Ya dai sa an ragi falon an bar mata Wan ?arami ya zuba mata tsofaffin kujerun falon. Rashin kunyar da Hadizan ta mishi lokacin ya isa sakinta, sai dai Sarin da tayi ne yasa ya bar ta ko Allah zai sa ya kuma samun wani rabon daga gare ta, don shi ya yarda har ga Allah ciki ne kuma ya amince cewa Sarin ta yi irin kuWin da ya kashe lokacin da suka zo da batun Sarin suna da yawa, sannan sun hana shi zuwa asibitin a cewar su ba sai ya je ba,daga ?arshe ma da suka ga ya matsa kan cewa zai je sai suka dawo da ita gida, Likitan da suka naWa na ?arya ya ci gaba da zuwa duba ta.


**** **** **** ****

A'isha tana matu?ar tausayawa kanta don zurfin cikinta ya hana ta sanar da wani bare a tausaya mata,don haka ta shiga rama ta koma sirit sai nono sai ko cikinta wanda ya bayyana lokacin Anty Maimuna ta yi ta yi da A'isha ta sanar da ita matsalarta, amma ta ?i cewa kurum take karatu ne don bata son tambaya ma ta rage zuwa gidan, cikin haka ne suka samu hutu na ?wana goma jal, tamkar kada ta tafi Katsina, amma ya zamar mata dole tunda bata da kuWi duk sun ?are komai nata ya yi ?ar?af, ta yi ta kiran Uncle a waya don ta sanar da shi a zo a Wauke ta, amma ya?i Waga wayar. Abin ma ya daina bata mamaki ya shiga bata tsoro,bata son kowa ya san halin da take ciki, don haka ta ?i kiran kowa ta nufi tasha.

Sun iso Katsina biyar saura,nan ma ta Wauki shatar Taxi zuwa gida, har cikin harabar gidan ta ce ya shiga. Maigadi na ganinta ya buWe Gate Win gidan,tana fitowa Uncle ta gani tsaye jikin mota yana waya, Jabiru yana ri?e da jakar Uncle Win ta Office da alama dawowarshi kenan daga Office ya bi motar da kallo don ganin wanene ya shigo masa cikin gida da Taxi? Ranshi ya yi mugun Saci lokacin da suka yi arba da A'isha, sai ya ji tamkar ya hau ta da duka,nan take ya Wauke kanshi daga kallon gurin da take. Ganin haka bai bata mamaki ba, domin nata zaton na ma zaya kore ta ne, ta ciro kuWi ta bawa Wan Taxi ta saSa jakarta tare da jan akwati, sai lokacin ta soma tambayar kanta wane gefe zata nufa, domin gaba Waya fasalin gidan ya canza, tana kallonshi ya nufi sabon ginin wanda take zaton shi ne na Hajiya Jumman.

?ofarsu ta da ta nufa duk da ta kula nan ma akwai ?an gyare-gyaren da aka yi,taja ?ofar a kulle take gam don haka ta shiga ?wan?wasawa. Jim kaWan ta ji muryar Tabawa tana tambayar wanene? A'isha ce ta ce,nice Tabawa buWe. Ganin A'isha sai ta hau she?a dariya,dama ke ce haka? Ta taSa baki,ai yanzun ?ofarki ta koma can, ta nuna gefen gareji, A'isha bata gane ba, amma yarda Tabawa ke tuntsire dariya shi ne ya sa ta saSa kayanta ta nufi gefen gareji. Sule mai bawa fulawa ruwa ya nufo ta da sauri yana yi mata sannu ta amsa mishi, ya Wauki akwatin tare da cewa ai Hajiya an samu ?an gyare-gyare ne a gidan suna isa ?ofar tana kulle ya ce bari in amso miki makullin gurin maigida, da gudu ya nufi sasan Jummai.

