MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   10 / 13

27K to 30K   out of 38.3K words

da ita a haka ba to ya sauwa?e mata domin kam dan cutarwa an cutar da shi Hajiyarmu kuwa shawartar shi ta yi da cewa in ya saketa to don Allah yabar ta a muhallinta wato gidan shi kenan, ya amince da hakan don haka yana shiga gidan Wakinta ya nufa zaune ya sameta gefenta Hajiya Kari ce tana cewa, haba Jummai yaya zaki saki baki ki yi ta tona ma kanki asiri? Alhajin da basu san da shigowar shi ba ya ce ko bata fada ba dole ne wata rana asirin ya karye, domin ta Wauki rayukansu ba tare da ha??insu ba,shawarata gare ku ke da ita in kuna son samun sau?i gobe kiyama ku kai kanku kotun musulunci domin a zartar muku da hukuncin da ya dace da laifukanku,in kuma kun fi son Allah ya yi muku nasa hukuncin da kansa to kuyi shiru ya ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa Jummai am sorry to say na sake ki saki biyu in kina so za ki ci gaba da zama cikin gidan nan sai dai ni yazama dole in barshi.

Wani irin ihu ta saki mai ?arfi tana cewa ka taimake ni kai ne kaWai ka rage min saboda sonka Win ne fa na aikata duk waWannan laifukan shi ne yanzun za kayi min haka? Ya ce ke kika zaSo hakan, wacece ke da zaki ce ba za'ayi miki kishiya ba saboda kin ?washe kayan ki daga gaban Manzo,ya dubi Karima ku saurari ?arshenku yana zuwa. Yasa kai ya fita abinshi, Jummai an shiga sabon ruWu, hauka hauka ne ya sameta nan take. Lamari fa ya ta'azzara su Jummai yau gashi an kai ga rufe mata ?ofa domin zabura take zata gudu tana faWin ga sunan ba?in wani kashi da ke jikin Jummai tuni ta yi mishi fizgar kaza,ya zama abinci sai dai a kulla ?wano da igiya a tura mata Alhaji Saddi? tuni ya tattara su Hadiza da wasu daga cikin ?an aikin gidan suka koma wani gidan shi da ke can cikin G.R.A. Hadiza a baWini murna take amma a fili kuka rurus ta ringa yi wai ita dole nan me imani, shi ko Alhaji tuni ya dawo rakiyar su shi dai tsoron lamarin mata yake bashi domin bai taSa zaton Jummai zata iya kashe koda ?iya shi ba bare mutum. Shine dalilin da ya ji mata sun fita ranshi, hatta A'isha da bata san ma meke faruwa ba duk yasa su gefe shi ne dalilin da hankalin A'isha ya yi matu?ar tashi ga zatonta abinda ya faru ?wana kin baya ne zai kuma faruwa cikin sauri ta kira Nafisa da kukanta tana cewa Uncle ya yi watsi da ita kota kirashi ba ya Waga wayarta,nan take Nafisa ta ce daina kuka mijinki yana cikin ruWani ne sannan ta sanar da ita dukkan abinda ya faru. A'isha tasha mamaki lallai dole ne maigidan nasu ya shiga rudani.

Karima kuwa taje tazo da bokansu don ya yiwa Jummai magana,suna shiga inda take ta ri?e shi fatar jikinshi ta shiga yaga tana surutai Karima ta yi baya da gudu,tana fita mashin ya yi ciki da ita nan take wuyanta ya karye shi ko boka da ?yar ya ?waci kanshi ya fito jina-jina ya fita da gudu, ganin ?ofa buWe itama Jummai ta yi ficewarta ta shiga gari tana fallasa dukkan abinda ta yi anyi watanni kusan uku kafin Alhaji Saddi? ya gano kanshi, ya zaunar da Hadiza ya yi mata nasiha tare da nuna mata cewar ta dauki ishara daga abinda ya faru kan Jummai, ta nutsu ta dawo cikin hankalinta domin itama zai iya kasancewa da ita, Hadiza kam ta Wan yi nazari game da batun maigidan nata lallai haka zancan yake. Amma Hajiyarta har yanzun tana nuna mata cewa aikin da suke yi ne nasara ta samu, sannan ta ?ara mi?e ?afa gidan miji ya zama nata, haka nan kada ta damu da zancan A'isha ita ma data dawo za su saukar mata da nata aikin don haka sai hankalinta ya kasu gida biyu, amma wata safiyar asabar da Hadiza ta nufi gidansu don duba jikin mahaifinta,taga Jummai wasu ?arti suna dambe zasu saka ta a mota don kai ta gidanta gefe kuma ga mijin nasu da alama shi ne ya bada umurni sai ta ?ara tsorata don haka ranar da kukanta ta dinga ro?on mijin nasu wai ya yafe mata insha Allahu ta daina kuma zata zauna da shi fisabilillah, to kun ji Allah yasa gaske ne.

