Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  SAMEENA ALIYU Category :  Arewa Pen

Chapter   37 / 52

108K to 111K   out of 153.1K words

da mahaifiyarsa ta ba ma matarsa akwai poison ciki ke meye naki a ciki.? Idan akwai wacce za a zarga bazai wuce Hajiya Kwaise Maitama ba. Unless kuma zaki b ullo ta wani hanyar kisan yanda zakiyi ki kutsa cikin d akin da Ummul take ki k arasata amma fah wann yafi had ari Anisa because you would easily get caught. Hanya d aya shine ki kyale mahaifyarsa ta d auki laifin nan because he already grows suspicious of her idan har zaice ki aiwatar da Abu ba tareda saninta ba. Kuma kinsan me matar nan fah mahaifyarsa ce he would forgive her, definitely. Even if she s convicted sabida ita d in mahaifiyarsa ce amma ke fah kika kuskura kika bari ya kamaki kashinki ya bushe Neesa ba hannun Haidar kawai ba harda hannun uwarsa.

Anisa ta jinjina Kai idanunta na kuma k ek ashewa  You are absolutely right Girl. After all, Haidar baya son wann auren tai masa. Akwai tarin tanbayoyi da ya kamata yai ma mahaifyarsa. Ta k arashe tana sakin murmushin cin nasara. Lokaci guda ta katse kiranta da Leenah ta soma shirin fita. Nan taga wayar Amminta na shigo mata.

Ta rausayar da ido kafin ta d aga kiran mahaifiyarta  Yes Ammi. I guess labari ya isa miki. Tace tana kuma juya ido.

Daga d aya b angaren Asshe tace  Da uban wa kiketa waya ina nemanki..?

Anisa ta kuma juya ido  Abinda kika kirani kice kenan kawai Ammi.?

 Ke bani son shashanci.. Wai meke faruwa ne a gidan Aunt d inki da banji daga gareki ba. Ko kin mance na barki a can ne matsayin ido na. Ki sanar Dani meke faruwa tsakanin Haidar da yarinyar can. Shin kin bata wann turaren ne da nace ki zubar.?

Anisa ta murmusa  Of course ban bata ba Ammi..Kuma na canza turaren kaman yanda kika umarceni.. Amma saidai..

Zuciyar Asshe yaci gaba da tsinkewa tinda tasan kalan shashancin  yar tata  Amma me Anisa..? Meye kika aiwatar ba tareda sanina ba. C mon tell me.. Meye kika aiwatar.?


Juya ido Anisa ta kumayi a hasale ta katseta  Nayi poisoning turaren da na canza mata dashi.. Ta juya ido tana jan tsaki  She s like a cockroach Ammi. Duk irin tuggun da nake k ulla mata taki mutuwa kaman dai kyankyaso.!

K iris ya rage Asshe bata saki wayarta ba. Baki na rawa take furta  Anisa kece kika zuba guba ma mutum..?Anisa waye ya aikeki.. Are you that dumb.? Bance Miki ki bar min komai ba zan kula da komai..? Bance miki kar ki yanke wani hukunci on your own ba.? Anisa kanki Kalau zakiyi kisan Kai kan namijin da baisan kinayi ba.?

Tsaki Anisa tai  There you go again Ammi. Very soon nida Haidar zamuyi aure as soon as wann makirar is out of the picture. And please do me a favour Ammi. Duk abinda zaki ji ko ki gani naki ido. Tana Ida fad in haka ta katse wayan. Asshe na k ok arin dakatar da ita amma inaa tuni ta kashe.

Tuni Anisa tayi kaman yanda Haidar ya umarceta. Sanda ta kawo masa turarukan asibiti sai ta dubesa da mamaki  Amma me zakayi da turare a asibiti.? Kodai Ummul d in ce ke so.. Amma idan itace ke son a kawo mata definitely zai kasance wann ne. Ta k arashe tana juya kwalban turaren cikin hannunta ga damuwa saman fuskarta kai kace zallan tausayin Ummul din ke d awainiya da ita.

Haidar ya tsareta sosai da ido sai ya girgiza Kai kad an  Meyasa kikace haka.?

 Because it s her favourite. Ta dan murmusa cikeda makirci tana nuni da tausayi sann taci gaba  Mommy ce musamman ta bata turaren nan. Ummul tana son turaren sosai. Allah sarki Allah ya bata lafiya. At first bama wani jituwa amma daga baya I have become fond of her sabida tanada zuciya mai kyau. Kowa yana sonta a gidan especially Mommy. Ta k arashe tana share guntun hawaye da ya gangaro mata.

Ba wai yana sauraron surutan da Anisa ke masa bane tinda yaji key points din da yake son ji ya daina gane mai take cewa sabida ta cika masa kunnuwa.

