MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   3 / 13

6K to 9K   out of 38.3K words

ko? Ta gyara zama, hakane, ya ce ya ya sunannasu? Ya jawo tiren ?asar gabanshi ta ce "Malam Hadiza da A'isha, amma nafi son komai ya fara takan A'isha,don tafi shige min gaba,na tsani yarinyar sosai. Ita ce ta soma karya min gwiwata, ta karya min shirina a cikin kishiyoyin da ake min ita ce ta fara kai labari har ma ta buWe fagen da ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aka ?ara min wata kishiyar, cikin zafin rai ta ke maganar. Malam ya Waga mata hannu ya ce, bari mu bincike su mu gani, ya Wan jima yana zane zananshi da ?asa cikin farantin, ya yi ya share,yana girgiza kai har ya gama, ya Wago kai ya dube su, dukkan su sun ?agauta da son jin sakamakon. Ya yi gyaran murya ya zuba musu idanu tare da fara yi musu bayani kamar haka.

"Wato ita wannan A'ishan da ki ke faWa ta banbanta da sauran mata da yawa, tauraronta yasha banban, wani tauraro gare ta mai ?arfi wanda yana wahala in kin tara mata dubu da wuya ki samu Waya mai irin shi, duk wadda ta kasance tana da wannan tauraron yana wuya ayi mata sihiri ya kamata, sannan duk inda ta shiga zata kasance mutane na sonta don zata kasance mai ?warjini,kin ga ke nan dole ta fi ku samun shiga gurin maigidaku,da ma danginsa." Jummai ta soma share zufa, "to yanzun Malam ya ya za'ayi mata?" Ta ci gaba, "shi yasa nike ta tafka asarar kuWina?" Malam ya ce, wannan shine gaskiyar magana, batun abinda zamuyi mata kuwa sai dai mu haWa da maigidan naku in muka biyo mata ta bayan gida zai fi mana sau?i, ita ko waccan yanzun zamu duba muku ita." Jummai ta yi karaf ta ce, "Malam ita ce muka ga sun fito daga nan ita da Hajiya Lanti." Ya zuba mata idanu, "kina nufin Hadizar Lanti ce Wayar kishiyar taki?" Ta ce "Eh." Ya yi Wan murmushi, "wannan nasan kowace ce bana bu?atar duba komai kanta."

Hajiya Kari ta ce," To amma hakan ba zaya hana ayi mana aiki ba dai ko?" Ya yi Wan murmushi, "Sam illa dai wadda tafi ?in jakarta aikinta ya tafi dai dai,in ko mutum ya so jakarshi nima in ri?e aikina." Jummai ta buWe jakarta ta ciro Waurin ?an dubu-dubu Wai-Wai ta dire gabanshi,sannan ta ce Malam me ya kawo Hadiza? Ina nufin da wace bu?ata ta zo?" Duk da ba tace kuWin na shi ba ne ya saka hannu ya Wauki kuWin ya juya su, sannan ya aje gefenshi ya ce,ta zo ne da bu?atar korarku,burinta shi ne ta mallake gidan da maigidan da dukkan abinda ya mallaka." Jummai ta yi murmushi, sannan ta ce, "Ni ko ban?i ace duk sun rasa rayukansu ba, amma yanzun Malam na baka zaSi me ka ke ganin za'ayi musu? Sannan ina son duk aikinta kar a mata cikin da ta ce tana da shi a zubar, sannan in ta zo da wani bayani in sani, kullum a dinga yi min binciken kome suke ciki." Malam ya ciro kuWin da ya ajiye a gefe ya ce duk a wannan kuWin? Ta ciro irin su ta aje mishi sannan ta ce, "Me za ka bani in soma dashi yanzun?" Hajiya Kari ta ce, "Malam ka mata wanda zata san kai me yi ne ba irin waWanda da an ce ga bu?atar da ake so sai su hau cewa Allah ya ce ba, yayi wata dariya sannan ya nuna Karima ya ce, "Ai ke kin sanni, wata roba ya ciro fara cikinta wata ?atuwar tsoka ce gata nan kamar zuciya,ya mi?a mata kin san wannan? Ta girgiza kai,zuciyar mutum ce ta zaro idanu ya ce ri?e da ?yau aikin wani da zan yi shi ne na fasa zan baki nasa a ciro min wata." Ta ce "a jikin mutanan ake cirowa? Ya ce to da ina za'a samu? Ta tsorata Malam da sassan jiki ka ke aiki? Kari ta katse ta tsoron me zaki ji bayan ke kanki rai nawa ki ka salwantar? Jummai ta ce amma ban taSa amfani da sassan jikin mutum ba,Malam ya mi?a mata hannu bani in kina ganin ba zaki iya ba ne, ta ce, "zan iya Malam, yi ha?uri." Ya mi?o mata wata leda tare da cewa, "buWe ki gani."