Ya samu maigidan nashi yana shirin shiga wanka in da Jummai ke ta faman riritashi tamkar ?wai, ya yi sallama Sofy ta zo menene? Ya ce maigida nake nema,taje ta sanar da shi. Jummai ta fito tace menene? Wanka zai yi, ya ce ranki ya daWe zan amshi makulli ne na gefen gareji, ta yi guntun murmushi sannan ta juya. ya fito fuskarshi Waure hannunshi ri?e da makullan, gashi ka bata sakaryar yarinya kawai,Sale ya amsa ya fita daidai sanda Alhajin ya ci gaba da cewa don iskanci sai ta kama shigowa motar haya Taxi har cikin gidana? Jummai ta taSa baki wannan tsageruwar yarinyar mara kunya mene ne ma ba zata yi ba,ya katse ta da Waga hannu saurara min tsagerancin me Beby ta yi miki? Nan ta tuna da sharadin boka da ya ce kada ta yarda ta kushe A'ishan a gabanshi, yin haka zaya ringa lalata aikin dole sai ta saka kissa cikin lamarin. Aikin da kissa zai tafi ba da hassada ba, don haka sai ta wayance da cewa ba Suwaiba ka ke nufi ba? Ya girgiza kai ni ban ce miki Suwaiba ba, kuma bana son in Ina ma wata faWa a dinga sa min baki ta dafashi muje kayi wanka mijina,ni kaina ban za ci kana nufin Bebynka ba, ina zaton Suwaiba ce shi yasa,ni ko me A'isha zata min na tsageranci,yarinyar da magana ma bata dame ta ba,ai ita ce ta dawo? Lallai ina mata Sannu da zuwa,tsaki yaja sannan ya nufi gurin wanka.

A'isha ta buWe ?ofa ta shiga, tsayawa ta yi tana kallon Wan tsuku kun falon, kujerun suna da ne cikin falon sai ko T.V ta tura ?ofar Wakinta ta shiga duk ko'ina ya yi ?ura,bata gaji ba ta tuSe ta shiga gyaran ko'ina, da falo ta soma har ga Allah ita waWannan dakunan sun ishe ta, ina laifi mutum mai zaman kabari ya samu ciki da falo a gidan duniya ai ya ishe shi rayuwa, ta goge komai sai abinda ke bata mamaki shi ne ba taga kitchen ba. Me hakan ke nufi? Ita dai tasha alwashin ba zata taSa mishi zancan ba,zata fito da kayan girkin ta ko a ?ofar Waki ne ta saka risho, ta yo wanka bata shafa mai ba saboda zufa ta zumbula doguwar riga ta zo falo ta zauna, yanzun matsalarta yinwa ta mi?e ta fita harabar gidan, duk mazan ?an aikin sun tafi gida sai Baba maigadi kurum. Ta isa gurin shi ta ce don Allah Baba duk su Sule sun tafi ne? Ya ce sun tafi Hajiya kina son wani abu ne? Ta ce biredi nake so, da kayan tea, ya ce to bari a karSo miki dama Wari biyar Win kenan ta mi?a mishi gashi duk yanda ya kama ka sai min,ta koma ciki. Can ta fito don tago ko ya dawo dai-dai lokacin da aka soma kiran magriba. Ya mi?o mata sa?on daidai lokacin da Uncle Winta ya fito,ya bi ledar da kallo ita dai ta amsa ta juya bayan ta ce ta gode.

Uncle Win nata ya bita da kallo tafiyarta irin ta masu ciki ya raya a ranshi ya isa gurin maigadi Baba ina ka je ne? Ya ce Hajiya na siyoma kayan shayi. Kayan shayi? Eh, inji Baba maigadi. Uncle ya kaWa kai ya nufi masallaci. Ranshi Sace,me yasa A'isha ke sha'awar wula?anta shi a idanun duniya ne? ?azun Taxi ta shigo mishi da ita har cikin gida yanzun kuma kayan tea ?ulli-?ulli kamar gidanshi, motocin shi nawa? Sannan shaguna nawa ke gareshi cikin plaza, daban-daban? Ya yi ?wafa.

Ita kam ta samu ta jona ruwa ya tafasa tasha tea Win ta ta ?oshi, ta yi sallolinta, ta ?wanta don ta huta. Sai dai maimakon bacci sai ta soma karanta matsalolinta. Tuni ta nemi bacci ta rasa, don haka sai ta mi?e ta soma da yin alwala, ta shiga kai kukanta ga Allah domin iyaka tunanin ta shi ne kurum zai yi mata maganin dukkan wannan halin da ta shiga.

