MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 38.3K words

maka abinci? Hawaye ya kuma zubo ma A'isha, ta ce sannu Hajiya, Allah ya baki lafiya, ta maida kallonta ga A'isha ta tsura mata ido tamkar tana son tuno da ita,can sai ta ce ina yini? Sannunku tare ku ka zo? Tana ta gaida A'isha cikin kuka A'isha ta ce Uncle gurin babu tsafta ya kamata a gyara mata gurin. Ya ce Beby wa kika ga zaya iya shiga wannan gurin,duka fa take yi da cizo duk wanda ta kama sai ya yi jinya, abinci ma fa sai dai a Waura igiya, gidan mahaukata ma sun ?i amsarta don ranar da muka kai ta mutum biyu ta sumar,zaman ta nan shi ne ?wanciyar hankalin al'umma. Yaja hannunta zo mu tafi, ya lura in bai jata sun bar gurin ba sai ta ja ma kanta ciwo don kuka, ya ce ishara ce Beby Allah ya saukar mata, saboda masu hali irin nata,duk wanda bai yarda da ?addara ba ya zaSi son zuciyarshi ina mai tabbatar miki da sannu zaya ga aya ta sauka a kanshi.

Cikin motar da ?yar ya shawo kanta ta yi shiru. A'isha ta ?ara tsoron Ubangiji tare da tsinkewa da lamarin duniya,lallai kam duniya budurwar wawa ce, kuma duk wanda ya Wau Wamarar zamanta ya wahala, domin wanda ba a haifeshi bama jiranshi take yi,yazo ya ci yayin shi ya wuce, Allah kasa mu fi ?arfin zukatan mu,Amin. A'isha ta ringa damun Uncle Win ta da son zuwa Jigawa, dole ya bar komai suka tafi. Mahaifanta sun yi murna da ganinta da Wan jikansu. Haka nan sun sha mamaki lokacin da Alhaji Saddi? ya basu labarin Jummai sun jajanta mishi game da al'amarin haka nan sun yi godiya mai tarin yawa a lokacin da A'isha ta sanar da su batun aikin Hajjinsu,babu ma kamar Yaya Abdulrahman,tamkar anyi mishi albishir da gidan Aljanna,ga kuma tsaraba aka yi ta rabawa dangi na ko'ina da ina,da zasu tafi mahaifan nata suka yi mata nasiha tare da nuna mata cewa ta bi mijinta sau da ?afa, kada ta biyewa ruWin duniya da kayan cikinta, suka Wauko hanya suka dawo gida.

Dawowarsu da ?wana Waya suka soma zirga-zirgar gidan Nafisa, ta haifi ?arta mace basu sami hutu ba sai da aka yi suna ta samu ?arta Asma'u,sunan mahaifiyar Alhaji Bello,suna ce mata Husna, A'isha sun sake haWuwa da Hajiya Aliya ta zo sunan ?arta,Anty Nafisa nan ta buWe bakin jaka ta ?washi kayan gyaran jiki, A'isha tana iyaka ?o?arinta don ganin ta ?yautata wa mijinta, shima yana nuna sonta ko gaban wanene, wannan dalilin shi ne ya ?ara tunzura Hadiza sai ya kasance duk ranar girkinta ta dinga ?orafi kenan ita baya sonta,ya fi son Aisha,kaza-kaza, shi kuma nuna mata yake cewa A'isha tana da biyayya tare da ladabi, itama in har ta bishi ha?i?a zata iya kamo matsayin A'isha a cikin zuciyarshi duk ran girkinta ta dinga cika kenan tana kumburi ita a dole ba ayi mata adalci. Hutun A'isha ya ?are ta tattara ta koma makarantarta tare da su Uwani,nan fa Hadiza ta soma tsiro mishi da kalolin tsirfa musamman in ya bu?ace ta nan zata tirje ta ce dan yaga A'isha bata nan i, haka kawai ita da shan wahala A'isha ke morar shi, nan nema ta sako maganar batun Hajji da ya biya mata da iyayanta, shi ko ya ce ya biya kuma babu wanda ya isa yasa shi fasawa, kuma ta fitar mishi daga Waki taje ta ri?e kayanta,tun daga lokacin ya share lamarinta ko kanta ta kawo Wakinshi baya sauraron ta daga baya dai ta bashi ha?uri tare da Waukar masa al?awarin ba zata ?ara ba.