Wasu allurai ne cunkus cikin wani gari ba?i, ya ce " Guda Wari ne da Waya, kullum ki dinga tsira Waya jikin wannan zuciyar,in zaki tsira ki ambaci sunan maigidanku sannan cikin zuciyarki ki ?udurce cewa aikin yi ci, kada kiyi wasi-wasi da zaran kin yi wasi-wasi aikin ba zai ci ba, sannan aikin za ya yi tasiri ne kan maigidanku, duk wadda ki ka soma tsira alluran da nufinta cikin kishiyoyin to ita kaWai ce zata samu matsala da mijin naku.

Sannan aikin mutum Waya ne,Wayar za'a mata nata daban, ta ce to wannan na A'isha ne? Ya ce shikenan,in kun dawo zan baki na Wayar, sannan kada ki ?agara fa, don yanda kike soka allurar nan da ?aWan-kadan haka aikin zaya dinga ci da kaWan-kaWan,ta ce shi kenan, sannan kada ki ajiye inda za'a gani fa, ta ce to.

A'isha tana ?wance sai zabga Game take yi, cikin wayarta sam bata ji shigowar Uncle ba,sai...



#######
[12/19, 15:33] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 4*



Sai da ta ji an ja mata yatsa da sauri ta tashi tana faWin Hasbunallahu wani'imal wakil" Ganin Uncle yana mata dariya sai ta tashi tana dariya, ya ce,"Beby kin cika shegen tsoro." Ta mi?a mishi kofin ruwan cikin risinawa tare da ladabi ya amsa cikin farin ciki sannan ya zauna a hannun kujera yana sha,ta zuba mishi idanu, komai na Uncle birge ta yake yi, ya Wago idanu ya kalleta ta yi murmushi shima yana murmushin ya ce kin san dame nazo miki? Ta girgiza kai, ya buWe jakarshi ta Office ya fiddo takardu ya mi?a mata,sai ki zaSi garin da ya yi miki, duk dai makarantun suna da ?yau, cikin murna ta shiga dubawa ta dube shi cikin Woki Uncle zaSa min Kano ko Sokoto,ko A.B.U za ni? Ya dinga yi mata dariya, kafin ya ce ke wacce ya fi ?wanta miki cikin su? A'isha ta yi shiru alamun tunani,can ta ce Sokoto ko Maiduguri, ya ce gara ma Sokoto, amma Maiduguri ya yi nisa sosai, daga nan. To shikenan Uncle na gode, cewar A'isha kenan.

Cikin abinda bai fi sati biyu ba, Uncle ya Wauki A'isha, Jabir ne ke jan su sai Sokoto.

Masauki ya kama musu cikin wani shahararren Hotel. Suna sama Jabir kuma a ?asa, ya kama mishi ?wana biyu suka gama amma yanda Uncle ke samun kulawa gurin Bebyn tashi, sai ya kasance tamkar kada su dawo,don haka suka ?ara ?wana uku ita kanta A'isha ta rubuta waWannan ?wanakin cikin zuciyarta.

Bayan sun dawo sai kuma aka shiga shirin tafiya makaranta, sannan ta ziyarci Jigawa ?wananta biyu su Hajiyarmu da su Anty Fati duk tayi musu yini,nan ne ma Nafisa ta bata lambobin wasu ?awayanta,kan cewa zata haWa su ?a Sokoto ne, kuma duk ba su da nisa daga makaranta. A'isha ta ji daWi,dama bata san kowa ba, Nafisa ta sake tabbatar mata cewa zata ji daWin zaman makaranta,don ita ma nan ta gama,ta ce mata waWannan ?awayan nawa wayayyu ne musamman harkar ri?e miji,ba ma kamar Maimuna Win nan , A'isha ta yi godiya tare da shan alwashin neman su, A'isha ka bata wasa da duk hanyar da ta ji an ce in tabi zata ?ara samun kusanta da mijinta matsawar ba hanyar saSon Ubangiji ba ce.

