MUMMUNAN ZATO Book 3 Hausa Novels Compelet By Halina Abdullahi k Mashi

Author :  Halima Abdullahi K Mashi Category :  Tknovels

Chapter   7 / 13

18K to 21K   out of 38.3K words

ciwon dai da ta saba ji ne yau da kullum,ya yi ya lafa,ya yi ya lafa cikin dare,biji-biji tayi zuwa lokacin ta gama yanke hukunci mutuwa zata yi,taso ace Uncle yana kusa ko zaya tausaya ya yafe mata laifin da ta mishi wani irin ciwo take ji wanda bata taSa jin ko labarin shi ba,nishi yazo mata ta ji tana nishi mai tsanani tare da salati sai taji tamkar ana buWe ta sai kurum wani ruwa tare da yaro jim kaWan sai ga wani abu shima ya faWo ashe mahaifa ce. Yaro ya shiga yanka ihu ita kuma ta koma gefe tana nishi.

Cikin bacci Hajiyarmu ta yi mafarkin wai ga A'isha an ban?are ta za'a yanka mata ciki, ta farka da salati dama duk dare tana zuwa duba A'isha kusan sau uku,ta kan ganta zaune ko kuma tana nafila,tana nufo Wakin ta ji kukan ba?on duniya, da sauri ta shiga tana cewa ni ?asu ke ?an nan shi ne kina na?uda ba zaki yi magana ba? Gashi ni yau sai Allah ya sauko min da bacci sannu kin ji? Ina kayan haihuwar? Ta nuna mata inda suke inda Nafisa ta ajiye su ko da yaushe tazo gidan tana shaidawa A'isha cewa tana jin burin Win ciwo to ga kayan da zata Wauka nan,reza ta ciro ta yanke cibi sannan ta sa zani ta Wauki jaririn lokacin da take karanto addu'ar da zata tofa ma yaron, idanu ta zuba mishi gabanta ne ya faWi domin yaron tamkar mahaifinshi lokacin da ta haife shi,kamannin ya yi yawa sosai,nan kuma sai ta samu kanta da jin nauyin yaron,don haka sai ta matso ta ba A'isha shi a inda take cikin jin nauyi. A'isha ta amshe shi nan da nan Hajiyarmu ta tashi duk ?an gidan suka shiga aiki, Uwani ita ce ta wanke yaro tas yayin da Baraka ta shiga gyara gurin Hajiyarmu kuwa gurin Alhajinmu ta nufa,kan sallaya ta same shi. Ya kalli agogo na jira ki sai naji shiru, shi ne na ce Hajiyar gidan nan yau batayi da ni, ya yi maganar cikin tsokana, ta ce Allah sarki,ba haka ba ne Wan bacci ne ya sace ni ba farka ba sai da nayi wani Wan mafarki haka ina tashi sai kukan jariri na ji,yarinyar nan ashe na?uda take yi ba ta faWa ba, ita kaWai ta haihu, da sauri ya mi?e A'isha? Ta ce eh,nan ya shiga murna yana cewa alhamdulillah,ya so zuwa Wakin Hajiyarmu ta ce ana gyara su ne.

Zuwa wayewar gari ko'ina labari ya je ban da gidan Uncle,domin daga Alhajin har Hajiyar babu wanda ya sanar dashi,su Nafisa kuwa an zo ana ta murna da ko tuno shi ba su yi ba, maijego tamkar ba ita ba,ta shirya tsaf asibiti za su je don Likita ya duba su . Ita da Nafisa suka nufi asibitin. Likitan ya duba su kuma ya tabbatar da lafiya suke. Aka yi wa yaron (Bcg) suka dawo,Likitanne ya kira shi lokacin yana shirin fita zuwa Office,suna gaisawa Likitan ya yi mishi barka,nan take Alhaji ya shiga tambayar Likitan ta haihu ne? Cikin mamaki Likitan ya ce ba ka sani ba kenan? Shi yasa banga ka biyo su ba? Ya ce Likita suna nan ne? Doctor ya ce a'a sun zo na duba sune gida ta haihu ko da ya gama shirinsa sai ya sake shiga bayinsa ya yo alwalla, nafila ce ya yi raka'a biyu yana yiwa Allah godiya, fuskarshi fal annuri ya fito ya dubi Hajiya Jummai Beby ta haihu,jin zancan ta yi tamkar saukar aradu, amma ta dake ta ce me ta haifa ne? Ya ce ban sani ba sai naje zan ji, ta shiga Wakinta da gudu ta janyo gyalenta muje tare. A zuciyarta kuwa cewa take Allah ya bata Sa'a ta Wauko mahaifa.

