MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 38.3K words

dubeta a zafafe,kiji nan kafin da safe kiyi ?o?arin sanar da ni kowanene ya yi miki wannan cikin,ya juya fuu ya fita tare da bugo ?ofar.

Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un,wane irin mummunan zato ne wannan Uncle za ya yi min? Ta ci gaba da kuka,ya ma ?i ya saurare na, yau shi ne har da marinta,to ko dai ya daina sonta ne? Shin dama haka ne maza ke yi? To in haka sukeyi me yasa Abbanta ba ya yi wa Ummanta haka? Ta tsorata da lamarin Uncle bata san me zai mata ba washegari cikin kishiyoyi,gara ta san nayi tun yanzun.

Fitar Uncle Tabawa ta mi?e cikin motoci domin tana laSe tana sauraron duk hidimar da ake yi,jin Uncle zai fito ta ruga ta Soye,da gudu ta nufi Hadiza tana faWin. "Antina zo ki ji." Ta shiga rattafo mata duk yanda ta ji, ta ce matar so har da mari ta sha,kin san ta dai dai wundon su na uwar Wakin na ma?ale, ciki tayo can a makaranta an zo a yaudareshi sai kuma Allah yasa ya gane. Hadiza ta ce kai Tabawa? Tabawa ta ce na taSa kawo miki wani labari daga baya ki kaga ba haka ba ne? Hadiza ta dafa ta,ko sau Waya ba'a taSa haka ba . Tabawa lallai ki ce lokacin fitar wannan matsiyaciyar matar ya yi,dama nafi jin haushinta sai inji da waccan guzumar ta bar gani yanzun tana jan zare na barta da ma in gama da wannan ne kai naji daWin wannan labarin Tabawa zan baki goro da safe amma yanzun bari in je gurinta a zuwan na zo in yi mata sannu da zuwa ne, Tabawa ta ce kin yi daidai tama san an sani.

Lokacin da Hadiza ta shigo ta same ta tana kuka da sauri ta ?araso, lafiya A'isha? A'isha ba taji shigowar Hadiza ba sai dai ta ji magana akan ta, ta ce cikina ke ciwo. Hadiza ta ce assha to bari in kira Alhajin a waya. A'isha ta ce ai ya sani ya tafi ya zo min da Likita,harara Hadizan ta sakar mata shi ne zai je yazo da Likitan? A'isha ta Waga kai, Hadiza ta ce, Allah ya sawa?e ta fita. Ta je gurin Tabawa tana cewa Tabawa gaske ne kuwa labarin da ki ka bani? Tabawa ta ce me ki ka gani ke? Hadiza ta bata labarin yanda suka yi, Tabawa ta ce to ke da kin zauna ne ta faWa miki? Ko ance miki kowa ma irin ki ne? Hadiza ta ce ?ar iska ni zata yi wa bariki,ai muna cikin gidan ma ga yanda za a ?washe.

Shi kam fitarshi ke da wuya ya nufi ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?sasan Jummai,tana zaune tana tunanin kada dai ta tura shi yaje kuma komai ya daidaita tsakaninsu? Kai ina ba zai yiwu ba, domin ta yarda da Malam Wari bisa Wari. Sai ko ga Alhaji ya shigo tamkar wani bijimin zaki, da sauri ta mi?e Alhajina lafiya? Ya zauna yana huci, ta ce kayi ha?uri ko mene ne ya ce wane ha?uri zan yi? Ya ci gaba, wallahi ba zan ha?ura da cikin da ba nawa ba, Jummai ta zaro idanu tare da dafa ?irji ban gane ciki ba? Ya ce A'isha mana yarinyar nan zuwana na ?arshe gurinta fashin sallah na samu tana yi, yanzun sai gata ta zo min da uban ciki don ina neman haihuwa shi kenan sai a kawo min shege? Zufa ce ta shiga keto ma Jummai,domin tana tsoron kada a juya a sake juyawa cikin ya zama na shi,ai ko da ta shiga uku.