Tun zuwan farko da ya yi gurin su A'isha bai sake samun sukunin zuwa ba sai wannan karon ita ko taso hakan saboda dama tana tsoron ciki, zuwan ba zata ya yi mata dawowarta kenan daga lecture ta samu Uwani tana tu?a tuwon shinkafa, cikin jin daWi ta ce Allah sarki Uwani,ke da kanki? Uwani ta ce ?an nan na gaji da cin shinkafar nan tuwan semo Win nan naku baya Waukana shi yasa na ce bari dai ki gani, cikin dariya A'isha ta ce nima fa ?uiya ce dani ina son cin tuwon wace miyar ki kayi mana? Ta ce a'a ga dai tumatur Win nan yana dahuwa. dama kiyi mana miyar ganyan nan me ?ara jini, ta ce ogun? Uwani ta ce shi kuwa, A'isha ta shiga haWa miyar ji suka yi ana ?wan?wasa ?ofa,Tani ce ta buWe su Hafsat Sulaiman ne, suna ganin tuwo suka ce sun zo a Sa'a. Uwani tana ta musu tsiya da cewa sai yau ?a?an nan ?wana biyu kun mana yaji har dake uwata, ta ce ma Hauwa'u. Hauwa'u ta ce karatune ya yi zafi Uwani,sunan mahaiyarta ne Hauwa'u, A'isha kuwa sunan ?arta ne ta fari ?ar ma ta rasu amma bata faWa don kara,kai dai dai da laraba bata cewa saboda a ranar Laraba ne ta haifi ?ar sai dai ta ce ranar samu.

Duk sun zube a falo suna ?wasar tuwo, A'isha ko ta ce sai ta yi wanka wai warin zufa take, mai kurum ta murza ta zuro doguwar riga ba?a ta zauna tana shayar da Abulkhairi sai kuma suka kuma jin ?wan?wasa gida, A'isha ta ce ma?otana ne suma su shigo mu ?ara yawa yau gidana ya yi albarka, na gode da Uwani ta yi tuwon nan mai yawa,tuni Tani ta je ta buWe ?ofa tun kafin ya iso falon ?amshin sa ya shigo da sauri ta mi?e har ta tsorata ?awayan nata tare da cewa Uncle da sauri ta fita, suka kalli juna fuskarshi tana Wauke da murmushi ta Wan sakar mishi irin hararar nan ta masoya cikin shagwaSa ta ce Uncle ba notis? Ya ?araso ya cafki yaronshi cikin jin daWi, sannan ya ce bana so in kira ki ce min karatu ya yi yawa gashi ina cike da kewarku,kin san saboda sauri ban zo da Jabiru ba, jirgi na biyo, ta ce sannu da zuwa Uncle shigo,yana shiga ya samu Wakin da jama'a sai ya ce muna da ba?i kenan? Ta ce eh,?awayena ne ta gabatar mishi da su da kuma sunayensu, sannan su kuma ta ce musu ga Uncle Wina dai yau kun ganshi suka ce lallai kam suka tashi wai za su tafi ya yi ciki tare da cewa suyi zamansu ganin yanda A'isha ta hana kanta sukuni yi wannan yi wancan Hafsatu ta ce kai Hauwa'u ina zaton Uncle Win nan nata shi ne mijinta baki ga kamar su da yaron ba? Ta ce na lura kuma fa haka ne don yanzun haka ma ta kan ce wa mazan su kai amma A'isha ta samu cikin ?wali da harmun kama Hafsa ta ce sosai kuwa, amma fa tayi dace mutumin ya haWu Allah da Uncle Win ta ne na gaske sai na ce don Allah ta haWa mu, suna cikin hirar sai gata za ta je kicin Hauwa'u ta ce ji mana A'isha Musty ta zo tana dariya Hauwa'u ta ce Uncle Win ki ya yi kasuwa Hafsa ta ce ki shigar da ita, A'isha ta ce wuu ba zai ?ara ba, matan shi sun ishe shi, cikin dariya Hafsat ta ce ?ar wula?anci dama Uncle Win ne Abban Abulkhairi shi ne kike ta samu cikin ?wali ko? A'isha ta juya tana dariya ganin sun harbo jirgin ta.