Sun samu Wakin cike da jama'a ?an barka, Uncle ya shiga mutane suna mishi barka, Hajiya Jummai cikin nuna zumuWinta ta shiga ina Wan nawa? Allah sarki,ko ?a ce? Aka ce mata Wa ne, Nafisa ta ce gashi nan mai kama da mahaifinshi,yaron na hannun Jummai Uncle ya tsura mishi idanu,wani farin ciki yake ji tamkar yau aka haife shi,ya mi?a hannu Jummai ta Wora mishi yaron,nan take ya yi wa yaron huWuba tare da addu'o'i,ko Nafisa ba ta furta ba lallai yaron hotonshi ne ji yayi tamkar kada ya bada yaron ya zauna yana ta kallonshi kawai, kaWan-kaWan mutane suka ringa fita har su Nafisa. Yana Wago kai tuni sun watse sai matan nashi kurum, ya dubi A'isha a ranshi yana so ne ya yi mata sannu amma yana kallonta sai ya ji tamkar ya Wauke ta da mari, Nan take fuskarshi ta canza ya ku??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ma juya mata baya, zuciyar A'isha ta sosu amma sai ta danne, ta ce Uncle Ina ?wana? Da ?urar kuma can ?asan ma?oshi ya amsa,ta ce ka faWa ma su Abbana? Hajiya Jummai ta ce sai dai yanzu ya faWa,mu ma ba yanzun muka ji haihuwar ba,wai tun yaushe ne haihuwar? Kan A'isha yana ?asa ta ce da dare ne. Uncle ya ce to kin ji abu da dare amma an kasa sanar dani. Hajiya Jummai ta ce Alhaji sai ka amshi mahaifar mu je gida ka rufe ko? Ya ce haka ake yi? Ta ce eh mana,ai ba'a wasa da ita,ya dubi A'isha sannan ya kauda kai, ina mahaifar? Ta ce sai dai a tambayi Hajiyarmu, Jummai ba ta san sanda ta furta Allah yasa ba su rufe ba, sai kuma ta ri?e bakinta saboda katoSarar da ta yi, ya dubeta in an rufe a nan laifi ne? Ni fa bana son canfi,ta ce a'a ina fa laifi wai mu ma muce an taSa rufewa a gidanmu.

Ya nuna murnarshi sosai a gaban mahaifan nashi da ?annanshi, in da har yake tambayar ?annan nashi me ake bu?ata game da jariri da mamanshi? Nan take Nafisa ta shiga lissafi har da na tsiya, lokacin da Uncle ya sanar da mahaifanta sun yi murna sosai, Abbanta ya ce Friend na tayaka murna sosai, Allah ya raya mana ya ce Amin friend,na gode ina fatan za ku zo kada ka ce min don A'isha tana ?arka ba za ka zo ba, dariya Abban ya yi kafin ya ce ban Waukar maka al?awarin zuwa ba, sai dai ko bayan suna zan zo insha Allah. Dangin A'isha suma labari ya karaWe ko'ina,ba labarin ciki sai na haihuwa, lokacin da labarin ya samu Hadiza tamkar zata suma don itama da yawa Malaman nasu sun sheda mata cewa duk wadda ta haihu cikin su shi kenan ita ce kurum zata yi ta haihuwa, kuma ta yi rantsuwa kan cewar in dai ba ita ce zata haihu ba, to sai dai kowa ya rasa cikin da yake cewa ba na shi ba ne shine zai amsa? In ko haka ne itama sai ta nemo shi wajen ai ba an fi su sanin kan bariki ba ne.