Komai na ?an gata Uncle ya haWa mata, wani gatan ma sai da suka isa garin Sokoto,dama gida ya kama mata, cikin makaranta ?wanansu biyu a hotel yasa ana ta gyaran gidan sai ka ce gidanshi,kaya yasa aka siyo aka shirya gidan tamkar sabuwar amarya ya zuba mata komai sabo ga kayan wuta har da laptop Win ta sabo, ya shirge mata abinci, shima sai da ya ?wana a gidan sannan suka je ya buWe mata account, tamkar kada su rabu lokacin da zai tafi, A'isha har da kuka.

Ya samu dai ya lallasheta, tare da yi mata nasihohi, sannan ya tafi. Ta koma ciki tana kallon falon, yanda ya tsaru ta shiga bedroom Win ta faWa kan gado,duk kewar Uncle ta dame ta,ita dai a rayuwa ta gode ma Allah,don bata isa ta ce ga abinda Uncle ya yi mata ba a tsawon rayuwarta a gidanshi,ta sani Uncle rainonta yake burinshi kullum ya faranta ranta,ya ji da ita daWi, ya fidda ta tsara cikin ?awayanta, Uncle koda wasa bai taSa yun?urin Sata mata rai ba,ko ta ko'ina abinda take so shi zata ci shi zata sha shi zata sa hannun iyayanta. Ta kula ko gurin auratayyane burinshi yaga ta shiga nishaWi, shi yasa itama ko yaushe ba ta da burin da ya wuce mishi biyayya tare da neman hanyoyin ji da shi daWi daga ni'imar da Allah ya yi mata. Kafin ya isa gida sun yi waya kusan sau goma, shi ya kira itama ta kira,shi kanshi bai san ya yi kewarta haka ba sai da ya yi ?wana biyun shi na sauran matan da ace tana nan da yau ita ce da shi,a zuciyarshi A'isha daban ce yana sonta,tana kula da shi tana da baiwar da ba duk mata ba,in yana kusa da ita ya kan manta da duk wata ?a mace a duniya. Addu'a kullum yake mata, Allah yasa da ta da rahamarshi duniya da lahira. Haka dai ta dangana ta rungumi karatun ta ka'in da na'in.

Jummai da Hadiza kuwa, duk sun mi?a lamarinsu ga boka, ko in ce Wan tsibbu. Jummai kam yanzun ta yarda Malamin nan zai share mata hawaye da A'isha ta jima tana sa ta zubarwa,ta gane hakanne lokacin da ta tinkari Alhajin da maganar son ya yi mata ginin da ya jima yana son mata a cikin gidan, daga baya ya share zancan. Alhajin bai Musa ba, ya ce zai sa a auna gurin duk dai da cikin gidanne. Malamin ya ce ta haWa da ladabi da biyayya, don haka yanzun wani sabon ladabi ta samo.

Hadiza kam tafi ga magungunan mata irin waWanda ke saka maza fitina, gashi ta ?ware gurin iya jan hankalin namiji,takan zuba mishi cikin ruwa ko abinci in ya ci kuma ta zo da salon tana jan hankali. Ba za ya iya ha?ura ba,don haka sai ta sara mishi kuWi haka zaya bata sannan ta yarda suyi auratayya wa'iyazubillah. Hadiza ba wai ?ya??yawa ba ce, amma irin matannan ne waWanda suka san kan shawo kan maza,ta hanyar fizgar hankalinsu ta iya ?war?wasa sosai, shi kan shi ya so ace A'isha ce ke mishi irin salon jan hankalin da Hadizan ke mishi.

Tuni an soma ginin Hajiya Jummai, gini ne za'ayi shi me tsari, shi kan shi ba zai ce ga dalilin da yasa ya ?u?e kan cewa sai an yi ginin cikin ?an?anin lokaci ba. Hadiza ta dame shi da son sanin wanda zai shiga ginin sai ya ce mata me rabo.