Dakatar da ita yai da fad in  You can go now. And don t say a word to Mommy. Are we clear.?

Anisa ta jinjina masa Kai tana mai tabbatar masa bazata sanar da Mommy komai ba. Bai kuma bi ta kanta ba yasa Kai yai shigewarsa. Anisa tabi bayansa da kallo yanda ya shige hannunsa rik eda turarukan cikin dan jaka.

Murmushi ta saki dan ta tabbata ko gwaji akai aka gano turare mai d auke da guba ciki Mommy ce zata rufta. Sann ne zata b ata sunan Ummul a wajen Mommy dan ta tabbata idan har aka d aura ma Mommy laifi zata tsani Ummul ne taji ta fita akanta. Zatai amfani da wann daman ta cire ma Mommy son Ummul cikin zuciyarta tinda dama ita kad ai ke son wann jarababben aure. Zuciyarta wasai ta dauki hanyar gida.
**


Tsaye Haidar yai gaban gadon da Ummul ke kwance bayan an fito da ita daga surgery. Yai mata k uri yana dubanta. Tanbayoyi da dama cikin zuciyarsa. Cikin zuciyarsa yake jero tanbayoyin da baida amsoshinsu  Who are you..? Maiyasa Mommy zata farauci rayuwarki.? Shin Mommy ta kawoki ne dan ki zame mata hanya mafi sauk i wajen ganin bayan rayuwa na.. Kina sane da shirin Mommy akaina.? Da yarda da amincewarki ki ka zab i ta cutar dake dan kawai ta cimma burinta akaina ko kuwa dai kema victim din Mommy ne.?

Daidai lokacin Dr ya turo k ofa ya shigo. Ganin Haidar tsaye ya saka Ummul gaba wacce ke kwance unconscious saman gado. Ya saki murmushi  Engr da alama kana ji da matar nan taka sosai. Kar ka damu in sha Allah bazata wuce kwana biyu bata bude ido ba. Alhamdulillah the surgery was successful and we can now say she s out of danger in sha Allah.

Har lokacin dubanta Haidar yake. A hankali ya kaikaito ya dubi Likitan  Har sai an Kama Whosoever is responsible an kuma tsaresa sann ya biya abinda ya aikata. Daga yanda yake maganar zaka fahimci tsananin son daukan fansa cikin muryarsa. Mommy kawai yake hangowa cikin idonsa zuciyarsa na tabbatar masa wann shine daidai lokacin da ya kamata ya d auki fansar duk abinda matar nan ta jima tana masa. Sann lokaci yayi da zata fayyace masa komai idan ma sato shi tayi duk sai ta fad a. Bazai barta ba sai ta fayyace masa komai gameda gaskiyan lamarin da ya danganci rayuwarsa.

Dr ya jinjina Kai yana duban Haidar din dan dik shi a nasa tunanin tsananin soyayyar da Haidar keyi ma matarsa yasa yaketa k ok arin ganin ya kamo mai laifin. Ya dan numfasa  The laboratory test for the perfume would take less than 24hrs. Zuwa gobe da safe in sha Allah zamu tantance wane turare ne mai guba cikinsa.

Haidar ya jinina masa Kai Dr ya k arada  Engr.. Emm nace are you spending the night here with the patient.? Sai ya k ara da  Kar ka damu if you have some matters to attend to kana iya tafiya.. You can be sure she s in good hands.

Ba tareda ya dube Likitan ba yace  I ll be staying here Doc. Ya k arashe yana mai zama saman soft sofa dake can gefe da gadon. Gani yake kaman zata bud e ido ta soma amsa masa tarin tanbayoyinsa.

Dr ya murmusa kafin ya jinina Kai yai Sallama ma Haidar ya fice.

Haka Haidar yai zaune ya sakata gaba yana kallo. Yana ganin wayoyi na shigo masa amma baida lokacin daukan ko d ayansu. Shi dai burinsa safiya tayi hunch d insa ya tabbata Akan Mommy.

**

Dareen sai safa da marwa take tana kuma duba time. Bai tab a kaiwa irin wann lokacin bai dawo gida ba. Tinda sukai aure bai tab a kwana waje ba. Ko aiki ya rik esa a Office komin dare sai ya dawo gida ya kwana. Toh wai meke faruwa ne. Wane irin al amari ne wann..? Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son sanin wani hali Haidar ke ciki. Hakan yasa ta yanke shawarin zuwa gidansu Haidar din kawai. Komai ta fanjama fanjam. Idan ma zasu hadu da iyayen Haidar for the first time ne ita kam gwara taje tasan meke faruwa dashi tinda gashi baya ko daga wayarsa.