Ta yi murmushi ganin yanda yake cin tuwon hannu da baka hannu ?warya, ta ce Uncle da alama ka jima ba ka ci tuwo ba ko? Ya dubeta "Beby ba ma tuwo ba,na jima ban ci abinci ba, tun da matsalolin Jummai suka tsananta wata rana ma yini nake ban sha ko ruwa ba, lamarin ya girgiza ni sai tayi tamkar bata ji labarin ba ta ce jikinta ne ya yi tsanani? Ya dubeta kina nufin baki san me ke faruwa ba? Ta ce, "Uncle ina zan samu labarin Katsina, ina Sokoto?" Ya ce na zaci Nafisa ta tsegunta miki, ta ce muna waya amma ba ta ce min ga wata matsala ba, ya yi shiru can ya girgiza kai Beby na ?ara tsorata da lamarin mata, kuma na amince sharri tare da kaidin mata ya Warar ma na sheWan, kazalika dole ne su fi yawa a wuta." A'isha ta ce "haba Uncle ya ya ka ke wannan zantuka ba duka aka taru aka zama Waya ba,wai ma duk me ya kawo wannan batun? Nan ya bata labarin komai, duk da cewa Nafisa ta bata labarin da take jin shi yanzun sai da ya girgiza ta, ta zuba tagumi cikin hawaye shi kam nasiha ya shiga yi mata da cewa A'isha na sani ke cikin mata daban ki ke,kin samu tarbiyya tare da yin gadon halayen mahaifanki, amma ina so ki ?ara zama cikin mata salihai,abin koyi kada ki amince ruWin duniya ya ja ki ga halaka, duk duniyar guda nawa ce? Duk sonka da ita wata rana sai ka barta, tare da duk abinda ka tara daga kai sai halin ka zaka tafi, abinda Jummai ta kasa ganewa kenan, yanzun wa gari ya waya? Mai sammako inji ?an magana, A'isha ta nisa ta ce to yanzun tana ina? Ya ce tana nan gidan sai dai ba a buWe ta don ?wanaki da ta ?wace sati huWu ana nemanta sai da ?yar aka ganta hauka tuburan fa. A'isha ta ce, Allah ya bata lafiya, sannan don Allah ina ro?on mata arzi?in ka yafe mata ta ji da na sauran,ya tsura mata idanu sannan ya yi murmushi, A'isha ina son halayan ki to har zuciyata ta ci albarkacin ki na yafe mata nawa laifin, shi kenan? Ta Waga gira suka yi ?ar dariya.

Kafin ya dawo sai da A'isha ta tabbatar da cewa babu sauran wata damuwa cikin zuciyarshi na shi ganin har wata ?ar ?iba yayi, A'isha kuwa dariya ta ringa yi mishi lokacin da ya iso gida Hadiza ta tare shi da nata salon tarairayar.

Yau da gobe lokaci yana tafiya,?wanaki na shuWewa haka satittika da kuma watanni har su A'isha sun sami Wan hutu suna ?arshen shekara, sun iso gida cike da Wokin ganin ?an'uwa.