Yau kimanin ?wana sha huWu kenan A'isha ta yi a makaranta, har yau bata saba da kowa ba, kasancewar ta mara saurin sabo,gata miskila bata cika sakin fuska ba,ran da ta cika ?wana huWu ranar ta nemi Maimuna ?awa Anty Nafisa izuwa yanzun sun saba sosai,in bata da lakca can takan je ta yi hirarta, Maimuna wayayyiyar ce ta gaske,tana ganin A'isha ta ga cewa A'isha ta yi mata,tana koyar da ita salo-salon yanda zata da kanta da mijinta,kai har da yarda zata dinga yiwa mijinta magana, tafiya da dai sauransu. Wani kunun Aya,dabino da cukwi da take bata mara suga sai madara,ga wata gumba da take dama ta da madarar shanu, A'isha da kanta ta ji tana sha'awar mijinta. Yau kam da ta je ?in sha tayi ta ce, Anty Maimuna Uncle ba ya kusa gashi kina ta bani waWannan abubuwan sai su dame ni fa, Maimuna ta ce ke baki san yanda zaki jawo hankalinshi ya zo gareki ba ko? Nan ta shiga tsara mata yanda zata yi, sannan ta bata garin bagaruwa ta ce ta ringa tsarki dashi in taji ranar zuwan nashi kafin ya iso.

yanzun haka da take ?wance kan gadonta kusan ?arfe goma tasan yanzun yana gida gaban laptop domin lokacin ?wanciyarshi bai yi ba. Ta shiga murza wayarta shi take nema,jim kaWan layin ya shiga ta juya rigingine, muryarshi ce ya ce "Beby" ta ce na'am Uncle ya ya ka ke? Ya ce lafiya lau ke fa? Ta Wan runtse idanu ta buWe sannan ta ce ina cike da kewar ka,ya cire gilashin idonshi tare da matsar da laptop Win, A'isha nima haka,ta ce,kai ai kana da wasu matan, ya ce, Beby basa min rainon da ki ke min, ba tonon asiri ba ne ko yi dasu,ke daban ce wancan satin fa da kin ganni al'amura ne suka yi min yawa, da kuma tunanin kada ki ce wannan Uncle Win ya nace min. Ta yi ?ar dariya cikin kissa sannan ta ce "Uncle Wina kenan,kana ganin in da zaka zo kullum zaka gundure ni ne?" Cikin mamakin ta ya ce, Beby sai ina ga tamkar ba ke ba, Beby da ba ki iya gaya min yanda ki ka damu da ni ba, da zaran abubuwa sun yi sau?i za ki ganni." Ta ce, to sai da safe, ya ce zan zo miki cikin mafarki kinji, ta ce sai na ganka. Sai ta samu kanta da sumbatar wayar tare da saurin kashe wayar. Sautin kiss Win ya daki dodon kunnanshi ya ratsa dukkan jikinshi. Ha?i?a ta saukar mishi da kasala,yana jin ba za ya iya ci gaba da aikin gabanshi ba, dole ya rufe komai ya tashi. Ita kuwa juyi ta yi tana jinjina ma ?o?arin da tayi tasan in a gabanshi ne duk da Anty Maimuna tana bata ?arfin gwiwar ta ringa mishi hakan ba zata iya ba.

Washegari wuraren ?arfe shida lokacin ta fito daga lakca don ranar uku da mintuna suka shiga, ta buWe gidanta ta shiga dama ta riga ta yi abincinta, magriba kawai zata yi sannan ta ci. Zaman ta kenan sai ta ji ana ?wan?wasa mata gida ta je ta buWe. Wasu ?ammata ta gani su uku, suka nuna mata wani gida kusa da nata,ga gidan mu nan munce ne bari mu shigo mu gaisa, cikin fara'a A'isha ta ce ku shigo ta matsa suka shiga.

