MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 38.3K words

yi mata sallah aka kaita da halinta, aka turbuWe, Allah yasa mu yi ?yak?yawan ?arshe Amin.

Ranar da aka yi ?wana uku A'isha ta koma makaranta ta ci gaba da karatunta. Hadiza kuwa dama haka ta fi burin gani, wato ita Waya a gurin mijinta, kuma har yau Hajiyarta tana nan kan bakanta na nemawa ?arta asirai ?auye da birni,sai dai in ta kawo mata ne wani tayi amfani da shi wani kuma in ta tuna da Jummai da kuma yanda ta ?are sai ta yarda, cikin haka ne ma maciji ya sare ta a wani daji cikin wani ?auye mai suna tsamiya. Da ?yar ta samu waWanda suka taimaka mata suka kawo ta gida, wannan saran macijin shi ne silar yanke mata ?afa, sannan ga ciwon Sarin jiki da ya sameta daga faWuwa zata dogara taje bayi.

Wata ziyara da Uncle Winta ya kai mata a makaranta,ro?onta ya dinga yi kan cewa in har yanzun tana kan bakanta na shan ?wayoyin nan don Allah ta daina,shi ko biyanta ne ma in tana so zaya iya yi saboda ta yarda ta haifa mishi yara, ta yi kuka sosai tare da sanar da shi cewa tunda yana zarginta har yanzun tana mai shawartarshi ya je ya ?ari aure ko Allah za yasa matar ta haihu, kallonta ya tsaya yi kafin ya ce shi kam ya gama aure, ya tsorata da lamarin mata baki Waya, tunda ya sani duk halin su Waya,in kuma ba yana neman wadda zata kai shi kabari ba ne. Shiru A'isha ta yi domin tana hankalce da shi tun lokacin da yaga ?wayoyin nan komai tayi mishi bata birge shi, ita kanta fata take Allah ya bata ciki ?ila shi ne kurum zai sa ya huce. Har dai ya dawo hankulan su ba'a natse ba.

Lokacin da ta kuma samun wani hutun ta zo gida, washegarin ranar ya Wauko Abulkhairi yaron na da wayo bai manta da mahaifiyarshi ba, yanzun ya tattara dukkan soyayyar shi ya maida ta kan Wan nashi, nashi ganin daga mahaifanshi sai ko Wan nashi sune masoyanshi na gaskiya,abin ya Waga hankalin A'isha, domin tunda ta dawo ko sau Waya bai nuna sha'awarshi kanta ba, ya kan saka Wan shi gaba ne su sha baccinsu kuma da safe shi ne yake yiwa yaron duk abinda ya dace uwa tayi mishi,daran ranar da ta cika ?wana huWu da dawowarta ita ce dashi,suna ?wance ya saka Wan nasu tsakiya ta kalleshi jira kurum take yi Wan nasu ya yi bacci zata mishi magana gara ma ita in ya yi mata amma Hadiza fa me ta mishi? Domin ta kula cewa Hadiza ma hakan yake mata har ma tana zargin dawowar A'ishan ne yasa ya juya mata baya, sannan koda gurin Hadizar yake ta daina shiga Wakinshi ta koma ?wana nata Wakin.

Ta dubeshi, Uncle Ina son muyi magana, ya ce ina jin ki, ta ce Uncle duk ka canza min tamkar ba kai ba, ya dubeta ya lumshe idanu, dole ne in koya ma kaina yanda zan cire mata daga raina, saboda me? Ya tashi zaune, Allah ya ce matayanku da ?a?ayanku ma?iya ne a gareku, ta dubeshi sosai amma kuma ya ce idan kukayi ha?uri kuma ku ka gafarta musu lallai shi Allah mai gafara ne a gareku, sannan in ni na maka laifi ita fa Hadiza? Kada ka tauye ha??inta domin Allah ba zai barka ba, ya ce to naji na kuma gode ya koma ya ?wanta. Cikin sauran ?wanakin da suka biyo baya ya Wan canza musu dukansu, ranar Lahadi ba shi da Office an tashi da ruwan safe. Ranar yana manne da Bebyn tashi, Abulkhairi kuwa yana can gurin Tani ta mishi wanka yana ta rigimar za ya ci Indomie, suka nufi kitchen tare, Uncle yana raWa ma Bebyn tashi cewa yau insha Allah sai ya samar ma Abulkhairi ?ani, ta sake rungume shi, Allah ya bamu mai albarka, Allah ya amsa.

