MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   2 / 13

3K to 6K   out of 38.3K words

ya sheda mata sa?on Hadiza sai ta ce kai wannan yarinya da shiririta take, maganin fa yana nan cikin durowarta ta gefen gado na kuma gaya mata shi ne zata taso ka don iya shege." Ya ce "Cikin ne ya matsa mata shi ne ma yasa nazo da kaina." Hajiya Lanti ta soma latsa waya "bari in kira ta mashiririciya." Ta kira ta ce"Hadiza kin manta na ce miki yana cikin durowa?" Ta Wan yi shiru sannan ta ce "A to ni dai nasan na faWa miki." Ta dube shi tana kashe wayar, "kaji wai sai bayan da ka taho ne sannan ta tuna, kuma ta sha ya faWa ciwon cikin." Ya ce "Ai shikenan." Ta buWe fridge ta ciro zoSon ta tsiyaya cikin kofi. "Gashi ni muna ta magana ko ruwa ban baka ba." Tamkar kada yasha, amma sai ya ji ranshi na so,ya amshi na kofin ya Wan sha,sam bai kai na Beby daWi ba,ya dai daure ya sha kusan rabin kofin,ta yi murnar shan da ya yi don an ce ko ya ya yasha,matsalarta Waya ya yi bismilla.

A'isha tana shiga gida falonsu ta samu Hadiza da Tabawa suna tsaye, Hadiza da waya a hannunta,ganin A'isha ta shigo sai ta hau yin wayar ?arya. Ta ce, "Hello ka wuce Darling? Yauwa amma don Allah kada ka je da wannan sarkin nacin,ok kama wuce kai kaWai? To sai ka dawo mijina." A'isha duk tana jin ta, kuma ta yarda wayar suke yi,tana ta kici-kicin buWe ?ofarta. Hadiza suka kalleta suka she?e da dariya, ita dai ta shiga Wakinta ta faWa kan gado, Uncle bai taSa mata haka ba kuma bata taSa zaton wata rana zata zo da Uncle zaya yi mata haka ba,ta jawo jakarta ta ciro wayarta. Nafisa ta kira,tana Wagawa ta ce, "A'isha kun iso ne?" A'isha ta ciji leSenta ta gefe, "Nafisa sai dai wani lokacin yau ba zan samu damar zuwa ba." Nafisa ta ce, "Saboda me A'isha, har kin sani jin haushi da ina ta murna zan samu abokiyar hira,wai ma me ya hana ki zuwa?" A'isha ta ce "Ba komai, da har mun fito da Uncle ya ce bari ya amso ma Hadiza magani." Nafisa ta ce "wai da gaske ne Hadiza tana da ciki?" A'isha ta ce "Gaske ne mana ana ?aryar ciki ne?" Nafisa ta ce "A'isha kenan,baki san waye Hajiya Lanti da ?arta Hadiza ba ne shi yasa ke ko Hajiyarmu bata amince cewa Hadiza ciki gare ta ba, amma ciki Wan duma ne,yaWo yake in ya fito ma ganshi." A'isha ta ce "Haka ne, yanzun dai ki min ha?uri, sai wani ji?on." Nafisa ta ce, "Allah ya kai mu." Suna yin sallama Uncle yana turo ?ofa,?in kallon shi ta yi ya iso gaban gadonta, "Beby tashi muje."

Yana magana yana kallon agogon hannunshi,ji ta yi tamkar ta juyo ta ce ba zani ba, amma tana kallonshi sai ?warjininshi ya hana,?imarshi gareta ta wuce nan, cikin sanyin murya ta ce , "ka tafi Office Winka kawai Uncle,ka yi latti wata rana naje." Ya ce, "amma ni ne nace ki tashi muje." Ta ce, "Ka bar shi mun riga mun yi waya da ita." Ya zuba mata idanu sai ya ji ranshi yana zafi,wato ita wannan haushi ta ji kenan? Ya Waure fuska. " Kina nufin cewa haushi ki ka ji?" Ta girgiza kai, ya ce to in ba kin ji haushi ba, menene na cewa kin fasa? Kina nufin kada in amso mata magani? Ko don ba ke ba ce? Mamaki ya cika A'isha, ta shiga kallonshi a tsorace, muryarta tana rawa ta ce ba fa nufina kenan ba, ya katse ta, "Ke da Allah yi min shiru,ke in kina naki ciwon menene bana miki don kawai na amso mata magani za kiyi fushi? To ki fashe duk wadda na aje sonta nake don ki ji ki sani." Ya juya ya fita.