Ta juyo tamkar ta zuga shi, amma Malam ya ce mata babu wannan aikin ta ba zai tafi da zuga ba sai da kissa ta daure ta ce to Alhaji ko dai zuwan naka na ?arshen ne ta samu cikin? Ya dubeta ta tana hailar ne za ta samu cikin? Jummai ta kuma jan dogon numfashi,ka dai a hankali, ya ce ke ni fa ba batun hankali cikin wannan lamarin, ta ce to ni bana sone ka ce zaka rabu da ita,ga mamakinta sai ta ji ya ce babu batun rabuwa amma sai na ji uban da ya yi mata wannan cikin,shiru Hajiya Jummai ta yi ilahirin jikinta kuwa rawa yake yi. Ta daure ta ce in ka samu wanda ya yi cikin tunda mu musulmai ne sai ka tuntuSi malamai, ya dube ta ke ce kika fini sanin yanda zanyi? Ta ce a'a ya ce ki bar ni ya mi?e ya nufi gefenshi. Da kallo ta bi shi,takan rasa gane kanshi wasu lokutan itama Waki ta shiga ta kira Karima Aminiyarta, don jin wane mataki ya kamata ta Wauka don cikin nan ba ?aramin firgita ta ya yi ba.

Tsam, ta mi?e ko jakar ratayawa bata Wauka ba domin tasan babu ko taro ciki, ta nufi barin gidan tun kafin gari ya waye ya yi mata tijara, gidan Anty Nafisa ta yi nufin zuwa saboda yanzun dare ne.

Da safe sai ta amshi kuWin mota a hannunta ta nufi garinsu. Kafin ma ta iso babban titi ta samu mai mashin cikin mintuna suka isa gidan Nafisa sai da ya jira ta shiga ta amso mishi kuWin. Mamakin ganin A'isha ya hana Nafisa zama har A'ishan ta dawo daga gurin mai mashin Win in da suka shiga Wakin baccinta suka zauna bakin gado, Nafisa ta zuba ma A'isha idanu lafiya kuwa? A'isha ta nisa hawayen yana zuba daga idanunta,ta shiga rattafo ma Nafisa halin da take ciki da kuma wanda ta shiga yanzun nan,baki Nafisa ta saki tana kallon ta, lamarin kamar almara, ta ce shi da kansa Brother ya ce ba cikinsa ba ne? A'isha ta ce wallahi ya ma ?i ya tsaya ya saurareni, balle ma yasan ga yanda Ubangiji ya juya lamarin cikin. Nafisa ta ce ni ko naji mamaki, amma yanzun yanda za'ayi bari in kira Anty Fatima ba zaki tafi gida ba,nan take ta shiga kiran layin Anty Fatima ko gaisawa ba su yi ba ta shiga sanar da ita abinda ya faru, cikin tsananin mamaki Anty Fatima ta ce,kada ki bar ta ta tafi zan zo da safe.

Ranar dai A'isha bata runtsa ba,?wana ta yi kan sallaya tana me zubar da hawaye, tare da sanar da Allahu matsalolinta. Ko kusa bata so ta tsani Uncle shi yasa take yawan ba shi uzuri, yanzu da haka zuciyarta na bata tabbacin in yaji yanda lamarin ya kasance za ya yarda da ita,?ila ma ya bata ha?uri.

Shida daidai na sai ga Anty Fatima, ta tausayawa A'isha matu?a yanda taga yarinyar ta ?are ta fita daga hayyacinta. Nan Fatima ta shiga faWa tana cewa, lallai Brother irin tsirfar da ya kama kenan Nafisa ta ce kin san ba haka yake ba,ni dai na ce ba haka aka barshi ba. Fatima ta ce shi dai ya sani yanzun dai ki tashi muje gidan Hajiyarmu ke Nafisa tunda mijinki ba ya nan ki zauna duk yanda aka yi zaki ji. Nafisa ta ce muje kurum babu wata matsala zan masa waya ai baya gari ne. Fatima ta ce shikenan mu je, cikin matar Anty Fatima suka tafi. Hajiyarmu ko tashi daga kan sallaya bata yi ba,ta ji sallama ta Wago idanu ta dube su, suka zauna kan kafet suka jira har ta shafa, sannan ta dubesu ta ce lafiya? Nafisa ta ce da sau?i, Hajiyarmu kallon A'isha kurum take yi. Anty Fatima ta ce wallahi Hajiyarmu Brother ne ya taso A'isha fa, gidan Nafisa ta ?wana,jiya,-jiya daga dawowarta daga makaranta har an soma tsiya. Nan ta shiga rattafo ma Hajiyarmu Nafisa tana ?ara bayani, Hajiyarmu tayi shiru Wakin ya yi tsit suna sauraron hukuncin da zata yanke. Ranta Sace amma ba kasafai mutane suka cika gane Sacin ran nata ba sai ?a?anta, ta dube su Nafisa ke da Fatima ku tashi ku koma gidajenku ita A'isha ku barta nan suka ce to, suka mi?e suka fito bayan sun yi musu sallama.