Cikin shirin tafiya masallaci sallar azahar ya shigo Wakinta, fitowarta daga wanka kenan, ya dubeta da murmushi na zaci zan sameki kina bacci? Ta ce haba dai sallah zan yi in sama maka abinda za kaci, ya fita yana cewa da kin ?yauta, ina Babana mu je masallaci? Ta ce yana falo.

Ta gama shirya tebur Win da kalolin abincin da ta yi su cikin lokaci kaWan, sannan ta nufi Wakinta don ?ara gyara jikinta, ta kalli agogo ta sanya tsayin la'asar ne ta ci gaba da shafe-shafenta a gaban madubi, Abulkhairi ya shigo da gudu hannuwanshi cike da kalolin sweet da cakulet..



#######
[12/23, 21:20] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 15*



Yana cewa gashi Ummi Abbana ne ya bani ta ce cin za?in nan ya yi yawa sufa ka ci kafin ka fita,ta amshe muje ka ci abinci,ya soma kuka ta Wora shi saman teburin cin abincin zauna nan in sa maka abinci,tun daga harabar gidan yake jiyo kukan yaron, da sauri ya shigo me ya samu Babana ne? Ta dubeshi Uncle cin za?in Abulkhairi ya yi yawa fa,shi ne na amsa na aje ya iso yasa hannu ya Wauke shi kasan in da ta Soye? Ya Waga kai alamun Eh, ya ce muje in Wauko maka, cikin marairaita ta ce, yanzun Uncle Wauko Mishi za ka yi? Ya ce haba Beby za?in nan da mai?o shi ne ya kawo kakanninmu da iyayanmu birni bar shi ya ci ko Babana? Ya ce eh, tagumi tayi ta rakasu da idanu har suka shige Wakin ta kai tsaye ya nuna durowar madubin ya jawo yana ?waso mishi gabanshi ya faWi lokacin da ya kuma arba da ?walayan.

Shirun da taji ya yi yawa shi ne dalilin da yasa ta bin shi domin tuni yaron ya fito da kayan za?insa a hannu, zaune ta same shi bakin gado ya ri?e kai da sauri ta isa gurinshi, Uncle lafiya kanka ne yake ci....?" Hannu yasa tare da Wauke ta da wani mari mai saka mutum yaga wuta, ya mi?e tsaye ki haWa kayanki ki tafi garinku ki je kiyi boko tunda shi ki ka fi so fiye da auranki,ku na.....ba tasan lokacin da ta daka tsalle ta faWa jikinshi ba, kada ka furta Uncle,ban maka abinda zaka sake ni ba, ta soma kuka mai tsanani, ya isa gurin durowar ya ciro ta gaba Waya ya yarda ita ?asa,kin ce kin daina gashi Allah ya kuma nuna min ki sani duk macen da bata son ta haihu da mutum to ko shakka babu bata son shi ne, kuma bata ?aunarshi,kin fi ?aunar boko, ta tsura ma ?walayan idanu, wasu hawaye masu zafi suka soma sunturi a kumatunta,ha?i?a na cancanci ka rabu dani tunda na kuma aikata laifin da na Wauki al?awarin tuba daga gare shi ta mi?e ta soma haWa kayanta, shi kuma ya fita ya Wauki Wan shi ya fita rai Sace suka yi waje.