?wanci tashi asarar mai rai, A'isha ta kuma zuwa hutu yaronta lokacin yana tafiya ya ?ara ?yau tare da birgewa,kowa ?aunar yaron yake yi. Hajiyarmu ta ce ba za a koma dashi ba yayeshi za'ayi. A'isha ta ce dama in zasu tafi aikin aikin Hajji nan zata barshi in ta dawo ma ba dashi zata koma ba, ta yi karatunta cikin nutsuwa, shi kuma Uncle Win cewa ya yi insha Allah kafin ki koma sai da wani cikin,shiru tayi mishi ya ce baki fata kenan? Ta ce ina fata mana amma sai na gama karatu bai ce komai ba cikin zuciyarshi kuwa sai ya Wan zargi wani abu,an ya A'isha bata shan komai? Amma sai ya share wannan zargin, baya son ya zargi abu.

Dukkan Waukacin musulmi suna ta shirin tafiya aikin Hajji, haka ma su A'isha da mahaifanta, kasancewar wannan shine karo na farko da zata aikin hajji duk ta bi ta hana kanta sukuni burinta kawai shi ne ta ganta gaban ka'aba, Nafisa kuwa kasancewar taje ba sau Waya ba ba so biyu ba sai dariya take yiwa A'isha.

Tabawa ta kalli Hadiza kada ki nuna musu damuwarki bar su in sun tafi can zasu ?waSe ?ila ma ya sako ta tun can ke dai kiyi ?o?arin zuba waWannan ?wayoyin cikin kayanta. Hadiza ta ce ?wayoyin mene ne? Tabawa ta ce " Na hana Waukar ciki ne,in ma mace tana da cikin zubewa za ya yi." Tsaki Hadiza ta ja, Tabawa kin cika abin haushi, to kuma ce miki aka yi ita mahaukaciya ce tana ganin ?wayoyin cikin kayanta sai ta hau sha ko? Tabawa ta dafats,saurara mana ke dai ba zaki ci ribar zance ba wallahi, ce miki aka yi zata sha? Mijinku kawai ake bu?atar ya gani,in ya gani kuwa kin san dai yanda yake son haihuwa, rigima ce zata ta shi, ballantana dama na gaya miki yana zargin tana shan wani abu, nasha jin yana ce mata ba dai ta yin tsarin iyali ko? Hadiza ta ce kai Tabawa, Allah ya biyaki sai dai ban san ya ya zanyi in sa mata ba. Tabawa ta sakar mata harara in nemo maganin in kawo miki sannan sai na koya miki yanda za ki sa? Hadiza ta ce taimakamin don Allah, Tabawa ta ce to kin dai san ita sakarya ce yanzun zata yarda da mutum, zuwa zakiyi har Wakinta ki shiga da sakin jikinki da kuma sakin fuskarki ki ce kin zo ne kuyi sallama sannan don Allah ta yafe miki duk abinda ki kayi mata, to a nan zaki shammace ta ki saka mata. Na ce zan zo miki da lokacin da ya dace ki shiga sai na le?o tukunna kin san za a sane in da zaya gani ba inda zata gani ta zubar ba, Hadiza ta ce to ina jiran ki sarkin ?an le?en asiri. Tabawa ta ce kuma ki sani in bom Win nan da muka Wana ya tashi da A'isha za ki bani ?yauta ta musamman, tare da yi mini ?arin albashi, don na lura da ke in dai ba ro?on ki aka yi ba baki ?yauta ba ki yin sadaka don tsabar rowar tsiya, Hadiza ta ce na ji zan miki uwar ?waWayi,don ke ko komai zaki yi don ki samu kuWi ko da halaka ne. Tabawa ta fita tana cewa,na ji dai ai halina Waya da uwarki, Hadiza ta ce iye? Lallai kinga gadon baccina, Tabawa ta yi wucewarta ta bar Hadiza tana surutai.