A'isha tana can ma?ale gefe, Uwani ta shigo Wauke da karin kumallon Hajiyarmu, ta dire a gaban Hajiyar, Hajiyarmu ta ce A'isha me ki ke son ci?

A'isha ta ce, sai anjima yanzun bana jin yunwa, to kurum Hajiyarmu ta ce bayan fitar Uwani, Hajiyan ta ce A'isha ki zama jaruma ba ki ga komai ba game da halin namiji,in zaki bincika duk matan duniya komai matsayin mace komai mulkin ta zata sanar da ke cewa ta yi kuka saboda namiji,wata ta yi shi a fili wata kuma ta yi shi a Soye, ta share hawayenta ta zauna a Wakinta kema ina so ki saba na sani kina da ha?uri, to ki ?ara. Sannan ki dage da addu'a wata rana za ki ci ribar ha?urin ki, da addu'o'inki bana so ki sama ranki cewa an mishi asiri ne da sauransu,ki yarda a ranki cewa jarabta ce daga Allah, sannan ko a waya bana son mahaifanki su san ga halin da ki ke ciki,ki zama mai Soye sirrinki zaya kasance ki sanar da su hankalinsu ya tashi ke kuma nan ku zo ku shirya da shi kin ji duk abinda na faWa? Kan A'isha yana ?asa ta ce,eh insha Allah zan kiyaye. Hajiyarmu ta ce na gode yanzun ina son ki ci abinci kinga ba ke kaWai ba ce, sannan ki yi wanka,matso nan ki zuba abinda ranki ke so, sannan ta mi?e in kin gama kiyi wanka bari in hau gurin Alhaji, A'isha ta ce to.

Cikin natsuwa ta yi wa Alhajinmu bayanin komai,shiru ya yi na tsawon lokaci, can ya nisa ya ce "Shikenan ki barta a nan kada a neme shi." Hajiyarmu ta ce, "Ni lamarin shi yanzun yana bani mamaki, haka kurum duk ya bi ya ruWa kanshi, ya hana kan shi sukuni." Alhajinmu ya ce,ki bar ni dashi kawai wannan karon, zan taka mishi birki, Hajiyarmu ta ce bari in shirya maka abin kari, ya ce inda tuwon nan nafi son shi, ta ce da akwai bari inje in Wumama maka,ta fita shi kuma ya ci gaba da nazarin matsalar Wan nasu,ko harkokinshi yanzun ba kamar da yake tafi da su ba,lallai dole ne ya zauna da yaronnan in har yana da wata matsala ne mu sani.

Daren Alhaji Saddi? bai runtsa ba,ya yi duk iyaka nazarin da ya kamata ya yi amma zuciyarshi ta ?i yarda cewa A'isha zata aikata wata alfasha,ya tambayi kanshi cewa to ko cikin ruwa tasha? Domin dai ya tabbata zuwanshi na ?arshe tana Haila. Hajiya Jummai ta so ta lallasheshi amma ya dakatar da ita kan cewa ta barshi ba ya so a dame shi.