#######
[12/22, 23:34] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 13*




Uwani garin su zata wuce don duba dangi haka ma Tani, Aisha kuwa gidan su da suka koma aka wuce da ita,tsarin gidan yafi nasu na da, haka nan kowace da gefenta babu abinda zai haWa wata da wata, komai sabo ya zuba mata, Hadiza har da yin girki don taran A'isha. Tabawa kuwa ta turo baki ta ce in dai kishiya ce fa baza kiyi gwaninta ba, Hadiza ta ce don Allah Tabawa ki ?yaleni,ni na gaji da halinku, Tabawa ta kuma taSa baki,nan gaba za ki kuma neman mu,kin kama tashar daji in dai kishiya ce,ta fita waje.


Cikin ?wanakin suna zaman lafiya da juna, Hadiza ko yaushe tana shigowa gurin A'isha musamman in ba ita ce da miji ba, sai dai ganin yanda A'isha ke kula da mijinta da yanda shi kanshi ke ji dasu ita da Wan ta sai ta kasa daure ma zuciyarta,in ta koma gurinta sai ta yi ta ?unci wannan damar Tabawa ta sake samu ta dinga zuga Hadiza tare da cewa in fa Aisha na gidannan ta bar Samun soyayyar mijinta har abada, sai dai ?unci ya kashe ta, Hadiza ta ce bana son in koma gurin ma?aryatan Malaman nan ne,sun jima suna ce min A'isha zata fita ba zata haihu ba menene, menene,sai gashi duk babu abin da ya faru,a ?arshe ma ita ce ta haihu. Tabawa ta ce tuni da kin yarda tun dawowarta da tuni mun soma shirya mata kissa, tunda ba ki son Malaman, Hadiza ta ce kada ki shirya min ramin da zan rufta, Tabawa ta ce kajiki da wani tunani, duk abubuwan da muka shirya can baya wanne ne ki ka rufta? Hadiza ta ce shikenan.

A'isha tana kallon su tana dariya, Uncle ne shi da Wan shi suke rigima, ya rarrafa ya janyowa Uncle Win waya daga chaji ya jefar sannan ya hau kan kujera ya zauna kan laptop ya hana Uncle Win aiki, ya dubi A'isha Beby zo ki Wauki yaron ki ya hanani aiki, A'isha ta ce tayaka fa zaya yi Uncle, ya dubi yaron Babana je ka gurin Mominka, A'isha tana tasowa yaron ya ?an?ame uban ta koma tana musu dariya, ya ce kina dariya ne ma ko kin ?i Wauke shi in gama ko? Shima ya yi ?ar dariya tare da rungume yaron dama muna magana ne kan tafiyar ki aikin hajji, tunda ba zaki ri?e shi mu gama ba shi kenan. Asha wasa ko yaron Baba?" Da sauri A'isha ta tashi ta cafke yaron zo kada kasa in ga samu in ga rashi, ta zauna kusa da shi tare da dafashi gaske ne Uncle Wina? Ya ce kalli ki gani lis Win sunayan waWanda zasu tafi aikin hajji ne sunan waye farko? Ta kalli screen Win laptop Win, Beby ta gani farko cikin murna ta ?wantar da kanta a kafaWarshi tana cewa na ji daWi bari na gani su waye sauran nayi musu albishir koda in samu tukuici, daga sunanta sai nashi ta dubeshi kai fa duk shekara sai ka je ya Wora yatsanshi kan leSanta ke zan raka ta ci gaba da dubawa, sai sunan mahaifanta biyu da yayanta Abdulrahman sai Nafisa da Uwani mai aikinta sauran kuwa bata san ko su waye ba,?ila cikin danginsu ne. Ta dube shi ban san da wane baki zan maka godiya ba Uncle, ya ce kawo kunnanki ki ji dame za ki bani tukuici, ta mi?a kunne ya raWa mata, dariya ta shiga yi sannan ta ce ka samu ban ga Hadiza ba, ya ce kin san dai ance Hajji kiran Allah ko? Ta Waga kai ya ce to Allah bai kira ta ba, A'isha ta ce to Allah yasa tana da rabo nan gaba, ya ce Amin.