Washegari da misalin ?arfe sha Waya lokacin maigidan ya fita zuwa Office. Tabawa ta shigo tana cewa ina Hadizan? Zo ki shiga yanzun wata jaka ta na nan cikin ta zaki sa, saboda ta haWa suturarsu ciki,za yayi amfani da shi kinga zaya gani in ya zo Waukar kayanshi. Hadiza ta ce tana ciki kuma? Tabawa ta ce tana ciki mana kefa sokuwa ce yanzun sai ki ce sai na gaya miki yanda za ki yi ko? Hadiza ta ce ba wani sokonci,ban ga ji makirci ba, ba dole sai an nuna min sannan zan iya ba? Tabawa ta ce amma ai kin gaji asiri, makircin ma ?ila ta gurin uba ne ba'a gada ba, ta ci gaba da cewa yanzun in ki ka je kusa da jakar zaki zauna ki ba jakar baya kan gado kuma jakar take, tashi kiyi azama kada ta fito daga uwar Wakan ta dawo falo.



######
[12/23, 11:57] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 14*



Aisha tana ta haWa kayan Abdulkhairi,in Babanshi ya dawo za su kai shi gidan su Hajiyarmu, tare da yi musu sallama, domin tashin Asubahi za su yi, sai ta ji sallamar Hadiza cikin sakin fuska ta amsa tare da faWin shigo, bakin gado ta zauna tare da ba jakar baya kamar yanda Tabawa ta yi mata ?watance. A'isha ta bar aikin da take yi don su gaisa, bayan sun gaisa Hadiza ta ce, ashe kuma tafiya ta zo? A'isha ta ce wallahi kuwa, yanzun nake cewa bari in gama in shigo muyi sallama." Hadiza ta ce, "Ina Abulkhairi?" A'isha ta dube ta yana bacci a falo, ba ki ganshi ba? Hadiza ta ce ban lura ba, to Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya, kusa mu cikin addu'a. A'isha ta ce insha Allah ai naso ace dukkan mu ne zamu je, Hadiza ta ce to ai kin san an ce Hajji kiran Allah, kafin A'isha ta ce wani abu cikin Sa'a sai wayarta ta soma ruri,da sauri ta nufi falo domin ringing Win na musamman ne,don Uncle Win ta ne,hakan ya yi wa Hadiza daWi, don haka tana fita ita kuma ta danna maganin ciki ta rufe ta koma ta zauna A'isha ta shigo tana waya, Hadiza ta bita da kallo tana cewa Uncle babu sauran nono fa,ya ce bana turo a kawo ba? Ta ce bai zo ba, bari na tambayi Hadiza." Ta dube ta Jabiru ya kawo nono? Ta ce a'a. A'isha ta ce bai iso ba in yazo zan dama in bashi ya ce to Beby. A'isha ta aje wayar ta dubi Hadiza Na barki ko? Hadiza ta ce sai ka ce wata ba?uwa? Suka yi shiru kasancewar ba su saba ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ba, can dai Hadiza ta mi?e bari in koma sai kun dawo, A'isha ta ce haba dai zan shigo kafin mu wuce." Hadiza ta ce, "to sai kin shigo, ta fita cikin murna ta isa sasanta zaune ta samu Tabawa ta zuba ma T.V idanu, Hadiza ta kalli T.V Win wasannin turawa ake yi a tashar MBC max ta ce Tabawa duk kallon ne haka sai ka ce zaki shiga T.V Win kuma,abin haushin ma ba wai kina jin me suke cewa ba ne. Tabawa ta ce Um ni dai ba ina binsu da idanu ba,to kin dai saka ko? Hadiza ta ce na sa mana da Allah ya taimake ni in gaya miki sai ga kira wayarta ta hau ringing tana fita na tura. Tabawa ta ce ya yi ?yau, yanzun sauran mu jira sakamakon da zai biyo baya, Allah dai yasa ya gani,amin.

Da ace A'isha tana tara sani da Ubangiji, da ba ta bari jakar kan gadon ta ba har zuwa yanzun da suka dawo daga kai yaron nasu gurin Kakanninshi da sunan yaye. A'isha ta dawo da alhinin rabuwa da Wan wanda ko yaushe suna tare musamman irin wannan lokacin,wato dare.