**** ***** *****

Yana dawowa daga sallar Asubahi, gefanta ya nufa dole ne ta mishi bayanin inda ta roro wannan ciki? Ko tana nufin taje jami'a ne idanunta sun buWe? Da wannan tambayar ya tura ?ofar ko ina ya duba bai ganta ba don haka sai ya za ci tana bayi,shirun da ya ji ya yi yawa ne yasa shi duba bayin,bata ba dalilinta, ya tsaya shiru sai kuma ya fita gurin Baba maigadi ya nufa,bai amsa gaisuwar da Baba maigadin ke masa ba, tambaya kurum yake masa,Baba ko kaga fitar Beby? Baba maigadi ya ce gaskiya ba wanda ya fita yau, sai dai kuma jiya da dare Hajiyar da ta dawo ta fita, amma bata dawo ba, ya ce ita nake faWa,tun jiya kenan ta fita? Baba ya ce,?warai kuwa ya juya cikin sasan Jummai zuciyarshi tana harbawa, to ina wannan yarinyar ta nufa? Me take nufi? Ya zauna bakin gadonshi ya lalubo wayarshi ba za ya iya tuna rana ta ?arshe da ya kira wayarta ba,nan ya lalubo lambarta ya shiga kira, sai ta yi tayi har ta yanke ba'a Waga ba, shi bai ma san bata Wauki wayar ba ya fito ya shiga mota sai da ya hau titi sannan ya soma tunanin ina ma zaya nufa ne yanzun? Ya kira Nafisa don yasan yanda suke,ya ce mata sister ko A'isha ta zo? Nafisa ta ce, a'a ta dawo ne? Ba tare da ya bata amsa ba ya katse wayar, gidansu Hajiyarmu ya nufa babu kowa cikin falon kai tsaye ya nufi Wakin Hajiyarmu daidai lokacin da A'isha ke shan wani Wan kunun gyaWa da ta tarfa cikin kofi don dai kada Hajiyarmu ta ce bata ji maganar ta ba,yana ganin ta sai ya ji wani sabon Sacin ran.

Ke me ya kawo ki nan gidan? Kina zaton za'a tursasa ni ne in amshi cikin da ban san daga ina yake ba? Ta zuba mishi idanu, muryarta na rawa ta ce, "Uncle da ace zaka saurareni da ka gano yanda Ubangiji ya zo da al'amarin. Ba zan saurari shirme ba, kuma ina so kiyi maza ki fita daga nan gidan, muryar Hajiyarmu ta katse shi gidan ai bana zaton naka ne ko? Ya juya da sauri, kada ku yarda da dukkan abin da yarinyar nan zata gaya muku."

Hajiyarmu ta ce, "to ubana." Jin haka yasa shi yin shiru tare da kauce mata daga hanya. Ta nuna ?ofa sai anjima ko? Zai yi magana ta haWe fuska,sai ya fita domin babu sha?uwa tsakanin su ko in ce suna jin nauyin juna.

Saman Alhajinmu ya wuce, Alhajin yana cin tuwanshi, Uncle Win ya shigo da sallama,kan kafet ya zube ya dubi Alhajinmu ga mamakin shi sai yaga fuskar Alhajinmu tamkar hadarin mangariba murtuk, iya tsawon rayuwarshi bai taSa ganin Alhajin cikin wannan yanayin ba,nan take fargaba gami da tsoro suka shige shi cikin sanyin jiki ya zauna kan kafet ya soma da gaida Alhajin a dake kuma ba tare da ya dube shi ba ya amsa zai tashi Alhajin ya dakatar dashi da hannu.



######
[12/20, 23:02] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 7*


Ya koma ya zauna cike da tunanin me zai biyo baya,ya san Alhaji tamkar yunwar cikinsa, dattijo ne mai sau?in kai mai zafi kuma ga wanda ya taSa shi, sai da ya gama karyawar shi tsaf sannan ya dube shi jeka Wauki matarka kuje gurin Doctor gani nan zuwa,za ya yi magana Alhajin ya katse shi da cewa, kada ka ce min komai bana son ji, Uncle ya mi?e ba tare da cewa ?ala ba, ya fito yana tunanin shin me yarinyar nan ta faWa ma mahaifansa ne da zafi irin haka? Na shi ganin ai ita ce da laifi,laifin ma mai girma.

?akin Hajiyarmu ya koma shima ranshi a Waure ya ce ke taso, Hajiyarmu ba ta ce ?ala ba, ganin haka sai A'isha ta mi?e ba tare da tasan inda za suje ba,ko cikin mota ?ala bai ce mata ba ita kuma ba tace mishi ba, sai dai taga sun tsaya asibiti. Tun kafin su iso Likitan yasan da zuwansu don sun yi waya da Alhajinmu, don haka suna zuwa Likitan ya shiga yiwa A'isha tambayoyi.

