Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   42 / 52

123K to 126K   out of 153.1K words

Saurayin Fannah ne Wanda mutuwan mahaifinta ya hana aurensu& Hasalima mahaifin Fannah kafin ya rasu ya masa alkawarin bashi ita..!

Daddy ya dago jiki a sanyaye yana duban Fannah wacce kuka yaci k arfin ta  Haka ne.? Wann D an iskan saurayinki ne.?! Ya tambaya yana dubanta.

Jin bata amsa shi ba ya sa ya kuma daka mata tsawa  Ki amsa min..! Haka ne..!

Auwalu ne ya bama Daddy amsa da fad in  Duk Wanda zaka tambaya Rankayadade haka ne. Fannah toshuwar budurwata tace da nake matuk ar so. Kuma mahaifinta ya min alk awarin bani ita.. Amma  yanuwanta Sun karya wann alk awarin sabida kwadayin abin hannunka. Saidai ni da Fannah bamu rabu ba.. Washe garin ranar da ta tare gidanka ma ba aiki na tafi ba gidanka na taho.. Kuma duk randa nazo mukan mu amalanci juna da yarda da amincewarta. Amma yau din ba da son ranta na aikata mata ba fyade nai mata sabida ta sanar Dani akwai ciki jikinta Wanda batasan nawa bane ko naka..! Bai Kai aya ba yaji saukar naushi a bakinsa. Duka Daddy yake Kai masa ta ko ina yana hawaye tamkar zai aikasa lahira A haka mai gadi ya shigo a guje yana sanar da Daddy window din section dinsa a fashe dik yanda akai b arawo ya shigo gidan. Dan shi dawowarsa kenan daga masallaci ya tadda haka.

Daddy ya ci gaba da huci  Ga b arawon a nan. Ya Saba shigowa Shayibu ba tareda kayi la akari ba. Yau da dubunsa zai cika sai ya fasa window. Ya damk a sa ma shayibu yana fad in bari yaje ya duba section d insa. Ai kaw nan Daddy ya tadda an fasa safe d insa na cikin gidan an kwashe kud ad en ciki.

Koda aka mik a Auwalu ma  yansanda bai yi musun shi ya kwashe kud ad en ba. Ya ce da taimakon Fannah ya kwashe kud ad en dan su gudu su bar gari.

Daddy bai saurara daga b angaren Fannah ba. Musamman da ya tabbatar da gaske Auwalu tsohon saurayinta ne kowa yayi wann shaidar.

Sosai take kuka duk e gabansa tana girgiza Kai tama kasa cewa komai. Mai ma zata ce bayan an kulleta ta ko ina. Daddy yaci gaba da jinjina Kai yana dubanta  Ki sani wann shegen da yake cikinki ba nawa bane. Kuma har Abada kar ki taba danganta ni dashi. Kije can keda wancan Daniskan ku rainesa a gidan Yari. Yana ida fad in haka ya mik e yana hawaye sosai. Bai wata wata ba ya tura su duka biyun gidan Yari.  Yanuwan Fannah suka barranta da ita cewa basu ba ita. Ta tona ma kanta asiri ta cuci kanta. A prison Fannah ta raini abinda ke cikinta har ta haifesa. Bayan faruwan haka da wasu watanni Mommy ta fara nuna alamu na masu ciki. Batai gaggawan sanar da mijinta ba Wanda tsawon shekarun da suka diba tare suna jiran wann batu mai dad in ji tin kafin shigowar Fannah cikin rayuwarsu. Yau gashi ta samu juna. Tasan Engr zai farin ciki fiyeda lokacin da Fannah ta samu. Tai shiru tana tinanin da Fannah tana nan k ila da an fara k irga ma abinda ta haifa watanni.

Suna hira itada Asshe wani rana, nan Mommy ke zayyano ribar da taci bayan ta k ulla ma Fannah Makirci gashi ta fice cikin rayuwarta cikin ruwan sanyi. Tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu.

Sam bata San Daddy ya shigo ba take b arin zance.

Daddy ya dubeta da mamaki  Kwaise.. Sharri kikai ma Fannah.?!

Sai Mommy ta mik e tana girgiza Kai  A a Engr dan Allah ka saurareni.

 Mai zan saurara bayan abinda naji da kunnuwa na.. Ki bud e baki ki sanar Dani.. Sharri kikai ma mata..? Kece kika shirya komai..?!

Cikin kuka Mommy ke jinjina Kai  Wllhi Allah shine shaida na Engr sharri kawai nace yai mata.. Wllhi ban ban bashi umarnin wani abu bayan haka ba..

Gijif ya zauna cikin kujera yana jin duniyar na juya masa yayinda Mommy ta rarrafo zuwa gabansa tana Neman afuwa.