Uncle Win ta kuwa don takaici ya kasa cin duk kayan alatun da Hajiya Jummai ta shirya mishi, zuciyarshi sai ?ara zafi take game da Beby. Jummai tasan komai,don tun lokacin da ta ji dawowar A'ishan sai ta zuba rushi cikin kasko ta kara hantar nan mai cake da allurai, shi yasa zuciyar maigidan ?ara zafafa,kamar yanda Malamin ya tsara mata, ta dube shi maigidana wai me ke damunka ne? Ya ce wallahi Jummai A'isha ce ta bani haushi. Ta ce haba Alhaji me A'isha zata yi maka ka ji haushi, irin haka bayan ka sani cewa yarinya ce? Ka dai same ta ne ka nuna mata baka son shiga motar haya tunda Allah ya hore maka, ya dubeta, to bayan ma wannan ina fita sai naga wai ta aiki Baba maigadi siyan biredi da madaran ?ulli dibi wannan cin zarafin? Hajiya Jummai ta ce,lallai bata ?yauta ba, amma ka mata uzurin cewa daga tafiya ta dawo,kai itama da rashin dabara take maimakon ta zo nan ta amshi abinci in tana jin yunwa ne? Ya ce girman kan nata zai bar ta ne? Ya sake yin ?wafa, zuciyar Jummai kar da murna, ta ce to kaje can gurinta don yau ita ce da kai tunda tafiya ta dawo. Ya ce bar ta ba zan je ba. Ta haWa fuska wallahi sai kaje don bana son shiga ha??in wani, Allah ma ya sani. Ya ce kina korata ne? Ta ce a'a ni dai nafi son ko lahira mijina ya tashi daga cikin maza masu adalci, ya ce haka ne zata ci albarkacin ki ne zan je amma ba don ita ba, ta mi?e ta zo ta ?wanta a bayan shi na gode mijina nasan kai nawa ne daga duniya har abada, tashi ka je bari na bika da abincin,ya ce bar su kawai ya fita ta bishi da kallo fuskarta Wauke da murmushin cin nasara tasan in ya yi arba da ita wani sabon haushin nata zai ji kamar yanda Malam ya tsara mata.

Yana ta bugun ?ofa ba ta ji ba sai daga baya, da sauri ta sallame ta nufi ?ofar, ta buWe lokacin ya cika tamkar zai fashe "waton wani sabon salon wula?ancin ne haka,da kimarshi da komai a ce yana bugun ?ofa ?an aikin gidanshi suna ji,ya dubeta a zafafe, watan kina jina ina ta faman bugun ?ofa ki ka min banza ko? Cikin sanyin murya ta ce kayi ha?uri Uncle wallahi ban ji ba, ina sallah ne ta kau ce ya shige ya kalli falon ko'ina ya taSa baki sannan ya shiga bedroom Win zuciyarshi na zugi so kurum yake yaga abinda zai yi faWa a kanshi ta buWe fridge da nufin ta bashi ruwa amma sai taga wayam ta manta Wazunnan ta gyara shi babu komai ciki, ta dube shi yi ha?uri Uncle,ba ni da ruwa cikin fridge, ya katse ta nace nazo shan ruwa ne? Ta girgiza kai, ya zauna kan kujerar madubi ita kam gabanta ne ke ta faWuwa, ta cire hijabinta tana ninkewa, ya zuba mata idanu can ya ce "ke." da sauri ta dubeshi "mene ne a jikinki? Ta kallo cikinta kunya take ji ta ce mishi ciki ne don haka sai ta sunkuyar da kai tana Wan murmushi da ?arfi ya ce "dake fa nake magana?...



######
[12/20, 19:35] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 6*



Ta dube shi cikin in ina ta ce shi ne dama nake ta kiranka ina son nayi maka bayanin baka saurareni ba, ya ce bayanin me? Ya ci gaba da magana cikin Waga sauti kada ki ce min kina da ciki, ta zaro idanu gabanta na faWuwa, ya ce ko shi ke gare ki? Ta Waga kai. Ya mi?e da sauri ina ki ka samo shi? Jin furucin shi yasa ?an hanjinta juyawa me Uncle ke nufi? Bata ankara ba sai ta ji ya cakumi wuyan rigarta, abinda za ki min kenan ko A'isha ya Wan tausasa murya,kin dai san zuwana gurinki na ?arshe kina haila ko? Muryarta tana rawa ta ce eh, amma bai san sanda ya Wauke ta da wani wawan mari ba,amma me? Ya hankaWata kan gado kin cuceni don ina neman ?a?a ido rufe shi kenan sai a kawo min shege? A'isha kin yi kuskure yanzun so nake ki gayan uban da ya yi miki cikin? Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, ina ma ta mutu ta huta da wannan ba?in cikin? Ya ce zaki gaya min ko sai ranki ya yi mugun Saci? Jin shi yake tamkar ya sha?e ta ta mutu ya huta, ya

4 / 13