#########
[12/21, 18:37] Ummi Tandama=??: *=???=???=??? Page 9*



Hajiya Jummai ita dai damuwarta ta samu mahaifa, don haka lokacin da Alhaji zai fita bin shi ta yi gurin mota, faWi take shin Alhaji ka amshi mahaifar? Ya dubeta,au Ina zuwa,ya koma ciki sai dai ya kasa tambayar mahaifiyarshi saboda nauyin da ke tsakaninsu,ya ce Nafisa zo mana,a gefe ya ke cewa ta tambaya mishi ina mahaifar don ya je ya rufe. Lokacin da ta yiwa Hajiyarmu batun sai ta bata amsa da cewa zasu yi ta ajiyar mahaifa ne ba za su rufe ba har zuwa yanzun? In kuma ya fi son ya rufe da kanshi to sai ya jira mahaifin nasu in ya shigo sai ya ce ya tono mishi yana son ya rufe da kanshi ne,yana jin lokacin da take faWa wa Nafisa wannan batun,don haka sai ya juya kurum yasan har yanzun mahaifiyar tashi tana ciki da shi.

Jummai ta dube shi ka amso ne? Ya ce sun rufe tuni, ta zaro ido har ma ya tsaya yana kallonta, sun rufe? Ta Wora hannu akai tare da cewa kash! Ta dubeshi Wan jira ni in Sari inzo muje gida, da sauri ta suri gyalenta ko sallama ba ta yi wa mutane ba ta wuce. Yana ?o?arin tada mota ta fito, sannan abinda ya dinga ba shi mamaki yanda duk surutun da yake yi bata san ma yana yi ba,ga uwar zufa da take zabgawa sai ka ce wadda ta haWiye kunama. Suna isa gida tun kafin ya gama parking ta buWe mota kaWan ya rage ta faWo, ta fita da sauri sauri gudu-gudu tana shiga falonta suna cin karo da Aminiyarta Hajiya Kari, ta ce Jummai tunda na samu labarin haihuwar matar mijinki na ce bari in zo kada kiyi sakaci, Jummai cikin wani huci mai tsanani ta ce na nawa kuma,ai an riga an gama sun rufe ta. Karima ta yi saurin cewa, sannu Alhaji dan ganin ya riga ya shigo kuma ga Jummai da shegen Sarin baki, sannan ta yi mishi barka,cike da murna ya amsa tare da godiya, ya kalli Jummai ya ce, wani abu na damunki ne? Ta share zufa ta ce me ka gani? Ya ce duk kin canza irin kamar kina cikin mawuyacin hali? Ta kuma share wata zufar haba dai mu yau da muke cikin farin ciki? Ta yi ?ar dariyar ya?e,ai mu yau dai babu bacci, ya tsura mata idanu Jummai wannan zufar fa? Ta ce tsabar farin ciki ne, sai ta soma matso hawaye shekaru nawa ba mu taSa jin kukan Wa ba cikin gidan nan sai bana, dole in yi zufa, Karima ta ce haba Jummai ai godiya zamu yi wa Allah ba kuka ba, Alhajin ya dafa kafaWarta, Jummai na san dole ne kiyi murna, sannan ina miki albishir da zaran an tashi ya ye shi ke ce zaki Wauke shi kiyi rainonsa har abada, ta dubeshi cikin muryar kuka tana cewa na gode Alhaji ni dama nasan Wan ka Wana ne Allah ya raya mana shi, suka ce amin ya ce bari in je in Wauki wasu takardu ina da ba?i a Office suka ce to ya fita. Hajiya Jummai ta Wora hannu a kai zata zunduma ihu Karima ta saka tafin hannunta ta rufe ma Jummai baki, sannan ta ci gaba da cewa kina hauka ne? Na kula garin taSargazarki wata rana za ki tona kanki,Wazun kin ?waci kanki yanzun in yaji ihunki ya dawo me za ki ce?

Cikin kuka Jummai ta ke faWin na shiga uku ni Juma, yanzun shi kenan ni ko me nayi babu nasara cikinshi,na fi wata ina zirya gidan su Hajiyarmu na ringa daure zuciyata ina zama tare da tsinanniyar yarinyar nan ina kashe ma tsinanen cikinta kuWi duk don in samu mahaifar nan amma ha?ana bai cimma ruwa ba, Kari ta ce naji yi shiru ki shirya yanzun da ya fita muma sai mu nufi gurin Malam mu ji ta bakinshi.