Abinka da wayayyun ?an boko,nan suka sake, ita dai taje tayo sallah ta basu abinci suka ci har suna santi, nan suka sanar da ita sunayensu. Saliha da Amina,Kiristar kuma Linda ?ar kaduna ce,su kuma biyun nan Sokoto suke,suma course Win da take yi shi suke yi. Tana zaune dai ta ma kasa cin abincin don bata sake da su sosai ba,su ne dai sukayi tamkar dama sun santa, sai ta ji ana bugun gida, ta kalli agogo cikin zuciyarta ta ce to ko wanene kuma, ?arfe ba?wai da rabi,ta fita tun kafin ta buWe ta ji ?amshinsa, cikin hanzari ta buWe tare da cewa, Uncle tafiyar dare? Jawo ta ya yi zuwa jikinshi ya rungume, tare da faWin I miss You Beby, ta amshi Jakar hannunsa "zo mu je Uncle kai kaWai ne? Ya ce ni da Jabiru ne, sai da na kai shi masauki sannan nayo nan. Anan nayi magriba da isha'i, suna shiga falon ya yi turus yana kallon ?an matan da ke zaune, fuskarshi da alamun tambaya, ta ce ma?otana ne suka shigo don mu saba,ta dube su ga Uncle Wina, nan suka shiga gaishe shi kafin suka mi?e suka ce sai da safe A'isha Mustapha, ta ce na gode. Ya zauna nan ta shiga rawar jikin kawo mishi wannan da wancan,shi kam duk in da tabi kallonta kawai yake yi yana sonta.

Yana cin abincin suna hira tana mishi mitar zuwan ba zatan da ya yi mata, gashi bata mishi wani abu na musamman ba, ya ce shi ai ita ce ta musamman Win shi, cikin ?wanaki ukun da ya yi a Sokoto ya kuma yarda A'isha ce kurum ta dace da rayuwarsa. Haka ya taho da kewar ta itama tana kewarshi, haka abubuwa suka yi ta faruwa lokaci ya dinga zuwa yana wucewa, Uncle yana ziyartar A'isha duk bayan mako Waya ko biyu.

?watsam! Wannan zuwa ya sameta ta tana fashin sallah, kuma ranar ta fara, da ?yar ta lallasheshi ya yi ?wana biyu tare da gamsar dashi ta hanyar wasu ?an dubarun nata.

Wani sabon al'amari tun daga lokacin sati na huWu kenan rabonshi da Sokoto, sannan wayar ma yanzun ba kamar da ba, kullum uzurin yake bata wai abubuwa sun mishi yawa gashi ana gyaran gida, daga baya ma in ba ita ce ta kira shi ba shi kam baya da lokaci. Abin ya soma ba wa A'isha tsoro,nan gefe kuma ga wata matsala da ke damunta. Motsi cikinta ke yi,ta sa rai ya zo ta sheda mishi, amma shiru suna daf da fara jarabawa abin ya matsa mata don haka ta kira Nafisa ta sheda mata,Anty Nafisa ta ce baki gaya ma Uncle Win ki ba? A'isha bata son saurin tona cikinta nata ganin gaske ne uzuri ya yi wa Uncle yawa ne, shi yasa har yanzun bai zo ba,ba zata yi saurin kai ?ararshi ba, ta ce abubuwa sun yi ma Uncle yawa bana son na gaya mishi zaya tada hankalinshi, ya ce zai bar aikin gabanshi ya taho. Nafisa ta ja tsaki,wane abubuwa ne suka mishi yawa baya ga komai da ya tsaida, Ya shiga harkar yiwa Jummai gini. Gabanta ya faWi ta ce gini kuma? Nafisa ta ce bai sanar da ke ba kenan? A'isha ta ce, yace min dai yana gyaran gida. Nafisa ta ce, to ai gyaran kenan, Jummai ya fafaramma gini irin kuWin da yake narkarwa a ginin sai kin gani yanzun ya gama kayan da za'a zuba ma daga (Chaina) za'ayo Odar su, A'isha ta ce to Allah yasa alheri." Nafisa ta ce,au! Ke bakiji haushi ba? Ta ce, to in naji ma Anty Nafisa ya ya zan yi? Tsaki Nafisa ta kuma ja,ke tafi can ke dai son miji ya yi miki yawa,ba ki iya ganin laifin shi. A'isha ta yi ?ar dariyar takaici, sannan ta ce to in ma naga laifinshi

3 / 13