Mik ewa yai ya fice ba tareda ya dubeta ba. Kai tsaye prison yaje amma koda yaje ta gama sentences d inta an kuma sallameta bayan ta haihu sann babu Wanda yasan yanda ta tafi. Shima Auwalu babu Wanda yasan yanda yake bayan Sallamansa daga prison da akai. Haka Daddy ya zauna yana kuka sharshar da hawaye tareda nadaman hukuncin da ya zatar ba tareda yayi bincike ko ya saurara daga Fannah ba. Gaba d aya Mommy ta rasa gane kansa tin daga wann lokacin. Baya mata magana baya kulata baya shiga sabgarta. Kasuwancinsa ta soma girgiza bayan hab akar da tai sabida halin k unci da damuwa da ya tsinci kansa ciki. Daddy ya koma tamkar baya rayuwa cikin wann duniyar. Ya daina fita ya daina magana ya daina mu amala da kowa da komai. A haka Mommy ke rainon cikinta cikin damuwa da k unci hopping idan ta haihu zuwan D an cikin rayuwarsu zai canza komai. Har zuwa lokacin da ta haihu Daddy bai dawo normal ba. Yana nan jiya iyau ba um ba um um. Bayan Mommy ta haihu ta shigo da jaririn cikin hannunta tana hawaye take nuna masa  See burinka ya cika Engr ka samu Magaji and I named him after you. Aliyu Aliyu Maitama.. Zai girma ya zama Engr kaman Kai. Zai girma ya zama d an da zakai alfahari dashi.

Tin bayan abinda ya faru bai kuma duban cikin idonta ba sai wann lokacin.

Mommy tana hawaye take dubansa cikeda Jin dadin yau yau ya kalleta. Amma sai taga ko kallon jaririn dake rik e cikin hannunta baiba balle ya karb e sa. Sai ma mik ewa da yai a ranan ya koma aikinsa gadan gadan. Baya shiga sabganta balle na D anta sai hidiman bunk asa Kasuwancinsa da yake. K unci da damuwa suka taru sukai ma Mommy yawa tinda taga wann lokacin Mommy ta shiga damuwa kullum cikin kuka da tashin hankali take bata kula jaririnta Wanda tinda taga mahaifinsa bai amshesa ba. A nata zaton zai zamto makamin da zatai amfani dashi ta kuma janyo hankalin mijinta gareta. Asshe ita ke rainon Haidar. Hasalima ita take kiransa Haidar bayan mahaifiyarsa ta sanya masa suna Aliyu har Haidar ya bisa. Asshe ita ke kula da Haidar tamkar itace ta haifesa. Madararsa d awainiyarsa komai itace. Mommy kullum cikin kuka da damuwan wofantar dasu da ita da D anta da Daddy yai take. Ta duk ufa Neman Fannah dan ta nemi yafiyarta amma Fannah was no where to be found. Sanda Asshe tazo aure ji tai kaman ta tafi da Haidar sabida son yaron da take da tsoron barin sa tsakanin iyayen da babu shi a gabansu. Damuwar gabansu kawai suke. Burin Mommy shine Uban ya kalli d an matsayin D a da ko wani Uba ke alfahari dashi yayinda Daddy ya ta allak a ga bunk asa Kasuwancinsa. Wann dalili yasa kasuwancin Aliyu Maitama ya fiye masa ahalinsa dan wann Kasuwanci shi yai keeping dinsa going a tunaninsa bayan abinda ya faru dashi. Shi ya zame masa tamkar therapy. A haka rayuwa take tafiya ma wad ann bayin Allah. A haka Haidar ya taso ya tsinci Kansa tsakanin iyaye biyu Wanda baisan wani Abu mai suna soyayya tsakaninsa dasu ba. Koda ya soma girma Mommy kullum cikin tilasta masa yake yai abinda zai birge uban ko zai alfahari dashi yayinda Daddy bai tab a ganin k ok arin Haidar ba har kawo girman sa.

Wann kenan.

(Kar mai karatu ya mance kacaukam labarin nan an Ginasa ne kan  ya ya da Allah kan jarabcesu da iyayensu da kuma iyaye da Allah ke jarabtansu da  ya yansu. Wasu mutanen ana sanyasu ne cikin rayuwar sashe matsayin jarabawa).

*
Ci gaban labari..


Haidar ya share hawayen da suka zubo masa  So that s the reason why he hates me.! Ya fad i haka Kansa a kife.

Mommy tai saurin girgiza Kai hawaye naci gaba da gangaro mata  No Haidar.. Your Dad doesn t hate you.. He loves you.. In fact inada tabbacin bayan abinda na masa albarkacinka naci bai koreni ba.. That s just.. his way of punishing me.!

 Well I don t care.! Ya fad i haka yana mai buga teburin gabansa da k arfin gaske. Ga wane irin huci da yake fiddawa. Yaci gaba da jinjina Kai yana ci gaba da fad in  I wish you let me die as a child. I hate you. I hate you.! Yai maganar a hankali har lokacin girgiza Kansa yake.