Kanta ya Waure matu?a,lafiyan Uncle kuwa? Itama ta mi?e ta shiga zirga-zirga a tsakar Wakinta, ba ta taSa shiga cikin irin wannan halin ba, ba ta taSa ganin Uncle ya faWa irin haka koda ga wani ba bare ita. A ?arshe ta ba wa kanta laifin cewa ?ila ya ji haushi ne ba ta bi umurnin shi ba,in ya dawo zata ba shi ha?uri. Ranar dai yini ta yi tana zubar da hawaye.

Shi ko yana fita ya shiga mota har zaya tada Jabir ya rugo da gudu ya ce, "Gani maigida, ya bashi makullin ya matsa gefen direba, maimakon baya da ya saba zama. Ya ?wantar da naganshi a kujera ya yi ajiyar zuciya, ya lumshe idanu. Yana son tuno meke damunshi ne? Jabiru ma ya lura yau kam maigidan nashi ranshi ya na Sace ne. Ko a Office bai ba wa sakatariyar sa damar ta shigo masa da kowa ba, duk da jiran da mutane suke mishi. Ya lumshe idanunshi yana karanta sunayan Allah,kusan minti talatin sannan ya soma ganawa da mutane. KaWan-kaWan zuciyarshi ta soma sanyi, ?arfe biyu yana zaune a ?ayataccen gidan cin abincin da nan ya kan ci abincin rana. Yana so ?warai ya sha zoSon A'isha, ya Wauki waya ya kira ta lokacin tana zaune kan sallaya har lokacin tana zubar da hawaye gaya ma Allah take yi da sauri ta mi?e ta Wauki wayar, muryarta a dusashe ta ce, "Salamu alaikum." Ya amsa sai lokacin ya ke tunawa sun fa Wan samu matsala da safe, take kuma ya ji a ranshi tamkar bai mata adalci ba, ya amsa da wa'alaikumus-salam , Beby zan samu zoSon kuwa?" Ta ce, sai dai a dafa, ya ce to Uche za ya kawo min ko?" Ta ce eh, ta mi?e ranta ya yi Wan sanyi ta shiga kujuba-kujubar dafa zoSo.

Cikin mintina ?alilan ta gama, musamman da ya ke tana da ?an?ara ta kira Uche da wayarta. Tabawa ?ar rahoto tana kallon lokacin da Uche ya amshi ?wando ya fita,ta shiga gurin Hadiza. "Antina wai menene ake fita dashi cikin ?wando kullum?" Hadiza ta taSa baki,zoSo ne wahalalliya kullum sai ta dafa shi an kai ma maigidanmu." Tabawa ta ce, amma ya kamata a Wauki mataki kan wannan zoSon, Hadiza ta ce,?yale ta tayi,ni dai ba zan iya wahala ba. Tabawa ta gyara zama ta ri?e ?ugunta tare da mi?a kai ta ?an?ance idanu, "Antyna an ce miki haka kawai Hajiya Lanti ta kawo ni aiki nan gidan? Ta cigaba to in baki sani ba bari na sanar da ke, sai da na Wauki al?awarin tarwatsa gidan nan tare da karSar miki ?anci gurin mijinki,ko kin san ni ce na kawo shawarar ace kina da ciki? Shin haka bai miki daWi ba yanzun? Cikin mamaki Hadiza ta matso daf da Tabawa ta ce ,"Da gaske ki ke yi?" Tabawa ta ja tsaki "An ce miki a banza maza suke shakkar aurena? In da zaki ji tarihina tun ina ?ar ?an?anuwata sai kin sha mamaki, domin tun ina ?ar shekara uku na kashe auren wata da Ubana kan daddawa, sannan na hana duk matar da ya auro zama,to ki gaya min auran wa zan bari? Hadiza cikin jin daWi take jinjina kai, sannan ta ce, "Tabawa nayi farin cikin samun ki, to yanzun me ki kace a batun zoSo?" Tabawa ta ce, "Yauwa kin san takan zoSon nan sai tafi ku ?warjini? Don haka ki bar batun zoSon a hannuna kina nan za a gabza rigima takan tsinanne kuma a daina yin shege,in kun bar ni da yarinyar nan ba sai an kai ta gaban malami ba,tsabar kissa ma ta isheta, ita kuwa waccan tsohuwar guzumar biyu zamu haWa mata." Hadiza cikin murna ta kai hannu suka tafa da Tabawa, tare da cewa. "Haka ni ke son ki ?ar gari."