In kin je me zaki ro?a? Ta ce Sa'a a karatuna sai kuma gamawa lafiya, tare da samun ?ya??yawan ?arshe. Ya ce ni duk shekara haihuwa nake ro?o, ta dubi Abulkhairi da ke bacci a jikinsu, sannan ta ce Uncle ba gashi ka samu ba, ya ce ni da nike son dozin biyu Beby kina da sauran aiki fa, ta ce wai ba zan iya ba ana shan wuya fa sosai,ni dai wannan ya isheni, ya zuba mata ido, Beby ba ki yin tsarin iyalin nan ko? Ta ce me yasa ka ce haka? Na gane shiru, ta ce Allah tunda ka ce baka so an wuce gurin, ya ce shi kenan. Ta mi?e da yaron a kafaWarta bari in shinfiWar da shi ka ?arasa ina zuwa yau zaka sha tukuici, murmushi ya yi tare da cewa Beby.

Tabawa wadda ke ma?e tana kallo tare da sauraron duk abinda ke faruwa tsakanin ma'auratan, ta ri?e baki sannan saWaf-saWaf ta bar gurin tana tafe tana tafa hannu gami da ri?e haSa, irin na wanda ya ji ko ya ga abin mamaki, har Hadiza ta soma bacci Tabawa ta tashe ta,tashi-tashi Antyna wato ma bacci ki ke yi ke,ni ina can gurin neman zaman lafiyarki. Ta ce Tabawa na ?i bacci tunda ke kin je kin yi zamanki? Ta dafa ta na taSa ki da alheri kin san me na jiyo? Hadiza ta ce sai kin faWa, Tabawa ta taSa baki irin na wanda ya kawo gulma to ke me son bawa kishiya amana to gata can ita dake makaranta an biya mata Makka tare da iyayanta har fa da wata ke da ke nan kullum sai ya Waga ?afarki ko oho,don kinibibi har tana cewa Hadiza fa? Cike da al'ajabi ta ce to shi me ya ce? Tabawa ta taSa baki,Sata rai ya yi tare da cewa,wai kiran Allah ne, wato ke bai kira ki ba, Hadiza ta ringa girgiza kai lallai gaskiyan su Tabawa ne ba aba wa kishiya amana.

Ranar kam ?wana ta yi babu bacci,ko da ya shigo da safe lokacin da zai fita ta cije sun gaisa amma shi kanshi ya lura tana cikin damuwa, ta so mishi magana amma Tabawa ta ce in ta mishi magana ba zata ci ribar zance ba,tunda ranar zata amshi girkin ke ki kasan yanda za ki riSa ce shi ki ji komai, amma ita ki bar ni da ita zan shirya mata gadar zare kuma zata faWa, akwai batun da sukayi na ji.

A'isha ce a gaban Uncle Win ta da ke Wauke da Abulkhairi yana cewa Beby tana duka fa? A'isha ta ce Ni ba zata min komai ba, ya ce ki dai le?a ta window ne tunda kin dage sai kin gaishe ta. Yanda A'isha taga Jummai kuka sosai ta ringa yi,lallai wannan shine in kasan farkonka baka san tsakiya ba, ?arshe dai dama mutuwa ce ta yi ba?i ta rame, jikinta babu sauran gashi,ga ciwuwwuka da ta jiwa kanta fuskarta tamkar ta ?one Wakin sai wari yake yi,da ta kalli ?afafun ta kuwa ai sai ta kuma sa kuka dan ganin yanda wasu manyan tsutsotsi irin na toilet mara tsafta Win nan suna fita daga jiki, gashi sai surutai take yi in ka saurara zaka ji tana faWin duk abinda ta aikata ne. Ta kalli A'isha ta window inda take kuka ta mi?e tsaye sai ta hango Alhajin,nan take sai ta soma dariya, Alhaji ka gansu ne? Zo ka zauna,in

10 / 13