Tun yaushe rabonki da al'ada? Uncle ya zuba mata idanu yayinda shi kuma Likitan yake ?an rubuce-rubuce, ta ce yau ?wana shida kenan, Likitan ya ajiye biron hannunshi ya Wora hannuwanshi kan teburin shi tare da maida hankalinshi kacokan gurinta,kina nufin duk wata kina al'ada? Ta ce eh, cikin ya shiga ne bayan wanda ya fita anan watanni bakwai da suka wuce? Babu wanda ya ji takun sawun Alhajinmu sai kaWai muryarshi suka ji ya ce ai cikinne bai zube ba, dukkan su suka juya suka dubeshi,ya ?araso yana ce ma Likitan shi yasa na ce ka ciro fayal Win ta ka duba sannan ka duba ta, Likitan ya bashi gurin zama sannan ya ci gaba da aikinshi, Uncle kuwa jinsu kurum yake yi yanzunne ya gano zancan da ta shirya wa tsofaffin nashi suka hau kai suka zauna, bayan tambayoyi da bincike gami da aune-aune sai kuma ya kira wani Likitan daban shi kuma (scan) ya yi mata sai da ya fitar da sakamakon sannan ya ba Doctor ya fita nan dai Doctor ya tattara bayanai ya tabbatar musu cikin nan shi ne dai bai faWi ba, sannan yana cikin ?oshin lafiya. Uncle ya yi zaraf ya ce, "Likita dama in mata suna da ciki suna fashin sallah ne?" Likitan ya zauna ya yi mishi dogon bayani tare da tabbatar mishi cewa akwai matan, kuma itama hakanne ya faru gareta, duk da yanda yake jin tsanarta cikin ranshi amma wani sashen na zuciyarshi na murna da wannan labari.

?warai ya so ya tafi da ita gida, amma sai Alhajinmu ya ce ya kai ta gidanshi can gurin Hajiyarmu, duk da ba taga canjin komai daga gare shi ba,ta ji daWin yanda ya amince da cikin koda suka dawo har yanzun Hajiyarmu bata sakar mishi fuska ba, ya fito ya nufi gida.

Hajiya Jummai ta ?osa ya shigo domin ta ji me yake faruwa, da kanta ta taka har gefen A'isha, amma bata nan lamari fa zaya jagule mata in bata yi Sa'a ba,ga Hadiza kuwa murna ce fal zuciyarta,tasan ?arshen A'isha ne ya zo,wa ya sani ma ko tun jiyan ya dan?ara mata saki? Inji Tabawa, Hadiza ta ce Allah yasa hakanne. Lokacin da maigidan ya dawo bai ce komai ba, Jummai kuwa ta yi ta maza ta daure bata ce mishi komai ba har sai da ya yi wanda ya zauna cin abinci, ita kuma tana kusa da shi tana zuba kissa da salo,can ta ce waini Alhaji daga masallaci ina ka nufa? Ya dubeta, gidan su Alhajinmu naje. Suna lafiya? Ya ce lafiyarsu lau, suna gaida ku." Ta yi shiru don tana son sanin ta ina zata fara batun A'isha? Can sai ta kira Uche wanda yanzun ta Wauke shi zuwa sasanta, ta ce shirya breakfast ka kai wa A'isha ko? Uche ya ce to zaya tafi sai Alhaji Saddi? ya ce bata nan,da sauri ta sha mur sai ka ce gaske,bata nan ina ta je Alhaji kada dai ka ce min ka saki yarinyar nan? Ya dubeta dama na ce miki zan saketa ne? Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a'a, ya ce to ?yamin wannan tambayar, kiyi harkar gabanki wannan ba matsalarki ba ce,ta karkata kai Allah ya baka ha?uri ni kaina bazan so ka rabu da ita ba,dama ganin yanda ranka ya Saci ne. Ya mi?e tsaye ya nufi Wakinshi ba tare da ya ce mata ?ala ba.

Lamarin fa ya dagule wa Jummai lissafi,in

5 / 13