Misalin ?arfe shida saura ya shigo, Tabawa ce kurum zaune a falo tana kallon T.V da sauri ta mi?e tana mishi sannu Alhaji sannu da zuwa,ya ce yauwa ya nufi Wakin jummy. Ta yi karaf ta ce "Ta fita Alhaji bata nan." Ya dubi Tabawa,a ranshi baya son irin waWannan mutanan, ya nufi Wakin A'isha,tana zaune kan kujera fuskarta na kallon T.V amma zahiri ba tasan me ake yi cikin a?watin ba, har yanzun in ta tuna kalaman Uncle suna soya zuciyarta,sam bata ji murWa ?ofar shi ba, kuma bata ji sallamar shi ba. Ya tsura mata idanu ya ce "Beby." Ba ta ji ba,ya sake cewa "Beby." Da Wan ?arfi ya yi maganar, firgigit ta ce "Na'am."



######
[12/18, 21:24] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 3*



Ta dubeshi ta zamo ?asa tana mishi sannu da zuwa. A sanyaye ya amsa ta mi?e kamar yanda ta saba,ta Wauko mishi ruwa ta cika kofi ta mi?a mishi cike da girmamawa,ya amsa yana kallonta, ya zauna yana sha,yasha kusan rabi kafin ya dube ta, Beby ba ki da lafiya ne? Ta dube shi hawayan da take Soyewa suka sulalo, cikin rawar murya irin ta masu kuka ta ce "Uncle don Allah ka yi ha?uri." Ya matso ya Wagata ya rungume yana shafa kanta,ina tsokanarki ne fa Beby,ba wai faWan gaske nake miki ba, daina kuka ya shiga share mata hawaye,kusan minti biyar yana lallashinta sai da yaga tabbas ta ha?ura sannan ta yarda kan cewa yana mata wasa ne sannan ya fita.

Tabawa tana son sanin me yasa Alhaji ke daWewa a Wakin A'isha, duk in ya shiga ba ranar girkinta ba? Kuma me yasa sauran Wakunan baya daWewa? ?akin Hadiza ya nufa wadda tuni Tabawa ta sanar da ita dawowarshi, ta kuma bata shawarar cewa tunda ita ce dashi ta aje ciwo ta tashi ta yi shirin amsarshi, ta kuma ce wannan garin maganin da na baki ki tabbatar cewa kin yi tsarki dashi." Ta juya da sauri zata fita don kada ya isko ta ciki,ta juyo ta ca "Af,na manta ki tatsi kuWi dai." Ta fice dai-dai lokacin da shi kuma ya fito daga gurin A'isha kamar ya wuce sai kuma ya tuna ya bar ta babu lafiya,don haka sai ya shiga. Tana cire kaya zata shiga wanka zaninta na Waure a ?ugu ta cire riga ta juya tana mishi sannu da zuwa,ya dubi ?irjinta ya kauda kai, ya ce kin samu sau?i kenan? Ta yi fari tare da cewa sosai ma,ya ce mun gode Allah, bari in shiga in Wan watsa ruwa kafin a kira magriba.