Ya dubeta kin isa a yi miki jaje, domin in baki dage ba ?ila lokacin rushewar al'amuranki sun zo,yarinyar nan ita ce zata yi ta haihuwa dama kin yi nasara ne ha?i?a da kin dace, cikin jimami ta dubeshi to ni yanzun yaya zanyi? Ya ce sai mun bincika ta ce yanzun in je in zura idanu kenan? Ya ce in kina da wata dabara sai ki je ki ?watanta, kafin mu mu binciko. Tamkar zata yi hauka ta baro gidan Malamin, Karima tana tausarta tare da lallashinta, tana nuna mata cewa ta yi a hankali kada mutane su gane halin da take ciki.

Gidan masu jego kuwa, al'umma sai tantsowa suke yi, wasu ma ba a san su ba,?wananta uku ?an Jigawa suka iso, murna gurinta ba a magana har da su Jafar da Munnir aka zo,sai da Hajiya Lanti da Tabawa suka taushi Hadiza sannan ta zo barka, Hajiya Jummai ma ta cije ta sake zuwa ana gobe suna, yanda taga ana sauke kayan ciye-ciye da shaye-shaye ga gidan ya cika da jama'a sai hankalinta ya kuma dungunzuma ta bar gidan suna. Tafe a mota direba na janta tana surutai ita kaWai.

Ranar suna yaro ya ci suna Usman,waton sunan Alhajinmu, labarta yanda sunan ya kasance ma ?auyanci ne. Sun samu alkhairi mai yawa daga abokan Uncle har da masu ba shi motar zuwa makaranta. Hadiza dai babu wanda yasan tafiyarta. Jummai ma tunda ta yi arba da maijego tun daga ?asa har sama take kallon A'isha kaya ?arshen tsada ga gwala-gwalai tun daga yatsun ?afa har zuwa na hannu,na wuya kam ai ba a magana, sai ta juya gida. Taro ya tashi lafiya danginta sun koma gida suna sambarka, haka suka ci da wankansu, A'isha tana matu?ar mamakin yanda dangin Uncle suke tsananin son yaron wanda Nafisa ta yi wa la?abi da Abbul khairi, Hajiyarmu ce kurum ke karantawa bata Waukarshi, hakan ne ma yasa A'isha sam in Hajiyarmu tana ciki bata Waukar yaron ta bashi nono, sai ta dinga kara itama musamman tun bayan suna Alhajinmu ya ce su A'isha su dawo Wakin Hajiyarmu. Matsalar A'isha Waya, Uncle wanda har yanzun bata cikin ?an kayan shi duk da cewa wani lokacin abun yana damunshi, A'isha har ta soma ?yau ta ci tasha duk abinda ranta ke so kuma Hajiyarmu ta ce kada ta damu da matsalar Uncle tana zaune za ya zo ya kawo kanshi.

Misalin ?arfe huWu saura ya fito daga sallar la'asar ya shiga gidan mahaifan nashi don yaga Abbul khairi. Yana shiga gefen Hajiyarmu sai ya soma jin kukan yaron, da sauri ya nufi Wakin domin ji ya yi tamkar an watsa mishi ruwan zafi, kuma ?ila Wakin babu kowa, amma ga mamakin shi yana shiga sai ya samu A'isha tana zaune tana cin abinci, Hajiyarmu kuwa tana sallah daga bakin ?ofa ya tsaya yana kallon A'isha,ji ya yi tamkar ya shiga ya hau ta da duka, waton tana zaune ma tana cin abinci? Ta bar yaro,ya Wauki yaron ya fita a falo ya tsaya yana jijjiga yaron, zuciyarshi na ce mishi A'isha bata son yaron kamar yanda Hajiyarmu bata so shi ba lokacin yana yaro kai har zuwa yanzun a fili ya ce tab in dai haka ne gara ya kai Wan shi gidan raino. Hajiyarmu ba ta tsaya doguwar addu'a ba,ta dubi A'isha,amso shi ki bashi ya sha, ta dubi Hajiyarmu tamkar ta ce a'a amma bata iya jan musu da Hajiyarmu, ta mi?e ta fita yasa kai zai fita daga falon zuwa inda zuciyarshi ta raya mishi watan gidan rainon yara sai ya ji muryar A'isha, Uncle ya juyo wai ka kawo shi in ji Hajiyarmu, ya zuba mata harara,ai dama nasan ba son shi ki ke ba, in dai irin rainon da Hajiyarmu ta yi mun ne zaki mishi gara na kai shi gidan rainon jarirai. Ta zaro idanu, yi ha?uri Uncle don Allah, ya dube ta ba zan amince da nufinku ba, duk cikin al'adun Hausa Fulani wannan al'adar ce bata yi min ba,babu hadisi ko aya da ta nuna cewa iyaye su dinga jin kunyar ?a?ansu, tun ina ?arami babu irin wuyar da ban sha ba,dan kawai ina Wan fari da kaina na dinga addu'a Allah yasa mahaifina ya sake aure,?ila matar zata kula dani,gara na kaishi in da zan zuba kuWina a luran min dashi.