Uncle Win nata shi ne yasa hannu ya Waga jakar da nufin saukewa ?asa,yana cewa Beby yau kamar kina jin kasala ne zan ce ko mene ne? Ta dube shi,me yasa ka ce haka? Ya ce na gane gadonki duk tarkace, ta kalli gadon Uncle jaka ce fa kawai, ya ce me kika zuba ne cikin jakar na ji ta da nauyi sosai? Ta ce ni me ma na saka ne? Kayanmu ne kawai fa,zai buWe ta ce don Allah Uncle ka bar ta da ?yar fa na shirya su, ya ce ni fa kada ki Waukar min abinda ba zan yi amfani da shi ba,ya soma ciro kayan ciki yana cewa Beby da duk ni kika Wibar ma wannan bolasas Win? Yana dariya, ta ce ai na zaci zakayi amfani da su ne,shiru ta ga ya yi yana karanta wani Wan ?aramin ?wali mai Wauke da wasu ?ananan rubutu,yana gamawa ya Wago idanu yana kallonta, yanda taga fuskarshi yanda taga idanunshi yasa ta razana ta nufoshi lafiya Uncle mene ne? Ya kuma kallon ?walin sannan ya ce dole ki ce kada in buWe jaka,da ?yar ki ka shirya, saboda kin san me ki ka taka, ya ajiye ?walin kan kayan ya mi?e ya fita. Gabanta na faWuwa ta nufo gurin ?walin ta soma Wauka, ta zaro idanu lokacin da ta fahimci kowane magani ne. Tuni zufa ta soma tsattsafo mata, to wanene ya kawo mata wannan maganin Waki? Duk da ta sani ba zai taSa yarda da ita ba akan cewar ba ita ce ta kawo maganin ba.

Ta sameshi a cikin falo yana ta zirga-zirga bata taSa ganin shi cikin wannan halin ba, ta ta tsaya ta daure ta ce "Uncle...." Ya juyo tare da Waga mata hannu,ba ki da wata kalma da zaki furta min, shi yasa bana so zuciyata ta zargi abu domin a ?arshe zaya zama gaskiya. Amma Beby kin bani mamaki ya sake juya mata baya da duk matan duniya zasu taru su ce min suna da amana zuciyata ba zata taSa yarda da su ba,ya girgiza kai A'isha ke ce kurum zuciyata ta aminta da ke,ke ce kika sani gardamar cewa mata suna suka tara, A'isha ke nake tunawa in gode ma Allah,don a zatona kin cike gurbin kowace mace a gurina, sai gashi kin yaudare ni kin ci min amana kin ?ara nuna min cewa halin mata Waya ne. Ya ?ara saitin muryarshi lokacin da zai ce dame za ki kare kanki? Cikin jakarki da kika zauna ki ka shirya kayan da kanki naga maganin tsarin iyali, ta ya ya zaki gamsar dani cewa ba ke ce ki ka sa ba? Ya tsura mata idanunshi da suka yi jajir. Ta girgiza kai babu amma wallahi Uncle ba ni nasa ba, kuka ya ?wace mata, kuma lokacin da nake shirya kayan ban gan shi ba,ya ce to wa ya sa miki? Cikin kuka ta ce Allah shi ne mafi sani, shi ne kuma shaida ta.

Ranshi ya sake Saci Beby nafi son mutum in yayi laifi ya amsa laifinshi fiye da ya nemi raina hankalina,tuni na jima da fahimtar cewa kin fi son karatunki fiye da auranki ko? Shi ne dalilin da yasa ba ki so ki haihu, ashe Jummai bata isa ta zama wa'azi a gare ki ba ko? Na gode, ya nufi waje. Nan A'isha ta zauna ta shiga rera kukan ba?in ciki, ta sani an yi wannan ne don a haWa ta da mijinta,ganin kuka ba zai zama mafita gare ta ba, sai kawai ta mi?e ta koma Wakin baccinta, alwalla ta Wauro ta hau yin nafilfili don gaya ma Allah.