Bayan sallar isha'i ya gama koman shi har yanzun zuciyarshi tana tana tausaya ma A'isha tana ?ara son Aisha tana muradin yarinyar sosai, ya kasa sukuni saboda Sata mata ran da ya yi gani yake har yanzun tana can ranta Sace, saboda bata iya fitina ba, ya Wauki wayarshi ya kira ta ta Waga ya ce, "A'isha me ki ke yi ne yanzun?" Ta ce, "Ina kan sallaya ne ina Istigfari yau duk ban samu zama ba sai yanzun." Ya ce, "Allah sarki, Bebyn Uncle yau ya Sata miki rai ko? Kiyi ha?uri..." Ta yi saurin katse shi da cewa,kar kace haka Uncle,kada ka bani ha?uri,ba ka min laifi ba,kai babba ne ba na zaton zaka yi abinda zaya sa har ka bani ha?uri,ta yi ?ar dariya,mun wuce gurin komai ya wuce, ya ce "shikenan Beby kiyi bacci tare da mafarki mai daWi" ta ce kaima haka.

Sha Waya da ?wata Hadiza ta shigo Wakin maigidan, lokacin yana zaune gaban laptop jikinshi sanye da fararen kar Win kayan bacci, ya ji shigowar ta amma saboda bata yi mishi sallama ba sai ya?i Wago kanshi,ta zo ta zuba yatsunta a kafaWarshi, lokaci guda kuma ta sumbaci kumatunshi, har lokacin share ta ya yi,ta manna ?irjinta da bayanshi tsaf ya tsaya sannan ya ce wai Hadiza yaushe za ki koyi shiga wuri da sallama ne? Ta sa hannu ta matsar da laptop Win,ta ?wanta a cinyarshi ni da Wakin mijina sai nayi sallama? Ya ce ko Wakinki zaki shiga ya dace kiyi sallama,tasoma yi mishi wasu salon nata da ta haddace su, na jan hankali,kafin wani lokaci ta zurma shi sai da suka yi nisa ya WanWani maganin ta lura kuma ya soma zaucewa, sannan ta yakice shi ta Sata rai, ya kasa Waurewa ya soma lallashinta ta ce ita shikenan kullum sai dai ya ?wanta da ita ba ya bata komai,ta gaji, ranshi ya Saci amma ba zaya iya ha?ura da abinda ya WanWana ba, cikin za?uwa ya ce gaya min me ki ke so tunda ke ba zaman aure ki ke ba,babu yanda za'ayi in amshi ha??ina gare ki sai na biya? Ta ce zaka sai min mota? Ya ce a'a ki je abinki, ta ce to in zaka bani dubu Wari to in ba zaka ba ni ba shikenan. Ta kuma ?wanta,don ta sani dole ne ya dawo mata tunda shima ba baya ba, ballantana ya dangwalo wannan la?anin nasu wanda suka yi wa la?abi da sa maigida hauka, yanda kuwa ta yi tunanin haka ne kasa jurewa ya yi sai da ya nemo ta tare da amincewa zaya bata dubu Wari, amma abinda ya ba shi mamaki irin daWewar da ya yi har kusan Asubahi ya kasa biyan bu?atar shi, sai da ?yar, tun a nan ya soma zargin ta yi amfani da wani abu tunda yasan kan shi.

Hajiya Kari ta kalli Hajiya Jummai," ke matsalarki kenan, kullum in an ce miki ga wani malamin sai kina gida ba su iya aiki ba,kin fi son na daji ko na ?auye, alhalin irin Sarnar da na gidan keyi,zaki sha mamaki" Jummai ta ce to ai ni sai in zata na cikin gari imani ne dasu ba za suyi maka wani abin ba, Karima ta ?washe da dariya sannan ta ce, "Bari in sanar da ke wani abu,kin ga wannan malamin da na ce muje gurinsa? Bata jira amsa ba ta ci gaba "Tantirin malami ne,kin san mun ci karo da gwamnan garin nan a gurin shi ranar da na je da daddare? Jummai ta ce, ke haba? Kari ta ce, wallahi ban ma gane shi ba shi kaWai ya zo a sace, malamin ke faWa min." Jummai ta ce in ko haka ne muje domin duk wanda ki ka ga ?an siyasa suna zuwa gurinshi kin san ya yi ne. Karima ta ce haka ne, yanzun dai abinda nike so da ke in mun je ya buga bai ga mutuwar kishiyoyinki ba, to sai ki ce mishi ya yi miki na wani abin abu ko ciwo ko hauka,ko ki dinga haWa su husuma da maigidan,ke kuma ki koma kiyi ta lallashin mijinki."