A'isha kuwa tuni ta soma haWa kayanta,tana gamawa Jabiru ya shigo, maigida ya ce zamu yi tafiya ko? A'isha ta yi ?arfin hali ta ce eh, yawan kayan da yaga ta fito da su kuma ba yaron shi ne yasa shi tambayar anya Hajiya lafiya? Ta ce lafiya lau,nan ya shigar da kayan bayan mota suka Wauki hanya, lokacin da suka kusa isa garin na Jigawa tuni ta tsure ta shiga tunanin me zata ce da mahaifan nata anya kuwa zasu yarda da ita? Lallai maza ba su da tabbas dubi abinda ya dinga yi mata can baya ta daure ta ha?ura ta yi ta bashi uzuri amma shi gashi ya kasa bata, cikin wannan halin suka isa Jigawa duk da gudun da Jabir ya yi sai da suka yi dare a hanya suna isowa ?ofar gidan A'isha hankalinta ya ?ara tashi,layin nasu shiru saboda dare ya soma yi amma yaya Abdulrahman yana zaune a ?ofar gidan saboda garin da zafi,don tun yamma suke saran za'ayi ruwa amma har lokacin shiru sai dai zafin da garin ya yi. Ya tsura ma motar idanu lokacin da ta tsaya ganin A'isha ta fito ya taso yana jiran yaga fitowar maigidan,ganin Jabiru ya fito sai Abdulrahman ya isa gurinshi, Jabiru lafiya kuwa da darennan? Jabiru ya mi?a mishi hannu tare da cewa lafiya lau, suka gaisa A'isha kuwa tuni ta yi cikin gidan cikin sanyin jiki Abdulrahman ya biyo ta ya sani ba lafiya bane domin tunda aka yi mata aure wannan ne karo na farko da ta zo batare da maigidan nata ba,tuni mahaifan nata sun rufe ?ofa, Abdulrahman ne ya ?wan?wasa,Abban su ne da ke zaune yana nazarin wasu takardu ya ce wanene? Abdul ya ce ni ne,Abban ya buWe yana cewa ba ka ?wanta ba? Ganin A'isha ya sa shi tsayawa yana kallonta, jikinta ya kuma mutuwa, Abbanta ya ce ke da maigidan ne? Ta ce a'a Abdulrahman ya ce ita da Jabiru ne bari inje in kai shi masauki,Abban ya juya ya koma in da ya taso ya zauna A'isha ta shiga ta tsugunna daga gefe ya dubeta, ina yaron? Hawayen da ta ma?e ya soma sintiri akan kumatunta, ya tattara hankalinshi gare ta me yake faruwa na ce? Cikin kuka ta ce Uncle ne ya ce in dawo gida, ya maimaita kalmar ki dawo gida? Ta ce eh, ya ce lallai kin aikata mishi laifi mai girma, ita dai ta ci gaba da kuka, ya ce shiga ciki Ummanta tana shafa'i da wuturi, tana jin su amma bata san dawa yake magana ba,ganin A'isha ta kaWu sosai, ta aje hijabi tana cewa dama ke ce? A'isha ta zauna bakin gado tana kuka,umma ta ce me ya faru? Cikin kuka ta ke sanar da Mahaifiyarta duk yanda abubuwan suka faru, Umma ta ce har da sakaki? Umma ta jinjina kai amma kin tabbata baki aikata ba? Ta ce wallahi Umma ba ni na kawo maganin ba ma, ta ce to shi kenan bari mu saurari sarautar Ubangiji."

Shi kuwa Abbanta take ya kira layin abokin nashi duka suna rufe hakan ya yi matu?ar Waga hankalinshi, amma ya ha?ura sai zuwa da safe. Yana yin sallar Asubahi abinda ya fara yi shi ne neman layin aminin nashi,daidai lokacin shima yana zaune kan sallayarshi,kiran na sirikinshi, kuma amininshi ya shigo. Alhaji Saddi?,yasa hannu ya Waga wayar,sai da suka gaisa tare da tambayar lafiyar iyalai sannan Abban ya ce Friend sai kuma naga A'isha jiya ita da Jabiru, ta shigo tana min kuka tana sanar da ni wai ka ce ta dawo gida,da shiga ciki kuma mahaifiyarta ta ke sanar da ni har da saki, Alhaji Saddi? ya ce ta tsorata ne zan yi magana sai ta yi zaton ko kalmar saki zan furta amma a zahiri ni ne na turo ta gida amma ban sake ta ba, Abba ya ce tayi maka halinsu na mata kenan wato shirme? Alhaji Saddi? ya jingina bayanshi da bango sannan ya ce wato Friend tun daga abinda Jummai ta shammace ni ta aikata min cikin gidana sai na shiga tsoron mata da kaidin su. Na samu kaina cikin ?in amince musu sai A'isha a ganina ita ce kurum tasha banban da sauran mata,?watsam wata rana sai take shawarta ta damu yi tsarin iyali saboda yaro da kuma karatunta,na nuna mata ban amince ba donni yanzun na soma samunta ta ce shi kenan zance ya wuce, ashe yarinyar nan ta hau shan maganin hana Waukar ciki ban an kara ba sai lokacin da zamu yi tafiya zuwa aikin Hajji,na ganshi cikin kaya hankalina ya tashi amma ta bani ha?uri tare da Waukar min al?awarin ta daina,na ha?ura kawai sai gasu jiya cikin durowarta da yawa ta Soye, wato abinda na lura tafi son karatunta bisa haihuwar shi ne yasa na ce ta zo gida don kusan me yake faruwa,in tafi son karatun babu damuwa sai in sawwa?e mata Allah ya raya wanda muka samu, kuma ba shi ne zaya shiga tsakanin hulWarmu ba, haka nan zana ci gaba da Waukar nauyin karatunta.