Dukan su ba suji shigowar Hajiyarmu ba, sai kurum suka ji ta ce A'isha koma ciki barshi ya kai shi ta kama hannun A'isha tamkar ta ?wace, amma ba zata iya bijirewa ba, ta bi ta suka shiga ciki, A'isha tana zama bakin gado yana shigowa ya mi?a mata shi. Ta kalli Hajiyarmu sai tayi mata alama da kai,don haka sai ta amshe shi shi ko ya fita. Hajiyarmu ta dubeta kada ki dinga barin shi yana kuka, mijinki za ya iya raba ki da Wanki, domin nasan da zaran ya sanar da mahaifinshi wannan matsala za ya gaya masa,baya kan ?udirinshi,kin ga ku, ?an zamani ne ki kula da Wanki kin ji ko? A'isha ta ce to haka suka ci gaba da wankan su.

Satin su shida suka soma fita asibiti suka soma zuwa sannan gidan Anty Sadiya sai gidan su Fatima da kuma su Nafisa. Ranar da suka je gidan Anty Nafisa cewa ta yi to A'isha an gama wanka lafiya yanzun kuma sai azo a soma shirin gyaran jiki, A'isha ta taSa baki um wane gyaran jiki bayan har yanzun Uncle yana fushi da ni? Nafisa ta ce ni fa nawa ganin tsakanin ku aka shiga, A'isha ta ce Anty Nafisa wanene zaya shiga tsakaninmu? Ni dai nafi zaton cewa na mishi wani laifi ne. Anty Nafisa tunda kuna shiri don Allah ki same shi ki tambayan min shi mana? Nafisa ta ce kada ki damu, insha Allah komai zai daidaita, yanzun dai bari na yi wa Hajiya Aliya waya can kaduna don gyara ki zan miki sosai, A'isha ta ce kin yi sabuwar Aminiya kenan? Ta ce"a'a dama muna tare lokacin da zan yi aure don dai kina makaranta ne baki ganni ba gyaran sati Waya naje tayi min amma ni kaina nasan nayi ne." A'isha ta ce ni da nike saran cikin watannan za'a buWe mana makaranta ko da nayi wani gyara sai inga kamar a banza ne. Nafisa ta ce A'isha ban san ki da jan zance ya yi tsawo ba, A'isha ta ce to nayi shiru,nan take ta yi waya da Hajiya Aliya mai Zahra Global,suka gaisa Nafisa ta ce ?anwata ce zata koma gidan mijinta daga wankan gida ina son ayi mata gyara ne sosai,Aliya ta ce wannan ba matsala zan aiko muku da duk abin da ya dace tare da bayani a rubuce, sannan zan miki ?arin bayani ta waya, suka yi sallama A'isha dai idanu ta tsura ma Nafisa ba zasu ga ne bane,sun san irin wula?ancin da Uncle ke mata kuwa?

Yanzun dai lamura sun juyawa Jummai,?wana take zaune tana sa?e-sa?en zuci, yanzun ita ce dai Jummai ita ce duniya ta yi wa haka, ashe akwai ranar da zata zo da kuWin ta amma ta kasa samun biyan bu?atarta,shin Malamai sun daina aiki ne? Rayukan da ta kashe a baya ba kuWinta ba ne ya biya mata bu?ata? Yanzun ma tana da kuWin amma malamai da bokayan su kasa,an ya kuwa ba zata Wauki hukunci a hannunta ba? Wannan

7 / 13