Shi kuwa rasa ina za ya dosa ya yi,mota kurum ya buWe ya zauna ya kifa kanshi kan kujera, yanzun wane mataki ya kamata ya Wauka kanta? Ina ma zata Waukar mishi al?awarin ta daina shi kam yanzun Allah Waya mace zata gaya mishi ya yarda,don in zata shekara tana rantsuwa cewa ita mai gaskiya ce za ya yi wuya ya yarda,bai san tsawon lokacin da ya Wauka yana tunani ba, har zuwa lokacin da ya fita ya nufi cikin falon ya dubi agogo Waya da rabi na dare. Ya ?wanta kan doguwar kujera,ha?i?a wanda ka yarda da shi ka amince mishi ya ci amanarka lallai abin yana da matu?ar ciwo.

A'isha wadda itama ta kasa bacci har lokacin tana zaune kan sallaya ta ji motsin shi, don haka ta mi?e da nufin amsa laifin da ba nata ba. Bai ji shigowar ta ba sai dai jin shashshekar kukanta lokacin da zata tsugunna kusa da shi, ya dube ta sannan ya Wauke kai, cikin muryar da ta ci kuka ta soma gajiya ta soma magana, "Uncle na sani cewa ba zaka yarda da abinda zan ce maka ba, amma gaskiyar magana shi ne ban aikata wannan laifin ba, amma tunda bani da mafita na amshi laifina, ni ce na aikata." Ta ci gaba da kuka, amma ka yafe min, insha Allah ba zan kuma aikatawa ba. Ya dubeta, "Na sani za ki kuma domin baki gama karatun ba, ta girgiza kai ba zan kuma ba insha Allahu don Allah ka yafe min.

Ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, shi kenan Allah yasa. Ta share hawayenta, to tashi kaje ka ?wanta, ya girgiza kai,nan ma ya ishe ni. Zata ?ara magana ya Waga mata hannu sannan ya ce koma ciki kawai, ta mi?e ba ko musu ta shiga ciki. Haka suka yi wannan tafiya cikin rashin walwala don ya kasa sakin jiki da A'isha,mahaifanta ta Kano za su tashi don haka ba su haWu da su ba lokacin tafiyar,sun ci gaba da gudanar da aikinsu yanda ya kamata, lokacin da A'isha ta ganta gaban Ka'aba sai ta ji tamkar ba gaske ba,nan ta shiga kaiwa Allah kukanta.


**** **** **** ****
Sun dawo da ?wana uku, lokacin su Tabawa suna cikin falo suna musu da Hadiza kan cewa Hadizan ba tasa ba gashi sun je sun dawo babu wata matsala? Ita ko Hadizan cewa ta yi sai dai in mugunta Tabawa ta yi mata ba da jar jakar zasu tafi ba. A'isha ta yi sallama ta shiga, duk basu jita ba sai da tayi sau uku sannan suka dawo cikin hayyacinsu, tsaraba A'ishan ta basu suka shiga godiya,suna zaro idanu ga nasu zaton ta ji su, ita kuwa sam bata san kanme suke musu ba kuma bata iya shiga shirgin da babu ruwanta.

Tsananin ihun Jummai shi ne ya firgita dukkan ma'aikatan da ke gidan, musamman masu mata abinci, don haka duk suka cikawa rigunansu iska, wato suka tsere duk masu ma?otaka da gidan sun ji ihun wanda ta Wauki ?wanaki uku tanayi,ranar na huWu sai suka ji shiru. Bayan wasu ?wanaki biyunne al'ummar layin suka shiga kiran layin wayar Alhaji Saddi? suna shaida masa ya zo ya yi musu agaji domin matsanancin wari ne ke fitowa daga tsohon gidanshi da ya tashi, shi kanshi da yazo ya kasa shiga sai da ya nemo waWanda suka shiga gidan don duba abinda ke faruwa. Jummai ce ta mutu kuma ta kumbura dam! Ko wanka ba'a yi mata ba don duk in da aka taSa a jikinta saluSewa yake yi, sai dai ruwa aka yayyafa mata aka

11 / 13