Abbanta wanda ya yi shiru yana sauraron shi kasa magana ya yi har sai da abokin ya kai aya, sannan ya ce ka jira ni muna tahowa yau insha Allah, batun ya sha ?arfin ayi shi cikin waya, lokacin da Abba ya baiwa Ummanta labari ta dubi ?ar tasu ta ce,dama kin taSa shawartar shi da batun tsarin iyalin? Ta ce eh, Umma ta ce ai ke ce ki ka aikata shi ne zaki ce baki ma san wanda ya kawo miki maganin ba,don kin raina mana hankali, A'isha ta yi shiru ta sani Allah shi ne kurum shaidanta, kuma shi ne zai fidda ta daga cikin wannan halin,don ta zama dole gareta ta kuma amsa wannan laifin a karo na biyu, Abbanta don tsabar takaici ya kasa ce mata ?ala, ya dai ce da Ummanta zai maida ta Katsinan.

Lokacin da zasu tafi Umman ta yi mata faWa tare da nasiha ta kuma kafa mata dokar cewa in har ta kuma aikatawa mijinta laifin da ya koro ta, to ta nemi wata uwar ba ita ba,ko cikin mota Abba yana gaba ne suna hirarsu da Jabiru, amma ita tana ?wance bayan mota abin duniya ya ishe ta, sai dai tana kaiwa Allah kukanta, Allah ya toni asirin wanda ya aikata mata wannan sherrin don kawai ya raba ta da mijinta.

Hadiza da Tabawa duniya sabuwa, domin duk abinda ke faruwa suna laSe kuma akan idanunsu A'isha ta tafi gida, tamkar su haWa fati don daWi, ta rungume Tabawa tana yi mata godiya. Tabawa ta hau yiwa kanta kirari,sai ni ?ar Audu naga ta kowa tawa ta yi wuyar gani, sai ni Laraba Tabawa ranar samu, ta dubi Hadiza ban taSa ?ulla makirci ya ?i shiga ba, kuma asirina bai taSa tonuwa ba,ba kuma zai taSa ba,ya ya batu na ?arin albashi? Tare da ?yauta ta musamman? Hadiza ta ce duk kin samu bugu da ?ari zan shiga in fita gurin kanainaye maigidan da kissa shekara mai zuwa ni da ke muje aikin Hajji mu ma kamar yanda A'isha ta je da mai aikinta Uwani, Tabawa ta ce da kin ?yauta,ni kuma da na dinga shirya miki kissoshin da mijinki shi da ?ara aure har abada, ita kuma wannan A'isha ta tafi kenan,ki yi yanda ki ke so ke kaWai cikin gidanki, kuma gurin ?ya?kyawan mijinki, ta kalli hoton shi da ke manne jikin bangon falon ta ce wannan maigidan naki da ?yau yake,ba don ban yi boko ba da nima sai na gwada sa'ata, Hadiza ta Waure fuska, Tabawa kina hauka ne? Hurumina fa kike so ki shiga kenan? Ta ce Allah ya baki ha?uri kin san bama zai yiwu ba.