Wata Zuciyar kuma ta soma raya mata toh kodai Shadow ne ya Sace Haidar to teach her a lesson tinda ga irin rabuwar da sukai a waya da Shadow d in. What if Shadow ya cutar da Haidar.? What if wani Abu ya samu Haidar.. No bata fata.. She wouldn t be able to take it idan wani Abu ya samu Haidar d inta. Jikinta na rawa ta soma kiran layin Shadow  Tell me. Do you have Haidar.. Did you kidnap him.. Ka sanar Dani mai kayi ma Haidar..? Ta k arashe hankalinta duk a tashe sai rawa jikinta keyi.


Murmusawa Shadow yai cikeda k asaita daga d aya b angaren  Har kin sare ne..? Da wuri haka.?

Ta dan furzar da huci kad an hankalinta na kuma tashi. Sai ta sassauta murya tace  Please don t do anything to him.. Dan Allah kar ka cutar da Haidar.. Na yarda daga yanzu zanyi duk abinda kace amma dan Allah kar ka cutar min da Haidar..! Ta k arashe kaman mai shirin kuka.

Shadow yai wata dariya irinta basawa  Dareen Dareen.! Yanzu kin tabbata I have both you and Haidar wrapped around my fingers. You don t want to mess with me Dareen.

Ta lumshe idonta a hankali tana mai sadda kai kasa kaman yana ganinta  Forgive me.! It won t happen again.. Please don t do anything to Haidar.. Nayi alkawari bazan sake sab a umarninka ba ko gaban Dodo akaje.

Yai murmushi cikeda k asaita  Good girl. Now that you realise your place, I want you to tell me where the hell is Haidar.?

Mamaki ya cika Dareen. Ta girgiza kai kad an  What do you mean.. Kana so kace min you don t have Haidar.?

 I wouldn t be asking you the same question if I have him.. Dareen wai meke damunki ne.? Shin amfanin ki Ya k are wajen Haidar ne.? Are you that insignificant to him.? Do I need to replace you with another woman for me to push through with my plans.?

Saurin katsesa tai  No please.. Wllhi amfanina bai k are ba.

 Then what the hell is the problem..?! Kaman kunnenta zasu fice sabida sautin maganar.

Jikinta na rawa take fad in  Na fara zargin mahaifiyar Haidar ke yunk urin rabamu.. Watak ila ta gano cewa Haidar din yayi aure a b oye ba tareda saninsu ba. Duk wasu calls da yake da ita yake tun muna Cuba. Idan ka mun izini zan tafi gidan su Haidar yanzu mai faruwa ta faru. Let them find out about me and Haidar.

Shadow ya daka mata tsawa da fad in  Don t you dare show your face to Kwaise Maitama.! This is not part of the plan. Bazasu san dake ba har sai ahalin Ya tarwatse ya lalace. Har sai sud in sun yak i junansu da gaske. Idan Har kika nuna kanki yanzu fad an zai dawo kanki ne. Let them fight each other. Let them hate each other. Let them go down together& I am warning you kar ki kuskura ki nuna ma Kwaise fuskarki.. You know me Dareen. No body double crosses me. And I have no patience with people who screwed up.! Ya k arashe yana sakin huci.

Ta jinina kanta a hankali  Got it. I won t go there.. But what about Haidar.. I m starting to worry.

 You are useless.! Ya fad i yana mai sakin gajeren tsaki kafin Ya katse kiran.

Dareen ta koma ta zauna jikinta duk a mace. Yanda taga dare haka taga rana dan bata iya bacci ba. Ita dai tafi tunanin mahaifiyar Haidar ta fahimci wani abu gameda Haidar din sann bata zauna ba.

**

A can asibiti kaw wayar Mommy ne Ya tada dashi. Yai gajeren tsaki yana mik ewa zaune daga nan saman sofa yanda ya kishingida ya soma k ok arin bud e idonsa da yai masa nauyi. Gaba d aya ji yake kaman an masa duka, dan a tak ure a nan wajen ya kwana. Yakai dubansa gareta Har lokacin idonta a lumshe suke ga nauran oxygen mak ale hancinta. Ya kuma duba wayarsa dake ci gaba da vibrating. Har lokacin Mommy ce mai kira. Bai d aga ba har ya k arashi ringing. Ya jima baiyi bacci da Ya makara irin haka ba. Ya duba yaga calls da dama ciki Harda na matarsa Dareen Wanda akasarin missed calls daga ita Ya samu. Harda tex message ta tura masa wanda bai bi takansu ba. Ya mik e yana stretching arms d insa. Ya shafi sumar kansa da duka hannayensa biyu. Nan wayar Mommy ya kuma shigo masa.