Jummai ta ce "ai ni na tsani in gansu ne a gidan,Kari ta ce in lokacin mutuwarsu bai yi ba ya za kiyi? Jummai ta ce haka ne, tunda gashi nayi-nayi Win sun ?i mutuwa, musamman wannan A'ishan duk nafi jin haushin matsiyaciya, wallahi da za a bani bindiga ace in kashe wanda na fi ?i ko? Wallahi Kari A'isha zan kashe ita ce mutum ta farko da ta karya min ?warina, irin kuWin da na narkar kan ta mutu yarinyar nan ko ciwon kai bata yi ba, sai ma Waukaka da kullum take samu gurin miji, nasara Waya na san na samu kanta shi ne cire cikin nan nata." Karima ta ce, "yanzun dai in mun je gaban Malam ki baje kolin matsalolin ki. Jummai ta ce shikenan.

Misalin ?arfe huWu suka isa gidan Malam, Kari ce ta zaSar musu wannan lokacin a cewarta ba'a cika samun layi ba, mutum biyu suka samu. ?aya a ciki Waya na zaune kan Waya daga cikin kujerun da ya jera a cikin zauran nashi,don zaman jiran shi. Suka dubi na zaunen suka ce da ba?i ne ko? Ta ce eh. Jummai ta kuma kallon matar lallai wannan mutumin da gani mai yi ne, tunda ta ga irin waWannan mata.

Tunanin ta ya tsinke lokacin da taga waWanda suka fito daga cikin Wakin Malamin suka kalli juna ita da Karima kamar yanda suma waWanda suka fito daga Wakin Malamin suka kalli junansu, mai jira ta shige gurin Malamin daidai lokacin da Hajiya Kari ta ce (cikin kissa irin ta matan bariki) a'a Hajiya Lanti duniya ashe kema ki kan zo wurin Teacher? Lanti ta gyara zama cikin ?arfin hali ta ce, a'a ai mu sai da su muke iya kama gashin kuma ko'ina sai mu cinye mu bada siWi." Karima ta ce,ana ki tunanin kenan, tunda dai jin ta take tamkar ta dawo ta koma. Hadiza kuwa ita ma duk ta warware kallon kallo suke yi wa juna, Hajiya Lanti ta kama hannun Hadiza suka tafi. tana cewa wa kada ki damu ni dama ai na daWe da sanin Jummai a wannan fagen sai dai ita da kanta ta sheda cewa ko gidan giya akwai babba,ta jima da sanin cewa ina samanta.

Ita ko Jummai ta kalli Kari ta ce, "Anya zamu shiga gurin Malamin nan? Kari ta ce, shiga kai,in kinji shiga Waya kenan." Ta ci gaba da cewa, "ke dai shawarata da ke Waya ita ce,ki saki kuWi in har ki ka cire ma?o, to har sirrin su sai mun ji a gurin shi." Jummai ta ce kuma zai faWa? Kari ta ce, sosai ma,in kin ji faWi Waya kenan. Da zaki ji tawa ma tashin farko ki bashi kujerar Makka,kin san Allah da kin sha mamaki." Kafin ta ce komai har ta ciki ta fito,dan haka Kari ta yi saurin jan hannun Jummai suka shiga.

Yana zaune kan wani farin ?aton buzu, gabanshi wani ?aton carbi ne da wata ?asa cikin faranti ko ina in ka kalla zaka ga kaya,?walabe ne, litattafai ne da dai sauransu, suka zauna kan tabarma,ya Wago ya zuba masu idanu zuwa can ya ce "Hajiya sannunku da zuwa,a tare suka amsa sannan suka gaidashi, Kari ta fara da cewa, " Na zata baka gane ni ba" ya yi ?ar dariya sannan ya ce me zai hana ni gane ki Hajjaju? Ina fatan dai aikin naki ya yi ?yau, ta ce fiye ma da yanda na zata, shine dalilin da yasa na kawo Aminiyata domin tata matsalar ta doke tawa,Malam ya jinjina kai ya mi?a ma Jummai ?aton carbi tare da cewa gashi ki Wauki Waya, har sau uku tana zaSa sannan ya bubbuga charbin a ?asa ya ri?e shi jim ya ce Hajiya kina da abokan zama, kuma ba ?ya bu?atar zama da su

2 / 13