Mommy na kuka sosai take girgiza masa Kai  I m sorry my Son.. I m sorry.. Ba garin Allah da zai waye banyi nadaman abubuwan da na aikata ba da yanda yai affecting rayuwarka.. Haidar ka yafe mun..!

Kauda fuska yai dan baya fatan ya kuma d agowa ya dubi fuskar mahaifiyarsa.

Ya saka tafukan hannayensa ya goge fuskarsa da ya koma jazir. Cikin wane irin tune yake furta  Serving jail sentences won t be enough punishment for you Mommy. Amma dikda haka nan shine yanda ya kamaci criminal irinki. Now more than ever, I won t rest until I see you locked up in jail.. Koda zaki k arar da duka resources dinki sai na tabbata you rot in jail. I don t want to see your face ever again.! Ya k arashe cikin tsananin huci hawayen zafin rai na fita daga idonsa. Lokaci guda ya mik e ya nufi k ofa kaman zai kifa Mommy na kuka na kiransa amma inaaa tuni ya finciki k ofa ya fice cikin tsananin huci..


SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*



*36*






*??Sameena Aleeyou&
'



A tsorace ta d ago tana dubansa.

 Can you walk.? Ya tambaya yana dubanta itama shi take duba. Ganin bata ce masa komai ba sai ma rawa da jikinta keyi alamun dai batada strength har lokacin yasa bai kuma yin wata wata ba ya fiddota daga cikin motar.

Ganin haka yasa ta soma girgiza masa kai tana fad i cikin rawar murya  A a dan Allah.. Ina ne nan& Ina ka kawo ni..?! Cikin muryarta da bai fita sosai take maganar.

 Shut up. Just shut up.! Ya fad i still tana cikin hannunsa. A haka ya tura k ofan parlorn suka shige. Ko ina an rufe da farin kyalle alamun dai babu mai zama cikin gidan. Wani d aki ya bud e ya ajeta saman gado.

Ta d ago a tsorace tana dubansa had ida girgiza Kai ganin na k ok arin ficewa. Da tangadi ta nufo k ofa tana fad in  Dan Allah.. Kar ka barni a nan.. Ka Kaini wajen Mommy dan Allah ina buk atan ganinta.

Haidar ya d auki lokaci yana dubanta kafin ya tako zuwa gabanta  Look, I don t intend to keep you here for good. If you cooperate with me.. Bazaki jima a nan ba zaki tafi.! Yana ida fad in haka ya janyo k ofan ya rufe kirif.

Ummul ta duka a wajen tana dukan k ofan da d an sauran strength dinta tana fad in dan Allah ya bud e ta ya barta ta fita.

Shiru babu agaji ba taimako, Haidar bai bud e ta ba sai sautin tashin motarsa da taji. Ta rarrafa da kyar ta isa jikin window nan ta hangi hancin motarsa na barin wajen. Wani irin kuka ta fashe dashi tana Jin zazzabi mai zafi na sauko mata.

**

Anisa ta dubi Dr  Dr wann ai kidnapping ne. We need to see your security footage.

Dr ya murmusa  How is that a kidnap.? Haidar shi ya d auke matarsa.. He s her legal Husband.. So wann ba kidnapping bane. Ya k arashe murmushi saman fuskarsa.

Anisa ta furzar da huci  But still you are her Dr. And it s your duty to call him and tell him exactly the consequences of what he s done.. I mean, she s still recovering.. She needs to stay here at the hospital.

Dr ya dubeta still murmushi saman fuskarsa  If you excuse me Miss. I have some patients to attend to. Ya k arashe yana mai shigewa.


Anisa taci gaba da huci  Ahhhg! Imbecile.! Ta fad i tana sakin huci. Wayarta ne ya soma ringing. Ta duba taga Leenah ce. Gajeren tsaki tai had ida kin d agawa. Leenah ta kira har kusan sau uku Anisa bata daga ba sai ta turo mata SMS.

_Remember you only have 2 days_


Tsaki Anisa tai tana sakin huci. Yanzu ya zatai ga wann D an zafin Kan ya d auke Ummul wacce take tunanin itace last alternative d inta. Kodai Hilal ne zata kira.? Ta d anyi gajeren tsaki kafin ta soma Neman layin Hilal.

Bugu biyu Hilal ya d aga  How s my fish brain sister doing.?

 Zanci k aniyarka Hilal. Anisa tace a hasale Jin ya kirata da sunar tsokanar da ya saba kiranta tin yarinta fish brain.

Hilal ya dara  Hey easy. Nayi kewar tsokanarki ne. How have you been.. Bazaki zo bane sai na tafi.?

Ta dan rausayar da ido had ida furzar da huci  Yaushe zaka koma school din.?