Sun iso gidan lokacin babu kowa Hadiza da Tabawa sun je kasuwa sai ko maigidan wanda ya dawo don jiran aminin nashi,tuni yasa Uche ya shirya musu abinci sai dai ban da Jabiru da ya amshi nashi ya fita babu wanda ya saurari abincin domin Abban ya ce yau zaya juya suyi abin da ya kawo su,a gaban A'isha Uncle din nata ya karanto ma Abban nata dukkan abubuwan da suka faru ciki har da marin da ya yi mata,Abban ya dubi A'isha ya ce kin tabbata hakan ya faru? Ta ce eh,ya faru Abba sai dai wallahi ba ni ce na kawo maganin ba, Abbanta saboda tsabagen haushi bai san sanda ya mi?e ya Wauke ta da mari ba yasa hannu cikin aljihun shi ya ciro dorina wadda ya yo guzurin ta tun Waga gida ya shiga zabga mata, abinda bai taSa mata ba ko lokacin da take yarinya. Cikin sauri Uncle din nata ya isa gurin Aminin nashi ya kuma samu sa'ar ri?e bulalar ya ce haba Friend wannan bai dace ba,ai Beby ta wuce duka.

Abban yana haki ya ce bata wuce ba, kuma daga yau bata babu boko na hana, ta zauna ta nemi aljannarta,bokon banza da iyakar shi duniya zata kashe aurenta saboda shi? Abu na gaba kuma ban yafe miki ba in har kika kuma shan wannan maganin sannan ki nemi wani uban ba ni ba,ke hanyar Jigawa ma kada ki yarda ki biyo ta, ya maida bulalar shi cikin aljihu ya nufi fita, Uncle Win ya bi shi don Allah ka tsaya ka jini, ya ce ba zan tsaya ba na kula kai ne ka shagwaSa ta in ta Sata maka tafi ?arfin duka ne? Kasan sa mata tukunna ta san kai ba abokin wasanta ba ne da zata aikata laifin sannan ta raina ma mutane hankali wai ba ita ce ta kawo maganin ba, to ba sai ta faWi uban da ya kawo ba? Uncle Win ya bishi suka fita ya yi yayi dashi ya bari sai gobe ya tafi ya ce shi sam bai shigo Katsina da nufin ?wana ba, Kano zai ?wana, dole ya kira wani direban domin Jabiru yana bu?atar hutu, ya shiga ya kaishi Kano.

Lokacin da ya shigo gidan har lokacin Aishan tana tsugunne a gurin tana kuka,sam bata ga laifin mahaifin nata ba domin ya yi mata haka ne domin gyara,in ma laifin ne tafi ganin na Uncle Winta wanda ya kasa yin ha?uri da ita koda kuwa ta aikata laifin da ake zargin ta dashi, ganin Uncle Win ya nufo gurinta sai ta mi?e da hanzari ta nufi Wakinta tare da maida ?ofa ta rufe. Ya yi ?wan?wasawar duniya ta ?i ta buWe, ya yi lallashin haba Beby yi ha?uri ki buWe mana,ta?i dole ya ?yale ta,sai in ta huce ya san fushi ta yi domin kuwa bata da taurin kai tun zamanta da shi yau ce rana ta farko da yaga fushinta.

Wasa-wasa har washegari ba ta fito ba,ya zaci in ya tafi aiki zata buWe, amma da ya dawo ya tambayi Tani ta tabbatar mashi bata fito ba, ita kuwa sallah kawai ke Wagata daga gado, aikin kuka kawai take yi bai Sata lokaci ba gurin nemo masu saka ?ofa suka cire mishi ita ya jingine ta gefe ya shiga tana ?wance ruf da ciki ta kifa kanta kan filo ya Wago ta Beby yi ha?uri tashi zaune,ji ya yi jikinta zafi rau, gashi fuskarta ta kumbura dam saboda kuka, ya yi lallashin duniya ta ?i shiru,dole ya kira Nafisa cikin waya cewa ta zo da matsala. Tabawa tana kallon Nafisa ta fito cikin motarta ta shiga she?a dariya taje gurin uwargijiyarta tana

12 / 13