Gajeren tsakin ya kuma yi  She won t stop calling.! Ya furta a hankali. Tsaban haushinta da yake ji sai ya jefa wayar a aljihu. Ya d auki mabudin motarsa ya nufi k ofa a gaggauce. Har ya isa k ofa ya kuma juyowa ya dubeta. Har kawo wann lokacin da zaka tanbayesa ya kamanninta yake bazai iya tabtancewa ba. Abu d aya ya sani shine baida burin da ya wuce ta tashi ta amsa masa tulin tambayoyin sa. Dan alk awari yayi sai ya hukunta Mommy da duk wani Wanda yakeda saka hannu a tarwatsewar rayuwarsa.

Ya furzar da huci kad an kafin Ya janyo k ofar Ya kulle.


Yana tafe Mommy na kuma kiransa bai daga ba har ya shige mota ya soma tuk i. Abubuwa fal cikin zuciyarsa.

Anisa da bacci Ya kaurace a idonta tin daren jiya ta window ta hango motar Haidar Ya shigo gidan. Ta mik e da sauri tana lek ensa. He looks exhausted. She couldn t believe it wai Haidar wajen bagidajiyar cen ya kwana kuma a asibiti. Ta lumshe idonta tana jin zuciyarta na mata ciwo. She couldn t bear the thought of it.


Suitcase d insa da dake cikin motar Wanda bai unpacking ba tun bayan dawowarsu daga Cuba 2days back ya bud e motar ya Ciro.

Kai tsaye section d insa ya nufa. Yai tsaye yana k are ma gidan kallo Wanda a halin yanzu yarinyar ke rayuwa cikin gidan. Tin daga haraban sashen har zuwa parlor a gyare ne. Sai k are ma gidan kallo yake dan shi mutun ne da baya shiri da k azanta. Da yawan cleaning ladies na gidan da ake canzawa sabida shi ake canzawa.

Dukda an canza fasalin gidan hakan bai hanasa nufan k ofan dakinsa ba. Saidai yana murda handle d in ya jita a rufe. Sai ya lumshe idonsa kadan. Ya mance shid in bak o ne a gidan a halin yanzu. Ya d anyi gajeren tsaki, ya d ago yana duban k ofan d aya d akin. He had no other option. Hakan yasa ya nufi k ofan d akin. Yai still kaman bazai bud e k ofan ba sai kuma ya murda handle d in had ida tura k ofan d akin. D akin ma kaman dai ko ina a gyare yake. Ya tabe baki kad an dan ba abin mamaki bane dan yaga babu datti yanda yarinyar ke zama tinda ya sani ma aikatan dake gidan sunfi ahalin cikin gidan yawa amma dukda haka shi zai iya cewa b angaren nasa bai tab a kasance masa cikin gyara da zuciyarsa ta aminta dashi irin haka ba. Suitcase d insa ya bud e ya dauki abun buk ata kafin ya nufi bathroom. Nan ma the same komai a gyare. Idonsa suka sauka kan inners dinta dake shanye a band akin. Yai saurin janye idonsa sirirn tsaki na kufce masa. Sauri sauri ya sakar ma Kansa shower yana mai lumshe idonsa cikin k ok arin haramta ma idonsa abinda ya gani. Koda yai wankan ya mance babu towel cikin wann jakan. Ya d ago kai yana duban bathrobe din dake mak ale nan cikin bathroom d in. Ya jima sosai yana bin bathrobe din da kallo wai shi Haidar zai amfani da somebody else s bathrobe. Shi da ko towel d in matarsa Dareen bai tab a amfani dashi ba. Ya lumshe idonsa a hankali yana furzar da huci. Akan dole ya d auki bathrobe din Wanda baida haufi na yarinyar ne ya zira jikinsa ba don yaso ba. Sanda ya fito daga bathroom din Anisa na nan lab e jikin k ofa tana lek ensa. Zuciyarta yai wani irin tsinkewa ganin Haidar da gaske wanka yai a d akin Ummul sann abunda yafi tada mata hankali harda bathrobe d in Ummul d in ta gani d aure jikinsa. Dan bata mance ba zuwansu shopping tareda Ummul suka sai wann bathrobe din Wanda saida tai masu kauyanci akan bata iya amfani dashi ba. so definitely nata ne. Ji tai kuka na Neman balle mata. Ji tai k afafunta suna barazanar gaza d aukarta. Ta koma da baya a hankali had ida jingina jikin garu. Ta soma tuhumar kanta anya batai gangancin saka ma Ummul poison din nan ba.? Anya wann ciwo da Ummul take bazai sanadiyan samun kusamcinta da Haidar ba. Ya zama dole ta yi duk yanda zatai ta tabbata Ummul da Haidar basu samu kusanci ba. Ta lumshe idonta da k arfin gaske tana Jin bugun zuciyarta na karuwa. Da kyar da iya ficewa daga sashen cikin k ok arin maida hawayen da suka gaza Jin lallashinta.


A b angaren

37 / 52