 Nayi postponing akwai abinda nake a nan. Ya bata amsa Kai tsaye.

Anisa ta dan zaro ido  Kuma Abba na sane da haka.?

Hilal ya dara kad an  He doesn t need to know.. Wani Abu kawai zan k arasa sai na tafi.

Anisa ta jinjina Kai  Hey Hilal, brother& Alfarma nake nema.

Hilal ya kuma d an darawa tinda yaji ta fara kashe murya tana kiransa brother yasan abu take nema wajensa  Fad a kawai meye kike nema wajena.?

Anisa ta furzar da huci  Money Hilal. Kudi nake nema wajenka.

Hilal ya kuma darawa teasingly yake fad in  Kuda kuke Abuja gaki ga shugaban k asa ina zan samo kudi a state na baki.

 Hilal I m being serious here. Da gaske kudi nake nema. And it s urgent.

 Ok fine. Nawa kike nema.?

 1M..! Ta fad i kaman mai tsoro.

Dariyar rainin hankali Hilal yai  What.! Are you kidding me Neesa.. 1 million a wajen D an makaranta irina..? You ve got to be kidding me. Why not ask Abba. shine D an kasuwan bani ba. And hey I m not his manager.

Anisa tace  Haba Hilal. Nasan kanada hanya Shiyasa na kiraka.. Wllhi ina tsananin buk atar kudin nan. Look zan biyaka da zaran na samu.

Hilal ya d anyi Jim Jin tayi sounding serious. Shima sai ya daina wasa  Wait Anisa. Be honest with me.. What have you got yourself into..? Gambling kika fara..? Dan nasan dai ba business din da kike. Kodai kinje kin hadu da wasu scammers ne.?

Anisa ta rausayar da ido  Hilal dan Allah ka taimaken mana nasan Abba naji dakai wllhi na rantse maka da Allah matsala nake ciki. Haba Hilal meye amfanin  yanuwa ma junansu idan bazasu rufa asirin juna ba. Nasan Mommy zata bani idan tasan ina nema amma bana so ta sani. Kasan masu kudin nan the moment suka gane abun hannunsu ya rufe maka ido akwai matsala.

Hilal ya d anyi jim  Anisa ni fah kudin dake account dina pocket money na ne. Kuma idan har na baki su yanzu za azo a shiga tsakiyan semester ne ina nema. And kinsan Abba komai da lissafi yake bazan zo masa da labarin rashin kudi ba tinda yasan ya sallameni. Cewa zai wasa nake da kudi sai naje nai ko aikin k arfi ne a can na ci da Kaina.

Anisa tace  But you are his favourite.

 Even so Neesa. Kinsan yanda mahaifinmu yake idan aka zo maganar kudi.

Zata kuma magiya Hilal yace  Fine& Zan tura miki.. Amma ko da wasa kar ki bari ko Ammi tasan na baki banso na hadasu fad a da Abba.

Anisa tai alaman zipping bakinta da yatsa kaman Hilala na kallon ta  An gama my dear Brother. That s why I so much love you.

Da haka Anisa taita gwada Hilal tana fad in irin son da take ma tilon dan uwan nata.

Gama wayar da zatai ta waigo gabanta yai wani irin fad uwa samakon ganin mutum da tai tsaye bayanta. Taci gaba da yatsina fuska tana dubansa  Malam lafiya.? Wanene kai.?


Huci kurum Hisham yake yana dubanta kaman zai shak ota. Yaci gaba da jinjina Kai yana fad in  Nasan kece.! Kece kika tassama kashe Ummul.!


Anisa ta zaro ido waje ganin stranger da ko saninsa batai ba yana fad in laifin da ita da Laila suka binne. Ta soma girgiza kai tana fad in  No.. I don t know what you are talking about Malam. Meyasa zanyi yunk urin kashe Ummu. What could be my motive.? Wait why am I even explaining myself. I don t even know you. Excuse me. Tasa kai zata shige.

 You are the only person with the motive to kill her.. Because you love Haidar.. Haka ne.? Ya k arashe yana tsareta da ido.

Anisa taja Birki tana dubansa shaye da mamaki. Sai ta soma girgiza kai kad an ganin dai guy d in nan da gaske ya sansu  Mai kake nufi..? Wanene Kai.?

 Na tuna miki ne. Kwanakin baya lokacin da motar ki tabi bayan motar Haidar. Cikin k ok arin bin bayansa da kike dan ki gano yanda yake zuwa. Someone hit your car and stopped you from following him.. That someone.. Was me.. Ni ne na bigi bayan motar ki na hanaki bin bayan Haidar.

Anisa ta soma tuno kwanakin baya Mommy tasa ta bi bayan motar Haidar dan gano yanda yake zuwa amma sai tai accident a hanyar ta wata mota da bata tantance ba ta bugi

42 / 52